Tuesday 6 December 2016

‘YAR GATA CE!

BY MIEMIEBEE
PAGE 06



        Yau Tuesday ya kasance ‘public holiday’ ba school don haka yaran duk ba wanda ya tafi school ko wannen su na a d’akinsu yana bacci. 7:00AM Zeezee ta tashi kamar meh alarm as usual ta fita tabar d’akinsu tayi d’akin su Ibraheem yau kuma, a kulle ta samu k’ofar don haka tayita knocking dan dolen Ibraheem yasa Omar ya bud’e mata.
   “Me kuma ya kawo ki nan?” Ya tambayeta in between hamma. “In kinsan fitina kika zo yi maza ki juya ki koma.”
   “Ya Omal zan kwanta ne.”
  “D’akin ku ba wajen kwanciya aiko?” Ibraheem yayi maganar fuskarsa rufe da pillow. Ganin zata soma masu kuka suka shigo da ita, a tsakiyar su ta kwanta tare da shigewa bargon Ibraheem. Tun tana shiru taga barata iya ba ta soma kiran sunan su, shiru suka mata wane basu jinta chan ta miqe ta nufa toilet tayi pupu.
   “Naaa gamaaa!!” Ta fad’a da k’arfi. Banza su kayi da ita se a karo na biyu Ibraheem yaja dogon tsaki. “Nifa shiyasa banason ta shigo nan, shegen k’azanta sekace farillah kullum se mutum yayi pupu da safe mschw! Omar jeka wanketa ka kuma tura ta waje ga teddyn ta.”

   “Ni wallahi-”
  “Kai wallahi meh?” Ibraheem yayi saurin katse sa “da ni kakeso in wanke mata? Lallai yaro will you stand up my friend!” A sanyaye Omar ya miqe se kumbure kumbure yake ya shiga bayin yana wani mata mugun kallo. Se da ta bari ya k’ariso ciki ta kallesa tace, “ni banashon ka, ba kai zaka wanke min ba.”
   “Mumu daman ni d’in nace maki ina sonki ne? Tsaya nikam na wanke miki bacci nakeji.”
   “O’o banashon ka tab’ani banasho!” Tasa kuka. Fitowa Omar yayi yaje ya samu Ibraheem yace, “Ya kaji wai bata son na wanke mata har kuka take.”
   “Toh da waze wanke mata? Ke Zeezee ki miyar da hankalinki kinajina koh?”
   “Ni kai zaka wanke min.”
  “Lallai yarinya zaki mutu da kashi a jikinki inde ni zan wanke miki”
  “Ya Ibyaheem na gama” tasa kukan shakwab’a.
  “Barta gun hau gado ka kwanta” yace da Omar haka suka barta zaune kan toilet sit da abin ya isheta tasa wani irin d’an iskan ihun da har su Baba seda suka jiyo ta. Ba tare da b’ata lokaci ba Baba ya tashi miqe, a zaton shi ma wai ko ita da Mariam ne ganin ba haka bane ya nufa b’angaren su Ibraheem, tsaye a d’akin ya iskesu suna raba ido. Kai kawai yayi nodding ya kira sunan “Zeezee.”
   “Baba! Baba!” Toilet d’in ya nufa ya sameta. “Ya haka K’anwata pupun yak’i fita ne?’
   “Ya Ibyaheem ne nace yamin tsarki yak’i.”
  “Yak’i tun yaushe?”
  “Tun d’azu.”
  “La ila! Ibraheem!” Ya kira sunansa a fusace, “Zo nan d’an banzan yaro kawai.” A sanyaye Ibraheem ya k’ariso cikin bayin. “Na’am.”
   “Nanata abinda ka gaya mata.”
  “Nifa bance mata komai ba.” Masifa sosai Baba ya masa harda make sa a k’eya sannan yasa sa ya wanke Zeezee tas harda yi mata wanka ya shirya ta tsaf sannan ya d’au K’anwarsa suka bar musu d’akin. Omar da dariya keson fin k’arfinsa se kare fuskarsa yake amman inaa seda dariyan yayi finding way nasa out.
 
    “Ma wa kake yiwa dariya?” Ibraheem yayi maganan in a serious tone.
  “Bb... Babu.” Yayi stammering.
  “Da yafi ma kam.”

****
  _Later during the day, 1:30PM_
    Zaune yaran da Maman su suke duk a tsakar gida kowa na harkan gaban sa. Gefe guda Zeezee ce rik’e da ipad nata se game takeyi a yayinda Yasmeen ke zaune gefenta itama duk ta zuba mata ido tana me kwad’ayin son buga game d’in itama.
   “Zeezee na baraki sammin ipad naki inyi game ba koh?”
   “Eh ba kin ce min Mumu ba d’azu.”
  “Toh ai kuma na baki hak’uri kuma kinga nima in Mama ta sai min nawa zan baki.”
   “Bana shon naki kowa ya riqe nasa.”
  “Zeezee yi hak’uri mana fad’uwa d’aya zanyi in baki.”
   “Sekin ce min Aunty Zeezee.”
  “Aunty kuma? Ni dake waye babba?”
  “Toh cikenan balin baki ba.”
   “Toh Aunty Zeezee bani toh.”
  “Toh ki tsaya mana in yi nima tukunah.” Duk maganan nan da suke Mama na kallonsu daga bisani tace, “amma ke Yasmeen Sokuwa ce wallahi, yanzu k’anwarki kike kira da Aunty akan banzan game?”
    “Ai kuwa sede Sokuwan kam” Omar ya mara wa Mama baya. Ibraheem da keson sa baki amman baison ruining plan nasa yaja baki yayi tsit.
   “Ai duk laifin Babanku ne, bari kema zuwa next week na kwashe adashe na in siya miki naki, ke kuma Zeezee kar kibar wannan banzan rowan kinji ba? Ki cigaba muga ina ze kaiki.” Harara mai rai da lafiya Zeezee ta galla wa Mama da dala-dalan idanunta kan zasu zubo a k’asa.

   “La’ila! Ni kike harara?” Mama tayi maganan tana k’ok’arin miqewa kenan Baba dake lab’e jikin k’ofa tin dawowan sa daga Masjid ya k’ariso ciki a hanzarce tare da dakatar da Mama. “Koma ki zauna” ya nuna mata gun zamanta da yatsa “da dukanta zakiyi sabida ban gida komeh?”
   “Baban Zeezee harara na fa tayi.”
   “Eh toh ai ke kika jawo da kikace mata marowaciya, yayyun nata ba duk haka suke ba suma?”
   “Lallai Alhj ka goyi bayan harara na da tayi kenan.”
   “Why not? Nide karki tab’a min K’anwa.” Kai Mama ta gyad’a continiously cike da mamaki “toh wallahi Alhj ka cigaba da b’ata yarinyan nan.”
   “Kanki akeji, kuma bayan nan meh naki dan Yasmeen ta cewa Zeezee Aunty? Ba sisters bane su? Ni na lura bakison Zeezee a gidan nan komi Yasmeen komi Yasmeen to kema ki cigaba.”

   “Me kake implying wai Alhj?”
  “I mean baki adalci mana, kinfi son Yasmeen kan Zeezee ko ke bakisan Zeezee ce auta ba?” Hannu Mama ta tafe sannan ta d’aura a waist nata “lallai har kura kece wa kare maye? Baban Zeezee kai baka ganin abinda kake ma Zeezee a gidan nan ne? Ai in akwai wanda ke partiality tsakanin yaran nan toh kai ne” ta  nuna sa da yatsa “mena siyawa Zeezee ipad kabar Yasmeen ba waya? Waye babba cikin su?”
   “Hafsah kinji na rantse duk abinda ya samu ipad na Zeezeen nan kece, dan bakin ki kad’ai ya isa yayi destroying ipad d’in kuma believe me idan hakan ya faru cikin kud’in adashen ki za’a sai mata sabo.”
  “Hmm Allah kyauta Yasmeen Mama na karki damu Tablet me kyau zan sai miki in shaa Allahu.” Da gudu Zeezee tayi wajen Baba ya d’agata “Baba kaji Mama koh?” tayi maganan a shagwabance.
  “Share ta K’anwata nasu tablet ne naki kuma ipad duk girman tab na Yasmeen bare kai naki ba ko kema kinaso a sai miki tab d’in?”
   “Eh” tayi nodding kanta.
  “Toh angama.”
   “Gaskia nima in ta haka a sai min tab d’in na had’a da waya na” cewar Omar.
   “Kai asuwa? Wai daddawa acikin kunu in kaga na siya maka tab agidan nan to kabar mugun halin kan nan ne.”

   “Shikenan Baba komi Zeezee komi Zeezee sekace ita kad’ai aka haifa a gidan.”
   “Kai! Ni kake gayawa magana?”
  “Bar shi ai gaskia ya fad’a” Mama tasa baki. “Kai nan da Zeezee ta harare ni ba cewa kayi batayi laifi ba don haka bar sa shima.”
   “Haka kikace koh? Yayi kyau muje d’aki Zeezee akwai dambun naman dana saya miki.” Mariam glutton jin an ambaci dambun nama ta lasa lips nata.
  “Yauwa Baba zaka siya wa Ya Ibyaheem machine?”
   “Machine kuma Zeezee? Me zeyi da machine?”
   “D’azu fyends nashi sukazo dukan su suna machine illa shi.”
   “Shi ya turoki koh?”
  “A’a Baba” ta kad’a mai kai. Juyowa Baba yayi yana kallon Ibraheem.
  “Kai ka turota ko?”
   “A’a fa Baba ka tambayeta kaji.”
  “So kake a siya maka machine kafara yawo a gari anyhow ko?”
   “Wallahi a’a Baba.”
  “Se a sai mishi ai tunda nasan da akwai kud’i a k’asa” cewar Mama.
   “Eh dake kina biya na salary ai dole kice da akwai kud’i a k’asa” ya watsa mata harara.
   “Baba dan Allah ka siya min wallahi barin na yawo a gari ba.”
   “Zeezee a siya mishi?”
  “Eh Baba” ta basa amsa.
  “Toh K’anwata anything for you” ya dawo da kallonsa kan Ibraheem “seka bari in na samu kud’i tukunah.”
  “Toh Baba nagode Allah ya dad’a bud’i.”
   “Ameen” ya amsa sannan ya fice.

_Few minutes later..._
    Mariam ce tsaye bakin k’ofan d’akin Baba tun ji da tayi an ambaci dambun nama ta kasa samun sukuni, gabad’ai kwad’ayinta ya shiga cikin dambun naman. Dabara ce ta fad’o mata tad’an yi baya da k’ofan kad’an ta shiga k’wala wa Zeezee kira ina irin tana nemanta ta bata abu d’innan.
   “Zeezee! Zeezee na!”
   Daga cikin d’aki Zeezee dake cin dambunta akan cinyan Baba hankali kwance tace, “Baba wancan ba mulyan Adda Mayyam bane?”
   “Nata ne shareta kici abinki nasan yanzu haka wayo take son miki.”
   “Zeezee!” Mariam ta cigaba da kiran ta.
  “Baba zanje” ta gwada yunk’urin sauk’owa daga cinyansa.
  “Tsaya tukuna. Ke Mariam!” Ya k’wala mata kira. Dum! Zuciyarta ya buga sannan ta amsa “na’am Baba.”
   “Me zaki bata kike wani kiranta haka?”
   “Baba na siya mata Awara ne.” Zeezee najin an ambaci awara miyan ta ya tsinke arayuwa tana son Awara.
   “Baba zanje, Adda Mayyam kar ki cinye ina zuwa.”
  “Toh kiyi sauri Zeezee ta.”
   “Toh Zeezee da dambun naki zaki tafi? Baraki ajiye anan ba sekin dawo?” Baba yayi maganar yana kakkab’e mata kayanta.
 
  “O’o zan je dashi.”
  “Toh karki ba wa kwad’ayayyun nan fa kinji ba?”
  “Toh Baba” ahaka ta fice ta tarar da Mariam tsaye bakin k’ofa, d’agota tayi kaman dagaske, “muje d’akinmu in baki ko?” with a nod takai Zeezee d’akinsu ta direta kan gado sannan ta shiga neman Awaran da bashi a d’akin, tafi minti uku tana nema har Zezee ta gaji da jiranta, “Adda Mayyam ina Awaran? Ni nagaji”
   “Na nan Zeezee ina nema ne” ganin Zeezee ta kusa cinye dambun nata dabara ta fad’o wa Mariam tace, “laaa Zeezee ashe Yasmeen da kwad’ayintan nan ta cinye d’azu amman kinsan meh? Muka fita Islamiyya I promise zan siya miki kinji beautiful Sis?” Kai Zeezee ta gyad’a mata tare da miqewa dan ficewa daga d’akin, ganin haka Mariam tayi saurin tare ta “toh Zeezee bara’a sanmin Dambun bane?” Kafad’a ta make “o’o.”

   “Aww ni in baki Awara ke ki hana ni Dambun ki? Nima inta haka na fasa.”
  “Toh ai baki bani ba.”
  “Zan baki ai Zeezee I promise.” Da k’yar ta sha kan marowaciyan ta bata.

~* ~* *~
   Bayan tafiyan yaran Islamiyya Mama ta fiddo da duka kayakin ta daga wardrobe da nufin gyarawa, Zeezee na a zaune kan gado tana kallon kowani move nata kasancewar Ipad nata yayi running outta charge. Sallaman Aunty Sis da Mama taji yasa ta bar duk abinda take ta fice da sauri dan taro wannan babbar bak’uwa. Nan fa uwar b’arna ta samu kanta, a nitse ta sauk’o daga kan gadon, ninkakkun kayakin Mama Zeezee ta shiga wargazawa tana warwarewa tana sa saura kusan minti ishirin Mama sukayi da Aunty Sis, koda ta tambayi ina Zeezee Mama tace tana ciki bari ta kirata. Haka Zeezee naji Mama na kirarta tak’i fitowa da k’yar ta fito daga baya. Aunty Sis wane ta cinye Zeezee haka kawai yarinyan ta shiga mata rai kamar yadda ta saba shiga wa mutane rai. Aunty Sis da son kyauta koda tazo tafiya seda ta d’au dubu biyu ta bawa Zeezee. Bayan tafiyan ta Mama ta dawo d’akin only to see the biggest suprise of her life.

  “Zeezee! Meh haka? Bakida hankali neh? Kayakin nawa kika ma wannan tabargaza?! Iyyeh!”
  “Mama bani bane.”
  “Ni ce ai tunda ba keba wallahi me hana ni dukan ki a gidan nan yau se Allah” kafin Zeezee tasa gudu Mama ta yi kanta ta shiga mammaketa, kuka sosai Zeezee tasa ganin ba mahalicci se Allah tayi shiru don kanta sannan ta kama hanyan bakin k’ofa seda taci ready sannan ta kira sunan Mama. Mama na juyowa Zeezee ta d’aga hannu ta seta ta tayi mata alaman ‘Uwaki’
   “Ke! Ni kika zaga? Zaki raina wa kanki wayo yau” Da gudu tabi Zeezee nan itama tasa gudu har sunkai bakin k’ofa kenan sega Baba shigowa, chak ya d’aga Zeezeen da tuni tasa kukan munafirci.
  “Ya haka Hafsah? Me kika ma Zeezee? Karki gaya min bin yarinyan nan kike.” Nan Mama ta labarta masa dukkanin abinda ya faru to her suprise Baba yace shi sam be yarda Zeezee ta zageta ba wai sharri take mata har maqora yakai Mama tace, “wallahi Baban Zeezee ka cigaba da goye ma yarinyan nan gindi wataran kaima barata barka ba, mu zuba da kai.”
   “Ba ruwanki nide karki kuskura kitab’a min k’anwa. Inba sharri ba wai har Zeezee zakice ta d’aga hannu ta zageki” A fusace Mama ta juya zata koma ciki Zeezee tace da Baba, “kuma Aunty Sis tazo tabani kud’i Mama ta k’wace wai zata siya wa Yasmeen tab dashi.”
   “Haba ita da Sultan suka zo?”
  “A’a tace ya tafi islamiyya.”
  “Hafsah!” Baba ya kira Mama data kusan shiga d’aki. “Ina kud’in da aka bawa yarinyan nan? Maza ki bata abinta ba naki bane.”
   Da tafin ta tajuyo tana kallonsu sannan tace, “LOL ni kuma me zan da dubu biyun K’anwar ka? Zoki amshi abinki.”

  ★★★
   Haka Zeezee ta cigaba da girma cikin *_GATA_* maras misaltuwa. Ko kad’an Baba bayi ganin flaws nata duk abinda tayi da dai-dai da ba dai-dai ba shi dai-dai ne a idonshi. Kuma duk abinda tace ayi shi akeyi machine da sabon wayan da tace asai wa Mariam da Ibraheem seda aka sai musu. Da yaran suka gano haka kuwa duk wani abinda suke buk’ata Zeezee suke samu suyi ta mata zak’in baki daga baya har Mama itama in tanason abata kud’in anko kokuwa na d’inki muddin bata son tab’a kud’in adashen ta Zeezee take turawa wajen Baba. Sede kafin Zeezee taje musu se sun sha wulak’anci harta Mama tace se Mama tace mata Aunty Zeezee tukun taje.
   Ahaka har yarinya takai 3 years sosai ta k’ara wayo ga kyau har na k’in k’ari in aka barni ma se ince tafi Mama kyau. Sede uban rashin kunya kan ba gobe, bata ganin kowa da gashin ido se Baba shi kad’ai ne in yace mata bari zata bari in bahaka ba sauran duk bata jin maganansu ciki harda na Mama.
   Mama kam dad’i kashe ta za’a sa Zeezee a school this year, ko a babu bakinta ze huta da surutu.
 

      CIKIN GARI.
   Kasancewar yaran sunyi hutun 3rd term a School, in aka koma yanzu new section zasu shiga ga kuma siyar da admission da ake yanzu a school nasun yasa Mama tsayawa dan sai wa Zeezee form a cika mata itama. Bayan isarta gida ta tarar da family’n ta zaune a babban parlour’n Baba kowa na harkan gabansa bayan duk sun bita da sannu da zuwa Yasmeen taje ta d’au mata ruwan sanyi. Tana shanye ruwan tasa hannu a jakarta ta ziro form data siyon “gashi Alhj form na siyo wa Zeezee se a cika mata gashi Yasmeen miqa wa Babanku.”
  “Form na wani school?” Baba yayi tambayan lokacin da Yasmeen ke miqa masa form d’in.
  “Ji Alhj da wata magana da na wani school zan sai mata? Na Havardth mana ba duk can yaran suke ba.”
  “Se kuma akace miki can za’a sa Zeezee? Nifa banason shishshigi wallahi, waya rok’eki? Waya saki siyo matan?” Attention na kowa ne ya dawo kan Baba fuskokin su duk d’auke da neman k’arin bayani.
  “Ban fahimce kaba Alhj.”
  “Ai baraki tab’a fahimta taba daman, toh I mean kinyi asaran kud’in siyan form d’in dan ba’a Havardth zan sa Zeezee ba.”
   “Ikon Allah wani school zaka sata?”
  “Wai ina ruwan ki? Tambayoyi sekace ‘yar jarida? When the right time comes you’ll know.”

  “Hmm! ba gaskia kam ai dole kak’i fad’a anyways tayi tsami ma ji.”
  “Wai ma tsoronki akeji ne? A LYS zan sata.”
  ”L meneh?” Mama ta kwararo manyan idanunta waje disbelievingly, ba ita kad’ai ba haka siblings na Zeezee mah.
  “LYS!” Yaran sukayi exclaiming in shock a tare.
  “Eh shi ‘yan bak’in ciki kawai, shi za’a sata.”
  “Alhj kasan me kake shirin yi kuwa? Kasan ko nawa ne fees na school d’in kuwa kake wannan magana?”
   “About N70k (dubu saba’in) fah” cewar Ibraheem still in shock.
  “Ina sane, shi yamin shi zan sa ta ba ruwan ku tunda bada kud’in ku bane.”
  “Lallai Alhj! Makarantan dubu saba’in sekace bamusan me zamuyi da kud’i ba? Ni wallahi ban goyi bayan shawaran nan ba. Yaran nan naga duk a Havardth suka fara karatu kuma shi zasu gama in shaa Allah, d’an dubu ishirin zuwa talatin gashi yanzu SS 3 Ibraheem ze shiga kuma naga ana karatu bawai ba’ayi ba amman kace Zeezee se makarantar dubu saba’in?!” ta k’are maganan still not believing whats happening.
   “Toh ni yanzu na ce miki dama ba’a karatu ne ciki? Kawai achan d’in nafi son insa Zeezee. Makarantan ‘yan gayu, makarantan masu kud’i ba kalan nasu Ibraheem da kowani d’an unguwa ke ciki ba. Harta ‘ya‘yan Sarkin Bauchi a LYS Academy suke.” Kafin Mama tayi magana Yasmeen tayi saurin fad’in “Baba nima asani.”
  “Ja chan tsohuwa dake kawai! Kamar yadda sauran ‘yan uwanki suke Havardth kema chan zaki cigaba.”
  “Oh ni Hafsatuu! Partiality a filin Allah haka! Nide kar a zo ana cemin ba’ada kud’i aga ko I will care dan makarantan 70K kam ba abin wasa bane.”
   “Kanki dana yaranki akeji K’anwata de LYS zata shiga ko kuna so ko baku so ‘yan bak’in ciki kawai instead kuyi rejoicing za’a k’anwarku a School mekyau se uban kishi da hassada koda shike ba laifin ku bane halin Mamanku ne.”

****
   Washegari bayan sun gama breakfast Baba yasa Mariam tayi ma Zeezee wanka tsaf ita de Mama nata ido ne. Bayan an gama shirya ta cikin leggings and armless top nata suka fita chan akayi mata passport sannan ya wuce dasu New GRA, LYS Academy inda ya siya mata form. Washegari suka koma inda akayi mata interview, yarinya da uban baki duk abinda aka tambayeta ta sani Baba se dad’i yakeji ana yaba K’anwarsa ana ce mata zatayi ilimi.

                _One Week Later..._
     CIKIN KASUWAN CENTRAL, BAUCHI.
  Zaune family’n Alhj Isma’il Yosouf suke cikin wani babban shagon da ya kasance mafi girma cikin kasuwan. A gobe zasu koma makaranta shine sukazo yin shopping. Kowa an sai mai jaka d’aya takalmi d’aya seda dozen na socks banda Zeezee da aka sai mata school bags uku had’ad’d’u, takalma ma uku da dozen na socks masu uban kyau guda uku suma. Itade Mama ba abinda take banda kallon Baba dan kuwa yafi k’arfinta yanzu. Bayan nan suka wuce shagon provisons juice carton-carton kala uku ya d’au wa Zeezee ba a maganan chocolates da sauran snacks, shopping de kaman ba gobe yayi wa Zeezee bayan isansu gida duk suka fiddo da kayakin kowa ya shiga gwada nasa yana jin dad’i sede any moment suka tuna komi na Zeezee yayi tripling nasu se sujiyo tokari a zuciya amman ya suka iya? Zeezee *_‘YAR GATA CE!_*


   *© MIEMIEBEE*
  👄👄👄👄
   www.beeenovels.blogspot.com

2 comments:

Anonymous said...

fatan alkhairi

Anonymous said...

09060223328