Wednesday 7 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 68
BY MIEMIEBEE






     Kasa koda amsashi tayi wani kunya taji ya rufeta, she can’t believe abinda ta aikata sede kuma chan cikin zuciyarta tana miradi da abinda tayi atleast tayi proving masa tana sonsa bare sake kokwanton san da take masa ba. Hannunsa ta sauk’e daga hab’arta tare da juyawa kafin ta soma tafiya yasa hannu a kunkuminta ya juyo da ita tare da matse jikinta a nasa. “Flower look at me” har a yanzu tak’i d’ago kai su had’a ido. “Flower baraki kalleni ba?” Kai ta kad’a masa. “Then look at me” kai ta sake kad’a masa kunya bare barta ta kallesa ba.
     “You love me right?” Ya tambayeta. Kai ta gyad’a masa. “I want to hear it again Flower.” Hannunta ta zagaye a bayansa tayi hugging nasa “I love you Anas, I love you so very much *My Lion”* shima a hankali ya zagaye hannayensa a bayanta pulling her closer to him. Gashinta yayi kissing “I love you so much more Flower.” sosai yaji dad’in sunan data kirasa dashi *•°LION°•* it means everything to him.

       Sun d’au tsawon lokaci suna atsaye sannan a hankali ya raba jikinsa da nata tare da jawo hannunta suka zauna kan kujera. Hannyensu ya had’a duka waje d’aya cikin sanyin murya a hankali yace, “Flower fad’amin mesa kikayi shunning d’ina jiya? Nasan kina da qwararren dalili koh?” Kai ta gyad’a “then tell me kinji? Karki b’oye min tell your husband” Innocent eyes nata data k’ayatasu da kajol ta d’ago a hankali ta azasu akansa.
      “I’m afraid Anas tsoro nakeji” ta sanar dashi cikin cracky voice.
     “Tsoron meh Flower? Kin d’au zan miki wani abu neh?” nan ma kai ta gyad’a. “Don’t be kinji? Ba abinda zan miki seda yardan ki I will never do anything to you ki saki jikinki dani kinji?”
        Batasan lokacinda hawaye yasoma ciko mata a ido ba cikin sautin kuka tace, “for how long Anas? For how zaka ta zama haka? For how long zanta toye maka hak’k’in ka?”
     
     “For as how long it takes Fannah ni ban damu ba I love you so kema kibar damuwa kinji?” Kai ta kad’a “Anas dole in damu saboda na miji ne kai dole wataran sha’awah ze taso maka and saboda bakason kayi forcing d’ina seka hak’ura ka tauye wa kanka hak’k’i saboda matarka batason baka hak’k’inka? In hakan ya faru kasan me mala’ikum Rahma zasu min? Anas tsine min zasuyi, zasu tsine min...” ta fashe da wani irin matsanancin kuka. Duk tabi tasa Anas rikicewa a rayuwa ba abinda ke tada masa hankali kamar kukan flowersa. Matso ta yayi ajikinsa yana bubbuga bayanta “Flower kibar kukan nan please I can’t take it please kibari kidena.” Pecking gashinta yayi “stop crying kinji? Ba tsinuwan da za’a miki in shaa Allah ni nayi deciding I won’t touch you se in rananda kika yarda so kibar kukan kinji?” Kai ta gyad’a masa a hankali tasoma shanye kukan nata.

     Seda ya tabbata tayi shiru ya d’ago ta daga jikinsa yana kallonta “Flower but what are you so afraid of? Mesa kike tsoro haka? Saboda kin ganni kind of large?” Ya tambaya tare da d’age gira. Murmushi kad’an ta saki tana kad’a kai danko yabata dariya shi ya d’au wai tsoronsa take amman ko kad’an. “Tsoro na kikeji flower?” Kai ta girgiza masa “mesa zanji tsoron ka *Cherie Pie?”*
     “I don’t know kodan kinga inada builded body kinga muscles all over my hand kike tsoro I might destroy you on bed kekuma gaki ‘yar k’arama” Dariya sosai ta tsaya tanayi harda rik’e cikinta. “Anas I’m not small kadena cemin small.”
      “Yes you are Baby and thats why kike tsoro.”
      “Ko kad’an ba haka bane *Doodle bug* matsalar ba daga gareka bane...” Sekuma tayi shiru take mood nata ya canza.
    Hannunta ya rik’o “ba daga ni ba Flower? Bani kike tsoro ba?” Kai ta gyad’a masa “toh daga waye ne Flower?” Take idanunta suka ciko da hawaye “Anas daga ni ne, matsalar daga ni ne...” Sekuma ta fashe da kuka. Hankalin Anas in yayi dubu be tashi ba kamar ya daga ita? Me take nufi? Mesa take kuka haka? Is she lacking something as a woman? Subhanallah!

     Kwanto da ita yayi a kan k’irjinsa yana fad’a mata dad’ad’d’un kalamu masu kwantar da hankali. Duk yabi ya k’osa yaji dalilin dayasa take tsoron had’a kwanciya dashi. Seda ya tabbata tayi shiru ya d’ago ta tare da rik’o fuskarta da hannayensa bibbiyu.
      “You don’t have to be afraid anymore, Flower ko a yaya kike I love you koda you are lacking something as a woman I still love you ahakan ina sonki nake tsakani da Allah badan wani abinda kike dashi ba.” Idanunta taji suna sake cikowa da hawaye “Anas koda... Koda...” sekuma ta sake fashewa da kuka. Haka ya sake rungumota seda tayi kukan me isarta sannan ta taso da kanta, hannunsa ta rik’e cikin nata tana kallon cikin idanunsa da kumburarrun idanunta da sukayi ja “Anas I’m insecure of your love gani nake kamar I’ll lose you, gani nake kamar in na fad’a maka sirrina zaka gujeni ka nisanta daga gareni ka kuma tsane ni, abinda baran iya jurewa ba kenan, I don’t want to lose you My Lion.”

      “Flower I will never hate you kibar fad’an haka, I will never leave your side koda kuwa wannan sirrin kin is as worse as kisan kai God forbid I will never leave you Fannah. I love you for the sake of Allah and nothing more ki d’au wannan sirrinkin k’addara ne a rayuwar aurenmu kinji? And stop saying zakiyi losing d’ina kinji na rantse I will never leave you, never.” D’an sanyi taji a ranta duk da cewa kuwa bata gamsu ba acewarta Anas na fad’in hakan ne dan besan ba cikakkiyar budurwa ce ita ba.
      “So can you tell me? Zaki iya fad’amin dalilin dayasa kike tsoron wani abu ya shiga tsakani na dake? trust me koda mene barin tab’a barinki ba Flower *_INA TARE DA KE”_* kai ta gyad’a masa tsili-tsilin hawaye na gangarowa kan kumatunta wanda yasa hannu ya share. “Anas kayi hak’uri dan Allah kasani bawai nayi hakan bane dan cin amanarka, I just can’t bring myself to tell you I’m.. I’m not complete as your woman I’m lacking something. Anas banida... Banida...” sekuma kuka yafi k’arfinta.
     
     Zuciyarsa yaji ya buga tsoro shi kansa ya somaji. “Shhhh is okay” yayi hugging nata “ya isa you can’t talk right now ya isa kinji? Mubar maganan” sosai hankalinsa ya tashi shima yarasa meke masa dad’i me Fannarsa ta rasa? Mesa da zaran ta tuna abin take kuka? Ko kad’an be kawo a ransa wai ko nufi take batada budurci ba saboda yasan hankalinta ya yaba da tarbiyyan ta yasani barata tab’a siyar da budurcinta ma kowani k’ato ba. Seda ya tabbata tayi shiru yace da ita “tashi muje d’aki ki kwanta kinji?”
     “Anas I’m sorry trust me I really want to tell you, wallahi inason sanar dakai I can’t-” katse ta yayi “I trust you My Flower shikenan don’t bother kinji? Mubar maganan I trust you ko baki fad’a min yau ba you will some other day ko ba haka ba?” Kai ta gyad’a. “Shikenan tashi muje d’aki.” Tana manne ajikinsa suka k’arisa d’aki ya kwantar da ita ajikinsa har a yanzu nishinta be dawo normal ba yana bubbuga bayanta har tasamu tayi bacci.
     “Flower” yakira sunanta. Jin shiru yad’an lek’a fuskarta yaga tayi bacci. Hannunsu ya had’a “Fannah I love you kinji? Banga abinda zesa in barki ba no matter what _*INA TARE DA KE_* forever” ahaka shima yasamu ya kwanta da tunanin Fannah a ransa.

   *****
        Seda Maghrib Fannah ta tashi a hankali ta raba jikinta da nasa ta fad’a toilet bayan tagama duk abinda zatayi tafito tayi kan Anas cikin wani irin romantic salo ta tayar dashi daga bacci yayi alwala shima yajasu Sallah. Bayan sun idar suka ci dinner, kallo kad’an suka tab’a suna hira suna tambayan junansu questions about likes and dislikes nasu dakuma age da sauran abubuwa da dama. Sosai shekarun Anas ya bata mamaki ashede mijin nata yaro ne ko 25 be cika ba gashi kuma ajebo abubuwa dayawa bayya chi. Haka suka tayi har zuwa 10:00PM sannan suka koma d’aki shi da kansa yaciro mata rigar baccin dayakeso tasa.
      “Babe wannan?” ta tambaya tana zaro idanu waje “Ai wannan ba marabansa da babu jibi fah.” ta d’aga shimen sama.
     “Flower shi nakeso.” Wani daban taciro “zansa wannan.”
    “A’a flowor ni wancan nakeso” zata sake magana yace, “zanyi fushi in baki sa ba” da sauri ta katse sa, “a’a karkayi zansa.” murmushi ya saki yana binta da kallo ta shige d’akinta ta koma tasa tare da k’are wa kanta kallo jikin mirror. Kai ta kad’a no gaskia yayi tsireci dayawa wata zuciyar ce tace mata toh ai mijin ki ne bawani gardi ba. Sam ta kasa fita da kayan hijabi ta b’urma akai tana kai k’ofan d’akinsa ta tsaya daga bakin k’ofar a nitse ta bud’e k’ofan kad’an nan ya maido da kallonsa wajen. “Come in Baby” ya buk’ace ta. Ido ta rufe ta cire hijabin da k’yar ta iya shiga cikin d’akin kanta a k’asa se murza hannayenta take duk kunya yabi ya cinyeta kallonta ya tsaya yi wane yau ya soma sata a ido ji yake kamar ya had’iyeta ko kyafta ido ya kasa why is she so damn beautiful? Abinda yake ta nanatawa a ransa kenan. Da kallon ya isheta seta fara k’ok’arin miyar da hijabin nata kamar a kyaftawan ido ya k’ariso gabanta tare da k’wace hijabin.

      “Anas kabani please.” Murmushi ya saki me k’ara masa kyau. “Flower you are damn beautiful” hannu yasa ya zagaye a kunkuminta ya matso da ita kusa dashi. “Kiss me” ya buk’ace ta. Yi tayi kamar bata jisa ba. “Flower I said kiss me.” Kai ta d’ago ta k’are masa kallo sannan tayi d’agel ta yi pecking nasa a kumatu. “There bani hijabi na toh.”
      “Are you kidding me? Kiss me like you did d’azu.”
     “Barin iya ba” ta fad’a stubbornly.
    “Nima barin bada hijabin ba.”
    “Anas please kabani.”
    “Kiss me first.”
    “Okay naji sakeni toh.” Kafad’a ya buga mata. “Ka sakeni toh I will kiss you.”
    “Are you sure?”
   “Yes My Lion.” Ba musu ya saketa hannunta ta zagaye a wuyansa sannan ta k’are wa light red lips nasa kallo seda ta tabbata ya shagalta yana jiran tayi kissing nasa tasa hannu ta fisge hijabin ta ta haye kan gado a 360 tana mai dariya. Murmushi ya saki ya juyo yana kallonta se faman dariya take masa. “Kin min wayo koh?” Abinda yace da ita kenan. Dawowa yayi ya haye gadon shima tare da k’wace hijabin hannun nata jawota yayi ya haye kanta se faman chakulkuli yake mata itako se dariya take harda hawaye tana basa hak’uri ya dena sam yak’i chan zuwa shad’aya suka kwanta a gajiye dan wasan da suka tayi sukayi bacci.

    _7:42AM_
        Yanzu su Fannah suke gama breakfast. Yau breakfast d’inma a plate d’aya suka yi har suka gama tana zaune a kan cinyarsa, tabashi ya bata ahaka har suka gama karyawan. Tayasa tayi ya gama shiri sannan ta rakosa har bakin k’ofa ta miqa masa lunch pack nasa.
     “My Handsome” ta kirasa.
    “Yes Flower.” murmushi ta saki masa;
    “Yau in ka dawo I’ll reveal my secret for you. Kai mijina ne be kamata ace ina b’oye maka wani sirri na ba zan fad’a maka komai”
    “Are you sure Babe?” ya tambayeta.
   “Yes I am, na yarda da kai dakace baraka barni ba koda kaji wannan sirrin nawa so zan fad’a maka My Husband Baby.”
    Taku d’aya ya k’ara ya rufe gab dake tsakaninsu. “I will never leave you Flower I love you” yayi pecking nata a goshi. “I love you too My Lion take care of yourself for me kaji?”
     “I will Baby.”
    “Me kakeso in dafa maka yau?” Ta tambayesa tana gyara masa necktie nasa daya d’an gauce.
    “Anything yummy” ya kashe mata ido.
    “Okay toh I will cook your favorite”
     “Kina nufin pounded yam da Eghusi soup?”
    “Yes Baby off you go I love you.” Kai ya girgiza mata cike da rashin fahimta ta tambayesa “why?”
    “You don’t love me” yace da ita.
    “Ofcourse I do My King I love you kadena fad’in haka zuciya na bare iya d’aukawa ba.” Hannu yasa ya taro fuskarta.
     “Flower bakiya sona, in har kina sona be kamata ace zan fita office baraki bani ko d’an goodluck kiss ba.”
    Murmushi kad’an ta saki “dalilin dayasa kace bana sonka kenan Baby?” Kai ya gyad’a. ‘Yar murmushi ta saki “wannan bare kawo fad’a ba My Lion.” D’agel d’in k’afa tayi tare da zagaye hannayenta biyu a wuyansa sannan tayi kissing nasa passionately ba kamar jiya da tanayi zuciyarta na bugawa ba, kissing nasa take fiye da yadda tayi jiya duk sun zurfafa cikin abinda sukeyi daga bisani tayi pulling out. Kallon idanun juna suke suna murmushi peck ta manna masa a duka kumatunsa one-by-one sannan tip na hancinsa tayi tayi ta masa a goshi amman takasa dukda d’agel d’in k’afa da tayi. Daya gano haka seya sa hannu ya d’aga ta sama nan ta manna masa peck a goshin sannan ya sauk’e ta.

     “Here are goodluck kisses seka dawo koh? I love you.” Hugging nata yayi “I love you too Flower” daga nan sukayi ba-bye wa juna ya fice. Kan kujera ta fad’a se blushing take tana fad’in “love is the sweetest thing” a ranta “His lips are sweeter than everything and his eyes? OMG!” throw pillow taja ta rufe fuskarta dashi. Shima Anas yana tuk’i amman hankalinsa na akan irin kiss da sukayi sharing da Fannah, “your lips are probably the most sweetest thing I’ve ever tasted Fannah.”

   _3:25PM_
      Fannah tagama duk wani aikin da zatayi, abinci na nan ready ajiye kan dining wanka ta sakeyi tasa wata black lace me torches na pink wanda ya bala’in tafiya da surar jikinta. D’aurin network ta kashe me kyau ta tsara kwalya sannan ta feffeshe jikinta da turare masu k’amshin bala’i. D’akinsa ta shiga ta bud’e wardrobe nasa haka kawai taji bari ta gyara masa dukda kuwa a gyare yake neman abinyi kawai take.
      Drawer’n under wears nasa ta bud’e ta zazzagosu acikin haka diary nasa data soma karantawa da jimawa ya fad’o. A nitse ta d’aga ta miyar ta soma ninke masa boxers da shorts nasa kap ta gama se fad’a mata zuciyarta ke ta bud’e diary’n ta karanta ai matarsa ce ita abinda zata sanar dashi sirrinta itama yau toh se meh dan ta karanta nasa? Hannu tasa wane ana ganinta ta zaro diary’n kwad’o tagani datse a jiki nan tashiga neman key’n cikin inda yake adana cufflinks nasa tasamu ta bud’e. Flipping first 3 pages d’in tayi saboda ta tab’a karantawa. A page 4 d’in taga heading an rubuta da manyan bak’i
 
    THE UNFORGETABLE INCIDENT (THE GIRL)
     Wani irin kishi taji ya gulleta wani girl yake nufi? Dama Anas nada wata bayan ita? So she is not his first love as yadda ya fad’a mata jiya? Bata hankara ba taji hawaye na cikowa a idanunta (Toh fa Fannah uwar kishi) tsuka taja tare da juya pegin ita a dole kishi barata karanta ba. Kujera tanema ta zauna ta soma karanta rayuwarsa na London tana murmusawa tana jin wani sabon sonsa me d’anko yana sake k’aruwa a birnin zuciyarta da zaran taga wajen daya rubuta yasha barasa sekuma ta had’e fuska.
      Dogon tsuka taja sanadiyar ganin mafarke-mafarken yarinyar datake da tabbacin itace wanda yake nufi a page 4 na littafin. Wato ma itace yarinyan dayake mafarkinta time to time yana ce min *_TANA TARE DA SHI?_* Koh”
       “Wallahi Allah kawo ka Anas gaskiya barin yarda ba, waima wace wannan yarinyan?” Duk wannan magana da take a fili take yinsu. Page 4 d’in ta koma ta bud’e tasoma karantawa kamar haka...;


     *© MIEMIEBEE*

  beeenovels.blogspot.co.ke

27 comments:

Unknown said...

Woow God bless you miemie thnz

Unknown said...

I can't Wait for de next one

Unknown said...

Hmmmmmm luv one tin tin, plssss add one episode before u sleep.Allah ya Kara basira👍

Unknown said...

Wowww!!! Cant wait��

fatima said...

Tnx pls add more

Unknown said...

Wowww!!! Cant wait��

Unknown said...

Woow thnks larv... amma double yakamata a mana yau😆😆

Unknown said...

Gbam anzo wurin am eager oh my God

Unknown said...

Wlh bansan wani irin so nakema book din nan ba wlh .... bacci ma inayi natashi bcos naga ko kin saka new episode... gashi nakaranta yanzu i need more....😦😦😦

Unknown said...

Very interesting love story,Allah ya Kara Basira namesake

UMMUL-HAMEEF ENTERPRISE said...

Woow CNT wait any longer but u nid add more pls oooooooooo

Unknown said...

Enter your comment... waiting for the next page please........ thanks

Unknown said...

waiting for the next page please........ thanks
Allah Ya Kara basira

Dijjetu said...

Wayyo Allah!!

Unknown said...
This comment has been removed by the author.
Unknown said...

Thanks alot, buh pls a qara mana 😩

kafilat said...

Wow a very very nice and interesting story,more grace to your elbow Allah kara basira.waiting for d next episode .

Unknown said...

I'm telling you.... I don't know how many times nake dubawa inga ko tayi uploading new page or not, I'm soo possessed with the book, she's such a good writer kam I have to admit.

Unknown said...

So Interesting Allah Ya Kara basira

Unknown said...

Wlh bansan wani irin so nakema book din nan ba wlh .... bacci ma inayi natashi bcos naga ko kin saka new episode... gashi nakaranta yanzu i need more....😦😦😦

Unknown said...

Wlh kuwa i thought am the only one dake haka nayita refreshing page din😂😀

Unknown said...

Tnx sis u ar d best

Mybarma said...

Pls. Let's have the continuation, very interesting. Eager to wallahi

Unknown said...

Very interesting. Waiting pls

Unknown said...

Very interesting. Waiting pls

Unknown said...

Kudos to you interesting write up keep it up

Abba salis said...

Allah sarki fannah