Tuesday, 7 March 2017

‘YAR GATA CE!

   *BY MIEMIEBEE*
*March, 2017*
Page 60

   Yo! Beautiful people down here, I got my blog design changed for y'all again due to the complaints I've received. I hope you like this one, #OneLove Team YGC!




Takawa yayi har izuwa gabanta sannan ya miqa mata envelope d'in. K'in amsa tayi instead seta tsaya tana kallonsa bewildering. "Amsa Zainab naki ne."
   "Nawa kuma?"
  "Don't reject my offer also amsa kinji." Kai tayi saurin kad'awa "no Ya Al'ameen thank you ni don Allah na kawo maka."
   "I know ni kuma as kyautatawa nake son na baki, amsa kinji?"
  "No tha-" bata k'arasa maganan ba ya d'aga hannunta ganin haka tayi saurin kulle tafin hannun nata. "Yi hak'uri ki kar6a kinji?" Kai kawai take kad'a mai, "in kira Mama ince na baki kyauta kin k'i kar6a?" Nan ma kan ta sake kad'awa. "Toh bud'e ki kar6a kinji?" Seda yayi dagaske sannan ya samu ta bud'e hannun yasa mata envelope d'in tare da kullewa. "Thank you kinji?" Me yake shirin gani? Kuka Zeezee ta rushe dashi a wajen.
   "Oh God! Zainab did I say something wrong? I take it back" Kai kawai take kad'a mai ta kuma kasa dena kukan. "I'm sorry Zainab please kibar kukan, in kud'in ne bakiya so I'll take it back but please stop crying" yayi maganan har yanzu yana rik'e da hannunta. Ba kalan surutun da Al'ameen beyi ba gabad'aya Zeezee ta tayar mishi da hankali gashi duk maganan da yayi mata sede ta kad'a mai kai. At long last tayi magana tace, "ba kai bane Ya Al'ameen." D'an relief yaji "toh wayene?" Ya tambayeta sede Shiru ba response. "Tell me kinji? Is this about your Ex?"
    "No."
  "Then waye?"
  "Ya Al'ameen I want you back, I want to go back to you, I want to be your wife once more." Ta furta tana kallon k'asa. Hannunsa dake rik'e da nata ya sake a hankali cike da mamakin jin wannan kalamu daga bakin Zeezee. Da sauri ta d'ago kan ta tana kallonsa. "I know am wrong to say this, you'll be getting married in some couple of months but I can't keep it in again. I love you Ya Al'ameen, I love you so much that I can't afford to lose you for the second time, koda as your second wife ne bring me back, I just want to make you happy one last time." Tunda ta fara maganan kallonta Al'ameen ke as yadda take kallonsa itama tana hawaye. He never expected to hear all of these words from Zeezee. Since when ta fara sonshi? Why him and not Adeel yanzu? Meya faru tsakaninsu da bata maganansa yanzu? Wani irin cutarwa yayi mata har yasa bata sonsa haka yanzu?
    "Zainab..." ya kirata a nitse.

 "Please don't say no Ya Al'ameen, in kana ganin Mama ko Hjy Sadeeyah bazasu yarda ka dawo dani bane thats not true. I've called them both and have asked for their forgivenesses kuma sun yafe min. I just want to be with you and make you happy, I want to prove to you just how much I love you Ya Al'ameen. I can wait, koda it'll take me eternity ne muddin ka amince zaka dawo dani d'akina, please don't say no. I'm sorry if my words have offended you but I just need you to know how I feel about you." Ta k'are maganan cikin kuka sosai wanda ta mugun bawa Al'ameen tausayi. Just what hell did she went through a rayuwar ta da Adeel? Ji yake kaman yaje ya 6a66alla Adeel into pieces for hurting Zeezee like this. Jin yayi shiru har yanzu tace, "I should go, thank you for listening to me." Hannunta ya rik'e immediately tana juyawan, chak ta tsaya kanta na pointing downwards. Hannu yasa a aljihunsa ya zaro hanky sannan ya d'ago face nata ya shiga share mata rolling tears nata affectionately. "Don't cry again kinji?" Da k'yar ta iya nodding masa kai saboda wasu sabin hawayen da takejin suna shirin 6allo mata. Hanky'n kawai ta kar6a ta juya ta fice a guje se gun motarta inda ta zauna tayita shar6an kuka, gidansu Lubiee da take son zuwa ma bata jin zata iya zuwa yanzu. Seda ta tsagaita kukan nata sannan taja motarta ta koma gida inda har ta isa d'akinta Mama bata ganta ba.

***
    Abincin da ta kawo mishi ya d'iba kad'an a plate amman ko kad'an ya kasa ci saboda tunanin Zeezee zallah da yakeyi. Duk irin aromatic taste da abincin nata yayi masa ya kasa yaci kamar yadda yakamata don tunaninta dayake tayi. He knows exactly what she must be going through, saboda he went through it before shima. Baze iya zama yana ganinta tana shan wahala haka ba knowing there's something he can do. Tausayinta yake sosai but inhar Mama tace she ain't letting him ya dawo da Zeezee dole ta hak'ura kaman yadda shima ya hak'ura ya cireta daga ransa lokacinda ta auri Adeel. Even though har yanzu yana son Zeezee, but not as before ko a yanzun ma ze dawo da ita ne saboda abinda take so ne not because he loves her as he does before. Yanzu bama wannan ba, Mama Babba zata yarda ne ayiwa 'yar uwarta Murja kishiya? Ji yayi tunaninsa gabad'aya ya dak'ule mai dan dole ya fita ya shiga training men nasa in order to let go off tunanin nata. Kamar yadda take son miyar da tunanin Al'ameen hobby, haka yau ma ta yini ta kuma kwana da tunaninsa. Koda Mama ta tambayeta ya suka k'are da shi ce mata tayi babu ta kai mai abincin ne yabata kyautan d'imbin kud'ad'd'en data nuna mata d'azu.

   Washegari Al'ameen ya shirya ze koma Kaduna, half of him is telling him ya sanar da Zeezee while half of him na ce masa ya basar. Har ya shiga mota sun d'au hanya se kuma yaga be kyauta mata ba don haka yayi asking driver'nshi da yayi parking sannan ya kirata. Kaman me jiran call nasa kafin ya shiga ringing ta d'aga tare da yin sallama.
   "Wa'alai kumus salam Zainab."
  "Ina kwana Ya Al'ameen?"
  "Lafiya ya gajiyan ki na jiya?"
  "Ba gajiya."
   "Kaman kinsan rice and stew is my fav, thank you kinji? Ashe Zainab namun is such a great cook."
  "Kai Ya Al'ameen banda zugi."
  "Seriously fa ga ragowan nan nayi heating kafin mu isa KD zan tsaya inci."
   "Aww har kun d'au hanya ne?"
  "Eh nace bari na sanar dake."
  "Toh Allah ya kare hanya ya kaiku lafiya Ya Al'ameen."
   "Ameen Zainab thank you ki gaishe da Mama."
  "Zata ji in shaa Allah safe journey."
  "Thank you" yace tare da katse wayar. Wayar ta miyar kan heartbeat nata tare da rungumewa tsam, ji take as if Ya Al'ameen d'in take hugging. Remembering the thought that jiya fa bayan data fayyace mai abinda ke zuciyarta har izuwa yanzu bece komi ba taji she is broken again. Bata da fatan da yafi Allah yasa Al'ameen ya dawo da ita d'akinta, she know she can count on him saboda yadda yake sonta se inde time da sukayi spending apart yasa ya mance da ita, which she believes not.

    *****
   Isan Al'ameen gida wato Kaduna ya nufa site nasa direct inda aka shirya mishi komi tsaf for his arriavl. Bathroom ya fad'a ya watsa ruwa. Yana fitowa yajiyo knocking daga bakin k'ofa, sanin its no other than Mama yaje kai tsaye ya bud'e mata. "Oyoyo my only son" ta fad'a tare da hugging nasa not minding how wet his body is.
   "Kai Mama, har kin tashi kenan" yayi maganan yana k'ok'arin k'wato kansa daga rik'on da Mama Babba tayi masa "Shigowa na gateman yace min kina bacci."
  "Eh mana shigowanka yasa na nemi baccin nawa na rasa, ya hanya?"
  "Lafiya" ya amsa sama-sama.
  "Toh kuma bazaka matsa min in shiga ba se nace ka matsa tukun?"
  "Mama kije zan zo in sameki, kinga bako kaya a jikina."
  "Jimin d'a!" Tayi exclaiming "mene a jikin naka ban ta6a gani ba mschw! matsa min do Allah." Ganin baida niyyan matsawan ta tunkud'esa tasa kai abinta. "God help me" ya furta a ransa sannan ya koma d'aki inda ya barota a parlour. Three quarter wando ya sanya da free sized T shirt sannan ya fito. "Harka sa kayan ne?"
  "Eh."
   "Muje dining kaci abinci."
  "Bana jin yunwa."
  "Ka taso daga tafiya kace bakka jin yunwa? How's that possible?"
  "Naci a hanya."
  "K'arya ne ai baka tsayawa a hanya da sunan cin abinci."
  "Noo daga Bauchi na taho dashi."
  "Toh! Wace 'yar albarkan muka samu achan tama girki?" Murmusawa yayi alokacin da yake neman zama kan kujera a gefenta sannan yace, "Zeezee."
  "Kai dan Allah Son!" Tayi exclaiming.
  "Dagaske fa."
  "Ayyah Zeezee, yarinyar tayi hankali yanzu wallahi d'azun nan ma ta kirani tace min kana hanya yau."
   "Ayyah." Ya amsa yana unlocking wayansa.
  "Kaji wai sun rabu da mijinta ko?"
  "Haka take fad'amin."
 "Da alama kuma tasha wuyan auren don har take cemin in yafe mata alhak'inmu ne yak'i barinta mu yafe mata don Allah, nide na yafe mata haka Hjy mah."
  "Ayyah wallahi ko baki fad'a ba Mama, Zainab kaman ba ita ba ta rame ta rage haske."
  "Ayyah toh Allah kawo mata miji na gari da ze kula da ita ya kuma rik'e ta amana, marainiyar Allah."
  "Ameen" ya amsa cike da tausayinta. Kaman ya bud'e baki zeyi magana sekuma ya fasa. Take Mama ta gano hakan "Son kayi shiru fah?"
  "Dama magana nake ne?"
  "Kaman zakayi se kuma kayi shiru."

   "A'a forget, Mama ina son in d'an huta gobe zan koma office kindly excuse me kinji? I love you."
   "K'arya kake Al'ameen, ina nan ba inda zani, there's something going on your mind, what is it?"
  "Babu Mama" yayi insisting "I just want to rest that's all."
  "Karka fad'a tayi tsami ma ji, rest well." Tana kaiwa nan ta fice mai anan ya miqe kan kujeran yana me tunanin Zeezee. Yana cikin hakan yajiyo ringing d'in wayarsa, da kai dubansa yaga Zainab na flashing akan screen d'in, without hesitation yayi sliding. "Hello Ya Al'ameen?"
  "Na'am Zainab."
  "Ya hanya? Ka isa lafiya?"
  "Lafiya Alhamdulillah."
  "Toh Masha Allah just called to check up on you."
  "Toh Zainab thank you."
  "You're welcome" daga nan ta jira yayi hanging. Hannayensa ya had'a gu d'aya a k'eyarsa yana me zura wa ceiling ido. Through out ranan a ciki ya yini, tonight Mama Babba ta kawo masa dinner da kanta tayi serving nasa sede har yanzu yak'i kai spoon baki. Zama tayi a gefensa tana k'are mai kallo. Ba haka Al'ameen nata yake ba what must be wrong with him?
  "Al'ameen?" ta kira sunansa sede sam hankalinsa bayi jikinsa bale ya amsata.
  "Muhammad Al'ameen!" Ta kirasa da k'arfi. Spoon dake hanging a hannunsa ya yasar a rikice. "Ka jini ai yanzu."
  "Haba Mama! Kunne na."
  "Rufa min baki do Allah, duk k'arfin murya na yakai na bindigan da kuke har6awa kullum ne?"
  "Ni bacci nakeji, akwai tafiya a gabana gobe." Yayi maganan da nufin tashi, shirt nasa ta kama forcefully making him to sit back.
  "Ai sekaci abincin nan wallahi bazaka min kwante da abincin rana ba na daren ma kace haka seka ci."
  Toh ki sake ni."
  "Nak'i se kaci wallahi ai na rantse."
  "Mama wai in tambayeki."
  "Ina jinka amman zauna tukuna." K'in sake sa tayi dan dolensa ya zauna, "how old am I?"
   "43 going to 44 koba haka ba?"
 "Toh kema kin fad'a am 43 kinga ko am old enough to take care of myself, ba sekin rik'a sani cin abincin dole ba."
  "Ai ni kallon yaron da na yaye sa jiya nake maka gomma kaji ka sani don haka zauna kaci abincin nan, kai kam Murja na ta huta da girki wallahi sam kaman ba na miji ba bazaka zauna ka gabzi abinci ba? Zauna nace!"
   Chan k'asa-k'asa ya ce "gobe zan tafi ma ai kowa ya huta."
  "Na jika kuma, ka ga dama ka tafi a daren yau ma abinci ne sekaci." Haka dan dolensa ya shiga cin abincin seda yaci rabi Mama Babba ta yarda taja plate nata gefe. Kaman d'an yaro haka take tattalin Maj-Gen tana bala'in sonsa da kuma ji dashi kodan shi kad'ai ne d'anta oho. Har d'aki ta rakasa sannan ta zauna gefen sa.

  "Al'ameen?"
   "Na'am Mama."
   "Meke damunka?"
 "Babu wani abu ne?" Hannu ta mik'a ta make sa a hannu. "Awch! Whats that for?"
   "For lying to me, Wai in haifeka kake tunanin zaka iya 6oyemin wani abu? Gayan meneh? Batun Murja ne?" Kai zallah ya kad'a mata. "Baka koyi sonta ba har yanzun?"
  "Mama ba ita bace please."
  "Then wace ce?"
  "Zainab ce."
  "What about her? Bade wai kanason ka dawo da ita d'akinta ba?" Shiru yayi mata "da kai fa nake magana Al'ameen? Murja fah? Bama wannan ba ita Zeezeen tace maka tana son dawo maka ne da zaka ce kai zaka dawo da itan?" Tashi yayi ya zauna, "what if she really did? " Ya tambayeta.
   "Did what Maj-Gen.?"
  "Did ask me to bring her back."
  "No thats a lie, k'arya ne har Zeezeen ne zata ce ma tana son ka maido ta d'akinta?"
   "Mama zan miki k'arya ne?"
  "Bazaka min ba kam am-"
 "Aswear to you, she came to me crying like a soaked puppy in the rain tana pleading d'ina kan nayi hak'uri na dawo da ita d'akinta koda as second wife zan dawo da ita, bayan Murja kenan she don't care, I so much pity the girl Mama." Hannu kawai Mama ta dafe a bakinta, totally out of it. "Kai me kake gani yanzu? Kana ganin dagaske take bawai so kawai take ta sake cin kud'in ka ba?"
  "Not all Mama" nan ya zana mata yadda sukayi da Zeezee kamin ta yarda ta amshi kyautan daya batan mah.
  "Oh ni Mama Babba! Amman kenan seda shi Adeel nata ya juya mata baya zata zo tace tana sonka? You are like her second option fa kenan."
   "I don't think thats so, ko ban tambaya ba Mama nasan shi mijin natan nason dawo da ita yanzu saboda Zainab ta cika 'ya mace aduk inda ake neman hakan."
   "Kana nufin to say Zeezee na sonka kenan yanzu fiye da yadda takeson Adeel ne ko waye d'in?"
  "Exactly, her words said it all."
  "Allah sarki marainiyar Allah, Al'ameen kace da bakinta tace maka ka dawo da ita d'akinta?"
   "Da zan miki k'arya ne Mama abinda yake ta bothering d'ina kenan nima, ta gaji da zaman zaurancin da takeyi cause she told me tun kafin rasuwan Baban nasu suka rabu da mijin. Kinga its been a while kenan."
  "Tabbas! So kai me kake gani yanzu Al'ameen? Zaka dawo da itan?"
 
 "I don't know Mama, koda zan dawo da ita ma ai se keda Hjy kunyi approving tukuna regarding abinda ya ta6a shiga tsakaninku."
  "In don wannan ne ka ajiye a gefe saboda ni na yafewa Zeezee, abin a tausaya mata ne yarinyar, matsalar daga kaine yanzu."
  "Daga ni kuma Mama kaman ya?"
   "Kana ganin zaka iya rik'e mata biyu ka kuma yi adalci a tsakaninsu?" Kai yayi saurin kad'awa "gaskiya no Mama I can't assure you of that saboda ni auren mace fiye da d'aya baya daga cikin tsari na."
 "Toh kaji inda matsalar take kenan.
  If you have to choose tsakanin Zeezee da Murja wa zaka d'auka?"
  "I don't know either, but kinsan right from the start ni Murja bata wani kwanta min ba, bawai ta gaza ta wani fannin bane kawai bata cikin tsarin matan da nake so ne."
  "And Zeezee?"
   "I love her Mama even though not as before but har yanzu she holds a special place in my heart."
  "Toh Son nikam bansan ya zamuyi ba gaskiya, dole cikin su d'aya ta hak'ura tunda baka iya ajiye mata biyu kace."
  "I know Mama zan bawa Zeezee hak'uri kawai."
  "Why?"
  "Saboda I can't keep two wives."
  "But kace baka son Murja."
  "Yeah bana sonta amman ai ke kina sonta ko?"
  "You mean don ni zaka auri Murja?"
  "Your happiness means the world to me."
   "Iyyeh Yaro na ya girma, yanzu ka gaya min wa kakeso ka aura acikinsu, Zeezee or Murja?"
  "If I'll have to choose Zeezee, but Murja fah? She loves me also and I don't want to hurt her."
  "Karka damu Murja d'iya ce me hankali da kuma tunani. Ni na soma had'aku ai zanyi mata magana muji me zata ce inhar ta nuna zata iya yafe son da takeyi maka kaga shikenan seka dawo da Zeezeen ka saboda ni abinda kakeso nima shi nakeso."
  "Are you sure about this Mama?"
  "I am Son, tunda har Zeezee ta iya tinkararka ta fad'i maka da bakinta akan ka dawo da ita d'akinta kam ai abu ya lalace am sure no matter what she won't ever hurt you again."
   "Thank you Mama" ya tashi da niyyan hugging nata.
  "Matsa min do Allah! d'azu dana ke maka oyoyo ba tureni kake ba? Kaima ka d'ana bouncy'n kaji idan da dad'i." Yana dariya sosai wanda ya bayyano da white perfect teeth nasa yace, "hakane Mama? Shikenan nayi accepting bouncy'n but can I hug you now?" Murmushin ta miyar masa sannan sukayi breaking into a mother-son hug. "Am damn proud of you Al'ameen Allah ya cigaba da yima albarka yakuma farinta maka kaman yadda kaima kake farinta min."
  "Ameen Mama thank you." Ya fad'a tare da breaking hug d'in.
  "Allah yasa decision naka na dawo da Zeezee d'akinta ya zamo the most best decision of all."
  "Ameen I love you."
  "Toh kar tsohuwarka ta cika ka da surutu bari na barka ka kwanta naji se k'orafi su Aysha suke wai da zaran ka dawo nake share su."
  "LOL tell them gobe ma zan koma."
 "Ai kuwa deh kwanta ka huta Baba na seda safe."
  "Allah ya bamu alkhairi Mama."

 ****
   Washegari da safe Al'ameen ya wuce Abuja. Kafin Mama taje ta samu iyayen Murja da ita Murjan kanta seda ta tambayi shawara gun Hjy Sadeeyah inda itama ta goyi bayan shawaran sa Mama da Al'ameen d'in suka yanke d'ari bisa d'ari. Anan ne itama take sanar da Mama kad'an daga cikin wahalallen rayuwan da Zeezee tayi living a gidan Adeel, giving Mama Babba more reason to return Zeezee back to her only son.
   Cikin tsan-tsan fahimta da nitsuwa Mama Babba da family'n Murja suka fahimci juna, inda itama Maman Murjan take sanar da Mama cewa daman Murja itama nada wanda takeso amman dan nauyi da kuma girmamawan da sukeyi ma Mama Babba yasa koda ta fara kawo shawaran had'a Al'ameen da Murja basu nuna mata hakan ba, so walillahil hamd yanzu zasuyi mai magana ya turo magabatansa. Hak'uri Mama Babba ta sake basu insa suka sake nuna mata sufa ba komai bata yi musu komi ba. Fatan Allah bawa Al'ameen da matarsa zaman lafiya sukayi mata inda itama in return tayi musu haka. Bayan ta dawo gida ne ta kira Zeezee kasancewar tayi saving lambarta ranan. Be jima ba Zeezee ta d'aga tare da yin sallama suka gaisa sannan Mama Babba tayi moving straight to the point without hesitation.

   "Uhm so Zeezee jiya Al'ameen yake sanar dani dukkanin abinda ya gudana a tsakaninku, ina so ne inji daga bakinki tsakaninki da Allah kike kina son ki dawo d'akinki nan gun Al'ameen?"
  "Wallahi tsakani da Allah ne Mama, I can't tell you guys how sorry I am."
   "We know Zeezee, ki gayamin meyasa kikeso ki dawo mishi?"
  "Saboda ina son shi Mama, ban ta6a sanin Ya Al'ameen shine masoyina na hak'ik'a ba seda Adeel wanda nayi mai sacrificing komi ya wulak'anta ni ya nuna min dabba ma ya fini daraja a idanunsa. Yanzu haka shi Adeel har ya gaji da zuwa yana bani hak'uri batun na koma mishi, harta magabatansa da mahaifiyarsa ya turo da su bani hak'uri na koma mishi amman nak'i saboda na dawo daga rakiyarsa bana sonsa Ya Al'ameen nakeso badan komi ba kuma nake son na dawo mishi illa don na farinta mishi rai na kuma biya shi alkhairun daya min da a baya."




*MIEMIEBEE.        Team #YGC!🎀*
 Beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄👄👄

8 comments:

Unknown said...

Ohhh my god, am gonna cry, i have been trying to open the read more but it kept showing me samr error message that the page is not available. Pls pls pls do something about it. We like the older page. 😥😥😥

Unknown said...

Tears rolling down my eyes I'm so happy for zeezee

Unknown said...

Wayyo zeezee! I'm so happy 4 u, sis MIEMIEBEE godia muke.

Unknown said...

Enx sis kudos to u, d new blog design is superb

Unknown said...

TANKS

Unknown said...

Masha Allah next so episode please

Unknown said...

Naji dadi sosai nima

Unknown said...

Ayyah, I'm so happy 4 zeezee. Can't wai for the next post. Tnk u sis