Saturday 3 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 60
BY MIEMIEBEE


"Anas wai me haka? Kasake min hannu." Se k'ok'arin k'watan hannun nata take amman takasa.
"Barin sake ba, is better kibar wannan fad'an da kikeyi 'cause sena shafa miki zan bar nan."
"Anas dan Allah kayi hak'uri zan shafa da kaina, kaji?"
"Banji ba" kayan nata yasoma yunk'urin kwayewa, wani ihu ta sakar seda ya tsaya yana toshe kunne. "Me haka? Fyad'e zan miki? Ko yanka ki zanyi?"
Kai take girgiza masa, "a'a Anas dan Allah ka sakemin hannu banaso please dan Allah."
"Amiki a sanyi kink'i ba, barin sake miki hannun ba." k'afafun nata ta gwada shurewa aiko cinyar tata suka soma zafi.
"Wayyo Allah! Cinya na!"
"Ai kad'an kika gani, I told you to stop fighting it kink'i." Kayan nata ya kwaye zuwa guiwarta. "Anas dan Allah kabari ba kyau wallahi haramun ne karka kwaye min kaya please." bata bar k'ok'arin k'watan hannun nata ba har yanzu sede sam ta kasa dan ko rawa hannun Anas baiyi. Beko saurareta ba ya d'aga kayan nata sama, harta panties nata seda ya bayyana, santala santalan fararen cinyoyinta masu gashi dogaye kwance akai suma suka bayyano. Ganin haka ta fashe masa da kuka "Anas dan Allah kabari ka rufe min cinya bakyau wallahi."
"Gomma ma kiyi shiru dan ba sauraranki zanba." Maganin ya bud'e da d'ayan hannunsa ya matse kan cinyartan duk da hannu d'aya. Yana gwada murzawa ta saki wani irin k'aran da sekace ana cire mata rai, da ace akwai mutane kusa dasu da se sun fiffito.
"Wayyo Anas dan Allah kayi hak'uri in kanayi wa Allah karka sake tab'amin cinya wallahi da zafi, kayi hak'uri dan Allah" ta kuma fashewa da kuka.

"Fannah inba'a murza ba bare wassake ba k'afan naki tsami zeyi."
"Na yarda wallahi amman dan Allah karka sake tab'awa da zafi sosai." Kuka take harda majina. "Fannah I'm sorry bareyi inbar ki haka ba, just close your eyes kinji?"
"Anas dan Allah karka sa-" ihu ta sakar sanadin murza maganin kan cinyarta dayayi da k'arfi. "Arghhhh! Wayyo Allah na mutu." Murza man yake sosai kan cinyarta da k'arfi in bahaka ba tsami zeyi. Sosai Fannah take kuka fuskar nan duk hawaye da majina seda ya tabbata yashafa mata man zafin kota ina a cinyan ya sake mata hannu ta huta kafin ya shafa a d'ayan. Bata bar kukan ba har yanzu, hannunta har yayi shati dan yadda Anas ya rik'eta, kayan nata ta mayar a wahalance ta rufe jikinta dashi. Ruwa ya tsiyayo mata daga dispenser tare da d'ibo tissue.
Nishinta har wani sama sama yake dan kuka. "Fannah ya isa mana" fuskarta ya rik'o ta fisge da wuri. Murmushi kad'an ya saki "yi hak'uri toh. Kawo face naki na miki clearing."
"Banaso zanyi da kaina."
"A'a ni zan miki."
"Nikuma banaso haka kawai dan kaga kafi k'arfina seka na min mugunta." Fuskar nata ya sake rik'owa "don't fight it Fannah ki tsaya." Badan tanaso ba tasaida fuskar natan hancinta ya goge mata sannan ya share mata hawayen. "Ga ruwa sha kinji?"
"Banaso."
"Yi hak'uri kisha kinji?" ya d'ago cup d'in tare da kai mata baki. K'in bud'e bakin tayi. "Fannah kisha or else in sake matsa miki k'afan" jin haka ta bud'e bakin nata tasha kusan rabi.
"Good sauran d'ayan koh?"
"A'a wallahi d'ayan baya ciwo." Tsbagen yadda ta tsure bata ma san seda ta rantse akan k'arya ba.
"Naji baya yi tsaya mu shafa miki shima." Sabon kuka ta soma "Anas kayi hak'uri dan Allah" jikinsa take turewa daga gareta.

"Fannah kinga ki tsaya mushafa miki a hankali ko kalan na d'azu kikeso?"
"A'a banason ko d'aya." Kayan nata ya soma kwayewa a yayinda take taresa, "dan Allah karka min haka please." Be saurara mata ba ya had'a hannayenta biyu gu d'aya cikin nasa. "Anas wallahi zan cije ka in baka sakeni ba."
"Don't worry ko kin cijen barin bari ba" nan ya sake kwaye mata kayan, ganin yasa man zafin kan cinyarta ta tsala ihu, ignoring nata yayi ya soma murzawa da zafi zafi se ihu se kuka take, daga k'arshe ma seizing muryar tata tayi se hawaye kawai take zubarwa. Bayan daya gama ya share mata hanci da fuska sekuka take har a yanzu. D'agota yayi chak kamar 'yar baby ya aza ta kan gado ganin batada niyan barin kukan yayi joining nata akan gadon shima tare da kwantar da kanta akan k'irjinsa yana bubbuga bayanta a hankali. "Shhh! ya isa kinji? Bar kuka."

"Allah ze sak'amin" tace cikin sautin kuka.
"Eh ze sak'a miki bar kukan amma." Se chan datayi shiru ya tambayeta, "are you hungry?" Kai ta gyad'a masa nan ya miyar da kanta kan pillow yayi musu ordering abinci. Bayan abincin ya iso ya buk'ace ta da ta sauk'o da k'yar take taka k'afar bayan sun gama chi ta mik'e da tafiyar tata d'ai d'ai, towel nata ta ja da hijabi ta shiga bayi ruwa ta watsa sannan ta fito, kamar yadda ta saba cikin hijabi take sa kaya, wata red simple doguwar riga tasa ta haye gado ta kwanta.

****
_9:30PM_
Yanzu suke gama cin dinner, inbanda bin Fannah da kallo ba abinda Anas yake, bayan tagama duk wani abinda zatayi ta haura gado ta kwanta se anan ya d'auko maganin zafin tare da hayewa gadon shima. "Oya mik'o k'afan ashafa miki."
"Wallahi barin yarda ba, ai yazama mugunta kenan, ka shafa min d'azu ai ya isa."
"In miki kalan na d'azu kenan."
"Ai wando ne a jikina ba yadda zaka ciremin kuma." Murmushi ya saki ta gefen da dimple nasa yake. "Haka kikace?" Kai ta gyad'a masa. "Okay" kawai yace mata tare da jawo ta da hannu d'aya seda ta fad'a jikinsa. "Anas me haka? Ka sakeni bacci nakeji." D'ayan hannun nata ya sake ja tare da had'asu waje d'aya da d'ayan hannunsa ya soma sauk'e mata wandon baccin nata.

"Anas dan Allah kayi hak'uri wallahi ba kyau kadena dan Allah. Wallahi iskanci ba kyau."
"Ba cewa kikayi barin iyaba? we shall see."
"A'a zaka iya, wallahi zaka iya kayi hak'uri dan Allah karka ciremin dan Allah." Ko saurara mata beyi ba seda ya sauk'o da wandon nata har guiwa light pink pant nata ya bayyana. Haka yabi duka cinyoyin nata yashafa mata man zafin. Ba irin had'asa da Allan da batayi ba. Bayan daya gama ya sake mayar mata da wandonta sannan ya sake mata hannu. "Wallahi Allah ze sak'a min."
"Toh me zan kalla a jikinki Fannah? Light pink panties naki ko meh?" Pillow taja ta rufe fuskarta dan kunya she still can't believe Anas yagane mata pant.

Bada dad'ewa ba shima ya haye gadon ya kwanta. "Fannah" ya kira sunata. Batayi bacci ba amman tak'i amsa sa. Pillonsa ya matso kusa da nata nan tayi baya da nata haka suka tayi seda ta isa k'arshen gadon rukuna. "Wai Anas me haka?"
Shiru ya mata bece komai ba. Chan itama tayi baccin bata jima da farawa ba ta fara mafarke mafarkenta sede na yau beyi nisa ba ta tashi da wuri. Tsoro ta soma ji hannunta ta had'a da nasa ta matse gagam, ganin bata dena jin tsoron ba tabar kan pillonta ta kwanta akan k'irjinsa tare da zagaye hannunta kan cikinsa nanne tasamu tayi baccin itama.

Sab'anin kullum Anas ne ya fara tashi yau, ganin Fannah yayi kwance a jikinsa se baccinta take sha koda ya gwada d'age hannunta daga kan cikinsa gangamesa ta sake, da k'yar yasamu ya raba jikin sa da nata.
Suna zaune bayan sun idar da Sallan Asuba sungama Azkhar kenan Anas yace, "ya k'afan naki?"
"Da sauki ya warke."
"Aikoda ya warke se na sake shafa miki anjima."
"Wallahi Anas ya warke kayi hak'uri."
"Yau bakiyi mafarki ba."
"Eh..." Ta amsa shiru.
"Kodan saboda kwanciya da kikayi ajikina?"
Bata masa k'arya ba tace "eh, kaima ai da kayi mafarkin yarinyar chan seda ka kwanta kan cinya na." Shiru yayi kamar be jita ba dan bayason maganan yarinyar.
"Anas wace yarinyar?"
"Kinga irin suratan ki d'inba? Ke waye mutumin? I'm going back to sleep." A rarrabe suka kwanta.

_10:40AM_
"Anas kayi hak'uri ka kaini Saloon d'in mana."
"Barin kai ba ina ni kike cema mugu."
"Nikuma da yaushe?"
"D'azu da nake shafa miki muscle pain reliever."
"I'm sorry zafi ne yamin yawa."
"Shine zakije saloon da k'afar nakin?"
"Toh Anas nagaji da zama dakan a tsefe haka, ko calaba ne zasumin it won't take long."
"In calaba ne ai nima na iya."
"Ka iya kitso?" Ta tambaya tana zaro ido.
"Ba kitso nace miki na iya ba, calaba na iya, inayi wa Amal."
"Toh ai ni ba Amal ceba ka kaini saloon d'in please."
"No Fannah barakije ba, naga har maza ake ajiye wa a saloon na mata yanzu barakije wani gardi yaga gashin kiba."

"Toh Anas sekace nikad'ai ce mace a wajen? Ai hak'uri zakayi."
"Barin iya ba nemo comb na miki calaban." A zuciyarta tace ai kuma wallahi seka kitsa. Nan ta d'au comb cikin jakarta ta kawo masa yana zaune kan gado. "Gashi" ta mik'a masa, amsa yayi tare da mik'ewa. Gaban dressing mirror ya jata ya zaunar da ita kan kujerar. Ribbon nata ya warware seda yaji tsoro dan yadda gashin yayi wani buf!
"Ke wani irin gashi ne haka? Dama haka gashin naki yake? Barin iya ba miyar da ribbon nakin."
"Haba mana Anas sekace yau ka fara gani, to ka kaini saloon d'in tunda baraka iya ba."
"Nifa na fad'a miki bara kije ba." Gashin nata ya taje sama sama sannan ya tsaga ya soma kitsa mata calabar daga ta k'eya.
"Awcchh! Anas da zafi kad'an rage zafin hannun naka mana."
"Kinga fa banason fitina ko ki zauna ko in fasa, kinma samu zan kitsa miki kai kina min tsiya."
"Toh yi hak'uri amman kad'an rage zafin hannun please."

Sun d'au kusan minti biyar be gama kitsa ko d'aya ba, har Fannah tagaji da zama. "Anas har yanzu bamu gama ko d'aya ba?"
"Acewarki kitsa wannan uban gashinkin is easy neh? Ni barin na k'arasawa har bakin ba yayi tsawo dayawa."
"Amman Anas ai ze warware, yi hak'uri ka k'arasa." Cikin awa d'aya guda biyar kacal sukayi.
"Nagaji se anjima."
"Anas biyar kacal fa mukayi."
"Ina sane ai, in kinaso mu gama a yau muyi trimming bakin gashin seya dawo d'aya dana Amal kinga then zan iya kitsa miki."
"Toh ai ba kyau Anas."
"Naji Malama ke dama komai ba kyau" ribbon nata ya nema ya kama mata gashin. "In na huta zamu cigaba." Hannunsa ta rik'o "Anas please kowani biyar d'in ka k'ara seka huta gaji? Yi hak'uri."
"Fannah kalli nan" ya ciro hannunsa dake nan sekace bana miji ba dan laushi. "Kiga yadda gashin ki ya yanke min hannu."
"Yi hak'uri kaji zan maka tausa, please ko biyar ka k'ara." Biyar d'in kuwa ya k'ara yace ze huta.
Haka har dare yayi basu gama ba rabi sukayi sauran rabi.

Se a washegari suka gama kitson, sosai kuwa k'ananun calaban daya matan yayi kyau sosai sekace wani k'wararre. "Wow! thank you yayi kyau." ta fad'a a lokacin datake kallon kitson nata a madubi.
"I know ba sekin fad'a ba."
"Kai Mr. Fauzi kullum cikun girman kai, in aka yaba abin da mutum yayi cewa yake thanks."
"Aww in miki kitso kuma in sake miki godiya? Lallai fah, kema girman kan Mr. Fauzi ya soma tab'aki Mrs. Fauzi."

★‡★‡★‡

Da bikin Mr. Fauzi and Mrs Fauzi sati biyu kenan yau, sosai sun sake sabawa da juna sede kunsan halin Mr. Fauzi in abin nasa ya bugesa suburbud'awa Fannah rashin mutunci yake iya san ransa baiwar Allah kam sede ta zauna tayi kuka, inya tashi nuna mata care kuwa kamar ba gobe. Sauran sati uku agama masa gininsa su tare. Tun a daren jiya Sunday Fannah takejin alaman zuwan period nata ta duba kayakinta tasa ba pad ko d'aya ciki ta rasa wani irin shirya kaya Afrah ta mata dayasa ta mance da important abu haka ba. Gashi sunyi fad'a da Anas basu magana bale ta tambayesa kud'i taje ta siya.
Kasancewar yau Monday, leave da Anas ya karb'a ya k'are yau zeyi resuming office. Kwance suke kan gado Fannah nachan nata b'angaren shima haka, Allah ma ya sota batai mafarki ba yau data shiga uku.

Tun kafin Asubah ta tashi tana rik'e da k'asar mararta dan azaba, batasan lokacinda ta soma kuka ba. Sautin kukanta ya tada Anas dukda fad'a sukayi amman ganin ta tana kuka yaji tausayinta ya ratsa sa, duk yadda yayi dan ignoring nata ya kasa. Wutan d'akin ya kunna, tare da dafe bayanta "Fannah what is it? Mesa kike kuka?" Shiru ta masa har yanzu haushinsa takeji inta tuna yadda yata mata masifa jiya dan kawai ta gyara masa wardrobe nasa ko me yake b'oyewa ciki se Allah. Shiru ta masa bata amsa ba se k'ananun kukanta take.
"Okay Fannah I'm sorry about yestarday kinji? Barin k'ara ba. Meke damunki?"
Kamar wacce baratayi magana ba tace "Anas marata ciwo."
"Sorry ina zuwa" cikin kayansa ya shiga ya ciro pain killer da ruwa ya mik'a mata "gashi sha kinji? Sannu." Amsa tayi ta had'iye har yanzu ciwon be dena ba. "Kwanta" ya buk'ace ta.
"Barin iya ba Anas barni ahakan kawai."
"Fannah ki mik'e nace." Nan ta kwanta juyo da ita yayi ta yadda tana kallon ceiling. Hannunsa ya aza kan cikinta daidai gun marar tata yana massaging. Hannunsa ta d'aga daga kan cikinta, "Anas meh haka? Ni banaso."

"Why do you always think negative? Niba abinda zan miki am just helping you."
"Toh shine seka tab'a min ciki?"
"Fannah stop it" hannun nasa ya cire daga nata yacigaba da mata tausar. Sanyi taji sosai, har taji ciwon na raguwa haka yayi ta mata. Asuba nayi Anas ya shiga bathroom yayi alwala nanne Fannah taji sauk'an period nata. Anzo wajen tace a ranta. Batasan ta ya zata fara sanar da Anas batada pad ba duk yadda tayi barata iya ba kunya bare barta ba.

"Anas I need money please kabani d'ari biyar."
"Me zakiyi dashi?"
"Abu zan saya."
"Wani abu ne haka zaki siya da Asubah? Ko Sallah fa bamuyi ba." Kawar da kanta tayi daga garesa, "banayi." Tace chan k'asa k'asa. Sam be jitaba "tashi kiyi alwala muyi Sallah."
Kai ta girgiza masa. "Dan ciwon cikin ne barakiyi Sallah ba?"
"A'a... Kawai kayi zanyi anjima."
"Kefa kikace Sallan jam'i yafi lada."
"Nasani kawai kayi naka yau d'in."
"Nak'i tashi kiyi alwala muyi Sallah kinsan inada office yau."

"Banayi" tace chan k'asa k'asa tare da kare fuskarta.
"Shine baki fad'amin ba tun d'azu kika tasani surutu. Mschw!" Yaja k'aramin tsuka "kinada case wallahi." Bayan ya idda Sallan ya hauro gadon ya kwanta. "Anas kaji kabani koda N500"
"Wai kiyi me dashi?"
"Abu zan saya"
"Abu like?"
"Anas ermm. Ermm" kasa fad'a masa tayi. Wayarta tajawo daga kan side drawer tayi typing abu a text bar ta mik'a masa wayar seda ya gama ja mata aji ya amsa karantawa yayi kamar haka;
"Anas I need N500 please, I want to buy p...a...d."
"Ke wace erin mace ce? Ko Amal ma ta rik'e date nata kece baki rik'e ba? Ina zakije ki saya yanzu?"
"Ba ruwanka bane, ni kawai kabani kud'in." Tsuka yaja ya mik'e tare da zira jallabiyansa ya fice.

Kuma ina zeje ta tambayi kanta.

_25 minutes later..._

Dawowar Anas kenan, shinfid'e a k'asa ya tarar da Fannah se juyi take. Da wuri ya nufe ta tare da d'ago ta "cikin ne?" Kai ta gyad'a masa.
"Sannu kinji? Ko zamuje asibiti?"
"A'a zuwa anjima ze dena, please kabani kud'in inje in siya kaji?"
"Gashi" ya mik'a mata ledar hannunsa. Tana dubawa taga pad d'inne har guda biyu. Dad'i taji sosai "thank you." Tayi tayi ta mik'e amman ta kasa daga k'arshe shi yayi assisting nata yakaita bathroom d'in sannan ya bata space bayan minti biyar tafito se wani rik'e cikin ta take. Coffee ya had'a mata dukda be k'ware ba, sosai tayi appreciating ta shanye duka tare da masa godiya.

Ajikinsa ta kwanta har tayi bacci. Se k'arfe 9:30AM Fannah ta tashi sema yanzu ta tuna Anas nada office. "Ya Salam!" ta fad'a a fili. "Anas! Anas ka tashi." A hankali ya bud'e idanunsa. "Ciwon be dena bane har yanzu!"
"A'a da sauk'i, Anas barakaje office bane?"
"Yes se gobe."
"Why?"
"You are sick I need to take care of you."
"But An-"
"Shhh! lets go back to sleep." Hannunta yaja ta fad'a jikinsa ya matseta gam tare da cigaba da baccinsa.


*© miemiebee*

4 comments:

Unknown said...

Nice post

Unknown said...

Miemiebee I like you, you are kind, intelligent and skilful, may Allah bless your affairs, Aameeen

Unknown said...
This comment has been removed by the author.
Anonymous said...

Nice