Sunday, 20 November 2016

HEEDAYAH!


                1⃣0⃣3⃣
   written by miemiebee👄


         "Well bara kisha bane?" Kai ta gyada masa, tasowa yayi dgsk ze d'ura mata kuka ta fashe masa dashy "don moha baran iya shan mganin ba pls dont force me too", yace "mesa bara kisha ba? Kin gommaci kita vomiting life naki out? Yau fa sekinsha maganin nan", volume na kukanta ta kara tana hada sa da Allah. Ran don moha in yayi dubu be baci ba "shknan since u prefer to stay sick i'll let you", yana kaiwa nan ya fice tare da banging mata kofar sanda taji tsoro. Har ynxu kukan take da kyar ta iya tasha tea'n nd alhmdulillah bata harar ba. Bacci tayi me kyau se kusan maghrib ta tashy ta dafa indomie tana zaune a d'akinta tana ci tajiyo amai, dagudu ta ruga bathroom tana cikin yi don moha yashigo bathroom din yatayata wanko bakinta da kyar take takawa dan wani jirin dake dibanta akan gado ta baje.
       Moha yace "baby mesa kke da taurin kaine? Mesa bara kisha magani ki warke ba, kullum cikin amai kga bakida ma karfin zama, there must be a reason dayasa bakisan shan maganin tell me, are u really pregnant?" Heedayah tace "wani erin mgn kakeyi ina zan samu ciki nifa na gaya maka am not pregnant". Don moha yace "then mesa barakisha maganin ba?" Shiru tamasa bata ce komi ba. Yace a zuci inma cikin ne dake kke boye min I'll found ouf myself, goodnight peck ya bata take tasa hannu ta goge, murmushi yamata yafice dakinsa. Cikinta ta rike "baby why are u giving ur mum a hardtime? Is it bcux I dont love ur father? Pls am sorry if u continue like this baranzo in iya ba", isha ta idar da kyar ta kwanta.    
           Washegary ta tashy da kyar ta shirya office bayan aman datayi sekace aikin dole, d'akin don moha ta shiga har ta dau key bejita ba sanda tazo rufe kofar yajiyota tashy yayi da sauri ya nufa kanta key'n ya kwace, "ahaka zakije office din yau? Kalleki ko karfin kirki bakida, ure not going anywhere!"  Heedayah tace "seka hanani ai, thank god ba motarka bane kadai means of transportation", bakin kofa ta nufa da sauri don moha yasha gabanta key ya juya a bakin kofar, sannan ya zaro "lets see ta ina zaki fita yau" back door dinma rufewa yayi sannan ya nufa dakinsa. Ashar heedayah ta riga durawa.
      Around 10:45AM don moha yatashy bayan yayi wanka ya nufa dakin heedayah ya sameta kwance bargon da ta dukunkune kanta dashy ya yaye iya face nata dakyar take bud'e idanta hannu yasa ya tab'a tempreture'n jikinta yaji kamar wuta. Custard yaje ya had'o mata da kamar barata karba ba amman dan yunwan da takeji ta amsa, kwata kwata spoons biyar tayi shima ta harar take. Tana jingine a jikin gado don moha yace "heedayah look at me, ure pregnant isn't it?" Yauma answer'n jiya takuma basa ba yadda beyi da ita ba kan ta gaya masa gaskia amman tak'i.
         Acikin sati heedayah ta zube takoma kamar k'ashi da rai ba abinda yake zama a cikinta komi taci seta harar, office kam ba labarinsa. Around 4:15PM don moha na zaune a parlour ya tara kayan k'olama a gabansa erinsu tuwon madara, gullin tsiya, tsamin gaye... Ba abinda babu yana jiran fitowar heedayah. Karap! ta bude kofar dakinta da tafiyan ta kamar wanda koi ya fashe ma a ciki, fridge ta nufa tasha ruwa tundaga dining space ta hango abubuwanda suke gaban don moha kawai taji kodayin ta ya shiga har zataje ta dauka sekuma wata mind tace mata "dont u get it, don moha is playing games with you. Yanason yasan ko kinada ciki ne, nd the moment kka je kka dauka shknan ze sani", mind nata tabi da kyar ta iya had'e kwad'ayinta ta nufa d'akinta don moha na binta da kallo. Yace kinmin wayo knan dont worry I have a bttr plan in store for you.
        Kash! Sede duk plan da don moha yake setting heedayah is always one step ahead of him. Rana d'aya bayan don moha ya dawo daga masjid har ya kai bakin kofan dakinsa se wani abu yace yaje ya duba heedayah dab yakaiga bud'e kofar seya jita tana kan waya tana fadin "ai baran tab'a gaya masa ina d'auke da cikinsa ba, I don't love him ni rayyan nakeso..." Haka ya kasa kunne yana sauraronta kap duk abinda ta fada yajita, take idanun sa suka kad'a sukayi ja, zuciyarsa tana me masa rad'adi. Tana gama wayan ta bud'e kofar, gabanta ne ya mumanan fad'i ganin yadda don moha ke kallonta dagani yajiyo duk abinda ta fadi hannunta yajawo ya zaunar da ita kan kujera a parlour. Ba abinda heedayah keyi se raba ido, don moha yace "so its true ure carrying my baby? Nd kka min karya that ure not pregnant?" Zatayi mgn yace "shush! Am tired of listening to ur lies, ko Allah ma sheda ne heedayah tunda kkaxo gdan nan ban taba hurting naki ba abinda kkeso shi nake miki, abinda nakasa ganewa har yau shine mesa kkayi hating dina haka? What have I done to you da kka gommaci ki kuntata min heedayah, ace you are pregnant but kkayi deciding to keep it to urself toh yau Allah ya gano dani gaskia, barin ce zan kai karanki gun mummy ko ummu jalila ba as if u do good kayi wa kanka anytime kke needing abu just let me know nd no matter me kka min know that i'll always love you" yana kaiwa nan ya fice zuwa dakinsa. Heedayah da tuni zuciyarta ta karye tayi karfin halin fad'in "toh se meh dan kasani it still wont change a fact btw us bana sonka muhammad rayyan nakeso".
        Tun daga ranan word be sake had'a heedayah da don moha ba kwata kwata yafita daga harkanta, itama haka ba wanda yake cema dan uwansa ko uffan haka suke kwana su tashy. In sukayi bak'i kuma se suna pretendn as if they are on good terms, ummu jalila kuwa koda ta tambayi don moha about pregnancy'n heedayah ce mata yake shima be sani ba. Yana zaune a parlour aka danna doorbell yana bud'ewa yaga shams ba karamin mamaki tabasa ba "yanzu don moha heedayah ka aura? Bayan ina raye, mesa xaka min haka don moha kasan fa inasonka wlh wannan aure bata dauru ba dole ka saki heedayah ka aureni, ina raye barin bari wata ta mace ta mallake ka ba", don moha yace shams "what are u doing in my house? In ma wani ne ya turoki dan ki rabani da heedayah to baki isa ba". Shams tace "haba don moha after saying kanaso na zaka aureni sekazo ka auri heedayah? kace min after 2 mnths da bikinku zaka kawo ni gdanka amman har yau shiru, kana ganin ka kyauta knan?" ras mgnan ya fad'a kunnen heedayah data zo dining shan ruwa "what is she saying?" Lekawa tayi taga shams "Innalillahi so for all dis while don moha is cheating akaina, yakuma rasa da wa xeyi seda shams", gun ta nufa ta tsinke shams da mari don moha na ganinta bece mata komi ba. "Its really true bakida shame shams, ure a disgrace to all women, to in baki sani ba kisani yau don moha ba class naki bane, he's never gonna be urs tun kafin raina ya baci in miki abinda bakiso ki tattara kazaman kafafunki kbr min gda b4 raina yabaci inyi kasa kasa dake anan", ta dawo da kallonta kan don moha "get rid of this trash" tana kaiwa nan ta koma dakinta. Kuka ta fashe da ni miemie nace toh kukan meh? Bayan ke kkace baki sonsa, lalle kam heedayah akoi kishi.
            Me gadi don moha ya kira dan shi bare iya taba taba shams ba,waje aka jata tace "ko ma me de na cimma burina am sure heedayah barata yarda taxauna dakai a gdannan ba, since I can't have you no one can have u either!" Da sauri ya nufa dakin heedayah dake kuka tana ganinsa ta share hawayenta yace "heedayah dont tell me kinyi believing abinda shams ta fada dazu, shes just making up stories ai kema kinsan I'll never do that to you so take kawai ta rabamu nd ure allowing her to do that by agreeing to what she said". Heedayah tace "shut up! U liar, Don moha Allah ya isa tsakani na dakai daman all men are cruel bakuda imani after getting me pregnant ynxu kaje kana flirting awaje ka kuma rasa dawa xakayi seda shams?" Hannu tasa ta goge hawayen dakeson fito mata "anyways damuwanka kaga dama ka aurota kai kasani iyaka in abinku ya isheni in tattara kayakina in bar muku gdan ne". Don moha zeyi mgn heedayah tace "i've heard enough leave my room, now!"

No comments: