Saturday, 18 August 2018

RANA D'AYA!

BY MIEMIEBEE
PAGE 38




  "Amal why aren't you saying anything?" Ya tambayeta a maraice bayan dogon shirun da tayi, shirunta a garesa ba k'aramin tashin hankali bane but he really can't force it ya zama masa dole ya hak'ura ya bata space da take buk'ata har izuwa lokacin da za ta huce.
    Tabbas mutum ya guji fushin mey hak'uri koda wasa be ta6a tsammanin Amal zatayi masa fushi haka ba saidai bai ga laifinta ba ko d'aya saboda shi ya turata har bango, idan da wata ce da tun ranan da ya korata daga d'akinsu zatayi mai fushi amma dukda hakan bata fasa yi masa ladabi ba, he's sure with time she'll come by.

  Envelope da ya tanadar mata ya zare daga aljihunsa ya ajiye mata a kan gadon daga gefenta sannan ya mik'e "I have to go now, Allah k'ara miki lafiya I can't wait to see you back on your feet I love you so much my adorable Kitten" badan yana so ba ya mik'e ya fice juyawanda Amal zatayi hawaye ya tsiyaya daga d'ayan idonta. Tabbas har yanzu tana son Yaya amma idan ta tuna da abinda yayi mata se taji gabad'aya ya fita mata a rai, she never wished for things to turn out bad between them two like this, amma ya ta iya? She can't change the past only can she make the future better. Gyara kwanciyanta da tace zatayi taji k'aran paper, a hankali ta miyar da idonta wajen nan taga envelope da ya ajiye mata da hannunta d'aya ta d'aga ta zazzage inda ta tarar da kud'i da dama aciki, sabin dubu d'ai-d'ai. Da hannunta d'aya ta irga taga dubu ashirin ne sannan ta miyar ta ajiye a gefe.

***
  Koda Afzal ya shiga cikin mota ya kasa kunna engine d'in, be hankara ba kawai yaji hawaye na tsiyaya masa daga ido yau ina ze sa kansa? Ya ze rayu idan ba Amal a kusa da shi? Gani yake idan har bata dawo a garesa ba ze mutu saboda zuciyarsa bazata iya jure rashinta a kusa da shi ba da k'yar ya iya kunna motan ya koma office. Hud'u nayi ya tashi. Gabad'aya ya mance da labarin Hindu se yanzu ta fad'o masa a rai, gidan Nazeefah ya biya inda ya sameta kwance a d'akinta tana bacci, tashinta yayi sannan ya kira driver'n Amal da ya kaita gida bayan sallamarta da yayi. Tana isa gida Ummansu ta rungumeta tana kuka tun jiya take kuka har zuwa d'azu da taje ta duba Safiyya. Dama tun farko ita bata goyi bayan kawosu birni ba dan gudun sharri irin wannan.

   Se k'arfe shida Afzal ya wuce police station d'in yayi magana akayi releasing nasu Nazeefah. Da gudu ta fito ta fad'a jikinsa tana kuka "Ya Afzal dan Allah kayi hak'uri ka yafe mun na tuba bazan sake ba" hannunsa yasa ya janyeta "Don't misinterprete my intention, ba wai don ina so nasa akayi setting naki free ba Nazeefah se don Abba ne ya buk'aci hakan, idan da ta ni ne da se kotu ta yanke miki hukuncin da yake dai-dai da laifin da kika aikata sannan zanji dad'i because I want you to change, canji na tsakani da Allah bana muzurun da nake da tabbacin kikayi ba. Bazan 6oye miki ba Nazeefah, da abinda kikayi kinsa na tsaneki kaman yadda Amal ta tsaneni yanzu, ko k'aunan gani na Amal bata so a haka kike cewa kina sona? A tunani na idan kana son mutum har abinda yake so zaka so, kin san ina son Amal but you still went ahead and hurt her I'm still mad at you Nazeefah I might forgive you someday amma bazan ta6a mancewa da abinda kikayi wa Amal d'ita ba let's go home." Driver'n Amal ya kira yazo ya d'auki Safiyya itama kud'in sallamarta yabata sannan ya buk'aceta da idan ta isa gida ta tattare ina-inata tabar masa gida yayinda shi da Nazeefah suka koma nasu gidan suma.

   Babban akwatinta ya d'auko mata "Here start packing your clothes ki bar min gida bana k'aunan ganinki anan Nazeefah as long as kika cigaba da zama anan zakina sani tunawa da munanan abubuwan da kika rink'ayi wa Amal d'ita wanda hakan ze sa in sake tsanar kine kawai so its better ki koma gida gun su Mummy." Kuka take sosai ta k'arisa inda yake tsaye had'e da sauk'a k'asa akan guiwarta "Ya Afzal dan Allah karka mun haka, dan Allah don't send me home I'm terribly sorry please forgive me wallahi na tuba bazan k'ara ba dan Allah kar ka sakeni Ya Afzal bazan iya rayuwa ba kai ba please don't divorce me" ta k'arisa cikin tsananin kuka. Hannu yasa ya d'agata "Bazan sake kiba Nazeefah saboda despite everything I still love you and I cherish the moments we spent together, I just need some space and alone time anytime I'm ready zan dawo dake but you really have to go now." Rungumesa tayi tana kukan cire rai "Please don't send me away Ya Afzal I can't live without you dan Allah kayi hak'uri ka yafemun please don't send me home I'm so sorry" kuka ta cigaba dayi ajikinsa na sosai ta basa tausayi shima bawai dan yana so ze korata gida ba dan kawai bayida wani option ne saboda zamanta acikin gidan nan kawai sake sanyasa tsananta zeyi shi kuma baya son hakan saboda idan ya tsani abu ya tsanesa kenan no turbing back, so it's better ta tafi gida kawai. A hankali ya sauk'e hannayensa a bayanta hugging her back sun d'au tsawon lokaci a haka sannan ya janyeta na k'arfi dan yadda ta kankamesa kuka take sosai tana kad'a masa kai "Please don't do this Ya Afzal please don't."

  "I'm so sorry Nazeefah I'm really sorry I wish there's something I could do you have the next one hour to pack your belongings zan sa driver'n Amal yayi dropping naki a gida" yana kaiwa nan ya juya. Ihu Nazeefah ta k'urma tana kuka tana kiran sunansa amma ko waiwayawa beyi ba ya fice rushewa tayi a wajen tana kukan tsuma zuciya yau ina zata sa kanta? Ya zatayi da ranta? Ya zatayi da masifaffen son Afzal dake cikin zuciyarta? Bazata iya rayuwa ba shi ba, da ta rasa sa gara ta rasa rayuwarta gabad'aya, soyayyan sa ya riga ya zame mata jinin jiki, idan ba shi baza ta iya rayuwa ba. Tafi minti goma a wajen tana kuka sannan da k'yar ta iya lalla6awa ta k'arisa wajen wardrobe nata yayin da ta shiga tattare kayakin nata, tana yi tana kuka haka har ta samu ta gama tattare kayakin nata ta ja akwatin ta rufe sannan ta fito da akwatin parlour ganin ba Afzal a gurin se ta k'arisa waje nan ma bata gansa ba ashe acikin motansa ya 6oye yana kallonta daga mirror. Waya yayi wa driver'n Amal nan ya k'ariso ya ja mata akwatin nata cikin mota se kewaye take tana nemansa amma ko alamansa babu ga kuma motansa na nan a fake, haka ba don tana so ba ta k'arisa motan ta shiga har driver ya kaita gida tana aikin kuka. Ba k'aramin hamdala su Mummy sukayi ba ganinta ta dawo gida, text Daddy ya turawa Afzal yana yi masa godiya, kwana ranan Nazeefah tayi musu tana kuka, kukan zafin rabuwa da Afzal shima Afzal har hawaye seda ya zubar bayan tafiyan ta, yana sonta amma baze iya cigaba da zama da ita muddin Amal bata dawo a garesa ba toh baze iya dawo da Nazeefah ba, wannan haka take.

 ****
     GIDAN ALHJ AMIN

 Seda Ummi ta jira Abba ya gama cin abincinsa sannan tayi gyaran murya. "Alhj?" Ta kira sa.

  "Yes My dear?" ya amsa had'e da d'ago kai yana kallonta.

  "Dama wata magana nake son yi maka amma sena ga jiya kaman a gaje ka dawo yau kuma throughout baka yini a gida ba."

  "I'm sorry schedule d'ina ne kwana biyun nan is so tight se a hankali."

  "Ba komai dear Allah taimaka ya k'ara arziki da bud'i."

  "Ameen Hjy Mairama ta so what is it you wanted to discuss?"

  "Batun Prince ne dama."

  "What about him?"

  "Amal tayi masa yaji" bata tsaya yin corner-corner ba ta sanar da shi gaskiya kai tsaye.

  "What?!"

  "Amal tayi masa yaji yau kwana hud'u kenan."

  "Kina nufin har mukaje muka gaisheta dama ba a gidansa take ba?"

  "I'm sorry but yes."

  "Kuma kin sani?"

  "Dear I'm sorry."

  "Meyasa baki fad'a mun ba?"

  "Alhj ina gudun fushin da zakayi masa ne already matsaloli sunyi masa yawa kaga idan kaima ka k'ara da naka abun zeyi masa yawa."

  "Wow! Meya faru har tayi masa yajin? Batun abinda Nazeefah tayi ne?" K'arya taso yi masa tace eh amma tuna idan aka je yin sulhu gaskiya na iya fitowa taji kunya se kawai ta fasa ta irga masa gaskiyan al'amarin.

  "Afzal d'in?" Ya tambaya da mamaki shi kam da ba a bakin Ummi yake jin labarin ba se yace sharri akeyi wa d'ansa.

  "Unfortunately abinda ya faru kenan amma yayi nadama yanzu wallahi Alhj dan kad'an ya rage beyi kuka ba da yake ban labari kayi hak'uri kayi masa uzuri sharrin shaid'an."

  "Nadama? Bega komi ba tukuna kuma ki daina kawo zancen sharrin shaid'an wannan ganganci ne da rashin mutunci da kuma rashin tunani da rashin aiki da hankali a fili har 'yar yarinyar nan ne zeyi zarginta? Mey ta sani?"

  "Alhj yace shifa ba zarginta yake ba."

  "Maganan banza amma ai abinda ya nuna mata kenan kuma abinda zata fad'awa iyayenta kenan."

  "Alhj kayi hak'uri tabbas Prince yayi kuskure amma baza mu iya canza hakan ba kayi hak'uri a had'a kai ayi masa bikon yarinyar nan yaso yayi hakan da kansa amma abun ya gagara ko ganin Amal iyayenta sun hanasa yi wallahi yaron nan na cikin tsaka mey wuya ace cikin matansa biyu ba ko d'aya a wajensa."

  "Ai daidansa kenan ko nine bazan barsa ya shiga yaga min 'ya ba tunda ya walak'anta ta haka, iyayen Amal sunyi mun dai-dai ko a babu yanzu ze san matsayinta, ma wannan wani irin rashin hankali ne? Wallahi wasu abubuwan in ance min Prince ya aikata se inga kaman sharri ake yi mishi ban ta6a sanin sa da wannan banzan hali da rashin wayo ba."

  "Alhj kayi hak'uri ze gyara."

  "Kibar 6ata miyan bakinki kina bani hak'uri Hjy Mariam ba dani za'ayi abin kunyan nan ba in kinga na taka k'afa gidansu yarinyar nan toh takardan sakinta na kai mata dan nasan koba jimawa da dad'ewa iyayenta zasu nemi a kai musu takardan 'yarsu bayan nan ba abinda ze kaini gidansu, rashin hankalin Afzal ya isheni haka."

  "Alhj dan Allah kar kace haka kafi kowa sanin ciwon Afzal, kafi kowa sanin raunin zuciyarsa da kuma abinda rashin yarinyar nan a kusa dashi ze haifar, ina fatan baka mance da abinda likitansa yace ba."

  "Ai idan ma mutuwa yayi shi ya siya mutuwan nasa da kansa kawai dan yarinya na da hak'uri shikenan seya walak'anta ta? A idonsa yarinya ta tattare kayakinta amma dan gadara yak'i koda yi mata magana bale yayi tunanin hanata? A ina aka ta6ayin haka? Saboda yana ganin gidansa yafi gidan iyeyenta gata ko mey? Sannan kuma dan rashin kunya da rainin wayo yace wai bey d'au shirin yaji take ba? Kinga I've had a stressful day I'm very tired in kina da niyyan kwanciya bismillah in kuwa a'a ni seda safe."

  "Alhj please kar kayi haka wallahi mune da asara idan muka rasa Afzal kaman yadda Daddy'n Nazeefah yace hannun mutum baya ri6ewa ya yasar toh muma fa hakane komin yaya baza mu k'i Afzal ba kuma kaima fad'a kawai kake wallahi baka gansa kwance akan gadona asibiti bane fighting for his life" ko amsata beyi ba ya k'arisa d'aki abinsa ba tare da ya kewaya ba. Ita kanta bawai taji dad'in abinda Afzal yayi bane kokuwa tana goye masa baya kawai gudun halin da yake iya fad'awa ne idan ba a dawo masa da Amal a garesa ba sanin raunin zuciyarsa. Bazata gaji da basa hak'uri ba tasan zuciyansa yana da saurin fushi amma kuma hak'uri kad'an aka basa ze sauk'o.


***.        ****.           *****.          *****
    Kaman yadda likita ya d'au alk'awari bayan kwana uku ya tanadar da results na Daddy. Da yammacin ranan yaje ya amsa da kansa ko da driver be nema ya rakasa ba. Ba k'aramin tsinkewa gabansa yayi ba bayan da ya karance results d'in yaga komi positive yake nunawa, ma'ana Amal 'yarsa ce kad'an ya rage beci tuntu6e ba dan yadda ya razana se hailala yake yana maimaita innalillahi wa inna ilaihi raji'un.
 
   Yanzu Amal 'yarsa ce? Ashe ciki ya shiga jikin Jameensa bayan abinda ya faru a tsakaninsu, yau ina zesa kansa? Ta ina ze fara sanar da mutane wannan badak'ala? Wai wannan a duniya ma kenan Allah yake neman tozarta sa haka ina kuma ace a lahira? Wannan wace irin k'addara ce taya yaransa biyu zasu auri miji d'aya? Shin haka Allah yake kama duk wanda ya d'au alhak'in wani? Shin haka duk wanda ya aikata aikin banza yake fara ganin sakamako tun anan duniya ba ma se anje lahira ba? Shin ashe komin yaya mutum yaso 6oye laifi ko zunubi ta inda baya tsammani Allah ze tozarta sa a idon jama'a? Yau yana cikin wani yanayi ta ina ze fara sanar da Amal shine mahaifinta? Ta ina ze fara sanar da Hjy Surayyarsa yana da shegiya a waje? Ta ina ze fara sanar da Nazeefah Amal 'yar uwarta ce? Da wani ido yaransa zasu sake kallonsa? Da wani ido amininsa da kuma manyan abokansa zasu sake kallonsa harma da 'yan unguwa da masu aiki a k'ark'ashinsa? Shikenan k'wan da ya jima yana gudun fashewansa ya tsage yanzu k'iris ya rage kuma ya fashe ya zube. Kansa ne ya mugun d'aurewa gabad'aya ya rasa mey ke masa dad'i. Allah ne de kawai ya kaisa gida ranan saboda yadda ba hankali a jikinsa yake tuk'i tunda ya isa gida ya rufe kansa a d'aki yayi k'aryan migraine ne ke damunsa baya son a tak'ura mishi, tunanin ta inda ze fara 6ullowa al'amarin nan yake amma ya kasa tabbas acikin yaransa biyu dole se d'aya ta zama bazawara dan bazeyi Afzal ya cigaba da zaman aure da dukansu biyu ba tunda jini d'aya suke. Annabi beyi k'arya ba da yace idan kayi me kyau me kyau ze bika idan kuwa kayi na banza na banzan ne ze bika tabbas yaga hakan yanzu. Yanzu da ace aikin alkhairi yayi a baya sede 'ya'yansa suci riban hakan, amma daya shuk'a tsiya ba shi kad'ai ba harta yaransa seda hakan ya shafa.

  ****  
  Nazeefah bata fasa turawa Afzal sak'o tana neman tubansa ba safe ba dare tun tana kiransa baya d'agawa har ta hak'ura ta daina yau kwanan ta biyu kenan gabad'aya ta fita daga kamanninta dama ba k'iba bane da ita akan raman nata ta sake ramewa ba aikinta se kuka da tunani kullum, gashi ko makaranta ta shiga bin ta da kallo ake Rumaysa duk ta bazata a gari mijinta ya kaita cell sekace ba ita ta d'aurata akan gur6arcacciyar hanyar ba.
 
  ***
  Afzal na zaune a office amma hankalinsa gabad'aya akan Amal tasa yake kullum haka yake yini da tunaninta ya kuma tashi da shi gashi tun ranan be sake sanyata a ido ba, koya kirata bata d'agawa sak'o ma ya tura mata bata replying nasa, whatsapp messages ma ko reading batayi he can't explain how much he's missing her. So yake ya sake ganinta kafin a sallameta daga asibitin dan yaji daga bakin nurse d'in cewa yau za a sallameta jira yake lokacin lunch yayi yaje ya dubata wanda kafin nan ya d'au wayansa ya kira Ummi jin shiru tun ranan da sukayi magana har yau bata sake nemansa ba. Seda wayan ya kusa tsinkewa ta d'aga bayan sun gaisa yake tambayarta ko sunyi magana da Abba, bata 6oye masa komai ba ta fad'a masa yadda sukayi da Abba yadda ya nuna komin yaya shi bazesa hannu cikin wannan al'amari ba na sosai zuciyan Afzal ya karye.

  "Halo Afzal are you still on the line?"

  "Yes Ummi" ya amsa cikin wani irin salo ko daga jin muryarsa Ummi tasan zuciyarsa ta mace.

 "Don't lose hope Afzal ka cigaba da addu'a nima bazan fasa bawa Abbanka hak'uri ba in shaa Allahu ze sauk'i aje ayi maka bikon Amal kaji? Amal zata dawo a agreka da izinin Allah."

  "Ta yaya Ummi? Ko jiya naje na samu Papi amm he's not willing to talk to me in the case of Amal it's worse ko magana bata yimun Ummi I'm slowly dying I can't do without her."

  "Ka kwantar da hankalinka Afzal."

  "Ta ina hankalin nawa ze kwanta Ummi ina shirin rasa Amal? I'm definitely going to die."

  "Subhanallahi wai bazaka bar magana haka ba? Bazaka mutu ma kuma in shaa Allah Amal zata dawo a gareka kar ka gaji da bata da iyayenta hak'uri nima zan taimaka maka zan samu Mami inyi mata magana."

  "Thank you Ummi, I know I can always count on you thank you so much Allah sak'a miki."

  "Ameen ka kwantar da hankalinka kaji?" Kai ya gyad'a tamkar tana gabansa "Se mun sake waya zan kuma cigaba da bawa Abban ka hak'uri nasan ze sauk'o even though ba yanzu ba amma definitely he'll."

  "Thank you so much Ummi" da haka sukayi sallama. Azahar nayi bayan ya idar da sallah yaci abinci ya wuce TH sede yana isa ya tarar da sad news na cewa an riga an sallami su Amal har sun koma gida, tamkar yayi kuka haka yaji dama yaso yayi wa driver'nta magana yazo ya d'aukesu ya kaisu gida, a cewansa gabad'aya se yamma zasu tafi ashe ba haka neba. Be gaji ba washegari da yamma bayan ya taso daga office ko gida be je ba ya zarce gidan su Amal sallama yayi Mami ta amsa sannan yasa kai ya shiga ya nemi gu ya tsuguna. "Bismillah hau kan tabarman mana ka zauna" Papi yace da shi.

  "A'a Papi nan ma yayi nagode. Ina yini?"
  Gaishesu yayi duka cike da ladabi da biyayya inda suka amsa ba yabo ba fallasa har hakan yaso d'aurewa Afzal kai a tunaninsa gabad'aya zasu koresa yau idan ya shigo sekuma ya tarar da sa6anin hakan.

  "Papi ya jikin Amal?" Ya tambaya afterwards.

  "Da sauk'i Alhamdulillah."

  "Jiya naje asibiti na tarar har an sallameku kun dawo gida dama driver naso turawa ya dawo daku gida."

  "Ayyah karka damu mungode."

  "Papi bazan gaji da baku hak'uri ba dan Allah kuyi hak'uri ku dawo mun da Amal, nasan nayi kuskure amma kuyi hak'uri ba yadda banyi da Abba ba ya sa baki ya tayani baku hak'uri amma yak'i saboda shi kansa fushi yake dani akan abinda nayi wa Amal, dan Allah kuyi hak'uri wallahi sharrin shaid'an ne."

  "Tabbas d'an Adam ajizi ne amma a gaskiya bazan 6oye maka ba Afzal abinda kayi wa Baby ya ci mun tuwo a kwanu. Ban ta6a tsammanin hakan daga gareka ba Baba na, atunani na ko a bayan raina zaka kula min da Baby ka rik'e min ita amana se gashi tun a ido na ka soma walak'anta ta kodan gani kake bata da uba bata da gata?"

  "Wallahi Papi ba haka bane, sanin kanmu ne nan duka Amal tafi k'arfin a walak'anta ta kuyi hak'uri wallahi sharrin shaid'an ne."

  "Tafi k'arfin a walak'anta ta amma harda korinta daga d'akinta Afzal? Saboda ko tsinke bata kai gidan ba?" Mami da tayi shiru tun d'azu ta tsoma baki.

    "Mami Wallahi ba don haka bane sharrin shaid'an ne amma in shaa Allahu hakan baze sake faruwa ba."

  "Tabbas saboda Amal baza ta sake komawa gidanka ba, haka tace kuma ina biye da ita d'ari bisa d'ari."

  "Mami dan Allah kar kiyi magana haka Mami keda ya kamata ki tayani shawo kanta kuma kike cewa haka? Mami kin fi kowa sanin yadda nake son Amal kin fi kowa sanin yadda rashin ta a kusa dani yake babban hatsari da tashin hankali a gareni dan Allah kar kiyi mun haka."

  "Ina sane da hakan Afzal, shiyasa kai na ya d'aure na rasa gane dalilin daya sa kayi mata abinda kayi ko dan gani kake bata halacacciyar hanya aka sameta ba dan haka bata da wani k'ima da daraja? Kake ganin kaman alfarma kake mata saboda ka aureta hakane Afzal?? A jinka idan da anyi shawara da ita zata so ta kasance hakan ne? Ko a jinka ni d'in inda nasan sharrin dake jira na a yinin ranan zanje in sami azzalumin mutumin daya cuceni d'in ne?" Ta k'are maganan idonta na cikowa da hawaye, dama rana mey irin ta yau take gudu shiyasa bata goyi bayan Papi ya sanar da Afzal asalin Amal ba tun farko, ai ga irinta nan yanzu tun ba ayi nisa ba ya soma walak'anta ta.

  "Subhanallahi Mami dan Allah kar kice haka, Mami please don't ever talk like that ni wallahi in ba da kika d'auko maganan ba ma yanzu gabad'aya na manta da ita wallahi ban ta6a goranta wa Amal akan asalinta ba idan k'arya nake muku ku kira ta ku tambayeta wallahi bazan ta6a yin haka ba please forgive me if you felt that way I'm terribly sorry."

  "Ya isa Jameelah yi hak'uri ki koma ciki ni da Afzal zamuyi magana karki d'aga muryanki Baby ta jiyoki yi hak'uri ki koma ciki" batayi musu ba ta mik'e ta shige d'aki inda Papi da Afzal suka cigaba da tattaunawa.

   "Shin meya faru Afzal? Naji 6angaren labarin daga gun Amal kaima zan so inji naka 6angaren."

  "Papi kunfi kowa sanin yadda nake son Amal, wallahi sharrin abokiyar zamanta ne, ita tayi manipulating mind d'ina ta shiga tsakani na da Amal, Papi komi na saiwa Amal harta tsinke idan na koma gun 'yar uwar nata senaji a bakinta taya zan san wai ta had'a baki ne da 'yar aikin Amal tana kai mata rahoton duk abunda ke gudana a cikin gidan namu?" bayanin komai dalla-dalla yayi wa Papi.

   "Tanan kam kayi gaskiya ko ni ne zan fi yarda da Nazeefah akan ita Baby saboda wannan shaida k'wwak'k'wara amma batun shigo da maza cikin gidanka fah? Ka ko san Allah ya haramta auren da zargi ya shiga? Ashe har Allah ze kawo ranan da zaka yi kokonton tarbiyyan dana bawa Amal?"

   "Wallahi Papi ni ban ta6a zargin Amal ba, itace bata fahimce ni ba dan ko da 'yar aikinta ta gaya mun cewa sau biyu tana shigo da maza cikin gidan tunani na gabad'aya akan course mates nata ya k'are ba wai kwartaye ba, wallahi sam ni hankali na be kai ga chan ba saboda nasan da wata irin mata nake zaune. Kuma ko da na tashi yi mata magana ce mata nayi kar ta sake shigo mun da coursemates nata cikin gida ba wani abun ba, itace tayi mun mumunar fahimta dan haka nake sake baku hak'uri, kuyi hak'uri."

  "Na fahimce ka, amma batun kana ganinta take had'a kayakinta baka hanata ba baka kuma yi mata magana ba ba fa shin hakane?"

  "Wallahi Papi ban zata wai shirin yaji takeyi ba, dama tunda muka soma samun matsala na turata d'ayan d'akin kowani safiya takan shigo d'akin namu ta shirya toh ko da naga tana shirya kayakin nata senayi tsammanin ko zata tare chan gabad'aya ne washegari kawai na tashi na tarar bata gidan wallahi ban san lokacinda ta tafi ba."

   "Idan har haka ne meyasa baka nemeta ba bayan faruwan hakan? Da ace a ranan kazo bikonta ka deji rantsuwa ko? Wallahil azeem komin ya girman kuskuren da aikata yake zansa maka Amal a mota ka koma da ita gida saboda ka nuna tanada muhimmanci kenan amma bakayi hakan ba Afzal, ni kake tunanin zan kiraka ince maka naga Amal ta taho gida lafiya?" Kai ya kad'a a hankali cike da nadama "Abinda ya 6ata mun rai kenan, banzan da kayi da ita kak'i ka neme ta kak'i ka neme ni ko mahaifiyarta, anan ka nuna baka damu da ita ba, anan ka nuna ita ba kowa bace kasan komin jimawa da dad'ewa zamu sata a mota mu miyar maka da ita mu baka hak'uri tunda de gidanka yafi gidan iyayenta gata ko ba haka ba?"

  "Subhanallahi dan Allah Papi kayi hak'uri wallahi ni ba hakan a zuciya na nasan nayi kuskure kamata yayi in kira Amal idan banyi hakan ba kuma in kiraka ko Mami, amma d'an Adam ajizi ne kuyi hak'uri ku gafirceni in shaa Allah hakan baze sake faruwa ba wallahi fushinku a gareni babban tashin hankali ne especially in the case of Mami bana son ku d'au bana son Amal wallahi ina sonta, I really do love her kuma se inda k'arfi na yak'are zan cigaba da baku hak'uri har se Allah ya huci zuk'atan ku."

  "Ni ba fushi da kai nake ba Afzal nayi maka hakan ne dan ka gane kuskurenka ka kuma san k'ima da darajar Baby bayan nan kuma don in tabbatar da kalan soyayyar da kakeyi mata kuma na tabbatar da hakan yanzu don idan da wani ne da tuni yayi zuciya kodan irin abinda nida Maminta muka rink'ayi maka a asibiti amma haka baka fasa zuwa ba kullum dukda tokarin da muke maka. Hakan ya nuna mun dagaske ne komi ya faru bisa kuskure ne amma  kana son Baby kuma ina alfahari da hakan sosai Afzal tabbas se mey sonka ne ze so wani naka akan Baby kuma na tabbatar da cewa kai masoyin mu ne na hak'ik'a."

   "Godiya nake Papi, ba k'aramin farin ciki kalamunka suka sanyani ba kuma hak'urin nan shi zan cigaba da baka da Mami kuyi hak'uri duk sharrin shaid'an ne."

  "Shikenan Babana ya wuce Allah yasa mu dace."
 
  "Ameen Papi godiya nake, Allah saka da alkhairi."

  "Ameen."

  "Shin yanzu zan iya dawo da Amal d'akinta? Dan Allah kar kace a'a Papi, alk'awari na d'auka bazan sake k'untata mata ko yi mata ba dai-dai ba bi iznillahi."

   "Na yarda da kai Afzal amma nima ba daga ni bane, bazan iya tilasta wa Baby akan cewa lallai-lallai se ta koma maka ba iyaka inyi k'ok'ari in shawo maka kanta."

  "A hakan ma godiya nake Papi, Allah sak'a da alkhairi yabar zumunci."

  "Ameen ba komai ana tare ai."

  "Kuma dan Allah ka sake bawa Mami hak'uri ni wallahi sam ba hakan a raina."

  "Karka damu."

  "A kuma gaishe mun Amal da jiki nasan koba don tana bacci ba bazata amince ta fito mu gaisa ba."

  "Zan gaisheta in shaa Allah."

    "Godiya nake barin koma yamma nayi" hannu ya zira a aljihu ya zaro envelope daya tanadar da 20k aciki ya mik'awa Papi akan a sai wa Amal abinda take buk'ata sede sam Papi yak'i amsa daga k'arshe ajiyewa kawai yayi ya mar sallama ya fice. Mik'ewa Papi yayi ya d'au kud'in dan kai wa Amal a d'aki dukda cewan yasan bacci takeyi.  Bud'e k'ofan da yayi ya tarar da ita tsaye dai-dai wajen ta jik'e jak'ab da hawaye. Salati yasa ba shiri bade taji dukkan abubuwan da suka tattauna akai ba? Bade taji labarin asalinta ba?

  "Baby?" Ya kirata cikin mucacciyar murya, d'ago kan da tayi zata kallesa kawai ta zame k'asa a sume.
  "Baby?" Kumatun ta ya shiga tapping amma ba response. "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Jameelah! Jameelah! D'au waya ki kira Afzal beyi nisa ba Baby ta sume."
  Da gudu Mami ta fito ta fad'a d'akin Amal inda tasa ihu had'e da k'arasawa da salati "Abba meya faru? Na shiga uku!"

   "Ki d'au waya ki kira Afzal" da hanzari ta d'auko wayanta ta sanar da Afzal halin da ake ciki akan ya juyo, yana isowa ya d'au Amal ya kaita mota inda Papi ya zauna a gidan gaba Mami kuma a baya tana rik'e da Amal. Emergency ward akayi da Amal lokacin da suka isa asibitin.

  Cikinsu duka uku ba wanda ya iya ya zauna se safa da marwah sukeyi a waiting room d'in, Mami se kuka. "Abba meya sameta?" Ta tambayi Papi.

  "Ban sani ba Jameelah tsoro na d'aya Allah yasa bata jiyo abinda muka tauna akai ba, ina zaton taji komai saboda tsaye a bakin k'ofan d'akinta na tarar da ita tana kuka lokacin da na bud'e k'ofar."

   "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mami tasa salati "Yau na shiga uku Abba ya zanyi dan Allah? Mey zancewa Baby yanzu? Shikenan abinda nake gudu ya faru."

  "Ya isa haka Jameela ki kwantar da hankalinki in shaa Allahu Baby zatayi miki kyakkyawan fahimta."
  Bada dad'ewa ba likitocin da suka duba Amal suka fito nan su Papi suka duk'ufa suna tambayansu ya jikin nata.

  "In shaa Allahu ba wani abu serious bane kawai a bisa fad'in da tayin ne ta kusan fama ciwon nata amma Alhamdulillah achan Allah ya tsayar babu internal bleeding ba komai, ta ma riga ta farfad'o kuna iya shiga ganinta." Hamdala dukansu uku suka sauk'e a wajen sannan suka duk'ufa cikin d'akin, Amal na ganinsu ta shiga zubar da hawaye.

  Hak'uri Papi ya shiga bata Mami kam banda hawayen da take zubarwa ta kasa yin komai.

  "Kukan ya isa haka Mamana ko ta halal aka sameki ko kuwa ta haram kaf nan bamu damu da hakan ba saboda ba abinda ya isa ya canza matsayin ki a idanun mu da kuma yadda muke sonki a zuk'atan mu Baby, kece Amal nan da muka sani muke kuma so har yanzu."

  "No Papi" ta amsasa tana kad'a kai "Bakuwa sona idan da har kuna sona da bazaku min k'aryan asali na ba har na tsawon shekara ashirin da d'aya, I can't believe you and Mami could do this to me."

  "Baby dan Allah kar kiyi haka sanin kanki ne ni da Maminki ba wanda muke so sama dake."

  "That's not true Papi how could you do this to me? Har ku sanar da Yaya asalina amma ni ku hanani sanin gaskiya? No one deserves to know the truth above of me no one Papi" ta sanar da shi had'e da rushewa da wani kukan.

  "Baby dan Allah kiyi hak'uri" Mami tasa baki "Wallahi ni da Papinki mun so sanar dake gaskiya lokacin aurenki amma Afzal ya hana saboda baya son hakan ya jefa ki cikin wani hali."
  Mamaki sosai kalamun Mami suka sanya Amal, har Afzal ne yace kar a sanar da ita gaskiya kuma akan wannan dalili? Wow! She's speechless ita kanta tasan batada masoyi sama da shi bayan su Mami shiyasa har yau ta ke mamakin kanta na kasa yafe masa kuskuren da yayi mata. Kai ta d'ago a hankali ta sauk'e idanunta akansa murmushi ya sakar mata kafin tayi sauri ta kawar da kanta.

   "Meya faru Mami? For all my life you made me believed inada Abba akan cewa mutuwa ce tayi mana yankan k'auna ashe ba haka bane, ko a mafarki aka cemun keda Papi zaku yi mun k'arya haka bazan ta6a yarda ba, why do you have to lie to me Papi? Why Mami?" Kuka take sosai duk ta basu tausayi a wajen.

  "Baby kiyi hak'uri" Papi yace da ita "Bawai mun 6oye miki gaskiya bane don son kai kokuwa makamancin haka munyi hakan ne saboda muna sonki."

  "Papi ba haka so yake ba, idan da har kuna so na bazaku ta6a 6oye mun wannan muhimmiyar maganar ba."

  "Ya isa kukan haka Mamana ya isa dan Allah karki k'ara wani ciwon ma kanki." Kewayowa tayi kan Mami. "What happened Mami? Meya faru? Na tabbata bazaki cuceni haka kawai ba seda k'wak'k'warar dalili, na tabbata koma waye ne mahaifin nawa shi ya cuceki."

  "Tabbas 'yata, sanin kanki ne ba wanda nake so sama da ke a fad'in duniyan nan kuma idan da har Allah na shawara da bawa kafin ya k'addaro masa da k'addara da na hana afkuwan wannan mumunar k'addara, kin fi kowa sanin bazan ta6a sha'awar kawo ki duniyan nan ba uba ba Baby ko dan nayi miki tsari daga tokarin 'yan unguwa da kuma yara 'yan uwanki. Sai dai kaman yadda Allah ya fad'a a Qur'ani _fa inna ma'al usri yusrah_ kowani wuya da musiba na tattare da sauk'i.  Acikin ikonsa da sassauci se ya kawo mun sauk'i ta hanyan bani uba mey tausayi kaman Papinki, ubanda ze iya sadaukar da rayuwansa dan farin cikin 'yarsa, uban da yayi playing role na mahaifinki a rashin asalin mahaifinki Baby, ba abinda zance da Papinki sede Allah ya sak'a masa da mafificin alkhairi ya basa gidan Aljannah. Tabbas k'addarata mumunar k'addara ce wanda bazan yi fatan irinsa wa mutum ba koda kuwa mutumin ya kasance mak'iyi na" ta tsaya ta numfasa nan Afzal ya mik'e "I'm sorry let me excuse you" yace dasu duka.

  "A'a Afzal" Mami tayi saurin tsayar da shi "Ka riga ka zamo na gida tamkar d'an cikina kuma nakeji da kai, kaman yadda Baby zata ji wannan labari kai ma zanso ka zauna kaji komai" ta buk'acesa sede du da hakan Afzal beji ya cigaba da zama a d'akin ba gani yake kaman ya musu invading privacy.

  "Karka ji komai Baba na ka zauna" Papi ya jaddada masa lokacinda k'wayan idonsu ya had'e numfasa yayi sannan ya dawo ya zauna inda Mami ta fara daga inda ta tsaya...




RANA D'AYA!
#RD

Love... King Miemiebee👄✨

9 comments:

Unknown said...

Thanks dear. I can't wait for the other side of this book

Unknown said...

Hmm, my dear Allah ya kara miki basira

Unknown said...

Hummmmiy

Miemie Allah yakara karfin ido da basira

Unknown said...

Wohoh! I can't wait 4 the other side of face MIEMIEBEE please update soon
M

Unknown said...

Jazakallah khairan more update soon please

Unknown said...

Muna ta jiran update..... barka da Sallah. Ana hidimar sallah ina leka blog

Unknown said...

Muna ta jiran update..... barka da Sallah. Ana hidimar sallah ina leka blog

Unknown said...

Da ftn anyi hidimar sallah lfy ,Allah ya maimaitamana yasa ibadunmu karbabbune amin. Muna ta jiran update... Ko wani lokaci muna ta leka blog amma shiru, don Allah ayi kokari a taimakemu da wani update din. Saga mai kaunarki a kullum

Unknown said...

Sister miemie har yanxun naman be kare bA😄 we r expecting an update 2day plz nd barka da sallah