BY MIEMIEBEE
PAGE 37
"Ina securities?" Daddy ya tambaya "Nawa ne kud'in bailing nata?"
"Ranka shi dad'e ai baze yiwu kayi bailing nata ba saboda 'yarka is accused of an imprisonable offense wanda hukuma take tsoron saketa gudun kar ta sake tafka wannan laifi dan haka kotu ya nemi a ajiyeta under close supervision idan har ba wai wanda yayi filing case akantan bane ya buk'aci a saketa that is idan yaja baya da case d'in" d'aya daga cikin securities d'in yayi masa bayani.
"Alhj Amin dan Allah kayi wa Afzal magana yayi hak'uri duk nan mun san Nazeefah bata kyauta ba amma yayi hak'uri yaja baya da filing case d'innan hannun mutum baya ri6ewa ya yasar komin munin halin Nazeefah bazan so ta k'are a gidan yari ba kuma tabbas idan Afzal ya kai k'aranta kotu tunda tana da laifi chan zasu kaita, ni bazanyi fighting against Afzal ba saboda shike kan gaskiya. Amma dan Allah ba dan ni ko ita ba kayi wa Afzal magana yayi hak'uri, kai kad'ai keda ikon hanasa aikata hakan please." Hannu Abba ya dafe a kafad'ansa "Karka damu Alhj Abdallah zanyi masa magana in shaa Allahu za a sake Nazeefah."
"Nagode nagode sosai."
"Toh bari mu wuce Hjy Mariam mu tafi ko?" nan sukayi sallama suka fice. Har anan kuka Mummy keyi.
"Yanzu mey riban wannan abin kunyan da kikayi mana kika kuma yi wa kanki Nazeefah? Ki gaya mun mey riban hakan? Kiga yadda Daddy'nki ke rok'an Abban Afzal kaman mey maula yanzu hakan ya miki kyau?"
"Mummy dan Allah kiyi hak'uri, Daddy I'm sorry" ta amsa cikin sautin kuka.
"Wace wacan?" Mummy ta tambayeta tana nuni da Safiyya.
'"Yar aikin Amal ce."
"Mey tayi ita kuma?"
"Mummy please forgive me."
"Ki bud'e bakinki kiyi magana ana tambayanki!" Daddy ya tsawata mata.
"Daddy dan Allah kayi hak'uri wallahi sharrin shaid'an ne."
"Am asking you for the last time idan har baki amsa tambayan da Mummy'nki tayi miki ba wallahi tallahi kin deji rantsuwa ba kaffara ko? Zame hannu na zanyi acikin wannan al'amari Afzal yayi duk abinda yaga dama da ke tunda ke kince bakida hankali."
"Daddy wannan itace 'yar aikin Amal Safiyya wacce nayi amfani da ita na fidda Amal daga d'akinta."
"Kika fidda Amal daga d'akinta?" Mummy ta tambaya da d'umbun mamaki. "Kina nufin kinsa Afzal ya saki Amal?"
"Be saketa ba yaji tayi."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Nazeefah! Is this how evil you've become? A iya shekarunki kike wannan mak'irci? har kinsan ki raba aure ki shiga tsakanin miji da mata? Wallahi ba tarbiyyan dana baki ba kenan Allah ma shaidana ne" ta k'are maganan tana neman fara sabon kuka. "Duk kalan wa'azi da nasihan da nake yi miki ashe shiga kunneki kawai yake ta dama yana fita ta hagu ashe a wajen kike ajiye mun magana na, wallahi ba abun in ja miki Allah ya isa ba."
"A'a Hjy Surayya kiyi hak'uri duk bey kai ga haka ba" Daddy yace da ita yayin da Khaleefah ya cigaba da bata hak'uri yana shafa bayanta a hankali. Shi kansa mamakin halin 'yar uwarsa yake.
"Mey da mey kika rink'a sanya yarinyar nan yi haka har kika sa Amal tayi yaji iyyeh?" Tisata Mummy tayi a gaba seda ta irga dukkan abubuwan da ta aikata "Wallahi Alhj idan har baka bari an hukunta taba an yanka mata watanni ko shekaru a gidan yari ba uba kage ga 'yar nan ba, ni da kaina zan kira Afzal in k'arfafa masa guiwa in shaa Allah sekin biya abinda kikayi wa baiwar Allahn nan, har kisa mijinta ya zargeta? Zargui fa Nazeefah! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."
"Mummy dan Allah kar kiyi mun haka Daddy na tuba dan Allah karka saurari Mummy."
"Kin bani kunya Nazeefah, na d'au kinyi hankali dagaske har nake alfahari da hakan ashe halin nan naki na nan har yanzu, yaudara na da Mummynki kawai kikayi kika nuna mana kin shiryu, wallahi ban ta6a tsammanin hakan daga gareki amma bazan biye miki ba, Hajiya Surayya kiyi hak'uri hanun mutum baya ri6ewa ya yasar komin mey Nazeefah tayi har yanzu a matsayin 'yarmu take hakan baze ta6a canzuwa ba. Kuma ko kema fad'a kawai kike baza kiso ace an kai 'yarki gidan yari ba hak'uri ya zama dole dama acikin 'ya'yanka dole akwai wanda ze gagareka saidai mu a matsayin mu na iyaye muyi hak'uri mu cigaba da yi musu fatan shiriya."
"Hakane Alhj" ta amsa tana kewayowa kan Safiyya "Ke kuma Safiyya kike ko wa kinga abinda kwad'ayi ya janyo miki ai ko? Shin a ina ma kika samota tun farko?" Ta tambayi Nazeefah.
'"Yar mey aikin Su Rumaysa ce k'awata wallahi tun farko ita ta fara bani shawaran nan."
"Ke kuma dake dabbace Allah beyi miki hankali ba kika biye mata ko? Ai kinga ni da idonki kinga yadda ta kaiki ta baroki."
"Mummy dan Allah kiyi hak'uri wallahi na tuba."
"Tashi mu tafi Khaleefah."
"Mummy please don't go Mummy I'm sorry Daddy dan Allah ka bata hak'uri." Ko sauraronta Mummy batayi ba ta fice "Alhj muna jiranka." Juyowa yayi ya kalli Nazeefah ba shida bakin yi mata horo saboda abun kunyan da ta aikata kad'an ne a ganga da nasa, tausayi ta basa sanin duk abinda takeyi shi ya janyo komai, ko dan alhak'in Jameela daya d'auka yaci ace Allah ya basa gagararriyar 'ya kaman Nazeefah.
"Nazeefah kiyi hak'uri in shaa Allahu zan nemi Afzal inyi masa magana bazaki sake kwana cikin nan ba."
"Daddy kaima tafiya zaka yi? Dan Allah kar ku tafi ku barni."
"Mummy'nki na jira na a waje se anjima idan na dawo" kuka take sosai tana kiran sunansa amma haka ba waiwaya ya fice shima, nan aka sake miyar dasu cell ita da Safiyya, ba abinda take nadama kaman fara bin shawaran Rumaysa da tayi. Gashi yanzu tana chan tana morar rayuwarta a k'ark'ashin AC ita tana nan tana shan wuya. Tabbas duk duniya bakada abokiyar shawarar da ta fi mahaifiyarka, itace kad'ai zata baka shawarar da bazata cutar da kai ba amma idan ka biye wa k'awaye musamman na banza irin su Rumaysa da Suwy da ta so sata aikata shirka toh tabbas kana tattare da k'alubale. Yau ta gane bin shawaran k'awa bala'i ne musamman irin nasu Rumaysa. Tayi nadama, tayi nadama matuk'a.
Mummy ta kasa hak'ura suna isa gida takira maman Rumaysa bayan da suka gaisa take irga mata halin da Rumaysa ta jefa Nazeefah aciki. Atafir maman Rumaysa tace ita sharri ake yi wa 'yarta, 'yarta baza ta ta6a aikata haka ba. Itama Rumaysan munafukar kanta bayan da Mamanta ta kirata tayi mata maganar bushe ido tayi tace ita bata ma san da wannan zance ba iyaka abinda ta sani Nazeefah tace ta nemo mata yaran aiki guda biyu d'aya nata d'aya na kishiyarta.
***
Afzal kam yana fita daga police station d'in ya kama hanyan TH dan duban lafiyar Amal tasa, saidai kaman jiya yau ma nurse dake bakin k'ofan ta hanasa shiga. Ba irin rok'an duniyan da beyi mata ba amma ta hanasa shiga acewarta bashida appointment da kowa. Ana cikin haka sega Mami ta fito be 6ata lokaci ba yaje ya tareta. "Mami ina kwana?" Kaman wacce bazata amsa ba tace "Lafiya wani abu ne?"
"Mami ya jikin Amal?"
"Da sauk'i idan abinda ya kawo ka kenan kana iya kama hanyanka ka koma."
"Mami dan Allah kar kiyi mun haka, Mami nasan ban kyauta muku ba amma kuyi hak'uri ku bani wani daman, d'an Adam ajizi ne kuma na gane kuskure na please forgive me."
"Ka 6ace ka bani waje Afzal, duk kalan walak'anci da rashin mutuncin da kayi wa Baby har kana da bakin cewa a sake baka wani daman? Saboda ka kuma walak'anta ta? Toh wallahi kayi k'arya Afzal dan kuwa Baby tafi k'arfin a walak'anta ta shiyasa nake son tun kafin raina ya 6aci ka fice anan kar insa securities su ja mun kai waje" tana kaiwa nan ta bi gefensa ta fice. Kad'an ya rage Afzal beyi kuka ba a wajen, gu ya nema ya zauna ya had'a tagumi haka har Mami tazo ta wuce sa da bak'ar leda a hannunta da alama breakfast ta siyo musu anan restaurant bata yi mai magana ba, ko kallon kirki bata k'are mai ba. Mik'ewa yayi ya fice inda ya wuce gidan madara ya siyo kayan tea da dama wanda a hanyan sa na dawowa Abba ya kirasa, connecting wayan nasa da car Bluetooth yayi sannan ya d'aga.
"Halo Abba?"
"Na'am Prince kana ina ine?"
"Na d'an fita cikin gari ne Abba."
"Ko zaka iya biyawa tanan? Ina son muyi magana."
"Toh Abba ba matsala."
"Ya jikin Amal? Wani asibiti take kaga ya kamata nida Umminka muje mu dubata ai." Gabansa yaji ya fad'i yasan komin jimawa da dad'ewa gaskiya ze fito su Abba zasu gane Amal tayi masa yaji, daga nan kuma ya san nasa ya k'are har hango kalan masifa da fushin da Abba zeyi masa yake idan ya gano cewan Amal tayi masa yaji bisa ga rashin kyautatawan da yake yi mata.
"Prince?"
"Eh a TH aka rik'eta" ya amsa cikin sauri.
"Toh in ka taho se ka kaini da Umminka muje mu dubata ko?"
"Eh Abba sena shigo."
"Yauwa Allah ma albarka."
"Ameen Abba" sannan ya katse wayan. Ajiyar zuciya ya sauk'e sannan ya k'arisa asibitin nurse d'in dake gadin bakin ward d'in still yaje ya sameta.
"Bawan Allah wai baka gajiya ne? An fad'a maka bakada appointment da kowa baze yi ka shiga ba."
"Nurse na sani, na sani kuma bawai na dawo dan hakan bane" ledan daya ciko da gongonin madara da milo da kwalin sugar da su biscuit da cookies irin masu tsadan nan da kuma sauran kayan tea ya d'ago ya ajiye akan table natan.
"So nake in biya bills na drugs nata da kuma na d'akinta na kwana bakwai I'm sure kafin nan an sallameta."
"Karka damu da hakan, bawan Allahn daya kawota asibiti jiya ya riga ya d'auke nauyin komai."
"Ko waye shi?"
"Ya 6oye identity nashi."
"Allah sarki Allah sak'a mishi, ga wannan toh ina son ki kai mata amma nasan idan kikace in jini ne bazata amince ta kar6a ba."
"Inji wa zan ce toh?"
"Kice mata inji mutumin da ya kawota asibitin jiya."
"Toh zan sa akai mata kar ka damu."
"Kice ina gaisheta dan Allah."
"Karka damu amma ince inji wa?"
"Kije inji Habib Albinta."
"Habib Albi? Toh zan fad'a."
"Thank you and one more favor please."
"Don't you think you're asking for too much?" Ta tambayesa had'e da zuba mai ido.
"Dan Allah ai nace."
"Ma tukun mey had'inka da patient d'innan? Kai mijinta ne?"
"Yes."
"Then meyasa iyayenta suke korinka haka?"
"Matsala muka samu har tayi yaji ta koma gida shiyasa nake son ki taimaka mun dan Allah, I really love my wife, I love her soo much."
"Fad'i abinda kakeso."
"I want to know ko abu ya samu lafiyan cikin dake jikinta bayan hatsarin jiyan."
"Toh ni bani muka mata aiki ba jiya 'yar uwata ce sukayi mata kaga ko bazan sani ba."
"Please call her and ask I really want to know ko babyna na nan har yanzu." Shiru tayi bata ce komai ba tana contemplating. Hannu Afzal ya sa a aljihunsa ya ciro wallet nasa tare da irga dubu biyu ya ajiye mata. "Ki sa kati da wannan but please ki kira 'yar uwar taki ki tambaya mun ita."
Ba makawa ta d'au wayanta ta yi kaman yadda ya buk'ata.
"So?" Eager Afzal ya tambayeta bayan data sauk'e wayan.
"Your baby is still safe, tace ba abinda ya samu lafiyan cikin."
"Alhamdulillah" wani kalan ajiyan zuciya Afzal ya sauk'e. "Alhamdulillah! Thank you so much I really appreciate."
"Lallai da alama kana ji da wanan d'an naka, d'an fari ne ko?"
"In shaa Allah" ya amsa ta yana murmushi yayin da ya kasa 6oye farin cikinsa.
"Ayyah Allah ya sauk'eta lafiya toh."
"Ameen thank you bari zan koma anjima zan dawo."
"Toh seka dawo."
"Please make sure kin isar mata da sak'o na."
"Kar ka damu" da haka sukayi sallama yana ficewa ya bi ta gida inda Abba ke tsammaninsa.
"Ka hau kujera ka zauna mana sekace wani bak'o" Abba yace dashi.
"A'a Abba kar ka damu nan d'inma yayi mun."
"Batun Nazeefah ne dama, hukuncin da ka yanke yayi dai-dai Prince kuma nida Umminka muna bayanka d'ari-bisa-d'ari" ya sanar dashi yayinda Ummi dake gefensa take gyad'a kai cike da goyin baya.
"Thank you Abba."
"Tabbas duk wanda ya zalunci wani shima be kamata a barsa haka ba sai dai Allah ma muna yi masa laifi kuma idan muka nemi tuba yana yafe mana shine nikeson kai ma ka duba kayi mata hak'uri, Nazeefah matarka ce har yanzu Prince, nasan abinda tayi da zafi amma kayi hak'uri."
"Abba kasan evil acts da yarinyar nan ta rink'a yi kuwa? Inda ka sani baza ka ce a tausaya mata, ban so in irga abubuwan da tayi mun bane saboda darajan iyayenta amma abinda Nazeefah tayi mun ta kuma yi wa Amal yaci ace na rubuta mata takardan ta yanzu haka."
"Subhanallahi me tayi haka?" Kwashe komi yayi ya fad'a musu abu d'ayan da ya 6oye shine yajin da Amal tayi da kuma cikinsa da take d'auke da shi.
"Nazeefan de?!" Ummi tayi exclaiming.
"Ita fa Ummi."
"Subhanallahi yarinyar da nake cewa tayi hankali ta rungumi k'addararta? Toh inde haka ne head na Amal da aka d'auke ma ranan bikin dinner ku ita ce."
"Sosai ma kuwa Ummi kika barni har rushe cake d'in da yarinyar chan tayi ita ta turata."
"Kai amma yarinyan nan akwai ta da sharri, ace a iya shekarunta haka take wannan mak'irci? Allah sarki Amal baiwar Allah ya jikin nata?"
"Alhamdulillah da sauk'i."
"Bataji ciwo bade sosai ko?"
"Toh Alhamdulillah de" be isa yace eh gashi ba saboda shi kansa be san iya ciwon nata ba banda fashewan kai da mutumin shago ya fad'a masa.
"Gaskiya Nazeefah bata kyauta ba kuma koda nine a position naka abinda zanyi kenan amma Prince kayi hak'uri ko dan iyayenta kayi mata hak'uri kar ka kai maganan nan kotu dukanta da kayi da kuma sata kwanan cell da kayi ma kad'ai ya ishi ya sata nadama kayi hak'uri kaja baya da maganan dan Allah."
"Abba-"
"Dan Allah nace Prince wallahi rok'ana Abbanta yake dukda shima bawai ya ji dad'in abinda ta aikata ba amma sedon 'yarsa ce kasan hannun mutum baya ri6ewa ya yasar, yaso ko anyi releasing nata se iyayenta su d'auke ta su tafi da ita chan gidansu kai kuma idan kaji ka huce zaka iya dawo da ita d'akinta se kayi bikonta."
"Toh shikenan Abba amma dan Allah ka bari ta sake kwanan cell d'in yau yaso gobe se na sa a saketa abinda tayi wa Amal zafi yake mun."
"Ko ya kace Prince nide kawai kar akai maganan nan kotu."
"Toh Abba in shaa Allahu."
"Nagode Allah ya cigaba da yima albaraka."
"Ameen" shi da Ummi suka amsa.
"Toh Hjy Mariam kije ki shirya Prince ya kaimu muje mu duba Amal, seki d'iba mata fruit juices d'innan biyar ko shida haka da carton na ruwa d'aya, duk dey yadda kika ga ya dace."
"Toh Alhj" nan ta mik'e bayanta Afzal yabi izuwa sashinta yayinda yake tunanin ta ina ze fara sanar da ita cewan Amal tayi masa yaji. Shi kad'ai ya zauna a parlourn yayinda ta shige d'akinta dan canza kaya sede har ta fito ta zauna gefensa be sani ba tsan-tsan yadda yayi nisa a tunani.
"Prince?" Ta ambaci sunansa had'e da tapping nasa akan cinya a firgice ya d'ago kai yana kallonta "Lafiya? Tunanin mey kake haka?"
"Urhmm.. Babu."
"Yau kuma? Gaya mun menene? Tunanin Nazeefah kake?"
"Ummi no."
"Yaya ne toh? Feel free to talk to me kaji?"
"Ummi it's Amal."
"Innalillahi!" Haka kawai taji gabanta ya tsinke. "What about her? Bade wani abun bane ya sameta dai ko?"
"Ummi dan Allah kar kiga laifi na wallahi zafin so da kishin da nakeyi mata ne ya janyo komai, sanin kanki ne ina son Amal, son da ni kaina wataran har tsoro yake bani."
"Tabbas ina sane da hakan Prince, meya faru? Tell me already."
"Ummi Amal tabar gida."
"Tabar gida kaman ya?"
"Tayi mun yaji kwana biyu kenan yau."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kana nufin Amal bata gidan ka ma da Nazeefah ta tura aka kad'e ta?" Kai zalla ya gyad'a.
"Meya faru ta tafi? Akan abubuwan da Nazeefah keyi mata ne?"
"Kusan hakan."
"Prince ka bud'e baki kayi mun magana mana mey kake cewa?"
"Ummi ni ne, ni janyo komai tun da Nazeefah ta fara kawo mun k'aran Amal ban ta6a d'aukan mataki akai ba haka nan na cigaba da kallonta da shi har ya zammana ko magana ba ma yi, ana cikin haka kuma Safiyya tace mun wai Amal ta fara shigo da maza cikin gidan-"
"Kai kuma ka amince?" Tayi saurin katsesa.
"Ummi wallahi kishinta da nake ne ya jan-" mari me rai ta kai masa a k'eyarsa "Amma ban ta6a sanin kai soko bane Prince se yau" rai ya had'e yana susa k'eyan nasa bisa ga zafin marin.
"Har za'a ce Amal tana kawo maka maza cikin gida kuma ka amince ba tare da kayo bincike ba? Ai bama abin bincike anan daga ji an san sharri ne da k'azafi."
"Ummi ni wallahi ba zarginta nake ba."
"Toh mey kakeyi? Ai de idan ance mutum na kawo maza gida kwana dasu yake kenan."
"Wallahi ni ba haka nake nufi ba, I know Amal nasan baza ta ta6a cin amanata ba."
"Toh da aka fad'a maka se kayi mey seka sameta kace mata kana zarginta?"
"Ni kawai ce mata nayi ban yafe ba idan ta sake shigo min da maza gida."
"Wallahi kai ka sayi yin yajin Amal da hannun ka lallai ashe baka fasa halin nan naka na amincewa da duk abinda aka fad'a maka ba, yaushe zakayi wayo Afzal? Ace kaman ka amma ba bincike ba komai da an gaya maka abu ka d'auka ka zauna akai?"
"Ummi I'm sorry."
"Kai ka sani ai yanzu kam, bakin da ya sa Amal tayi yaji shi zeje ya dawo da ita d'akinta."
"Ummi please don't talk like that please help me get Amal back wallahi I can't do without her."
"Kaje ka samu iyayenta?"
"Jiya muna tare a asibitin amma ko sauraro na ba su son yi bale in samu daman basu hak'uri, duk fushi suke dani ko ganin Amal sun hanani d'azu ma naje amma fushi suke dani har yanzu."
"Ai daidanka kenan nan gaba ko d'an akuya ka gani cikin gidanka akace maka na Amal ne zakayi bincike ka ji bakinta kafin ka amince."
"Ummi please don't do this."
"Toh ya kake son inyi? Kai shikenan kullum bakada aikin da yafi ka ringa tafka shirme ka barni da Abbanka da bada hak'uri da neman alfarma?"
"Ummi I'm sorry wallahi bazan iya rayuwa ba Amal ba."
"Zaka koya kar ka damu ina Abbanka in sanar dashi wannan rashin hankalin da ka tafka" kafin ta mik'e ya zaunar da ita.
"A'a Ummi please karki fad'a masa kibari se idan mun dawo na koma gida, kema kika mun surutu wallahi na Abba bazeyi kyau ba."
"Ashe kasan kayi ba dai-dai ba kenan har Amal ce za ace maka tana kawo maza gida ka yarda? 'Yar da har yau ban ta6a ganin k'wayan idonta ba tsan-tsan kunya."
"I'm sorry."
"Ai ita zaka bawa hak'uri ba ni ba."
"Kema zan baki dan Allah karki sanar da Abba."
"D'agani ni kam mutum ga shekaru ga hankali amma bayi aiki dasu nan gaba zakayi wayo ai." Hannunta ya sake kankamewa "Please don't tell Abba Ummi dan Allah" ya sanar da ita tamkar zeyi kuka.
"Kuka zakayi mun ne?" Kai yayi saurin kad'awa "A'a."
"Aikin banza kawai duk nabi na 6ataka ka zama wani abun daban."
"Ita Amal d'in fah? Ka samu kunyi magana da ita tun tafiyarta?"
"Nata kiranta jiya amma bata returning calls d'ina tana matuk'ar fushi dani please help me out Ummi" hararansa tayi ba tare da ta sake cewa komai ba.
****
Haka har suka isa asibitin bata sanar da Abba ba. Tunda su Mami ba son ganinsa sukeyi ba ko k'udurin shiga ciki Afzal beyi ba gudun kar a garin hakan magana ya fito Abba ya gano gaskiya ya kuraresa, yafi son se idan har ya sauk'e su ya koma gida tukun Ummi ta sanar da shi komin yaya dey yasan ba kiransa Abba zeyi musamman yace ze mai masifa ba.
"Ermm Abba wayana ba credit ko zaka kira Papi kace mishi mun iso?" Ya k'irk'iro k'arya sanin ko ya kira Papi ba lallai ne ya d'aga ba.
Ba gardama Abba ya kira Papi ya sanar dashi isowansu.
"Toh gani fitowa."
"Ya wai?" Ummi ta tambaya.
"Yace yana fitowa." Jin haka se Afzal ya shafe aljihunsa "Omi'god!" yayi exclaiming da gan-gan.
"Ya lafiya?" Abba yayi saurin tambaya.
"Nayi mantuwa a mota ina zuwa Ummi d'an rik'e wannan please" yayi maganan yana mik'a mata ledan soft drinks da suka d'ibo wa Amal had'e da tura mata carton na ruwan gefenta. Sarai ta gane kan plan nasa, so yake ya gudu gudun kar asirinsa ya tonu. "Ummi" ya kirata a hankali through gritted teeth yadda Abba baze ji ba, yana mey mata ido kai ta kad'a sannan tasa hannu ta amsa da sauri ya bar wajen kafin Papi ya fito.
Har su Ummi suka mik'a gaisuwansu Afzal be dawo ba se chan daya hangosu daga nesa sannan ya k'arisa lokacin har Papi ya rakasu ya koma ciki.
"Kai kuma daga d'auko abu se ka k'i dawowa?" Abba yace da shi.
"Ermm" yayi maganan yana susa gefen kansa "Mun had'u da wani abokina na ne matarsa ta haihu shine naje nayi mata barka." Ita de Ummi banda ido ba abinda take bin Afzal da shi. Tun yana yaro haka nan yake da d'an banzan halin nan ba yadda batayi da shi ba amma ya kasa canzawa, mutum zeyi masa lefi baze samesa ya fad'a masa ba se aukin zurfin ciki bayan nan gashi duk maganan da aka fad'a masa ba bincike ba komai yake amincewa gashi ai yanzu inda banzan d'abi'ar tasa ta kaisa a banza ze rasa mafi son halittar rayuwarsa.
"Allah sarki Allah raya abinda aka haifa."
"Ameen mu tafi ko?"
"Ba zaka je ka duba matar taka ba yaso mu jira ka? ko kuwa?"
"Zan dawo anjima Abba bazan so in ajiye ku waiting ba ai."
"Toh shikenan mu tafi" nan suka koma gida.
***
"Ya na d'au ai zaka koma?" Abba ya tambayi Afzal dake k'ok'arin sauk'owa daga mota. "Zan ci abinci ne tukuna."
"Toh ni na wuce site d'ina zan shirya ma ina da meeting" daga nan Afzal ya bi bayan Ummi suka zarce site nata.
"Nifa banida abincin da zan baka" tace da shi bayan da suka shiga ciki.
"Badan hakan nake nan ba Ummi I just wanted to ask you ya jikin Amal."
"Da sauk'i" ta amsa shi sama-sama.
"A ina taji ciwon?"
"Kanta ne ya fashe ta gefe sekuma targad'e da ta samu a hannu da k'afa." Har cikin ransa yaji wa Amal yayinda yake sake tsanan Nazeefah ji yayi kaman kar ya ja baya da kai zancen kotu sa'an ta d'aya Abba ya sa baki da kuwa seta ga abin mamaki. "Allah sarki I wish I could see her."
"Toh kana iya komawa gida tun da na sanar da kai abinda kake buk'atan ji."
"Ummi kema fushi kike da ni?" Ya tambayeta a maraice.
"Taya bazan yi fushi ba da kai Prince akan wannan rashin hankali da tausayi daka tafka?"
"Ummi I'm so sorry Amal na fushi da ni, Papi da Mami suna fushi dani ke ma kina fushi dani a ina kikeson insa kaina? Dan Allah kiyi hak'uri." Se kuma ya bata tausayi.
"Shikenan mey kakeso kaci?"
"Ni bana jin yunwa abu d'aya nakeso ki daina fushi dani dan Allah."
"Shikenan na daina Allah ya bawa Amal lafiya."
"Ameen" ya amsa tare da rungumarta she's the only one he has left ba Amal ba Nazeefah yanzu. A hankali ta zagaye hannayenta a bayansa tana bubbugasa "Zan yima Abbanka magana in shaa Allahu Amal zata dawo a gareka amma da sharad'i" ta sanar da shi had'e da janyesa daga jikinta.
"Muddin muka samu muka dawo da Amal a gareka ka sake ka kuskura ka ci zarafinta zanyi fushi da kai sosai Prince fushin da komin yaya bazan sake sauk'owa ba."
"Ummi na amince in shaa Allahu bazan sake zaluntar Amal ba, wannan d'in ma sharrin shaid'an ne amma daga yanzu nayi hankali bazan kuma sake ba."
"Yauwa."
"Ummi?" Ya kirata.
"Wani abune?"
"Ummi Amal is pregnant."
"Iyyeh? Kace mene?" Ta tambayesa had'e da zaro ido.
"Amal is pregnant jikanki na hanya."
"Prince wasa kake kokuwa?" Ta tambayesa yayinda ta kasa 6oye farin cikinta. "Kasan fa ba a wasa da irin maganan nan."
"I'm serious."
"Masha Allahu, Alhamdulillah Alhamdulillahi ashe de akwai rabo nima watarana zanga jika na kai amma nayi farin ciki, wayyo Amal baiwar Allah. Yarinyar nan ta ko ina tayi ne Prince ga kunya, ga nutsuwa, ga hankali da ladabi, bugu da k'ari kuma gashi yanzu tana d'auke da jika na, wata nawa ne?"
"Nima ban sani ba a bakin Nazeefah nakeji ashe dalilin da tasa a kad'e Amal kenan dan ta samu ta raba Amal da abinda ke cikinta."
"Oh! Wallahi ko a mafarki ban ta6a sanin Nazeefah bata da hankali haka ba se yanzu. Yanzu saboda Amal ta rigata d'aukan cikinka shine har zata sa a bige baiwar Allah?"
"Wallahi Ummi shiyasa ban so Abba ya amince wa Daddy ba, na so ya barni in kai k'ara kotu saboda a hukunta mun ita."
"Kayi mata hak'urin kawai Prince ai ko a haka ma ta horu. Allah ma kansa yace yana tare da masu hak'uri da yafiya, kuma kaga wala Allah ma idan ka yafe mata kai ma Amal da iyayenta su yafe maka."
"Haken kam Ummi toh bari zan koma gida in d'an huta."
"Bazaka jira kaci abinci ba kace?"
"No need Ummi thank you."
"Toh Allah kare."
Gidan Amal ya koma ya mik'e akan gado se tunanin ta yake ya kasa daina yin hakan chan ya d'ago wayansa ya shiga kiranta missed calls kusan 5 yayi mata amma ba wanda Amal tayi returning aciki, da ya gaji kawai seya tura mata sak'o daga k'arsge kaman jiya yau ma ko karancewa batayi ba ta goge.
"Sannu ko?" Mami tace mata.
"Sannu da hidima Mami sakillahu bil jannah."
"Ameen wannan k'awarki Maamah na sonki wallahi, Allah yabar zumunci."
"Gaskiya sede ince Alhamdulillah."
"Kawai de Allah ya sanya rabo ne tsakaninki da Afzal in ba haka ba da Abdul d'inki kika aura na tabbata wancan baze walak'antaki yadda Afzal yayi ba."
"Hakane Mami ko nima saida nayi tunanin hakan, idan da Ya Abdul ne na tabbata ze min uzuri amma Yaya baya wa mutum uzuri kuma ace kamata har ze amince zan shigo masa da maza gida?"
"Kede barsa shike tattare da asara da alama ma be fad'awa iyayensa kinyi yaji ba shi kansa kunyan abinda ya aikata yake."
"Tunda Allah ya fitar dani kam ai sede inyi masa godiya, Yaya baya sake samuna bale har ya walak'anta ni yadda yayi a baya."
"Kina nufin kun rabu kenan?"
"Toh Mami a dalilin mey zan koma masa tunda zargi ya shiga tsakanin mu, ai ko Allah ma ya haramta zaman da zargi ya shiga."
"Hakane kam Baby amma-"
"Mami please bana k'aunan maganan da ya shafi Yaya."
"Toh shikenan, nace kayan tea d'in chan fa? Daga gun wa?"
"Oh wannan? Wata Nurse ce ta shigo min dasu d'azu wai inji mutumin daya biya min kud'in asibitin ne."
"Allah sarki wannan bawan Allah dagaske yake a neman aljanah idan da haka duk masu kud'i suke ai da talaka yaji dad'i Baby."
"Sosai ma kuwa wallahi Mami Allah sak'a mishi da alkhairi dey kawai."
"Ameen kina jin yunwa ko?"
"A'a d'azu na sha tea."
"Tea abinci ne Baby? Yanzu fa bake kad'ai bace dole kina cin abinci sosai dan lafiyan abinda ke cikinki."
"Toh Mami."
"Gashi kuma baze yi ana siyo miki abinci ba kullum kinsan halin da muke ciki dey amma bari yanzun inje gida in dafa miki duk abinda kikeso akwai nama akwai komi mey kikeso?"
"Banida matsala da hakan Mami dama Papi ne yayi insisting ni kwad'ayin kuka da brabisko ma nike, tun da nayi aure ban sake ciki ba Yaya baya so se bana yi."
"Allah sarki bari inje in hura wuta toh muyi miki alwala tun yanzu tunda azahar d'in ya kusa ko?"
"Gaskiya kam kika tafi ba wanda ze tayani." Bayan Mami ta taimaka mata tayi alwala tayi mata sallama ta fice.
Daddy na tasowa daga sallan Azahar yayo TH don duban Amal so yake ya samu koda tsillin gashin kanta ne da za a iya gudanar da DNA test da shi don ya samu ya gano 'yarsa take koko a'a. Cikin sa'a kuwa daya isa asibitin ba Mami ba Papi, k'ofan ward d'in aka bud'e masa sannan ya shiga inda yasa driver'nsa yi mai gadi daga waje. Sallama yayi amma shiru ba amsa kasancewar Amal na sallah shi ko se yayi tunanin ko bacci take tunda nurse d'in tace masa ba kowa akanta. A hankali ya bud'e k'ofan ya tarar da ita tana sallah a zaune. Tsayuwa yayi daga bakin k'ofan yana jiranta yayin da yake tunanin ta ina ze fara samun tsillin gashin kanta chan seya hango comb a gefen gadon nata wanda Mami ta taje mata gashinta da shi ta kuma manta bata yasar a bola ba. Wani hamdala ya sauk'e sannan a hankali ya k'arisa ciki ya d'au comb d'in had'e da zare gashin ya cusa a aljihu. Lokacin da yake ajiye comb d'in Amal take sallame sallar.
"Baba sannu da zuwa" tace da shi lokacin da idonsu ya had'u tana mey mamakin ko mey yakeyi a kusa da gadonta haka gano kaman tana suspecting nasa ne se ya wayence ya zaro envelope na kud'i a aljihunsa ya ajiye a gefen gadon "Dama nace bari in duba ki a hanzarce kafin in wuce sekuma na tarar kina sallah shine nace bari in ajiye miki kawai tunda ba abu bane mey yawa."
"Allah sarki Baba baka gajiya damun d'awainiya haka? Naga kayaki da dama d'azu nagode Allah saka da alkhairi" dukda cewan bey fahimci wani kayakin take nufi ba se kawai ya amsa "Ameen 'yata ba komai Allah k'ara sauk'i ina fatan jikin naki da sauk'i?"
"Alhamdulillah Baba ina samun kulawa sosai."
"Toh madallah barin koma ina da gun zuwa."
"Allah sarki nagode sosai Allah ya saka da alkhairi gashi kazo yau ma iyayena basu nan suna ta son suyi maka godiya."
"Ba komai kice musu kar su damu, toh na wuce se na sake zagayowa." Nan yayi mata sallama ya fito. A gurguje suka bar asibitin gudun kar su had'u da Mami ko Papi. Wani private clinic suka nufa inda ya sanya gashin kan Amal acikin wata farar leda sannan shima ya tsinke kad'an daga cikin na gemunsa ya sanya a leda daban ya mik'a wa driver'nsa tare da yi masa kwatancan likitan da yake son ya kai masa.
"Har ka kai masa?"
"Eh Alhj yace results ze fito nan da kwana uku."
"Toh madallah se mu wuce office ko? Ina da appointment da wasu."
***
Da yamma Daddy ya dawo gida sede har anan beji labarin an sako Nazeefah ba wayan Afzal ya kira inda yaji switched off dama da gan-gan Afzal ya kashe wayan nasa sanin Daddy ze nemesa da misalin k'arfe shida sabon layi ya kira Mummy tana d'agawa taji muryan Nazeefah.
"Mummy dan Allah ku taimaka mun Mummy bana son in sake kwana anan dan Allah kuyi hak'uri."
"Ba daga mu bane Nazeefah Daddy'nki yayi wa Abban Afzal magana shima yace zeyi wa Afzal d'in magana amma shiru har yanzu an kira Afzal d'in ma layinsa a kashe."
"Innalillahi dan Allah ku kira Abbansa please help me out Mummy."
"Naji Nazeefah ki k'ara hak'uri" anan ta katse wayan.
"Alhj ko zaka kira Alhj Amin d'inne kaji daga bakinsa?"
"Kar yaga kaman mun tak'ura masa Hjy Surayya."
"Amma ai ze iya yiwuwa ya mance beyi ma Afzal maganan ba."
"Da wuya mu jira de zuwa gobe."
"Yanzu a cell d'in Nazeefah zata sake kwana kenan?"
"Toh ya muka iya Hjy Surayya?"
"Wallahi Nazeefah ta cuci kanta duk mey hali irin nata yana tattare da asara."
***
Rok'an alfarma Nazeefah ta sakeyi gun securities d'in akan a sake ara mata waya ta kira Afzal sede wayan nasa a kashe, private numbernsa ta kira nan ya shiga a karo na biyu ya d'aga.
"Halo?" Ya soma da cewa.
"Ya Afzal" ta kira sunansa.
"Nazeefah?" Take ya gano muryarta.
"Ya Afzal I'm sorr-" katse wayan yayi nan take ta sake kira haka yana gani yak'i d'agawa daga k'arshe ma kashe wayan yayi gabad'aya. Kwana Nazeefah tayi tana kuka ranan yayinda take nadaman biyewa Rumaysa da tayi. Washegari Afzal yayi resuming office, wajajen k'arfe tara Daddy ya sake gwada layin Afzal se gashi ya shiga, sede har ya tsinke Afzal be d'aga ba instead seya tura masa sak'o akan cewa wai yana meeting ne idan ya fito ze biya police station d'in ayi releasing Amal.
Da misalin k'arfe sha biyu da rabi Afzal ya wuce TH dan duban Amal sede yau ma nurse d'in tak'i barinsa ya shiga, rok'anta yatayi kaman ba gobe har seda ya samu ya shawo kanta.
"Naji zan yi maka hanya ka shiga amma daga yau se yau."
"Thank you so much I couldn't ask for more ita kad'ai ce aciki?"
"Eh d'azun mahaifiyarta ta fice."
"Papi fah?"
"Shi tun safe yazo ya lek'a su ya koma dama shi ba a nan yake kwana ba."
"Okay."
"Muje in kai ka" bayanta yabi ta kaisa d'akin Amal. "Seka yi sauri" kai ya gyad'a mata yayinda ta juya ta fice. A hankali ya bud'e k'ofan yana lek'an ciki, akan gado ya tarar da Amal tana kwance, ciki ya k'arisa ya maida k'ofan inda ya tabbatar da bacci takeyi. Kujera yaja ya zauna a gefenta yayinda hawaye ya ciko masa a ido he can't believe yau kwana uku kenan be sanya ta a ido ba. Hannunta ya d'aga ya sa acikin nasa yana murzawa a hankali "I'm so sorry Amal, I'm terribly sorry" ya shiga bata hak'uri har anan baccinta take ba makawa. Strands na gashin da ya fad'o mata akan fuska ya shiga miyar dasu cikin hulan dake kanta sannan ya soma shafa fuskan nata a hankali yayinda gobaran sonta da tausayi yake ruruwa acikin zuciyarsa. A hankali ya sauk'e hannunsa akan cikinta yana feeling presence na baby'nsa. Gani yake kaman a mafarki, wai Amal na d'auke da cikinsa, oh he can't ask for more.
Ya kai kusan minti goma zaune akanta yana kallonta da hannunsa manne akan cikinta har anan. Cikin bacci Amal ta d'an motsa hannunta dake kan gado ta d'aga dan ajiyewa akan cikinta inda ya sauk'a akan hannun Afzal. Gagam ta rik'e hannunsa yayin da ta cigaba da baccinta minti biyar a gaba Afzal yayi tunanin komawa gudun kar Mami ko Papi suzo su iskesa. Hannun nasa ya shiga janyewa amma ya kasa dan yadda Amal ta k'ank'amesa. Gashi baya son ya tayar da ita, ya zeyi? Hannun nasa ya cigaba da k'ok'arin cirewa amma ya kasa wanda daga k'arshe seda Amal d'in ta farka. A hankali take bud'e idanunta har ta sauk'e su akansa ba k'aramin razana tayi ba ganinsa da tayi akanta. Kad'an ya rage bata sa ihu ba, shin har ya akayi ya shigo ciki? Ta d'au nan restricted area ne se idan an san da zuwan mutum ake barinsa ya shiga how comes toh?
"Amal" ya kira sunanta a hankali cikin wani irin salo hannun nasa ta sake da wuri ta shiga kalle-kalle cikin d'akin tana neman Mami.
"My adorable Kitten" yake sake kiranta lokacin da ta kawar da kanta gabad'aya daga kallonsa. "Amal please turn around and look at me" saidai kaman ba da ita yake ba.
"Amal I'm terribly sorry, please forgive me for doubting on your faithfulness, I've realized the truth nagane Nazeefah da Safiyya ne ke bayan komai dan Allah kiyi hak'uri maganan da nake miki yanzu haka na mik'a su ga hukuma a hukunta munsu, I can never forgive them for what they did to you, yau kwanansu biyu kenan a cell." Mamaki sosai kalamunsa suka sanyata, akanta har ya kaisu police station? Sede tayi shiru bata ce dashi komai ba.
"Amal I felt horrible when I found out Nazeefah ce tasa aka kad'eki however I'm grateful for the fact that you still chose to be alive and didn't leave me all by myself. Bazan iya rayuwa ba ke ba Amal, kinfi kowa sanin hakan, you're my necessity and everything I need to complete my life please don't leave me" hannunsa ya d'au ya ajiye akan cikinta hakan ne kawai yake tunanin ze sata yin magana ai kuwa ba shiri ta cire "Don't you ever touch me Yaya" ta sanar da shi ba tare da ta juyo ta kallesa ba.
"Thank you for speaking to me Kitten, at least yau zan iya bacci tunda na saurari muryanki thank you so much" nan ma shiru tayi masa "Baby why didn't you tell me? Meyasa baki fad'a mun kina da ciki ba?" Mamakin yadda akayi ya gano tana da ciki take, waya sani ko nurses d'in ya tambaya suka sanar da shi.
"Kitten gani kike kaman in kin fad'a mun zanyi denying baby'n ince ba nawa bane? Amal I've never and will never accuse you of cheating on me, I know who you're nasan bazaki ta6a cin amanata ba kuma koda nace miki ban yafe ba idan kika sake shigo mun da maza cikin gida bawai ina nufin wani abu bane course mates naki nake nufi kuma Wallahi ni ban san shirin yaji kikeyi ba da na baki hak'uri na hanaki, senayi tunanin ko so kike ki tare zuwa d'ayan d'akin gabad'aya ban san lokacinda kika tafi ba se washegari dana lek'a d'akinki naga bakiya nan."
So take ta ce masa meyasa be kirata ba toh bayan da yaga bata nan d'in se taga kuma ba amfani tunda ba komawa agaresa zatayi ba.
"I got so mad shiyasa ban kiraki naji daga gareki ba amma bawai hakan na nufin bana sonki bane ko kuwa nayi hakan dan in nuna isa ko dan in walak'antaki ba, Amal sanin kanki ne bazan ta6a yi miki haka ba, I love and respect you alot please come back to me abinda ya faru ya riga ya faru nasan ni mey laifi ne, nasan nayi kuskure, na san ban kyauta miki ba na k'in miki uzuri da nayi da kuma k'in baki dama kiyi bayanin kanki Wallahi duk sharrin Nazeefah ne, she manipulated me please forgive me Amal Yaya is so sorry."
RANA D'AYA!
#RD
Love... King Miemiebee👄✨
2 comments:
Thanks dear.
Weldone
Post a Comment