Sunday, 20 November 2016

HEEDAYAH!


                1⃣1⃣2⃣
   written by miemiebee👄



        Haka rayuwa ta cigaba da kasance ma wannan masoya guda biyu in suna gda suna makale da juna in kuwa yatafi office suna video call, ba ruwan don moha da matan larabawa. Heedayah kuwa cikinta se girma yakeyi yanada k'imanin 8 months ynxu knan dan kuwa sunyi 5 months a Dubai yanzu haka. Ta cika dam! cikin nan kaman ba shi ba gawani uban cin datakeyi kowani month kuwa se sunje sunyi scanning baby'nsu baruwansu da fad'a, ya hanata yin aikin komi gudun kar wani abu yasamu lfyrta da baby'nsu, komi shi yakeyi ita nata kawai ci ne. Siyayya kam sekace na 'yan hudu ko 'yan biyar. Dozen na akwatuna ya cika da kayakin babies da toys ba abinda babu.
       Tunda cikin heedayah ya cika 8 months 1 week don moha ya fara mgn komawa 9ja dan yafison ta haihu acan yadda mummy da ummu jalila zasu kula masa da matarsa mgn yayi da C.E.O'n yace ba komai zasu iya tafia Allah kuma sauketa lfya inhar dawowansa beyi ba kuwa yanada branch na company nasa a kano yaso seya mai transfer dad'i sosai don moha yaji ya masa gdy sannan suka rabu. Flight of return yashiga musu booking suka samu 3 days after... Se shirya kayakinsu yake musu kowani yammaci kuwa se sun fita strolling in sun dawo ya mata massaging kafafunta. Kamar da wasa ranar tafiyan su heedayah ya iso tun safe ya kai motar office sannan yadawo da taxi guda biyu d'aya yasa kayakinsu d'aya kuma suka shiga a daidai airport suka tsaya bada jimawa ba jirginsu ya iso saidai kam sunyi excess luggage har na fitan hnkl.
         Tafiya me nisa sukayi heedayah tayi bacci ta tashy ga wani kumburin da kafafunta sukayi hakan ma dan 1st class suka shiga ba economy class ba. Se can dare suka iso 9ja safyan ya daukosu ya kawo su gda sannan ya fice, dama already ummu jalila tasa sister'nta ta yi shara da mopping da 'yan goge goge, abinci suka kawo musu tare da musu sannu daxuwa. Ummu jalila se kallon heedayah takeyi dan yadda cikin yayi kato tawani k'ara kiba cewa tayi "wannan ciki kam sede 'yan biyu" heedayah tace "toh ummu jalila d'an d'aya nede", ta tab'e baki sannan tace "amman kam na miji ne, kin ganki kuwa heedayah? Kinfini girma ynxu" Don moha yace "bawaninnan karki jita kinji maman baby na? Bawani kiban da kkayi ni naga kin rame ma", heedayah tace "yawwa my mr romantic" hira kadan suka tab'a sannan sukayi seda safe wa juna. Abincin suka ci suka watsa ruwa sannan suka kwanta agaje washegary sanda suka makara asuba.
         Breakfast mummy da nanny suka kawo musu suma se mamakin girman cikin heedayah suke yadda yake da kamar bareyi girma ba, mummy tace "abinci kke ci sosai ko? Ai kicigaba zakiyi bayani a labour room", heedayah ta shakwabe fuska "kai mummy kidena bani tsoro mana". Hira suka sha sosai sannan su mummy suka tafi cewa zuwa anjima nanny zata dawo ta xauna dasu tana kula da heedayah tunda tayi nauyi yanzu. To maghrib nanny ta iso d'aya daga cikin d'akunan heedayah ta bata d'ayan d'akin kuwa washegary don moha ya kawo room planners aka fara shirya wa baby d'aki.
         Tun nanny na jin kunyan ganin abinda don moha da heedayah keyi har ta saba dan agabanta se suyi kiss abinsu ba kunya. Bayan sati biyu da dawowarsu rana d'aya heedayah na zaune a parlour tana game a ipad nata da wuraren karfe 12:00PM  na safiya haka ranan juma'ah tasoma jin ciwo daga karkashin mararta abu kamar dawasa se worse yakeyi kafin ace me yakaiga ko tashy bata iya yi se aukin kuka gashy mr romantic nata bai gda yatafi office. Ihu ta tsala wanda ya birkita nanny dake kitchen tana had'a musu lunch da sauri tabar abinda takeyi tafito taga heedayah zube a k'asa se juyi takeyi da hannunta kan cikinta, da sauri tayo kanta "heedayah ya haka? Ko lokacin haihuwar ne?" heedayah dake ta juye juye tace "ki kira min muhammad" nan da nan nanny ta kirasa sannan ta kira mummy atare suka iso a lokacin heedayah  se kuka takeyi tana ihu tana "wayyo xan mutu!" Asibiti suka nufa da don moha da heedayah da mummy, nanny kuwa ta tsaya had'a kayan baby sannan suka taho da ummu jalila. Tajima a labour room amman ina takasa haihuwan har karfe taran dare ana abu d'aya kwata kwata batasan ma ina take ba dan azaba don moha kuwa ko minti d'aya be iya yayi a d'akin ba dan tausayin da ta basa se kuka takeyi tana ihu shima tuni yaji kolla ya ciko masa a ido alwala yaje ya dauro se nafilfilu yakeyi yana rokan Allah sa matarsa ta sauka lfya. Haka fa suka kwana a asibitin heedayah bata haihu ba washegary ma still dsem thing, haka suka jera kwanaki uku a asibitin ba labarin haihuwa, daga karshe doctor'n yace sede a mata operation dan kuwa baby'n yayi girma dayawa sesa ta kasa haifosa, da kyar don moha ya yarda yayi signing papers din nan ma da mamansa ce tasa baki in bahaka ba shi baison a tsaga masa matarsa.
          Yana signing aka shiga OR da heedayah don moha kam kuka kamar shine me haihuwan. Awa d'aya sukayi cikin OR din sannan red globe din ya d'auke daidai nan dr'n yafito yana cire abin daya toshe hancinsa dashi don moha ne yafara shan gabansa yana "dr how's my wife? How's she?" Murmushi dr'n ya masa sannan yace "the operation was a success your wife has delivered a bouncing baby boy" wani hamdala yayi harda hugging dr'n su mummy duk se murna sukeyi. Dr yace mijin ze iya shiga ganin matarsa da sauri ya shiga yaga heedayah kwance kan gadon da drip a hannunta gefenta kuwa wani kyakkyawan hallita ne wajen ya nufa ya d'au jaririn sede ace tubarkallah baby'n kato ne ga kamanninsa sak na don moha ba abinda ya rage kiss yabasa a kumatu sannan ya matso kusa da heedayah dake kallonsu tana murmushi a wahale zama yayi agefenta sannan ya bata kiss itama a goshi tare da fad'in "thank you my baby, thank you for the blessing, sannu ko?" yana mgn yana matso mata da baby'n kusa kallon baby'n take tana mamakin girmansa sekace wanda yayi arba'in murmushi tayi sannan tace "mummy is right, our baby is huge" murmushi shima ya mata yasake bata wata peck a kumatu, tace "nd our baby looks exaclty like you!" Nan   ya ciro wayarsa ya kashe musu selfie nan mummy da sauran suka shigo harda guntun masifarta "aww se a dauki 1st selfie da baby ba kakaninnsa" nan ta karb'e baby'n se kallonsa suke sekace d'an larabawa kyau kam masha Allh yadda daddy'nsa keda kyau shima haka yake ga gashi sekace na mace. Dabino mummy ta tauna tasa masa a baki se lumshe bakin yake wch is damn so cute! Can grand daddies guda biyu suka iso suma se albarka suke tasa wa yaro kafin ace me mgn ya zagaya both families kan heedayah ta haihu.
            Washegari aka sallamo su heedayah se wani lallab'ata don moha keyi. Nan fa aka rasa wa zeyi ma heedayah arba'in dan mama da mummy sunnace su zasu ma 1st jikansu arba'in daga karshe akace dukansu biyu se su mata in yau wannan yayi ma baby wanka washegary se d'aya ta karb'a. A d'akin heedayah suka sauka. Tun daga ranan aka hana heedayah ganin don moha wanda ba karamin ci musu rai yake ba suda suka saba kullum suna mak'ale da juna in har sun had'u to heedayah ta saci idan mummy da mama ne sede video call da sukeyi nan ma se in basu d'akin ne. Sati ta d'auka sannan ta samu full recovery nanne aka sa ranan da za'ayi naming ceremony sede har ynxu Father don moha yak'i gayawa kowa name da zesa wa baby'nsu cuz yanason yyi suprising nasu ne ciki har da Mother heedayah!

No comments: