Monday, 19 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 79
BY MIEMIEBEE





     In dedication to *Aunty SisšŸ’•, Ummee, Anee and Lilmeerahcute.*
                 7⃣9⃣





    Alokaci guda k’wak’walwarta tabar aiki dan irin matsanancin tsoro da fargaban da ta shiga ji take inama ace mafarki ne. B’ari sosai both jikinta da bakinta suke ā€œFff.. Fa... Ya Farouq?ā€ Ta kira sunansa cike da tashin hankali dakuma rashin yarda gashinan zahiri a gabanta amman jikinta yak’i yarda mata shid’in ne. Bakin bindiga ya sake bugawa kan Moosa seda ya fad’i sume a wajen. K’ara ta saki sosai tare da toshe kunnuwanta wani irin la’anannen murmushi ya saki yana nan kamar yadda yake ba abinda ya canza tattare dashi illa duhun daya k’ara.
 
       ā€œOhh what a sweet voice I’ve been missing ashe matan nawa barata manta da suna na.ā€ Da k’afansa ya shure Moosa gefe guda dan wucewa ganin hankalin Fannah tashe akan sumemmiyar jikin Moosa yasa yace, ā€œwifey karki damu dashi, kuma haka ake karb’an baqo ne? ba ko sannu dazuwa toh shigo da kaina inga wannan one in town mansion da ake ta maganansa a gari.ā€ Nan ya miyar da bindigan aljihunsa yazo shiga kenan wani erin k’arfi yazo mata alokaci guda ta ture k’ofar sede aikin gama yariga ya gama hannu yasa ya kareta daga rufe k’ofar d sauri ā€œwifey wai haka kike karb’an bak’i? oh please don’t be like this.ā€ Baya baya ta soma yi har yanzu se b’ari take ganin haka ya cafko hannunta da k’arfin dayasa hawaye suka ciko mata a ido.  
   
     ā€œIna zakije wifey?ā€
    ā€œYyy... Yya Farouq dan Allah ka sakemin hannu ba kyau ka sakeni please na rok’eka da Allan da rana ke hannunsa let me go...ā€ Ta k’are maganan cikin sautin kuka.
    ā€œOhhh wifey don’t cry please kinji? Banason ganin hawayen nanā€ hanky yaciro na k’arfi da yaji ya share mata hawayen har a yanzu bata bar k’ok’arin k’watan hannunta ba.
      ā€œWhat a wonderful house inhar Mr. Fauzi ne yayi desging to gaskia kudos to him gidanku yayi kyau sosai baraki d’an zagaya dani ciki ba nima in d’an gani wifey?ā€ Ya k’are maganan dawani maqirin murmushin daya karkato ta gefe d’aya a fuskarsa. Hawaye take har a yanzu ā€œYa Farouq I’m not your wife kuma dan Allah kayi hak’uri ka koma inda kafito, ka sakemin hannu please matar aure ce ni ba kyauā€ ta sanar dashi cikin murya me rawa.
      ā€œOhh wonderful wifey ya kike magana haka? Rabuwa na dake tun yaushe amman ace wannan kalamu zaki fad’a mun don’t you miss me? Ko kad’an bakiyi missing d’ina ba?ā€ Hannunta ya ja da k’arfi seda ta fad’a jikinsa. ā€œI missed you wifey, kullum da tunaninki nake kwanciya in tashi inkuma sake yini dashi.ā€ K’irjinsa take bubbugawa da k’arfin da Allah ya bata tana kuka tana had’asa da Allah amman ko a jikinsa se sake matseta yake yana shunshuna daddad’an k’amshin jikinta dukda haka bata bar kaimasa bugi ba seda yagaji ya raba jikinsa da nata hannunta still rik’e da nasa a hanakli ya murza hannun nata.
 
      ā€œWhat a soft skin wifey, kinga wani fresh da kika k’ara kuwa? Mr. Fauzi ya riqe min amanar ki...ā€ D’an hamma ya saki ā€œyunwa nakeji nasan gidan Mr. Fauzi ba’a rasa kayan dad’iā€ hannunta yaja zuwa dining space ya bud’o fridge tare da ciro bufallo wings guda biyu da chapman drink, kan dining ya zauna ya buk’aceta da tayi hakan itama sam tak’i. Bindigan aljihun nasa ya ciro nanma tak’i se b’ari take duk yadda tayi dan kwantar da hankalinta ta kasa batason tsantsan tashin hankali tayi miscarrying babynsu, murmushi kad’an ya saki cike da mugunta ā€œko ki zauna kokuma in bindige kan Moosa dake waje.ā€
     ā€œYa Farouq mesa kake haka? When will you ever stop dan Allah? Me Moosa ya maka da zaka masa haka? Shin bakada imani ne?ā€
     ā€œImani? Yes Fannah banidashi sabida na siyar wa shed’an akanki Fannah kowa ze iya mutuwa bakisan yadda nakesonki bane shiyasa kike min wannan banzar maganarā€ rigan shirt nasa ya sauk’ar ya nuna mata tattoo dake hannunsa ā€œko ban fad’a ba kema kinsan hat F&F stands for, now sit!ā€ Ya daka mata tsawa cike da tsoro ta zauna gefensa se hawaye take kamar lalacaccen famfo cikin kwanciyar hankali yagama cin abincinsa sannan ya kora da drink ko kubya babu.
     ā€œTunda kink’i zagaya dani I think its time to goā€ ya sanar da ita a lokacin daya mik’e yana k’ok’arin rik’o hanunta. Hannun nata taja ta sa cikin hijabi sannan ta hsare unstoppong hawayenta, ā€œgo where Ya Farouq? Where are you taking me? Dan girman Allah karka min haka ka tausaya min please.ā€
    ā€œWifey ai tausayin ne yajawo hakaā€ cike da mugunta ya miqar da ita daga saman hannunta wani irin wahalallen k’ara ta saki ā€œAnas! Anas! Anas! dan Allah kazo ka taimakeni, Anas pleaze come.ā€ ta fashe da kuka...
    ā€œChill chill wifey Anas naki ba yanzu zezo ba saboda yana da meeting 1:30PM to 2:30Pm so kinga se k’arfe uku ko hud’u kamar yadda ya saba ze dawo dan haka kima bar kiransa for help.ā€
     ā€œYa Farouq me kakeso wallahi in kud’i ne zan baka dayawa muje safe na Anas zan baka ko nawa kakeso amman dan Allah karka kaini wani wajan karka rabani da gidana da mijina please Ya Farouq ka tausaya min nasan I can’t fight you kaji k’aina please.ā€ Ta k’are maganan tana kuka sharqaf sharqaf.

      ā€œOhh wifey meyayi zafi haka? Bar kukan nan please zancen kud’i kuwa wanda kike kira da mijinki shi ze dank’a min arzikinsa gabad’ai yanzu lets go.ā€ Bata bar rok’ansa ba har a yanzu se janta yake da k’arfi tana jan kanta baya tana ihu tana kiran sunan Anas har sun kai da bakin k’ofa ya dakata yaje ya d’ago jakarta da wayanta sannan yasa hannu a aljihunsa ya ciro wani ninkekken takarda ya ajiye gab da bakin k’ofar sa’annan ya bud’e k’ofar har a yanzu Moosa na nan a sume k’ara k’arfin sautin kukanta tayi tana me kiran sunan Anas har a yanzu. Cikin motan da driver ya turo Anas k’irar Audi jeep 2016 yasata ciki tare da zaro handcuff ya had’e hannunta da k’ofar ta yadda barata iya guduwa ba sannan yaje yaja sumemmiyar jikin Moosa yakai gefe d’aya daga cikin motocin da akayi parking nasu a lot kome ya sake canza masa ra’ayi se kuma ya sake jan Moosa yakai motar dayakeson tafiya da Fannah, cikin open booth ya jefa Moosa.

     *****
        Anas na zaune a office nasa dawasu files na Unity Global intercome yana going through kawai seyaji gabansa yayi wani irin mumunar fad’i wanda ya rasa dalilin hakan, coffeensa da Fannah ta had’a mai ya zuba kad’an a cup yasha amman inaaa yakasa samun sukuni rolex agogon hannunsa ya duba yaga 12:32PM har ya d’ago wayarsa dan kiran Fannah kuma se ya tuna ashe d’azu ya buk’ace ta takwanta tayi bacci bari ya tura mata text message kar ya tak’ura mata.
    Da murmushi a fuskarsa yamiyar da wayan bayan yayi mata sending ya ajiye sannan ya cigaba da abinda ke gabansa...

           *ANAS*  _3:57PM_
      Shigowan Anas gida kenan bayan ya miyar da k’ofan ya juya yana neman Flowersa normally inba wai bacci take ba she’s always around tamishi sannu da zuwa sab’anin haka yayi concluding a ransa koda bacci take har yanzu. D’akinsu ya nufa to his suprise be ganta ciki seyayi tunanin ko tana bayi, dining ya dosa dan ciro bufallo wings daya siyo wa kansa dankuwa Fannah bata ci sama da k’asa ya nema abinsa ya rasa mamaki ne kwance a fuskarsa. Yaushe Fannah ta iya chin bufallo wings da har zata cinye guda biyu? ā€œWow!ā€ Yayi exclaiming a fili ā€œbade cikin naki ze miyar dake glutton ba Flower.ā€

       Packaged chicken yaciro yad’an ci kad’an dan bawani yunwa yakeji ba bayan ya k’are ya koma d’aki sede still ba Flowersa bayin ya dosa yayi knocking. ā€œFlower?ā€ Ya kira sunanta.
    ā€œFlower kina ciki ne?ā€ Jin shirun yayi yawa ya murd’a hannun k’ofar ya shiga sede ba Flowersa ciki anan fa hankalin Anas ya fara tashi, d’akinta ya dosa a gurguje nanma ba ita ba alamunta haka ya duba d’akin babynsu nanma ba Fannah tirk’ashi!
     Gidan kap ya zagaye yana kiran sunanta yana nemanta aman ba ita ba alamunta ba. Toh kode tafita ne? Ina ma zataje ai Flower bata zuwa ko ina kuma inda wani gun zataje da ta sanar dani, toh ina take?
     A rashin samun amsoshi ga wad’annan tambayoyin yasa ya koma ciki dan d’auko wayarsa ya kirata yaji daga bakinta yashiga kenan kasancewar ba takalmi k’afansa yaji kamar ya taka abu a nitse ya miyar da kallonsa kan right foot nasa inda yakejin ya taka abu bayan ya matsar da k’afan yaga paper ne aninke dudum! Yaji zuciyarsa ya sake bugawa fiye da na da se ayanzu yakejin something bad is happening to his Flower and baby ba tare da b’ata lokaci ba ya d’ago paper’n ya bud’e cikin sauri ya soma karantawa;

      _Welcome back home Mr. Fauzi gida yayi kyau masha Allah nagode da riqe min amanan *whats mine* da kayi. I know baka mance ba whats mine is MINE 09011140607 you might get the chance to listen to her voice if you are lucky. Team F&F_

         Rawa jikinsa ya soma a yayinda tunaninsa ya jaqule, wani irin gumin da ko ACn ma yakasa d’aukewa ne suka soma gangaro masa from nowhere, blue eyes nasa suka sake shiga darker tsabagen tashin hankali, migraine nasa ne ya bugo sa a lokaci guda wanda bare iya tuna when last rabuwarsa dashi ba. Hannu yasa ya dafe kan nasa cike da azaba ayayinda k’afafunsa ke rawa.
    ā€œFAROUQ!ā€ ya furta a hankali cike da tashin hankali.

     ***** *FANNAH*
     _Chan bayan garin Maiduguri_
     Cikin wani abandoned uncompleted building me steps kusan biyar wanda ba’ayi painting ba windows ma ba’a gama sawa ba a floor na k’arshen. Irin tsagerun unguwa masu shaye shaye ne guda biyar k’ati a bakin entrance door d’in da alama gadi suke. Cikin gidan a second floor cikin wani d’an madaidaicin d’aki wanda yake nan da k’aramin rug seda sofas guda biyu da k’aramar fridge seda gado cikinsa. Fannah ne ke zaune kan wani kujeran katako hannunta da k’afafunfa duka d’aure jikin kujerar bakinta kuwa makeken cellotape ne anrufesa dashi hawaye ne ke gangarowa har yanzu kan lallausar kumatunta. Fuskar nan nata yayi ja dan kuka nishi take a hankali abin tausayi ayayinda Farouq ke tsaye a kanta yana shafa sajen fuskarta dayasamu fitowa dan yadda hijabin jikinta yayi baya.
   
      ā€œWifey I told you to stop fighting amman kink’i inda kin bani had’in kai daduk hakan be faru ba, bakiga d’akin dana gyara mana bane dake 3rd floor? Just for me and you nasan kin saba da california bed agidanki but karki damu jiran call nake daga gun Anas yana turomin kud’i zan canza mana gida sorry you have to manage.ā€ Y’unkurin magana take amman ba hali dan cellotape dake bakinta. ā€œShhh! Ba sekinyi magana ba so kike na cire miki wannan?ā€ Yashafa kan celotape d’in ta inda bakinta yake. Kai ta kawar da wuri idanunta basu bar tsiyayar hawaye ba har a yanzu. ā€˜Yar murmushi ya saki ā€œya naga kamar kina zufa? Acire miki hijabin ne?ā€ Yana tab’ata tahau shure shure da d’an k’arfin daya rage mata a jiki.
     ā€œKunyar nan taki ta munafirci na nan LOL karki damu zan cire miki shi a first night namuā€ dawo da kallonta tayi garesa tare da watsa masa wani irin disgusting kallo a zuciyarta tana me tsine masa albarka.
     ā€œSweetheart don’t look at me your husband like that banson raini.ā€ Jakarta dake kan medim sized bed ya d’ago tare da zazzagewa. Kud’i ne almost a bundle na d’ari biyar ciki seda turaruka da d’an kayan kwad’ayi irinsu tuwon madara, tsami gaye, tsamiyan biri da sauran tarukuce sam hankalinsa bekai kan photo scan dake a gefe ba.
 
      Kud’in ya d’aga yasa a aljihunsa duka sannan ya d’ago wayarta ganin new message from Habeebi yasa yad’an murmusa ā€œwifey bari muga wani saqo Anas ya turo manaā€ nan ya shiga ya karance a fili kamar haka;

        _How lucky I am. I am falling and falling deeply in love with_
_the prettiest girl in the world. I am not ashamed to say this. Infact, I am proud of you and I'm not going to let you go, remember those times when I woke up in the middle of_
_the night just to watch your innocent face while you sleep? Remember those times when I woke up very early in the morning just to to serve you coffee in bed?_ _Remember_
_those times when I hold your hands tight and find it difficult to let you go? It’s because I love you so, and I long to be with you more. This is no mere words, it's_ _from the depths_
_of my heart. I love you Flower._

      Dariya sosai ya b’arke da ā€œstupid kawai† yafad’a a fili. Nan k’arfin kukan Fannah ya dad’u kuka take sosai abin tausayi a yayinda son Habeebinta ke sake shiganta da zafi da zafi. ā€œIgnore the bastard wifeyā€ nan yayi deleting message d’inma kwata kwata tare da ajiye wayan a gefe sannan ya hau tattara tarukucan su tsamiyan biri gefe guda. ā€œWifey bansan ki da ciye ciye haka bafa, taya Mr. Fauzi ze barmin ke kina wannan ciye ciyen k’aza-ā€ be k’are maganar ba idansa yakai kan d’aya daga cikin photo scan d’in, sam begane me aciki ba seda ya d’ago ya matso dashi kusa da idanunsa yana examining anan ne ya gano kan mutum ne ga kuma hannaye da k’afafu dara-daran idanunsa ya zaro waje disbelievingly kai ya soma kad’awa gudun kar abinda zuciyarsa ke sak’a masa yazamo gaskia cike da tashin hankali ya maido da kallonsa kan crying Fannah wani irin tafasa zuciyarsa ke ga kishi bayyane karara a fuskarsa tun ba yau ba abinda yake gudu kenan rananda Fannah zata d’au cikin wani ba nasa ba.

       ā€œKe!ā€ Ya danna mata kira cikin wani irin husky voice sosai ta tsorata amman tak’i koda d’ago kai ta kallesa. A fusace ya mik’e ya nufo gabanta tare da murd’a mata kai seda ta kallesa na dole ā€œmeh wannan?ā€ ya d’ago hoton yana nuna mata. Bayan data kalli hoton sekuma ta sake fashewa da kuka babban tashin hankalin da take ta guduansa kenan, tun d’azu addu’a take kar Allah yakai Farouq jakarta tsoronta shine karyace ze illata mata baby she can’t afford to lose her baby ya mata komai amman karya tab’a mata baby.
     ā€œMagana nake miki ba kuka nace kiyi ba. What is this?ā€ Tsantsan kishi yariga ya mamaye masa zuciya besan a lokacinda ya d’aga hannu yakai mata wawan mari a fuska ba dukda bakinta a rufe ne amman seda d’an k’ara ya fito a yayinda hawaye ke ambaliya kan fuskarta.

       ā€œMeh wannan nace? Ciki kike dashi? Ciki?! Waya miki cikin? Am talking to you! Anas koh? Hahaha...ā€ ya sakar da wata muguwar dariyan bosawa. ā€œBazata saku ba, Fannah you are mine baraki d’au cikin wani mahaluqi ba a duniyan nan ba se nawa muddin ina raye. Ki ware kunnuwanki da kyau ki saurare niā€ ya nunata da yatsa ā€œzubar da wannan shegen cikin Mr. Fauzin zanyi in kinga kin haihu da d’an wani toh Farouq ya mutu baya duniyaā€ shaking kujerar take tana kad’a masa kai tana hawaye sosai aranta kuwa ba abinda take se kwararo addu’a...


 *Ā© MIEMIEBEE*

   beeenovels.blogspot.co.ke

10 comments:

MARICUZ said...

keep it up

Unknown said...

Hmmm farook u will not succeed sorry fannah tooo bad

fatima said...

Hmmmm

Unknown said...

😢

Unknown said...

Too bad Allah sarki fannah

Unknown said...

nothing bad will happen she will succeed

Unknown said...

Too bad Allah sarki fannah

Unknown said...

Anas were re u 😄

QUEEN MEEMI NOVELS said...

Nemcy Weldon

Anonymous said...

Anas pls come back home