Wednesday, 15 August 2018

RANA D'AYA!

BY MIEMIEBEE
PAGE 36



   Cikin tsananin kuka da azaba tace, "Mene Amal bata tare mun ba Ya Afzal? Komi ma Amal ta tare mun, tamkar katanga haka Amal ta shiga tsakani na da samun soyayyarka, yadda kake sonta ba haka kake sona ba, yadda kake jin zaka iya sadaukar da rayuwanka mata ba haka kake ji da ni ba, komi Amal komi Amal, ko shopping muka fita seka tambayi ina na Amal, wayanka duk hotunan Amal ne aciki, girki nasani Amal ta fini iyawa, tafi ni iya tarerayarka, ta fini iya nuna maka soyayya, ta fini kyau ta fini fasali, ta fini ilimin boko da na islamiya gabad'aya komi da nake tunani Amal ta fini da shi. Gashi da shigowanta gidan nan dududu bata fi wata uku ba amma har ta d'au cikinka ni shekarana uku da watanni na kasa yin hakan-"

   "Amal na da ciki?" Ya katseta cike da k'in yarda.

  Kuka take sosai ta gyad'a mai kai "Amal na d'auke da cikinka Ya Afzal bazan iya ba, ta ko ina Amal ta fini taya kake tsammanin zan iya yin kishi da ita. Ya Afzal I love you dan Allah karka ga laifi na wallahi son da nake yi maka ne ya janyo komai, akanka zan iya sa ayi ma mutum kallon me ta6in hankali ko ciwon aljanu, akan ka zan iya yin duk wani irin mak'ircin da kake tsammani, akan ka zan iya sa mutum ya zargi matarsa akan ka zan iya sa a bige mutum dan a illatamun shi, I love you Ya Afzal, akan soyayyarka kuma zan iya yin komai-" zuciya ne ya d'ibesa ya sake gaura mata wani marin, na hud'u kenan k'asa ta sauk'a yayinda ta shiga raira kuka.

   "Kinsan Amal nada ciki kika sa aka kwa6eta saboda ki kashe ta ki kashe abinda ke cikinta Nazeefah?" Har yanzu ya kasa amincewa da hakan. "So it's all been you these while, duk kalan mak'iricin da kika shuk'a har kika fitar da Amal daga d'akinta be isheki ba no har sai kin sa a kwa6eta? Ashe haukan naki har ya kai stage d'in da zaki iya yin kisan kai? D'ana kikeson ki kashe? Kuma a haka kike cewa kina so na? You're insane Nazeefah, ki sani na tsaneki, na tsani duk wani mey k'aunar ki, I hate you Nazeefah."

   "Ya Afzal dan Allah kar kace haka, Ya Afzal bazan iya rayuwa ba kai ba, a shirye nake da in hallaka duk wanin da yake da shirin shiga tsakani na da kai Ya Af-" zuciya ne ya d'ibesa ya shiga yin ball da ita a wajen. Belt nasa ya zare ya shiga zaneta ta duk inda zanan ya sauk'a dama gashi vest ne kad'ai a jikinta da wandon rigan bacci iya guiwarta.

   D'an banzan duka Afzal yayi mata sekace ya samu ganga ko jaki, dukan da tunda baabarta ta haife ta ba a ta6a yi mata irinsa ba seda yaga ta fara yin amai a wajen sannan ya barta se huci yake.

   "Ki bud'e kunnuwan k'ashin nan naki ki saurareni da kyau Wallahi tallahi kin deji rantsuwa ba kaffara ko? Idan abun ya samu lafiyan Amal mey hanani kasheki a gidan nan se Allah Nazeefah, da hannu na zan kasheki nace a dai-dai ina kika sa aka bigeta?" Nazeefah ba bakin magana banda kuka ba abinda take iyayi ga yadda jikin nata ya tashi nan take, belt d'in ya sake zabga mata "Ba magana nakeyi maki ba?"
 
  "Ya Afzal dan Allah kayi hak'uri na tuba."
 
  "Aww bazaki amsa ni ba?" Bata hankara ba ya sake zabga mata belt d'in Nazeefah se ihu take tana kuka tana neman agaji amma ba wanda ze iya taimaka mata, ba mai gadi Hindu kuwa uwar tsoro tuni ta rufe kanta a d'aki se hasbnullahu wa ni'imal wakeel take ta nanatawa. "Answer me! A ina kika sa aka kad'eta?"

  "Wallahi a dai-dai bakin makaranta ne dan Allah kayi hak'uri na tuba Ya Afzal."

  "No Nazeefah you're never sorry and I swear to you, na miki imani da Allahn da raina yake hannunsa you must pay for this, you must pay for everything you've put Amal go through I don't care if it costs you your life, sekin biya abinda kikayi wa Amal" yana kaiwa nan ya wuce kitchen ya kulle k'ofan da key ya zare sannan ya wuce d'akinsu ya tattara spare keys na gidan ya sanya a aljihunsa ya dawo ya d'aga wayanta ya fice ya kulle k'ofar ta waje yadda bata isa ta kira kowa ba bale tayi tunanin guduwa. A 360 yabar gidan nata ya wuce chan bakin unimaid ya shiga tambayan mutanen dake kusa batun hatsarin da akayi d'azu ina aka kai yarinyar dayawa suka ce basu sani ba da k'yar ya samu wani mai shagon da yace yana da tabbacin TH suka wuce tunda shine asibitin dake kusa da nan d'in. Be 6ata lokaci ba ya wuce TH d'in inda ya zarce emergency ward ya shiga neman d'akin da Amal take ciki.



******
   "Se anje an siyo jini ba jini a blood bank and the patient is losing so much blood" cewan likitan dake aiki akan Amal ma wata nurse. "Kuje ku nemo jinin yanzu type O- (negative)" a guje ta fito inda suka ci karo da mutumin da ya kawo Amal da driver'nsa.

  "Ya nurse? Ya jikin patient d'in?" Yayi saurin tambayarta.

  "I'm sorry sir amma patient d'in ta rasa jini sosai wanda dole se anyi mata transfusion se gashi anje blood bank kuma babu type nata."

  "Wace blood group ce?"

  "O-" ta sanar da shi.

  "O-?"

  "Yes Sir."

  "Idan ban manta ba nima blood group O ne."

   "Sir O+ daban O- shima daban O+ ze iya receiving daga O+ kaman shi da kuma O- amma O- dole se O- kaga kuwa yanzu idan kai O+ ne bazeyi ka bawa patient d'in jini ba."

    "I'm sure O- nake nima."

   "Sir you have to be certain."

  "Amma kun tabbata inda zakuje neman akwai blood group natan?"

  "Gaskiya bamu da tabbacin hakan sir se munje mu duba tukuna."

  "Toh ai duk 6ata lokaci ne wannan ina kuma ace anje chan d'in babu blood group natan? Ai mun koma baya."

   "Hakane kuma Sir."

  "And mey ze faru idan ba ayi mata transfusion d'in da wuri ba?"

  "Based on tests da muka gudanar sakamako ya nuna tana d'auke da juna biyu toh muddin ba ayi supplying nata da jinin akan lokaci ba eventually zata iya rasa ranta da kuma abinda ke cikin nata."

  "Muje ku gwada jinin nawa in irin nata ne se ku d'iba, bags nawa kuke buk'ata?"

  "D'aya da rabi Sir."

  "Let's go muje ku d'ibi nawa kusa mata da wuri kafin lokaci ya k'ure."

  "Sir are you sure?"

  "Let's go we don't have time" haka kawai wannan Alhj yaji wani irin strong connection tsakaninsa da Amal duk da cewan bey santa ba, amma jinta yake a kusa da zuciyarsa. Nan da nan akayi d'akin d'iban jini da shi amma da fari aka gwada blood type nasa inda yayi matching dana Amal, bayan nan aka kuma wani gwajin don tabbatar da cewa jinin nasa baya d'auke da wani cutan zamani. Anan aka zuge leda d'aya da rabi kamar yadda nurse d'in ta fad'a sannan akayi masa recommending magunan k'ara jini da zena sha dan ya maido masa da jinin nasa.

   Godiya sosai mutanen asibitin suka tayi masa. Nan da nan akayi infusing wa Amal aka bata taimakaon gaggawa da ikon Allah kuma aka samu aka ceto cikin nata ba tare da wani abin ya samesa ba.
   Har anan su Mami basu da labari saboda ko waya Amal bata fito dashi ba bale a lalumo layin wayansu aciki, saboda acewarta test kawai zatayi ta dawo gida se bata damu ta fito da wayan ba.

   Har anan wannan Alhaji da ya ba wa Amal jinin jikinsa be tafi ba ya na nan yana jiran farfad'owanta. Tana farfad'owa nurses sukayi masa magana nan ya k'arisa cikin d'akin inda ya tarar da ita kwance akan gado da bandeji nad'e a kanta da k'afarta, da kuma wani a hannunta wanda aka nad'e mata shi tun daga wuya dan support da alama shima hannun ta samu matsala ne. Sosai ya tausaya mata barin ma da yaji tana da ciki.

  "Ga wannan shine mutumin da ya baki jinin jikinsa har leda d'aya da rabin da aka sa miki kyauta se kiyi masa godiya" nurse d'in tace da Amal. A hankali Amal ta shiga juyo da kanta har ta kai akan wannan mutumi. Mutuwan tsaye mutumin yayi lokacinda k'wayoyin idanunsu suka had'e. Ita kanta Amal seda taji wani iri a jikinta, tabbas bata mance fuska amma seji take a jikinta kaman ta ta6a had'uwa da wannan mutumi amma kuma ta rasa a ina. Shi ma on the other side kallon Amal yake na sosai ba tare da ya koda kyafta ido ba, ji yayi kaman sun ta6a had'uwa a wani gun amma duk yadda yayi ya kasa tuna a ina, da ya cigaba da kallon cikin idonta kuwa se gani yake kaman kansa yake kalla aciki there's something about her eyes that reminds him so much of himself, he sees himself in her. Wani irin mumunan tsinkewa gabansa yayi yayinda rayuwansa na da ya fara taho masa.

  "Nagode sosai Allah sak'a da alkhairi Baba" tace da shi kai yayi saurin kad'awa had'e da sakar da murmushin dole "Ba komai 'yata sannu Allah sawwak'e."

  "Ameen" ta amsa da murya chan ciki-ciki.
 
   "Ya sunanki?"

  "Amal Abdallah" ta sanar da shi haka kawai yaji gabansa na fad'i jin sunan mahaifinta.

  "Mahaifiyar ki fah?"

  "Jameelah Muhammad" ido ya rufe na k'ank'anin lokaci yana k'ok'arin composing kansa. Baze ta6a mancewa da wannan suna ba, ko a ina yaji sunan nan yasan sunan Jameensa ce amma kuma ai ba ita kad'ai bace Jameelah Muhammad a duniya ba, ze iya yuwuwa wata Jameelah Muhammad d'in ce. Amma idan kuma itan ce fah? Can it be? Noo da sauri ya kad'a kansa yana d'auke wannan mumunan tunani it can't be possible it can never be.

  Murmushi ya sakar wa Amal "Ko zaki bada lamban mahaifinki a kirasa?" Da biyu ya tambayeta hakan don jin mey zata ce idan har tace 'eh' ta basa that means ba shida alak'a da ita idan kuwa har tace ba na mahafinta se na mahaifiyarta that means zarginsa akanta ya tabbata kawai se yaji tace "Eh."

  Wani irin ajiyan zuciya ya sauk'e had'e da yima Allah godiya tunda har tana da mahaifi toh ba abinda yake zargi bane barka. Nan da nan ya zaro wayansa daga aljihu Amal ta irga masa lamban Papi wanda ya kira take bayan sun gaisa ya sanar dashi abinda ke tafe da shi inda Papi yace yanzu haka ma suna hanyan zuwa asibitin ne mijinta ya riga ya kira ya sanar da su.

   "Iyayenki suna hanyan tahowa sunce mijinki har ya kira ya sanar da su" yace da Amal. A lokaci guda zuciyan Amal ya buga to the mention of Afzal's name. Idan su Mami sunayi wa Allah kar su k'ariso nan da shi, bata k'aunan sake sanya sa a idanunta har k'arshen rayuwarta, baza ta ta6a mancewa da abinda yayi mata a rayuwa ba "Toh Amal barin je inyi settling bills naki in amso miki magunanki ko?"

  "Baba da ka bari ai kayi mey wuyan wannan ko iyaye na zasuyi handling dan Allah kar ka damu."

  "Ba komai 'yata kede Allah baki lafiya"

  "Ameen nagode Allah sak'a da mafificin alkhairi." da haka ya samu ya fice inda ya tura driver'nsa ya biya komai aka amso magunan sannan aka mik'awa nurse ta kaiwa Amal.

  "Nurse?" Amal ta kirata.

  "Na'am kina buk'atan wani abu ne?"

  "How about my baby? Cikin na nan ko ya zube?"

  "Cikin ki na nan baiwar Allah, an samu an tsayar da bleeding d'in tun kamin ya isa cikin mahaifarki ya 6ata cikin." Wani hamdala Amal ta sake "Thank you, k'afa na da hannu fa? Targad'e ne ko kariya?"

  "Targad'e ne duka biyu" Tasan zato zunubi ne amma tana da tabbacin Nazeefah is behind everything, na sosai ta duba kwalta kafin ta tsallake har yashe ne bata ga wannan mota mey uban gudu ba idan ba wai dama fakonta motan yake ba. Tana sake zargin Nazeefah ce behind this saboda duk yadda akayi taji batun tana da ciki ne daga bakin Safiyya shine take son rabata da abinda ke cikinta, k'arshe kuma idan har ba a bakin Nazeefah ko Safiyya ba ba yadda za'ayi Afzal yasan tayi hatsari.

  "Don't mention" nurse d'in tace da ita tana me tsamota daga duniyan tunanin data wula "iyayenki sun sake yin waya anyi musu kwatancan d'akinki yanzun zasu shigo" kai zallah Amal ta gyad'a mata sannan ta maida kallonta ga jinin da ke kan shigewa jikinta ta canula. Mamakin halin alkhairi irin na mutumin nan kawai take, yadda be santa ba, be san wani nata ba, be san daga ina ta fito ba amma har ya d'ibi jinin jikinsa leda d'aya da abu ya bata gaskiya ne na Allah basu ta6a k'arewa toh Allah ya sak'a masa da mafificin alkhairi.

****
  Dab su Papi sun zo shiga k'ofan ward nasu Amal suka tarar da Afzal tsaye bakin k'ofan da tashin hankali bayyane karara a fuskansa yana ganinsu ya nufe su "Papi-"

  "Dakata Afzal" Papi ya tsayar da shi ta hanyan d'aga hannunsa "Bana buk'atan jin komai daga bakinka, ka kira mu ka sanar damu abinda ya samu Baby mungode Allah saka da alkhairi kana iya tafiya dan babu wata alak'a kuma tsakaninka da Amal yanzu."

  "Papi dan Allah kar kayi mun haka dan Allah kar ka rabani da Amal I beg of you please."

  "Miss" Papi ya kira wata nurse. "Dan Allah ku janye bawan Allah nan daga nan."

  "Bawan Allah ba tun d'azu aka sallameka ba? Baka da appointment da kowa anan bazeyi ka shiga ba nan restricted area ne dan Allah kayi hak'uri ka tafi, yes Sir how can I help you?" Ta kewayo tana tambayan Papi bayan da ta gama da Afzal.
   Nan Papi yayi mata bayanin komai lamban wayansa ta amsa ta zuba cikin computer'n dake gabanta yana gama scanning ya nuna wayan da sukayi last da phone desk. "Bismillah kuzo in shiga daku."

  "Mami? Mami please don't don't do this please" Afzal yace da Mami lokacin da tazo shigewa ciki "Please karku hana ni ganin Amal" ko kallonsa Mami batayi ba bale tasan yanayi ciki akayi dasu akayi directing nasu zuwa d'akin da Amal take yayinda aka bar Afzal tsaye a waje.
   Kuka wane d'an yaro Afzal ya shiga yi a wajen, yau ina ze sa kansa idan su Papi suka raba sa da Amal? Ya suke son ya rayu idan ba Amal a ganga da shi? Taya suke son ya fara neman tuba idan ko kallonta bazasu barsa yayi ba? Yau ina ze jefa kansa? Tabbas ya tafka babban sokanci na k'in saurara mata da yayi lokacin da take son yi masa bayani, tabbas ya tafka babban laifi na amincewa da maganan Safiyya akan na Amal da ta kasance matarsa, ta ina ze fara bata hak'uri? Ta ina ze fara nuna mata how deeply sorry he is and how badly he's regretted everything he's done to her? Tabbas ya tafka babban kuskure a rayuwansa na amincewa da duk maganan da aka fad'a masa ba tare da ya gudanar bincike akai ba. Tabbas duk mey irin hali irin nasa yana tattare asara, masifa da kuma nadama.

  ***
    Tunda Alhajin yaji isowan iyayen Amal ya 6oye kawai se basa jikin sa yake Jameensa ze gani. Ba k'aramin tsinkewa zuciyansa yayi ba lokacin da yaga ana shiga da Mami da Papi cikin d'akin Amal.

  "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" kawai yake ta furtawa yayinda jikinsa yayi la'asar. Shekaru ashirin da biyu da suka wuce kawai yake tunawa, yau ina zai sa kansa idan gaskiya ta fito? Shikenan mutunci da girman da 'yan unguwa suke basa ze rushe, shikenan reputation na family'nsa ze rushe. Shin da wani idon ze sake kallon Hajiya Surayya? (Mummy'n su Nazeefah) meke shirin faruwa da shi? Shin yanzu Amal 'yarsa ce? Shin ciki ya shiga jikin Jamee bayan abinda ya faru a tsakaninsu? Wannan ne dalilin da yasa suka baro garin Askira? Duk da cewan blood group nasu da yazo d'aya ma babbar shaida ce akan cewa Amal 'yarsa hakan baisa ya amince ba. He needs to carry out a DNA test. Test d'in da ze tabbatar masa da cewan Amal jininsa ce ko kuwa a'a.

   "Alhj yanzu PA'nka ya kirani batun meeting da kake da shi da deputy governor" Driver'nsa ya sanar da shi.

  "Ohh haka zamu tafi ko?" Ya amsa yana k'ok'arin composing kansa.

  "Eh Alhj" daga haka suka kama hanya suka fice har anan Afzal na zaune bakin k'ofan akan wani benchi inda ya had'a kai da guiwa. Seda Alhj'n nan ya wuce Afzal ya d'ago kansa bisa ji da yayi an bud'e k'ofar a cewansa ma Papi ne yazo shiga da shi sede yaga ficewan mutum, zama ya cigaba da yi a wajen yak'i tafiya

****
   "Sannu Baby" cewan Mami.

  "Ya kikeji? Ya jikin naki?" Papi ya tambayeta.

  Kai ta gyad'a musu a hankali "Da sauk'i" ta amsa.

  "Ya Nurse meya sameta?"

  Ta samu internal bleeding sannan tayi losing blood sosai bisa ga fashewan da kanta yayi bayan nan kuma ta samu targad'e a k'afarta da hannu amma ba abinda ya samu lafiyan abinda ke cikinta." Da mamaki both Papi da Mami suka juyo suna kallon Amal da alaman tambaya bayyane karara a fuskokinsu.

  "Ciki?" Mami ta tambayeta "Baby kina da ciki?" Shiru tayi bata amsa ta ba.

  "Meyasa baki sanar damu ba Baby?" Papi ya tambaya nan ma shiru tayi "Kiyi magana kinji Mama na? Kar kiji komi."

  "Papi, Mami kuyi hak'uri kar ku d'au na 6oye maku wannan al'amari saboda wani dalili ne k'wak'k'wara nayi hakan ne sabida gudun da nake kar kuce zaku miyar dani gidan Yaya saboda wannan lallura."

  "Sam baza muyi miki haka ba Baby shin baki yarda dani bane dana ce miki se idan ke kika ce kina so zaki koma gidan Afzal zaki koma? Ki sani nida mahaifiyarki bazamu tilasta ki akan abinda bakiya so ba, sanin kanmu ne nan duka Afzal be kyauta miki ba so ki kwantar da hankalinki kinji? Allah ya inganta kuma."

  "Ameen Papi thank you."

  "Wata nawa ne?"

  "Sati uku ne kacal Mami" ta sanar da ita.

  "Allah inganta Mamana sannu Allah sawwak'e."
 
  "Shin har ya aka bigeki Baby? Baki kalli hanya bane kafin ki tsallake kwaltan?" Mami ta tambayeta.

  "Mami na kalla kinsan shi tsautsayi baya wuce ranan sa" haka kawai taji ta rufa wa Nazeefah asiri saboda tasan halin Papi muddin yaji Nazeefah na da hannu acikin wannan al'amari abu baze zo yayi kyau ba saboda ba Afzal kad'ai ba har su Ummi da Abba da ze shafa ita kuma abu da tashin hankali ne bata so. Tun da de Allah ya raba ta da su yanzu sede tace Allah miyar masu da anniyarsu.

   "Ermm Nurse" Papi yayi ma nurse d'in magana.

  "Yes sir?"

  "Nace shin meyasa baku kai ta regular ward ba? Gani nayi nan VIP ne."

  "Tabbas nan VIP ward ne."

  "Toh ai kud'in zeyi yawa kuma kin dega ba k'arfi muke da shi ba."

  "Kar ka damu da wannan sabida bawan Allahn da ya kawo 'yarka asibitin nan ya riga ya biya kud'in d'akinta har na sati sannan ya saye mata magunan da duk likita ya rubuta."

  "Subhanallah! Wannan wani mutumi ne haka?"

  "Bayan nan jinin nan da kake gani ma na jikinsa aka janye aka sawa 'yarku leda har d'aya da rabi."

  "Blood type nasu yaso d'aya?"

   "Tabbas duk O- suke."

   "Alhamdulillah Alhamdulillah amma dan Allah waye mutumin nan? Nasan godiya kad'ai baze biya abinda yayi mana ba amma dole ne inyi masa godiya."

  "Shigowanku ya tafi kuma bey ajiye mana wani identification card nasa ba yana biya ya tafi."

  "Allah sarki Allah sak'a masa da alkhairi ya biya sa da gidan Al-jannah."

   "Ameen" duka suka amsa "Tabbas na Allah basu k'arewa" fad'in Mami. "Amma Baby kinga mutumin ke?"

  "Eh Mami har nan ya shigo nima na basa lamban Papi."

  "Allah sarki baki san sa ba?

  "Gaskiya ban san sa ba amma se gani nake kaman mun ta6a had'uwa da shi."

  "Allah sarki Allah ya biya sa, zaki ji yunwa ai yanzu ko Baby?" Ta tamabayeta.

  "A'a Mami."

  "Kaman ya a'a Baby? Kin manta zaki sha magani ne bayan nan kuma kinsan dole seda cin abinci yanzu in ba haka ba abun cikinki baze samu lafiya da k'wari ba ko dan shi seki hak'ura kina cin abinci."

  "Bari inje da kaina cikin restaurant anan in sai miki abincin" fad'in Papi.

  "Toh Papi nagode."

  "Allah ya baki lafiya shine babba uwata." A bakin k'ofan ward d'in ya sake had'uwa da Afzal da har yanzu yak'i tafiya. Wucesa Papi yayi niyyan yi amma Afzal ya dakatar da shi ta hanyan shan gabansa cikin hawaye yace, "Papi dan Allah kayi hak'uri nasan nayi kuskure, nasan ban kyauta maku ba, na sani na ci amanar rik'on amanar da na d'au alk'awarin zanyi amma wallahi sharrin shaid'an ne Papi kafi kowa sanin yadda nake son Amal dan Allah kar ku rabani da ita I beg your pardon."

  "Kana son Amal? Meyasa bakayi tunanin hakan ba kafin ka ci mata mutunci ka walak'anta ta haka? Ka sani Afzal Amal tafi k'arfin a walak'anta ta, Amal tafi k'arfin kace zakaci mata mutunci" ransa ne ya mugun 6aci ya shiga d'aga murya se tunawa yayi a asibiti suke "Kaga a asibiti muke bazan so in d'aga murya in shiga hak'k'in wasu ba so tun wuri kafin ka 6ata mun rai ka fice anan."

   "Papi dan Allah kayi hak'uri, Papi I'm not asking for too much nasani abunda nayi muku will take much time to heal all I'm asking is ku barni inga Amal, dan Allah kar ku hanani ganinta please Papi."

   "Baza ka ganta ba Afzal, ganin Amal ne nace baza kayi ba maza ka kama hanya kabar nan tun kafin insa a koreka."

  "Bazan gaji da baka hak'uri ba Papi kuma koda kasheni za'ayi bazan fasa zuwa duban Amal ina baku hak'uri ba har se idan Allah ya huci zuciyanku" Papi be sake cewa da shi komai ba ya fice haka nan har Papi yaje ya siyo abincin wa Amal ya dawo Afzal be tafi ba. Se chan wajajen k'arfu hud'u da rabi ya mik'e yaje yayi alwala yayi sallah ganin ba mahalicci se Allah kuma ko min yaya ba barinsa su Papi zasuyi yaga Amal ba kawai ya d'ibi kansa ya fice. Police station ya wuce inda ya tattaro 'yan sanda sannan yayi gida dasu inda aka d'au Safiyya aka sata a mota se kuka take tana had'a Afzal da Allah amma ina idan shima ze sha wuya toh se ya tabbata ita da uwar d'akinta sun d'ana wuyan da ze sha. Daga gidan Amal suka wuce na Nazeefah inda ya tarar da ita zaune akan carpet na parlour ta had'a taguni tana ganinsa ta mik'e tsaye yayinda jikinta ya hau 6ari. Kallonta yayi sau d'aya ya kawar da kansa dan yadda yayi mata jina-jina da jiki ko ina a jikinta ya kumbura yayi pink dan azaba ga shatin belt kaca-kaca.

    Takawa yayi yaje ya sameta cikin rud'ani tace, "Dan Allah Ya Afzal kayi hak'uri na tuba dan Allah kar ka sake ta6ani."

  "I'm so sorry Nazeefah, I'm terribly sorry" ya bata hak'uri cike da d'aurewan kai tace, "Ya Afzal ni ya kamata in baka hak'uri please forgive me."

  "A rayuwa ba abinda na tsana kaman inga na miji yana dukan mance, musamman ma inga magidanci yana dukan matarsa, tun da nake ban ta6a sha'awan d'aga hannu in mari 'ya mace ba bale har in d'au abun zana in zaneta hasali duk mijin da naga yana dukan matarsa tsanansa nake sega yau kinsa na aikata abunda nafi tsana a rayuwata Nazeefah. It pains me alot ace yau na d'aga hannu na mari matata ban tsaya anan kad'ai ba har seda na zaneta ta tayar maga da jiki haka" yayi maganan had'e da d'aga hannunta yana shafa kan shatin belt d'in a hankali cike da tausayi "Kinsa na tsani kaina yau Nazee I so much hate myself for hurting you like I did amma kuma babban abinda kikayi yau shine na sanya ni tsanarki. I hate you right now Nazeefah, I hate the fact that I'm married to you, looking at you disgusts me right now. Na so ki Nazeefah, na so ki har cikin zuciyata son da bana tsammanin wani d'a na miji ze iya yi maki irinsa, akwai gur6in da ke kad'ai kika mamaye shi acikin zuciyata, gur6in da ko Amal bata isa tace zata mamaye sa ba amma se mey? Se keda kanki kika 6ata rawarki da tsalle kika sa na tsaneki tsanan da bana jin zan iya sassauta shi. Zaman ki a gidan nan ya k'are Nazeefah yadda kika rabani da Amal kema dole ne in rabu dake idan har zanyi ma Amal adalci, yadda kika fiddata daga gidan nan be kamata ace ke kin cigaba da zama ba."

   "Ya Afzal dan Allah kar kace haka I beg of you dan Allah kar ka sakeni idan ka rabu dani ban san ina zansa kaina ba bazan iya rayuwa ba kai ba, Ya Afzal I love you, I love you so very much" ta sanar da shi cikin kuka.

  "Nima bazan iya rayuwa bake ba Nazeefah, batin duk abinda kikayi mun, batin yadda nakejin na tsaneki yanzu know that I still love you, kin riga kin zame ga6a a jikina Nazeefah amma bazan iya cigaba da zama dake a cikin gidan nan ba looking at you everyday remembering what you did to my innocent Amal, I can't Nazeefah."

  "Ya Afzal dan Allah kayi hak'uri I'm terribly sorry wallahi na tuba dan Allah ka yafe mun."
 
   "No Nazeefah, you're never sorry, you're never sorry na sani tuban muzuru kikayi ba dan wai kinyi nadaman abinda kika aikata ba, hungo" yayi maganan had'e da janyo hijabinta dake kan couch "Amsa kisa" ba gardama ta amsa tasa "Na taho da 'yan sanda sunzo su d'aukeki."

  '"Yan sanda?!" Ta nanata yayin da gabanta yayi wani irin mumunan tsinkewa '"Yan sanda fa kace Ya Afzal? Dan Allah ka rufa mun asiri Ya Afzal dan Allah kar kayi mun haka" jikinsa ta fad'a had'e da zagaye hannayenta a bayansa tana kukan tsuma zuciya "Ya Afzal dan Allah kar ka bari su tafi dani bazan iya kwanan cell ba Ya Afzal I beg of you please don't do this idan tuban Amal kakeso in nema na amince zanyi hakan amma dan Allah kar ka bari 'yan sanda su tafi dani" shi kansa seda idanunsa suka cika da hawaye dan yadda ta rik'esa gam take kuka take kuma had'asa da Allah. Na sosai ta basa tausayi shima har cikin ransa beso hakan ba amma hakan ne kad'ai hanyan da ze iya sak'awa wa Amal abubuwan da Nazeefah sukayi mata. Hannu ya sa na k'arfi da yaji ya raba ta daga jikinsa "Securities!" Ya kira su Nazeefah bata tashi rikicewa ba seda taga matan polisawa suna dosan inda take wani irin rikicaccen ihu tasa had'e da fashwwa cikin wani irin kuka mey tsuma zuciya "Ya Afzal dan Allah kar ka bari su tafi dani Ya Afzal I'm deeply sorry please don't let them take me wayyo Allah Mummy na dan Allah kizo ki taimakeni Ya Afzal please don't let them take me wayyo Allah na."

   "Take her away" yace da polisawan hawaye na tsiyaya daga idanunsa hannu yasa ya share da wuri. Ihu da bori Nazeefah ta cigaba da yi bata kuma fasa kiran sunansa ba tana da had'a sa da Allah sede he's mind is already made up, ko juyawa ya kalleta beyi ba se hawaye yake ta zubarwa shima kaman ba na miji ba haka yana ji yana gani aka janyeta waje aka sata mota d'aya da Safiyya sukayi police station.
   Ga shi nan yau ba Nazeefah ba Amal daga kansa se kansa sauk'a yayi a wajen ya zauna kan kujera sannan ya shiga yin kuka tsakaninsa da Allah, kukan da ya rasa akan wa yake yi, akan Nazeefah ne ko akan Amal ne. Daga k'arshe ya gane kuka akan dukansu biyu yake. Kuka yake akan zafin rabuwa da Amal da kuma abinda yayi wa Nazeefah a matsayinta na matarsa. Be ta6a tsammanin Allah ze k'addaro masa da ranan da zeyi wa matarsa jina-jina kaman yadda yayi ma Nazeefah ba har yanzu zafin hakan yakeji, sannan kuma har ya sake turata kwana a cell tabbas yau rana ne da baze ta6a mancewa da shi ba a rayuwansa.

     Yunwa yake ji amma baya jin ze iya sanya komi a bakinsa tuna Amal nasa na kwance a asibiti rai a hannun Allah, ruwan zafi kad'ai ya iya sha ya watsa ruwa sannan ya kwanta. Da ya rufe idonsa se ya tuna da abinda mey shagon d'azu ya fad'a masa akan cewa kan Amal ne ya fashe acikin jini aka d'auketa aka sanyata cikin motan da ya yi agaji. Wayansa ya d'auko ya lalimo lamban Amal sannan ya shiga kiranta.

  ***
    Tana rigingine jikin gadonta Mami na bata abinci wayanta ya shiga ruri a hankali take juya kanta ta kai kan wayan gani tayi Habib Albi🌹💍🔐 na flashing akan screen d'in da hotonsa wanda tayi saving contact d'in da shi. Silencing wayan tayi ta bar shi ya cigaba da ruri, be dad'e ba Afzal ya shiga kira again kafin tayi silencing Mami ta tambayeta "Wa ke kira? Afzal ne?"" Kai zalla ta gyad'a.

  "Amma baida kunya shin mey ze kira ya fad'a miki?" Wayan na tsinkewa Afzal ya shiga kira again kashe wayan Amal tayi gabad'aya yanzu. "Kin san kuwa d'azu yana nan? Tun kafin mu shigo yake nan amma nurses suka hanasa shiga saboda restricted area ne nan d'in, haka har seda Papinki yaje d'ibo mana kayakin mu sannan ya tafi."

   "Mami dan Allah kibar yi mun maganansa I'm not interested."

  "Shikenan Baby yi hak'uri yi sauri ki cinye mu kwanta ki huta." Wajajen goma da rabi ta d'au wayanta ta kunna da sak'on Afzal ta fara cin karo ko bud'ewa batayi ba ta goge baza ta ta6a mancewa da kalan walak'ancin da yayi mata ba, in shaa Allahu ba abinda ze sake had'ata da shi idan ta samu sauk'i zatayi ma Papi magana a amso mata takardanta dan muddin Nazeefah na cikin gidan chan bazata ta6a komawa ba.

  *****
   GIDAN ALHJ ABDALLAH.

  "Khaleefah d'auko mun glasses d'ina a d'aki" fad'in Daddy lokacinda suke zaune duka a kan dining suna shirin karyawa. Mik'ewa yayi ya wuce d'akinsa ya d'auko masa sannan ya dawo yana zama wayan Mummy dake kan dispenser.

   "My phone Khaleefah" ta sanar da shi kaman wanda zeyi kuka ya mik'e a rayuwa ba abinda ya tsana kaman aike. "Wa ke kira?" Ta tambaya.

  "Number ne" ya amsa yana mik'a mata, swiping tayi ta d'aga "Halo Mummy?"

  "Nazeefah?"

  "Na'am Mummy."

  "Ina kika ajiye wayanki? Tun jiya ina trying numban ki switched off."

  "Mummy dan Allah ki taimaka mun."

  "Meya faru?"

  "Mummy a cell na kwana."

  "A cell! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" chak Daddy dake karanta newspaper ya tsaya haka Khaleefah ma dake shan tea.

   "A cell? Meya faru? Ina Afzal?"

  "Mummy shi ya kawo ni."

  "Innalillahi mey ke faruwa me kikayi?"

  "Mummy dan Allah kizo police station na Damboa road muke."

  "Toh gamu zuwa" tana sauk'e wayan Daddy yayi saurin tambayarta "Ya meke faruwa?"

  "Nazeefah ce wai Afzal ya kaita police station a chan ma ta kwana."

  "Police station?" Daddy Yayi exclaiming "Dalili?"

  "Nima bata fad'a mun ba kawai cewa tayi muje mu sameta achan Damboa road take." Breakfast da basuyi ba kenan duk suka mik'e suka duk'ufa cikin mota se police station.

   Suna isa akayi dasu 6angaren da su Nazeefah suke kuka tasa lokacin da ta gansu haka Mummy ma. "Nazeefah meya faru? Meyasa Afzal ya kawo ki nan? Mey kikayi masa."

  "Mummy dan Allah kuyi hak'uri Mummy I'm so sorry."

  "Meya faru Nazeefah?" Daddy ya tambaya.

   "Ya Nazeefah?" Khaleefah da har yanzu ya kasa amincewa da abinda idanunsa ke gane masa kirata.

  "Daddy laifi nayi masa, laifin da ni kaina ina jin kunyan sanar daku please help me out Daddy dan Allah kar ka barni in sake kwana acikin nan." Waya Daddy ya zaro ya kira Afzal bada dad'ewa ba ya d'aga.

   "Ka taho inda ka kawo Nazeefah yanzun ina jiranka."  Bacci yakeyi lokacin da Daddy ya kirasa yana sauk'e wayan ya koma baccinsa seda ya k'ara baccin kusan minti talatin sannan ya mik'e ya d'aga wayan nasa sak'o ya tura wa Amal ya miyar da wayan ya zarce bayi yayi wanka ya fito ya karya da corn flakes ya koma d'aki ya shirya tsaf sannan ya fito. Isansa police station d'in ya tarar da su Abba da Ummi har su Daddy sun kira su. Saidai ko alamun tashin hankali babu tattare da Afzal dalili kuwa yasan shine da gaskiya. Binsu yayi duka da gaisuwa sannan yasa aka fito da Nazeefah daga cikin cell d'in jikin Mummy ta fad'a tana kuka sosai yayinda Safiyya ta la6e a lungu tana kuka itama. Breakfast da ya siyo musu ya mik'a aka basu nan da nan suka karya a wajen sannan Abba ya tambayeshi meya faru.

   "Baki fad'a musu abinda kikayi bane?" Ya tambayi Nazeefah da jikinta keta k'yarma har yanzu. "Magana nake miki Nazeefah confess your crime, crimes if possible" sede ta kasa magana gyaran murya yayi "Tunda bazaki fad'a ba ni zanyi hakan. Mutane tayi hiring tasa aka kad'e Amal yanzu haka Amal na kwance a gadon asibiti rai a hanun Allah duk wai a sunan kishi."

  "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" salati kawai kukeji yake tashi a wajen. "Nazeefah?" Mummy ta kewayo tana kallonta "Da hankalinki? Yaushe kika fara kisan kai?"

  "Mummy dan Allah kiyi hak'uri wallahi sharrin shaid'an ne."

  "Sharrin shaid'an? Sharrin shaid'an?" Mari me kyau Mummy ta zabga mata cike da 6acin rai, wannan wani irin haihuwa ne? Taya zaka haifi d'a amma d'a ya gagareka? Ashe duk kalan nasihar da takeyi wa Nazeefah a wajen take ajiye mata abinta? take Ummi ta shiga tsakaninsu tana bata hak'uri.

   "Tarbiyyan da na baki kenan? Da abinda zaki sak'a mun kenan nida Daddy'ki? Wannan wace irin rayuwa ce?" Tuni ta shiga yin kuka yayinda Ummi ta cigaba da bata hak'uri.

   "Afzal kayi hak'uri" cewan Daddy "Dan Allah kayi hak'uri."

  "Hak'uri nayi Daddy amma Nazeefah must pay for what she did" har a nan Abba bece komi ba yana bayan d'ansa d'ari-bisa-d'ari saboda akan gaskiyansa yake.
  Wayan Nazeefah Afzal ya zaro daga aljihunsa ya kunna "Gashi da hannunki zaki kira mutanen da kika sa suka bige Amal kice musu suzo su sameki dai-dai bakin junction d'innan justice must be served for Amal." Amsa Khaleefah yayi ya mik'a mata nan ta lalumo lamban d'aya daga cikinsu tayi kaman yadda Afzal ya umarceta se kakkarwa take. Har anan mamakin ta Mummy take, sam ba irin tarbiyyan data bata ba kenan, kunya take ace ita ta tsuguna ta haifi gagararriyar 'ya kaman Nazeefah idan a d'an shekarunta zata iya sa a bige mutum gaba mey zatayi kenan?

   Yaran suna isowa bakin junction d'in sukayi mata waya nan Afzal ya d'au 'yan sanda uku a motansa suka fice tare da ita Nazeefar a gaban mota suna isa wajen ya umarceta da ta sauk'a tayi musu magana achan aka kamasu aka k'ariso dasu cikin police station d'in. Mummy se kuka take Ummi da Khaleefah suna bata hak'uri.

   "Officers ku hukunta mun su hukuncin dake dai-dai da attempt nayin kisan kai" Afzal yace da polisawan yana nuni da yaran da Nazeefah tayi hiring samari guda biyu. "Wad'an nan biyu kuma" yayi nuni da Nazeefah da Safiyya "Ka miyar dasu cikin cell ka kulle mun su I'll speak with my lawyer in shaa Allah justice must he served for Amal nan gaba ko akan mey bazasu sake yin ganganci ta6a lafiyar wani ba bama Amal kad'ai ba."

   Yana kaiwa nan ya juya ya fice kiransa Daddy yake amma ko ya juya bale ya sauraresa motansa ya shiga ya basa wuta.

   Kaf wajen ba wanda kansa ya mugun d'aure yake kuma cikin tsananin tashin hankali kaman Daddy da yaji Afzal ya ambaci sunan Amal a matsayin wanda Nazeefah tasa aka kad'e. Shin wata Amal ce wannan? Amal da ya tsince ta a bakin makaranta jiya ya kai asibiti ne? Shin Amal Abdallah ce kishiyar Nazeefah Abdallah 'yarsa? yau wani irin k'addara ne wannan? Wani irin fallasa ne yake shirin afkuwa masa? Wani irin badak'ala ne wannan? Ta inda Allah ze kamasa alhak'in Jamee da ya d'auka kenan? Fatansa d'aya ne Allah yasa Amal Abdallah ta asibiti ba 'yarsa bace idan kuwa har hakan ya tabbata 'yarsa ce nasa ya k'are that mean 'ya'yansa biyu suna auran miji d'aya kenan. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.





RANA D'AYA!
#RD

Love... King Miemiebee👄✨

15 comments:

Unknown said...

Kwamacala kenan! I can't wait 4 the other side of story, osheey Miemiebee Allah ya kara basira
Nazeefah kadanma kika gani

Unknown said...

Ameen 😘

Unknown said...

Thanks dear

Unknown said...

Wow, tanks dear Allah ya kara basira

Unknown said...

Wao bravo ,this episode was very much interesting, ay kadan ma kenan daga cikin abinda ya kamata Afzal yayi ma Nazeefa da safiyya .don ma kwana daya kenan acikin cell.kafin ya sauwake mata.miemie Allah ya kara basira d karfin ido

Unknown said...

Uw

Unknown said...

Ameen uw

Unknown said...

Ameen you're welcome 😊

Unknown said...

Chakwakiya inji bahaushe
Miemiebee u r damn gifted bby

Unknown said...

Chabdi ana wata ga wata....I can't wait to read the next page.
Thumbs up miemiebee

Unknown said...

Hugs and kisses 😘

Unknown said...

Awwn thank you 😘

Unknown said...

Gaskiya yayi muna hiran nagaba

Unknown said...

Miemiebee yaya Labarin BWMH?

Fatima said...

Woooh it has been long since i read this..amma fa nidae am still on nazeefa's side amma fa bnjin dadin abunda tayi ma Amal ba... Finally daddy yaga Amal.. Am sorry mummy u will be disappointed... Weldone miemie dear