Saturday, 6 October 2018

RANA D'AYA!

BY MIEMIEBEE
PAGE 46




    Washegari...
Hayaniyan da Daddy ya jiyo a kitchen ne ya sanyasa fitowa daga d'aki inda yake kwance. Mami ya tarar tsaye gun sink ko mey takeyi oho.

  "Jamee na mey kuma kike yi?" Ya tambayeta tsaye daga bakin k'ofan.

   "Oh Alhj!" Ta juyo a d'an razane "Har ka tashi ne?"

  "K'aran kwanukanki suka tadani" ya sanar da ita.

  "Ayya yi hak'uri inzo in mayar da kai baccin ne ko zaka koma da kanka?"

  "Ko d'aya tambaya nake mey kikeyi?"

  "Oh! Doya nake ferewa Abba kasan bey karya ba."

  "Inji wa? Ai da kin tambaya, tare aka siyo mana breakfast d'in nasa mey gadi ya kai masa nasa se inde zaki site nasa ku gaisa."

  "Allah sarki nagode."

  "Jimin matan nan fa godiyan mey kuma kike mun? Dan na ciyar da Abban mu? Taho mu koma d'aki" ya k'are had'e da mik'a mata hannunsa murmushi cike da kunya ta saki sannan ta mayar da kayan aikin ta k'ariso ta mik'a hannunta ta sanya acikin nasa, janta yayi izuwa d'akinsu had'e da zaunar da ita kan gado. Cikin wardrobe nasu ya nufa ya d'auko wani package sannan ya dawo ya zauna a gefenta.

  "Hungo" ya mik'a mata.

  "Mey wannan?" Tayi saurin tambaya.

  "Kede bud'e ki ga" ba tare da yin gardama ba ta amsa ta bud'e d'an kunne ta tarar aciki k'waya d'aya. "Ko na waye wannan Alhj?"

  "Bazaki iya tunawa ba?"

  "A'a gaskiya" ta amsa tana kad'a kai amsa yayi daga hannunta yace, "Kin tuna rana na uku dana fara d'auko ki daga makaranta muna tsaye a k'ark'ashin makeken bishiyan chan muna hira muna shan rakke chan kika ta6a kunnenki kikaji ba d'an kunne? Muka ta nema amma muka rasa?"

  Murmushi take sosai cike da mamakin yadda akayi har yau Daddy be mance da wannan rana ba bayan ita da ba don ya tuna mata yanzu ba ta riga ta mance da shi shaf. "Toh ai bayan dana raka ki gida na dawo na cigaba da nema ashe ma ba a wajen ya fad'i ba tun a bakin makarantar ku ya fad'i."

  "Shine ka adana har yau Alhj?"

  "Kamar yadda na adana soyayyarki a cikin zuciyata na tsawon shekaru ashirin da biyu." Ya amsa nan take.

  Mamaki ne ya mamaye Mami gabd'aya ta rasa na cewa chan ta kira sunansa inda ya amsa a take "Alhj idan har kana so na haka toh meyasa ka gujeni? Na fahimci kayi mun abinda kayi ne saboda ka rama abinda Umma tayi maka amma meyasa ka kujeni? Meyasa ka daina d'aukan wayana?"

  "Duk da hakan ma be kamata inyi miki abinda nayi miki ba Jamee amma a lokacin shaid'an ya riga ya rinjayeni I'm terribly sorry."

  "Komai ya riga ya wuce Alhj ka daina neman tuba na."

   "Nagode Allah yayi miki albarka."

  "Ameen Alhj baka amsa min tambayan danayi maka ba."

 "Kinsan wani sa'in mutum baya sanin muhimmancin abinda yake da shi se idan ya rasa, da fari nak'i in amince da cikin Amal nawa ne saboda tsoro da nake kar in 6ata wa mahaifina suna acikin gari, kowa ya sani mahaifina sanannen malami ne ba k'aramin zubar masa da mutunci zanyi ba idan har na amince da cikin cewa nawa ne. Tsoro ne yasa na gujeki Jamee, na d'au bayan da nayi nesa daga gareki zan iya mancewa dake, na d'au yin hakan ne ze fiye mun kwanciyan hankali ashe sam ba haka bane. Tun bayan da nayi cutting off conact dake da duk wani nawa rayuwata ta dame, acikin k'unci nake kwanciya in tashi har seda Allah ya shigo mun da Surayya cikin rayuwata, wacce ta yaye mun duk wani bak'in ciki nawa take kuma bala'in tuna mun da ke ta kowani 6angare. Duk da hakan saide idan ban kwanta ba Jamee senayi mafarkin ki, lokacin da na fara neman layinki kuma se yayita cemun switched off."

  "Ba shakka nakega lokacin da muka bar Askira ne Abba ya buk'aceni da in yasar da sim card d'ina ze sai min sabo."

  "Tabbas ma hakanne, saide duk da hakan ban kariya ba kullum se na gwada layinki amma baya shiga, a wannan lokacin ne na tabbata da cewa guje miki da nayi shine babban kuskuren dana tafka a rayuwa na, a wannan lokacin na tabbatar da cewa akwai gur6in da kika mamaye a zuciya na, gur6in da se ke ne zaki iya cike mun shi. Lokacin da muka dawo Nigeria na koma Askira don nemanki inda ake tabbatar mun da cewa Allah yayi wa Abba da Umma rasuwa."

  "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un Allah ya jik'an su da rahama a tunani na gabad'aya wanda ka kaini gunsu sune iyayenka."

  "A'a wan Abba ne da matarsa."

  "Allah sarki."

"Daga chan se na wuce gidanku inda ake cemin kun bar garin Askira da dad'ewa kuma ba wanda yasan inda kuka dosa nayi cigiyarku har na gaji amma rana baya ta6a wucewa ban yi tunanin wani hali da yanayi kike ciki ba. Please forgive me Jamee."

  Hannunsa ta d'au ta had'a da nata tana murzawa a hankali "Alhj komai ya riga ya wuce wannan d'an kunne kuma zan cigaba da adana shi as a symbol of my love for you" Murmushi ya sakar yana mey jin dad'in abinda ta fad'a sannan ya janyo wayanshi "Bari in kira Hjy Surayya muji daga gareta."

  "Gaskiya ya kamata."  A karo na farko Mummy ta d'aga wayan inda suka gaisa. "Kun jini shiru ban kawo muku breakfast ba ko? Wallahi Khaleefah ne yamun tsiya na sa Alarm a wayana kawai ya saci ido na ya d'auke wayan sena makara."

  "Barka, dama waya aikeki? Karki damu mun riga mun karya."

  "Kai ina ruwanka? Idan na kawo se kar ka ci so ka fad'awa 'yar uwata kar tayi wahalan yin girkin rana I'll make it up to you guys."

  "A'a Hjy Surayya dan Allah karki sa kanki wahala."

  "Nikam ka had'ani da 'yar uwata mu gaisa" yana murmushi ya mik'awa Mami wayar "Assalamu Alaikum" ta soma da cewa. "Amaryar mu" Mummy ta amsa.

 "Kai 'yar uwa bazaki bar zolaya bade ya kike toh ya Khaleefah?"

  "Gashi se shiri yake ya kusan komawa school."

  "Allar sarki Allah kiyaye ya bada sa'a."

   "Ameen sena shigo anjima sauran kice zakiyi girki kuma."

  "Oh 'yar uwa kar ki sakaltani dayawa fah."

  "Ba ga Alhj ba yasan yadda zeyi dake ai."

  "Kai 'yar uwa."

 ""Ahtoh barin bar ku haka se na shigo anjima."

  "Toh muna godiya Allah kaimu."

  "Yauwa se anjima."

  Kaman yadda Mummy ta d'au alk'awari bayan sallan Azahar ta shigo da abinci kala-kala se sauk'e kuloli kawai ake tayi daga mota. Yini Mummy tayima Mami se kusan Maghrib da Daddy ya kusa dawowa ta koma gidanta. Zaman lafiya maras misaltuwa Mummy da Mami sukeyi sekace ba kishiyoyi ba wane wasu 'yan uwan jini, dai-dai da rana d'aya Daddy be ta6a jin kansu ba. Hasali har had'a kansu suke su biyu su waresa. Bayan ya k'are wa Mami kwana bakwai na amarchi ya soma yi musu kwana bibbiyu duka.

  ***
  Haka kwanaki suka cigaba da shud'ewa yayinda zama yake k'ara yima wad'annan abokan zama dad'i. Labarin Nazeefah kuwa duk sanda ta bugi iska takan d'au waya ta kira Mummy amma dai-dai da rana d'aya bata ta6an d'aukan waya ta kira Daddy ba ko da shi ya kirata ma se ta ga dama take d'agawa.

   9 months later...

  Abubuwa da dama sun gudana, Amal hutu ya k'are sun koma makaranta har sun k'are first semester suna second semester yanzu. Maamah kuma an kai goron tambayan auranta, labarin dawowan Ya Abdul kuwa shiru har yanzu ko su Mama sunyi mishi magana se yace shi ba yanzu ba. Sultan ko har yau labarin aure shiru ya tsaya rawan ido. Labarin k'awar Amal Falmata kuwa tayi aure abunta tabar Maiduguri ta koma a Azare take da zama inda mijin ke aiki. Har Azare su Amal suka kaita suka dawo. Tun tafiyan Amal wane akan allura Afzal yake zaune, minti-minti yake yi mata waya yaushe zata dawo. Sam baya iya jure rashin ta a kusa da shi.

***
  Amal ce zaune a d'akinsu da Afzal se faman karatu take gefenta kuwa plate ne cike da kayan k'walama ba abinda babu daga abinda ya kama kan tuwon madara, calanda, gullisuwa, tsamiyan biri, ba abinda babu ta d'au wannan ta d'au wancan. Haka kawai ta ke wani irin wawan kwad'ayi kwana biyu duk abinda tagani setaji tana so. Ba da dad'ewa ba wayanta dake ajiye a gefenta ya shiga ruri dubawanda tayi taga Afzal ke kira k'aramar tsuka taja ta cigaba da yin abinda ke gabanta. Yana tsinkewa ya shiga kira again nan ma tak'i d'agawa be dad'e ba sega sak'on sa.

  _Please pick up Rania I'm sorry._
  Tana cikin shawaran ta d'aga ne kokuwa sega call nasa again nan ma seda ya kusa tsinkewa ta d'aga had'e da yin shiru.
   ''Baby yi hak'uri mana."

  "Nifa ban ce kayi mun laifi ba."

  "Toh meyasa in na kiraki bakiya d'agawa?"

  "Karatu nake bana son distraction."

  "Baby Ya Omrin na kine kuma yau distraction? Yi hak'uri kinji Yaya is sorry."

  "Shikenan ni kayi ta mun wasa da hankali kenan kullum, yau kace gobe, jibi kace gata dan kawai kaga ina missing naka."

  "Haba baby yi hak'uri wallahi sune suka k'i sakemu saura mana trips biyu amma de yanzu."

  "Toh nikam se yaushe zaka dawo?"

  ''Zuwa next week in shaa Allah.''

  ''Har next week Ya Omri?''

  ''I'm sorry.''

  ''Promise?''

  ''I promise Baby.''

  ''Toh Allah ya kaimu.''

  ''Ameen kin daina fushin?''

  ''Ba dole na ba."

  "That's my Rania so ya kike? Should I FaceTime you?"

  "Okay." Nan ya katse wayayn ya yi mata video call inda ta d'auka suka cigaba da gaisawa. "Baby?"

  "Na'am'' ta amsa.

  ''Mey kikeci haka ba ni?''

  ''Oh tuwon madara ne.''

  ''Da kuma mey? Mey wancan bak'in abun?'' Plate d'in ta d'aga ta matso da shi kusa ''Tsamiyan biri ne.''

  ''Rania yaushe kika fara wannan ciye-ciye?''

  ''Ba ka nan ma ban tsira ba ko?''

  ''Toh ya Mami? Sun dawo?''

  ''A'a wai daga chan zasu wuce Dubai."

  "Oh ayyah Papi fa? Yana nan k'alau?"

  "Eh Mummy tana kula da shi."

  "Allah sarki toh yayi kyau."

  "Toh se anjima ko? Kaga karatu nake" tayi maganan tana nuna masa handouts nata.

  "Wait Rania d'an tsaya."

  "Yaya wai yau kai kake hana ni karatu?"

  "Not at all, Idona ne kokuma k'iba kika k'ara bayan tafiya na?"

  "K'iba?" Ta nanata tana duban jikinta

  "Eh mana kinga yadda kumatunki suka ciko."

  "Kai Ya Omri ka fa san bana son inyi k'iba."

   "Ai kuwa se kin fara slimming dan kin riga kin d'au hanya."

  "Omg! Dan Allah dagaske kake na k'ara k'iba?"
 
  "Kije ki duba mirror kiga" katse video call d'in tayi ta ruga gun madubi tana matse kumatunta. Kuma fa hakanne da gaske ta k'ara k'iba toh kode? Kai da k'yar tayi sauri ta kad'a kanta. Koda tayi missing period nata last month bata damu ba cause tunda ta samu miscarriage date nata ya rikice wani sa'in se yayi wata biyu be zo ba atimes kuma sati biyu zuwa uku ya dawowa. Amma kuma ai tabar shan planning pills nata there's possibility cewa tana da ciki. Toh amma wani irin ciki ne wannan ba laulayi ba komai? Ai wasu dama sunce  cikin fari ne yafi bada wuya na biyu da sauk'i yake zuwa. Ta shigesu Allah taimaketa ba ciki take d'auke da shi ba in bahaka ba zatayi bayani gun Afzal da yace su jira ta gama makaranta tukuna su fara bearing children kasancewar yadda cikin farinta ya mugun bata wuya. Da na sani ta shiga yi shin meyasa ma ta daina shan pills natan ta kuma cire implant d'in? Har ga Allah ba don rashin ji tayi hakan ba illa dan so da take ta azurta Afzal da yara, so take yaga jininsa shima bayan hak'urin da yayi na shekaru kusan biyar ba haihuwa. Bata son ta shiga hak'k'insa dan wani personal interest nata. Ko ba a tambaya ba tasan Afzal na son yara yadda kullum idan suka je gidan wani abokinsa da suke mugun zumunci yake wasa da yaran tamkar 'ya'yan cikinsa. Se kuma yanzu tsoro ya shigeta bayan alamomin juna biyu sun bayyana a  jikinta, ji tayi gabad'aya dama bata cire implant d'in ba. Ita de zata jira zuwa nan da jibi idan har period nata be zo ba zata asibiti a dubata.

   Washegari bayan lectures nasu ya k'are suka wuce restaurant dan chin abinci ita da Maamah sede Amal tak'i cin komai bayan kuma tana jin yunwan.

  "Wai toh mey zaki ci?" Maamah da abun ya isheta ta tambaya.

  "Ni wallahi ganda nake so."

  "Gan mey?" Maamah ta tambaya unbelievably.

  "Ganda wallahi."

  "Ahh gaskia kin so nishad'i ganda? Da ranan nan kuma acikin school?"

  "Wallahi shi nak so Maamah ki taimakeni."

  "Toh ya kikeson inyi Amal? Bawai ana siyar da ganda bane anan sede ki bari idan an tashi se driver'nki ya tsaya a kasuwa ya sai miki kije gida ki girka."

  "Toh ai yanzu nake so bazan iya jira har anjima ba."

  "Oh Amal! Ko mey sabon ciki sede hakan."

  "Nikam da Allah."

  "Kode cikin gareki?"

  "Kaman ya ciki sekace bakisan ina planning ba?"

  "Nasani ko kin cire."

  "A'a kam bayan Yaya yace kar incire."

  "K'arya kike."

 "Dagaske fah"

  Mak'aryaciya rantse muji! idan ma cikin ne da ke in Ya Afzal ya gano zakiyi bayani."
 
  "Maamah dan Allah ki taimakeni."

  "Aww cikin ne dake dagaske?"

  "Wallahi ban sani ba but ji nake kaman I'm pregnant jiya muna FaceTime da Ya Afzal yace wai na k'ara k'iba."

  "Ai gaskiyanshi kumatunki sun ciko."

  "Na shiga uku!"

  "Ya gane amma?"

  "A'a hankalinsa be basa ba."

  "Chab Allah ya taimakeki."

  "Da Allah ki daina tsorata ni nasan yadda zan sanar dashi idan har na tabbatar da komai."

  "Gara miki kam dan kinfi ni sanin halin ogan naki kikayi wasa se kunyi fad'a ma."

   "Kai Maamah ki daina razana ni."

   "Allah kuwa yadda seda ya ja miki kunne akan kar kije ki cire."

  "Nikam idan ba ganda zaki bani ba ki daina cika mun kunne."

  "Ganda kam sede unborn ya hak'ura dan babu inda zaki samu."
 
  "Ni bance miki ciki ne gareni ba" tayi maganan had'e da mik'ewa "Ina kuma zaki?" Maamah tayi saurin tambaya.

  "Out of school zanje in nemi ganda."

  "Lallai abu ya tabbata" Maamah tace cike da neman tsokana.

  "Kanki akeji" Amal ta amsa had'e da galla mata harara sannan ta fita. Nan da nan ta kira driver'nta yazo ya d'auketa, haka suka shiga bin restaurant by restaurant suna tambayan ko akwai ganda har seda suka samu.

   Na sosai hankalin Amal ya tashi bayan da tayi carrying pregnancy test a gida ya nuna mata positive sedai duk da hakan bata amince ba se da taje asibiti akayi mata tests da dama aka tabbatar mata da gaskiyan al'amarin cewa tana d'auke da juna biyu. Tirk'ashi! Yanzu mey abun yi? Tasan se sun haura sama idan Afzal ya gano gaskiya. Da fari tayi tunanin kwata-kwata ma kada ta sanar dashi amma kuma seta tuna idan har shi ya gano da kansa al'amarin zefi damewa. Yanzu what's the way out??

   Haka tana ji tana gani har Afzal ya dawo daga tafiya bata yanke hukuncin ko ta sanar da shi kokuwa a'a ba. Gashi koda ta gwada tambayan Falmata da Maamah shawara duk suka sake tsoratar da ita.

  "Rania k'iban nan naki lafiya kuwa?" Afzal dake mik'e akan gado ya tambaya yana mey k'ure mata ido yayinda take zaune akan kujera tana faman tsifan kanta. Zuciyanta taji ya buga, miyau ta had'iye sannan ta saki murmushin dole.

  "Kai Ya Omri dan Allah ka daina razana ni."

  "Aikam da alama kinji dad'in tafiyan da nayi tunda har kika yi wannan k'iba."

  "Ni dama tayani wannan tsifa zakayi."

  "In dawo daga tafiya kuma ki sani aiki Rania?"

  "Toh kayi shiru ka kwanta."

  "Zomu kwanta anjima in mun tashi se in tayaki."

  "Karatu nake so inyi anjuma."

  "Haba Baby na yi hak'uri mana."

  "Nikam barni inyi tsifa."

  "Toh zo kiji."

  "Mey?"

  "Kekam kizo mana."

  "Meneh ka fad'e shi daga nan mana." Ba salon da Afzal bebi ba amma haka Amal tak'i tasowa ta samesa gashi kuma baya son ya fito fili ya tambayeta saboda sarai yasan ta gane abinda yake nufi kawai bata son basa had'in kai ne. Mamaki ya sha sosai saboda wannan ne karo na farko da ya ta6a neman Amal tak'i basa had'in kai. Toh koma mey ne de Allah ya sa lafiya.
 
   Yau kwana uku kenan da dawowan Afzal amma Amal ta kasa mustering courage ta sanar da shi cewa tana da ciki se tayi kaman zata sanar da shi seta fasa.

   "Rania kiyi sauri mana I'm gonna be late for work."

  "Ermm ermm.." amma ta kasa yin magana se cin farcen hannunta take "Yaya"

  Anzo gurin Afzal ya furta a ransa dama duk lokacinda ta kirasa da Yaya toh laifi tayi ko ne mey yanzu?

   "Iyayen rashin ji mey kuma kikayi wannan karan?"

  "Yaya" ta furta cike da shagwa6a.

  "Rania speak up."

  "Kaga har past 7 hurry kar kayi latti."

  "Kin d'au na manta ne? Oya tell me what is it you want to tell me."

  "Dama so nake in ce maka I love you."
  Wani kallo ya watsa mata "We are not done Rania zamuyi magana idan na dawo." Kai zalla ta gyad'a mar tana turo bakinta. Tun fitansa har dawowansa Amal ta kasa samun sukuni.

   ****
   Fitowan Afzal daga wanka kenan ya nufi wardrobe nasa dan ciro kayan da zesa sede kap T shirts nasa Amal ta sanya tayi masa datti da su. "Huh! God help me Rania ina kika kai mun shirts d'ina?" Ya tambaya yana mey bud'e side na drawer'nta. Kaman a kyaftawan ido Amal ta mik'e dan dakatar da shi "Tsaya zan d'auko maka su da kaina kar ka d'aga chan" tayi saurin sanar da shi sedai ina tuni ya kai hannunsa wajen, paper ya ga wanda ya zaro waje. Hannu Amal ta mik'a zata k'wace amma ya janye "Yaya ka ba ni." Ta fad'a tana k'ok'arin yin tsalle amma ina ko kusa da hannunsa ta kasa kaiwa.

   "Yaya please dan Allah kar ka bud'e." Gabad'aya ta tsure tasan idan Afzal ya gani nata ya k'are.
 
 "Mey aciki?"

  "Babu ka bani please."

  "Babu? Toh in babu bari in bud'e inga."

  "A'a please Yaya ka bani" se k'ok'arin k'wata take amma ta kasa.

  "Dan Allah kar ka bud'e."

  "Mey aciki toh?"

  "Ermm ermmm script na test d'ina ne wanda na fad'i please kar ka bud'e." Dariya yasa "D'an tsaya toh muga zeron da kika ci d'in."

  "Yaya ple-" tana cikin yin magana ya bud'e sega pregnancy results na Amal da fari ma cewa yayi tun cikinta na fari ne sedai kuma da ya duba yaga data d'in ko sati be kai ba.

  "Amal?" Dum taji zuciyarta ta buga dama anytime ya kira ta da asalin sunanta toh tana cikin big trouble nata ya k'are.

   "Yaya-"

  "Mey wannan?" Yayi saurin katse ta.

  "Yaya-"

  "Wait! Is this true?" Ya kuma katseta "Are you really pregnant?"

  "Yaya-"

  "Just answer me Amal!" Ya fad'a a tsawace har seda ta razana.

  "Yaya yes amma kayi hak'uri I can explain."

  "Explain what exactly Amal?!" Ya kuna daka mata wani tsawan da ya mugun razana ta.

  "Yaya dan Allah kayi hak'uri."

  "Cire implant d'in kikayi?"

  "Yaya-"

  "I'm asking you for the last time Amal cirewa kikayi?"

  "Eh" ta amsa k'asa-k'asa.

  "Wow tun yaushe?"

  "Yaya-"

  "Amal answer me!"

  "4 months back."

  "Wow! Seriously? Ki ka kuma daina shan pills nakin?" nan kai zallah ta gyad'a.

  "Why? Mey na ce miki amma?"

  "Kar in cire."

  "Meyasa kikayi toh?"

  "Yaya I'm sorry."

  "Ba abun da na tambaya ba kenan meyasa kika cire?"

  "Yaya I'm sorry gani nayi kaman ina d'aukan alhak'in ka ne please don't be mad."

  "Tayaya? Tayaya kike d'aukan alhak'i na? Ni na kawo shawaran mu fara planning d'in kokuwa?"

  "Yaya kaine I'm sorry."

  "No answer me so kike kice kin fini sanin abinda nake so kenan komey?"

  "Yaya dan Allah kayi hak'uri."
 
  "Ban san meyasa bakiya ta6a jin magana ba koda nayi miki, seda na ja miki kunne nace miki this is my decision komin yaya kar ki cire implant d'innan se idan kin gama school amma kika k'i ji kika je kika cire saboda ni bansan abinda nakeyi ba ko?"

   "Wallahi Yaya ba haka bane I'm sorry."

  "Then yayane meyasa kika cire?"

  "Yaya-"

  "I'm not done" ya katseta "Answer me nace kin fini sanin ya kamata kenan ko mey? Kokuma ni da nace kar ki cire d'in bansan abinda nakeyi ba? Wanne d'aya?"

  "Yaya ko d'aya I'm sorry."

  "I'm very upset with you Amal sanin kanki ne last year result naki beyi kyau kaman yadda ya kamata ba, kinyi passing amma duk series of D ne dalilin da yasa nace mu fara planning d'innan kenan saboda ki samu kiyi concentrating a karatunki ba tare da wani distraction ba."

  "Amma wannan be bani wuya ba Yaya ko sau d'aya banyi amai ba."

  "I don't care Amal you're still not safe, and no matter what dole cikin nan zeyi miki causing distraction daga karatunki, abinda bana so kenan ni kuma I want you to focus on your studies just. Ko nid'in a jinki bana son inga jini na ne nace mu hak'ura se kin gama school? Na fiki damuwa Amal but haka nayi hak'uri because thsit is what is best for you for us all" ya k'arasa a tsawace.

  "Yaya I'm sorry bazan sake ba."

  "You're never sorry Amal bana ta6a gaya miki magana ki ji sede kiyi abinda ranki yake so bans-" sautin kukan Amal ne ya dakatar da shi, kuka ta shiga rera masa tsaye a wajen.

   Sedai Afzal be shiga yi ma Amal masifa ba kawai se ta yanki jiki ta fashe masa da kuka saboda tasan muddin ta fara kuka Afzal yana yin shiru. "Yaya I'm sorry" tace tana ta matso 'yar hawayenta. Kallo ya watsa mata kawai yabi gefenta ya fice izuwa d'ayan d'akin inda ya kwanta. Kukanta tasha a wajen seda ta gode wa Allah sannan ta mik'e ta je ta samesa a d'ayan d'akin Allah ya taimaketa ma be sa key ba. Akan gado ta tsincesa yana bacci, sid'ak-sid'ak ta taka taje tasamesa, jikinsa ta shige ta kwanta akan hannunsa haka har itama baccin ya d'auketa.

   Chan dab da goshin maghrib Afzal ya tashi se ganin Amal kawai yayi ajikinsa tana shar6an bacci. Ido ya k'ure mata yadda take ta baccinta cikin kwanciyan hankali da jurwayen hawaye a fuskanta. 'Yar murmushi ya saki tuna anytime ya fara mata masifa se ta rushe masa da kuka sanin baya iya jure kukanta. Ya rasa wani irin d'an banzan shagwa6a ne da ita kodan chan a gidansu ba a saba mata da masifa bane kokuwa da gan-gan takeyi ne oho shide amma shagawa6an nata na burgesa duk lokacin da ta fara kawai se yaji ya huce. Hannu ya aza akan cikin nata. "I'm sorry I got mad at you earlier, Rania bana son a sanadi na GP'nki ya sake sauk'a, I only want the best for you" tsugunawa yayi tare da pecking cikin nata. Daga haka ya mik'e yaje ya kama ruwa yayi alwala bayan ya gama shiri ya dawo ya tada Amal, yana tayar da ita ya fice ba tare da yace da ita komai ba. Sallah tayi ta tofe add'u'o'inta sannan ta zarce kitchen ta dafa macaroni da minced meat aciki ta dawo ta shirya kan dinning. Tunda take girkin take tsammanin shigowan Afzal amma shiru gashi ko da ta gwada trying numbanshi taga wayar ma a gida ya barta. Haka se chan kusan tara ya dawo Amal tayi jiran duniya har ta gaji. Yana shigowa ta zabura, mayar da k'ofan yayi ba tare da nuna ra'ayin yi mata magana ba so yake yaga ko zatayi masa.

   "Yaya sannu da zuwa" tace tana susan kanta yayinda ta kafe idanunta a k'asa.
 
  "Sannu" ya amsa sama-sama sannan ya shiga takawa gabansa tasha da wuri "Yaya I'm sorry dan Allah kayi hak'uri" ta sanar da shi idanunta suna masu cikowa da hawaye.

   "Ni ya kamata in baki hak'uri Rania I'm sorry kinji?" Cike da d'unbun mamaki ta d'ago kai tana kallonsa "Eh?"

   "I said I'm sorry for shouting at you earlier ki gafirceni."

  "Yaya-" dan mamaki tama kasa cewa komai. "Yaya ka daina fushi dani?"

  "Meyasa zan yi fushi da maman unborn d'ina? Na fahimceki Rania, and I appreciate your commitment to give me a family, to give us a family. Just know that I'll always be here for you if you needed me okay?" Hugging nasa kawai tayi tsabagen yadda takejin dad'i. "I love you so much Ya Omri."

  "I love you too babe" a hankali ya janyeta daga jikinsa. "How many months is my baby?"

   "Ko scanning banyi ba saboda tsoro da nake idan ka gano gaskiya zaka mun fad'a hala ma ka daina mun magana."

  "Be kamata in hau kanki da masifa ba d'azu Rania but I couldn't help it bana son saboda ni ki sake komawa baya a karatunki shiyasa nace mu fara planning I love you so much my Amal."

   "And I love you more Ya Omri a shirye nake da in rasa komi nawa saboda farin cikin ka, I'm willing to sacrifice my life for you Ya Omri. I've seen the way you so much love and adore kids shiyasa nima nake so in yi maka fulfilling this one wish."

  "And I appreciate that so much Baby, I can't believe I'm going to be a Daddy in anytime soon, Allah ya inganta ya cigaba da yi miki albarka."

  "Ameen Ya Omri."

  "So first thing gobe zamu je muyi scanning koba haka ba?"

  "Duk abinda kace my King Allah ya kaimu."

  "Ameen."

  "Muje muci abinci tun d'azu na sauk'e ina jiranka."

  "Har girki kikayi?"

  "Eh mana ba kayi mun fushi ba."

  "Yi hak'uri toh kinga ni bana son kina aikin wuya yanzu zan yi ma Ummi magana ta turo mana mey aiki d'aya daga gida."

  "A'a a'a nikam bana so bana so zan nayin komai nawa da kai na."

  "But Bab-"

  "Trust me Ya Omri koda zaka d'auko mey aiki ma kabari ba yanzu ba maybe idan nazo nayi nauyi amma yanzu kam da k'arfi na bana so."

  "What baby wishes she gets, fine se a bari se kinyi nauyi d'in amma fa karki na aiki sosai bana son ki galabaita mun baby."

  "Toh shikenan let's go and eat." Abincin su suka ci cikin kwanciyan hankali sannan sukayi wanka abinsu tare suka kwanta. Washegari kaman yadda Afzal ya fad'i suka wuce asibiti sukayi scanning ashe ciki har na wata biyu da sati d'aya ne tattare da Amal amma bata sani ba. Afzal dad'i kaman ze kashe sa se buge-bugen waya yake yana sanar da mutane Amal tasa is pregnant. Se tattalinta yake wane k'wai, idan ba abu yafi k'arfinsa ba sam baya barin Amal tayi aiki se inde shi yayi haka ta zama lalacacciya a gidan ko d'aga tsinke batayi sede tayita ciye-ciye tace tana son wannan tace tan son wancan. Wani irin d'an banzan kwad'ayi ta sake koyowa amma Alhamdulillah ba amai ba jiri ba ciwo ba komai. Haka Afzal ya cigaba da rainon cikin nata, kullum tare suke  zuwa yin scanning. Koda aiki yayi masa yawa ze buk'ace ta da ta jirasa seya dawo. Cikin na da wata biyar sukayi first semester exams nasu. Na sosai Afzal ya taimaka mata ta samu tayi passing with excellent results. Seda cikin ya kai wata bakwai tukun ya fara fitowa sosai acikin kaya, abinku da doguwar mace, tunda cikin ya fara fitowa Amal ta auri zama da hijabi a gida 24/7 saboda tsokananta da Afzal yakeyi sede bata cire hijabin ba seya nemi tsokananta. Har dan haka ma ta daina yin wanka tare da shi. Cikin nada wata takwas ya fito yayi k'ato tim, zama da k'yar tashi da k'yar kusan komai Afzal ne yakeyi mata. Haka kawi zata wayi gari rana d'aya tayita kukan banza in ya tambayeta dalili kuwa tace wai girman cikin ke bata tsoro.
   Bayan nan ga wani uban masifan da ta koya abu kad'an ta hau surutu da masifa.

   Da daddare wajajen goma Afzal na kwance yana bacci Amal ko se kuka cikinta yake sanadin yunwan da takeji, baccin ma ta kasa. Tun kafin su kwanta Afzal yake binta taci abinci amma tak'i saboda haushinsa da takeji har yanzu na hanata fita bikin sunan k'awarta da yayi. Shi kuwa dalilinsa wai saboda EDD nata ya kusa ne, it is more safe idan tana zama a gida kar labor yaje ya kamata acikin jama'a. Se harara take ta zuba masa shiko se baccinsa yake hankali kwance. Mik'ewa tayi da k'yar ta nufi kitchen ta bud'e fridge, jollof na shin kafa, macaroni, d'anyen awara, soyayyan kifi ta tarar a cikin fridge d'in sede duk ciki ba abinda ya gameta. Farin k'asa ta d'auko a inda take 6oyewa ta shiga tsotsa saboda Afzal ya haneta da sha tun lokacinda likitan ta tace musu abun baida kyau a jiki. Seda ta sha har biyu sannan ta koma d'akin, lokacin har goma da rabi yayi. Zama tayi daga bakin gadon tana tunanin ta yadda zata fara tada shi.

  "Yaya!" Ta ambaci sunansa. "Yaya ka tashi!" Cikin bacci ya amsa. "Mey ne Baby?"

  "Ni ka tashi" shareta yayi ya cigaba baccinsa.

   "Yaya ka tashi mana!"

  "Maman Baby na yi hak'uri mu kwanta kinga ina da office gobe yi hak'uri."

  "Toh ni yunwa nakeji."

   "Yaya ka tashi!" Tasa ihu, ba shiri ya mik'e zaune.

   "Dan Allah mey kikeso Baby?"

  "Ni pepper soup nakeso."

   "Toh ai akwai a fridge bari in miki micrwaving ko?"

  "Ni ba na kaza nake so ba na kayan ciki wanda ba thyme aciki nakeso."

   "Baby fisabillahi a ina zan samu pepper soup na kayan ciki cikin daren nan? K'arfe nawa ne?" Ya tambaya yana duban agogo. "Baby sha d'aya fa ake nema, sha d'ayan dare."

  "Toh laifi na ne? Ba baby'nka bace se kayi mata fad'a ba ni ba."

  "Ni ba fad'a nake miki ba yi hak'uri ki bawa baby hak'uri kice mishi gobe da safe zanje in siyo mishi."

  "Ni baby na ba na miji bane baby girl
ce ka daina canza mata jinsi."

  "Toh naji yi hak'uri Maman baby girl ki bawa baby girl hak'uri."

  "Ni wallahi shi muke so."

  "God help me naji toh naji zanje in saya miki."

  "Kuma in da thyme aciki bana so."

"Naji in shaa Allah ma babu." Nan da nan ya canza kayan jikinsa ya d'au key. "Toh sena dawo."

  "Allah ya kare I love you."

  "Ameen maman baby girl I love you too." Cikin sa'a kuwa a hotel na biyu da ya duba ya samu pepper soup d'in sede kuma da thyme aciki haka seda ya biya extra kud'i aka samu aka tankad'e masa romon aka yi getting rid of thyme d'in. Yana isa gida ya d'iba mata a saucer ya d'au mata ruwa. Sam bataji shigowansa ba kawai ji tayi karap an bud'e k'ofan. Kafin tace zata 6oye farin k'asan da take shan har Afzal ya gani.

  "Uhm uhm fito da shi na riga na gani fito da shi."
   "Yaya" kame-kame ta shiga yi. "Oya mik'a mun."

   "Yaya please"

   "Rania give it to me."
Bata sake yin gardama ba ta mik'a  masa.

  "Ina sauran?"

  "Babu wannanne na k'arshe."

  "One... Two..." ya shiga counting inda ta dakatar da shi da sauri. "Ka tsaya zan fad'a zan fad'a."

  "Oya a ina kika 6oye?"

   "Baby na" ta maraice fuska.  
 
   "Three... four..."
 
   "Yana cikin second cupboard a kitchen."

   "Kika sake saya se na kai k'aran ki gun Abba zance ko na miki magana bakiya ji ga shi zauna kisha an samu pepper soup d'in."

   "Na fasa sha ni awara nakeso."

  "Dan Allah kiyi hak'uri Rania bacci nakeji."

  "Ba zaka kai k'ara na gun Abba ba? Ni bazan ci ba."

   "Yi hak'uri wasa nake."

  "Nide wallahi awara nake so in ba haka ba inyi ma kuka."

  "Yi hak'uri Baby ta, ai bama haka dake kema kin sami, haba maman baby girl yi hak'uri ki sha mu kwanta ko? Gobe da kaina zan kaiki gidan k'awar naki kiga baby'n nata."

   "Daga baya kenan bayan an gama komai mey zanje inyi? Ni de awara nakeso."

   "Wannan d'in fa? In zubar?"

  "Ka sa a fridge amfaninsa ze taso wataran."

 "God help me!"

  "Ni de awara nake so." Haka dan dolensa ya juye pepper soup d'in a fridge ya fito da d'anyen awaran daga fridge dama already a yayyanke ne soyawa kawai za'ayi har ya shiga soyawa ya tuna da gardaman Amal ze iya kai mata yanzu tace ita mey k'wai ajiki takeso dan haka ya koma d'aki ya tambayeta. Ai kuwa tace mey k'wai ajiki take so cikin mintuna k'alilan ya gama soyawa ya kai mata nan ne ta zauna tacinye tas shide Afzal tausaya mata yake tun cewa da likita tayi idan ta fiye cin abinci sosai toh baby'n nata zeyi girma in akayi wasa ma ta kasa haifa da kanta se anyi mata CS. Amma inaa ita Amal ko a jikinta se aukin ci kaman  gara. Dam tayi sannan ta mik'e kan gado ta fara bacci. Se anan Afzal ya samu kansa ya kwanta shima.
   Haka yayi ta fama da Amal har zuwa lokacin da haihuwanta yayi. Dama likita ta basu tsakanin 12th-15th on the 14th Amal ta tashi da wani irin ciwon ciki mey tsanani, dama Mami tace mata anytime taji cikinta na ciwo ko bayanta toh tayi mata waya. Aikam Allah ya taimaketa ranan asabar labornta ya tashi bata fita school ba saboda ba wani serious lectures sukeyi ba, shima Afzal na a gida saboda ba aiki, tana zaune a d'aki ta nad'e k'afa tana tsotsan tsamiyan biri tajiyo wani irin sharp pain a mararta. Tuni tayi watsi da plate na tsamiyan birin ta sauk'a k'asa, da cikin nata ya sake murd'awa ta sa wani d'ankaren ihun da seda Afzal dake parlour ya shigo ba shiri, kanta ya yo da wuri yana tambayarta ko lafiya.

  "Yaya call Mami up I think I'm in labor."
 
  "Labor?" Ya sake nanatawa a razane. "Sure!"

  "Yaya kayi sauri wayyo Allah cikina zan mutu"  nan da nan ya kira Mami. Cikin mintuna k'asa da talatin ita da Mummy suka iso kafin nan ba irin yak'ushi da masifan da Afzal be sha ba. Amal se kuka da k'yar Afzal ya d'agata ya kaita mota Mummy ta biyo su da maternity bag nata duka suka yi asibiti inda akayi delivery room da Amal. Mutum d'aya aka buk'ata da ya shiga cikin d'akin da Amal nan su Mummy sukace Afzal ya shiga amma d'ankaren tsoro ne dashi atapir yace shi baze shiga ba sede cikin d'ayansu ita da Mami d'aya ya shiga. Baze iya jure ganin Amal tana kuka haka ba bayan ba abinda ze iya yi daze tsayar da azaban da take ji ba. K'arshe de Mami ce ta shiga, Amal se ihu take yi muryanta akeji ko ina a cikin asibitin Afzal ko zama ya kasa se safa da marwa yake a haraban d'akin yana mey rok'on Allah ya sauk'e masa matarsa lafiya. Bayan several pushes Amal ta samu kanta, ta haifo zankaleliyar 'yarta. Ana gama kimtsa su akayi ma Afzal magana.

   "Congratulations matarka ta sauk'a lafiya ta samu 'yarta both the mother and the baby are in good health zaka iya shiga ganinta." Dr ya sanar dashi da Mummy.

  Wani irin sanyi Afzal ya jiyo a jikinsa "Alhamdulillah Alhamdulillah thank you so much Dr." Ita Mummy dan farin ciki tama kasa magana.

  "You're welcome" daga fad'in haka yabi gefensa ya fice nan Afzal da Mummy suka k'arasa cikin d'akin. Wajen Amal tasa ya soma nufa had'e da placing mata peck a goshi. "Sannu da k'ok'ari my Rania, Allah yayi miki albarka sannu ko?"

   "Ameen Ya Omri" ta amsa a galabaice tana mishi murmushin dole.

  "Ga chan 'yar tamu achan" Mami tayi masa nuni da crib da aka sanya baby'n aciki. Nan da nan yaje ya d'aukota, baze iya kwatanta irin farin cikin da ya ziyarci zuciyansa ba a lokacin da ya rik'e baby'n nasa a hannu. Se kaman Amal kawai ya rik'e, yarinyan ba abinda ya rabata da Amal wane kakinta Amal tayi. Se masha Allah kawai Afzal yake ta furtwa har izuwa lokacin da ya dawo ya zauna a gefen Amal. Addu'a yayi mata Mummy ta mik'a masa zamzam da aka jik'a dabino aciki ya bata.

  "Rania she looks just like you" ya sanar da ita had'e da mik'a mata ita. Har kuka seda Amal tayi da ta rik'e yarinyar a hannu, yau Allah ya amsa mata addu'arta dan azaban data sha a labor room har cewa tayi ita mutuwa ma zatayi. Amshe baby'n Mami tayi ta mata addu'a itama sannan ta mik'awa Mummy itama tayi mata inda Afzal ya sake amsanta. "Gaskiya 'yar nan ta d'ibo Amal dayawa" cewan Mummy.

   "Nace miki kaman Amal kawai na rik'e a hannu ba abinda ya rabasu" Mami tace.

  "Alhamdulillah" Afzal ya sake mik'a godiyansa ga mahalicci. Ya rasa wani kyauta zeyi wa Amal wanda zey sanyata farin ciki kaman farin cikin da ta sanyasa a ciki yau. "Rania?"

  "Na'am?" Ta amsa mik'a mata baby'n yayi "Wani suna zamu sa mata?"

  "Yaya nice zan bata suna? Ai kaine mahaifinta kai zakayi deciding."

   "Na baki wannan dama, ki sanya mata duk wani sunan da kika ga ya dace." Shafe fuskan baby'n tayi a hankali had'e da placing mata kiss a kan hanci "Ina son mu sanya mata Nazeefah sunan k'anwata tilo." Gabad'aya wajen seda sukayi mamakin wannan ra'ayi na Amal, barin ma Mummy. Ina ma ace yadda Amal ke son Nazeefah haka itama Nazeefah take son ta? Da kuwa ba abinda ze fiye wa Mummy farin ciki. Duk sunyi murna matuk'a barin ma Mummy da har hawaye seda ta zubar taso ace ta iya ta bawa 'yarta tarbiyya kaman yadda Mami ta baiwa Amal, ta so ace Nazeefah tana da kyawun halatayya irin na 'yar uwarta Amal. Amsan yarinyan Afzal yayi ya mata hud'uba. "Welcome to the family Nazeefah, Allah ya albarkaci rayuwanki."

  "Masha Allah" fad'in Mami.

   "Allah miki albarka Amal, Ya k'ara muku lafiya keda Nazeefar mu."
  Ameen duka suka amsa a gun.




RANA D'AYA!
#RDđź’•

Love_ king Miemiebeeđź‘„

Monday, 1 October 2018

RANA D'AYA!

BY MIEMIEBEE
PAGE 45




     "Ameen Alhj na."

  "Mey hakan ke nufi kenan Hjy Surayya? Kin hak'ura kin yafe mun kenan?"

  "We all make mistakes Alhj amma ba dukan mu bane muke gano kuskurenmu har ma mu nemi tuban wanda muka wa laifi, shin meyasa bazan yafe maka ba tunda har kai ka gane kuranka ka kuma nemi tuba? Na yafe maka Alhj Allah kuma ya yafe mana gabaki d'aya" ta k'arashe tana murmushi. Daddy baze iya kwatanta irin farin ciki da murnan da kalamun Mummy suka sanyasa ba. Da murmushi kwance fal a fuskansa ya mik'a hannunsa ya rik'o nata "Thank you so much Hjy Surayya I can say my life has never been better until I met you, Allah ya cigaba da miki albarka ya kuma barmu tare."

   "Ameen Alhj you're welcome."

  "Kinsan wani abu?"

  "Seka fad'a."

  "I love you" yana sanar da ita bata san lokacin da ta fashe da dariya ba "Ji Alhj de, yaushe kuma muka fara wasan nan?"

   "I'm serious Hjy Surayya saboda bana fad'a miki doesn't mean I don't love you, I love you like the day I just met you Hjy Surayya never forget that."

   "Thank you Alhj."

  "Thank you kad'ai? Ni bazaki cemin I love you in return ba?"

  "Ka ga La'asar ya kusa gara ka tashi ka fice muyi niyya duka."

   "Yau kuma? Toh sekin fad'a min zan bar nan."

  "Lallai kuwa, nikam ka ga tafiya na" bata kai ga mik'ewa ba ya dakatar da ita ta hanyan kama hannunta. "Alhj ka sakeni mana!"

  "Nak'i"

  "Zan tara maka jama'a fah."

  "Ni d'in Hjy Surayya? Ni d'in naki?"

  "Toh ka sakeni."

  "On one condition."

  "Name it."

  "Yaushe zaki dawo gida? Ina matuk'an kewarki."

  "Kai da zaka k'aro amarya kode ka manta ne?"

   "Amarya daban ke daban so yaushe zaki dawo keda 'yan'yan namu?"

   "Zamu dawo karka damu."

  "Promise?" Kai zalla ta gyad'a mar sannan ya saketa "Toh se anjima ki gaishe mun da Nazeefah da Khaleefah."

  "I'll semun sake magana." Da haka ta fice ciki inda shi kuma ya mik'e ya yi tafiyarsa.
  D'akinta da Nazeefah ta wuce direct inda ta tarar da Nazeefah mik'e kan gado kaman maciji ta zurfafa a cikin tunani ko makaranta tak'i fita. "Tashi ki zauna muyi magana" Mummy tace da ita bayan ta zauna a gefenta ta bakin gadon. Ba gardama ta mik'e ta zaune.

  "Ina son ki saurareni da kunnen masu hankali a matsayinki na musulma me kar6an k'addara me kyau ko akasin sa." Tun anan gaban Nazeefah ya fara bugun d'ari-d'ari dukda cewan bata fahimci inda Mummy ta dosa ba.

  "Ki sani cewa komai na faruwa ne bisa dalili fatan mu kawai Allah ya sa hakan kawai shi ne mafi alkhairi a gareku gabad'aya."

  "Mummy ban fahimce kiba shin mey kike fad'i? Meya faru?"

   "Ga wannan takardan ki ne Afzal ya kawo wa Daddy jiya yana mey baki hak'uri kuma" ta fad'a had'e da mik'a mata. Jiki na k'yarma Nazeefah ta mik'a hannu ta amsa had'e da bud'ewa sannan ta karance hawaye kawai Mummy taga na gangara daga idanunta ba makawa.

  "Nazee-"

  "Noooo!" Tasa wani irin d'ankaren ihu "Noo this can't be happening, bani Ya Afzal yayi niyyan saka ba na tabbata munafukan chan ce ta tilasta mai ya rabu dani wallahi bani yayi niyyan saka ba Munmy."

  "Nazeefah ya isa" Mummy ta fad'a tana k'ok'arin shawo kanta saidai hakan sake tunzirata yayi. Zabura tayi tana kad'a kai yayinda hawaye ke ambaliya a fuskarta "Mummy wallahi bani Ya Afzal yayi niyyan saka ba ki yarda dani."

   "Nazeefah please-"

  "Tsaya kiga ina key'n mota na inje in samesa kiji bani bace wannan takardan Amal ne ba nawa ba."

  "Wani irin banzan magana kike Nazeefah? Bayan ga sunanki nan boldly rubuce akai? Taya zakice ba naki bane na Amal ne?"

  "Wallahi Allah ba nawa bane ina key'n mota na yake?"
 
   "Shin wai ina zakije?" Ta tambayeta. "Zan je in samesa saboda bani yayi niyyan saka ba."

  "Nazeefah there is no point kiyi hak'uri ki rungumi k'addarar ki kowa yasan rabuwa da masoyi da zafi amma ba yadda kika iya."

  "Hak'uri? Hak'uri Mummy? Wallahi inde akan Ya Afzal ne bazan ta6a hak'ura ba."

  "Toh ya zakiyi? K'addara ta riga fata, the earlier kikayi accepting gaskiya the better."

  "How Mummy? So kike kice mun shikenan na rasa Ya Afzal a rayuwa na kenan? So kike kice in nad'e hannu in bar Amal ta sace mun miji ina ji ina gani?"

  "Kema kinsan Amal baza ta ta6a yin hakan ba, Amal ba ita ta sace miki miji ba Nazeefah, Allah ne ya k'addara rabuwan ku."

  "No Mummy kinyi kuskure, idan ba mutuwa ba banga abinda ze rabani da Y Afzal ba" mayafinta ta sanya ta janye key daga gaban dresing mirror da niyan ficewa inda Mummy ta cafke mata hannu.

  "Bada yawu na zaki fita ba Nazeefah."

  "Just let me go" tace da ita had'e da fisgan hannunta. Kaman a kyaftawan ido Mummy ta isa bakin k'ofa ta kulle da key had'e da zarewa ta rik'e a hannunta.

   "Mummy ki matsa mun."

 "Ba inda zakije Nazeefah saki ne ya riga ya auku ba abinda kika isa kiyi da zeyi reversing case d'in sede hak'uri kawai, ki d'au komi a matsayin k'addara ki yi tawasalli."

   "Na gaya miki Mummy inde akan Ya Afzal ne bazan ta6a hak'ura ba har se sakin nan ya koma kan Amal, bazan rasashi ni kad'ai ba se inde mu biyu duka mu rasa sa so move out."

   "Ina nan tsaye anan ba inda zaki." Dube-dube Nazeefah ta shiga yi a d'akin chan ta hango wuk'a a kan bed side drawer nan da nan taje ta d'auka ta saita dai-dai wuyan hannunta (wrist) "Ko ki matsa ko in yanke kaina in mutu" Baki Mummy ta hangame cike da mamaki da k'in yarda tana kallon Nazeefah, batayi tsammanin rashin sanin addinin nata har yakai matakin da za tayi tunanin d'aukan ranta da kanta ba.

  "Nazeefah?" Ta kirata da d'umbun mamaki. "Da hankalinki?"

  "Mummy banida wata amfani tunda na rasa Ya Afzal gara in mutu in huta kowa ma ya mutu."

  "Da hankalinki kike tunanin d'aukan ranki da kanki? Shin baki san hukuncin hakan bane a addinance?"

  "I don't care Mummy amma bazan iya rasa Ya Afzal ba I can't because I love him, I love him so very much and Amal stole him away from me, what else can I do?"

  "Idan kika hak'ura komi mey wucewa ne Nazeefah wataran se labari."

  "No Mummy I can't move on, bazan ta6a iya son wani bayan Ya Afzal ba, I can't do without him dan Allah ku bashi hak'uri ya mayar dani d'akina."

  "'Yar uwarki Amal kuma fah? Ya kikeson ayi da ita?"

  "Ki daina kwatanta ta da 'yar uwata, idan da ta d'aukeni a matsayin 'yar uwarta da bazata sace mun miji ba so ki matsa ko kuma in yanke kaina."

  "It doesn't have to be this way Nazeefah" Mummy ta sanar da ita tana mey matsowa kusa da ita a hankali.
 
  "Mummy stay away."

  "Nazeefah dan Allah kiyi hak'uri karki yanke kanki" ko kallon ta Nazeefah batayi ba ta sa wuk'an ta yanke hannunta wani irin ihu Mummy ta k'urma had'e da k'arisawa kan Nazeefah da ta shiga zamewa k'asa. Tarota Mummy tayi suka sauk'a k'asan atare tana mey bubbuga fuskanta yayinda idanunta suka cigaba da kakkafewa. "Nazeefah? Nazeefah? Innalillahi dan Allah ki tashi Khaleefah!" Ba shiri ta saketa ta d'auko wayanta had'e da kiran Daddy. A karo na farko ya d'aga, ko daman magana bata basa ba tace, "Alhj ka juyo ka juyo da wuri Nazeefah ta yanke kanta."

   "What?!' I'm on my way" U-turn yasha nan take ya dawo ba tare da 6ata lokaci ba akayi da Nazeefah nearest clinic inda akayi emergency room da ita.

  _53 minutes later_
  Da wani irin gudu Afzal ya shiga haraban asibiti sannan ya nemi waje yayi parking ya fito ya k'arisa ciki. Tsaye a inda akayi mai kwatance ya same su da tashin hankali bayyane karara a fuskokinsu.

  "Afzal?" Daddy ya kirasa yana mey mamakin yadda akayi yasan halin da suke ciki.

  "Afzal waya sanar da kai muna nan?" Mummy ta tambaya.

  "Mummy nine" Khaleefah ya amsa.

  "How's she?" Afzal ya tambaya. Shiru ne ya d'auki wajen se chan Mummy ta amsa "Muma jira muke likitocin su fito tukuna."
  15 minutes more sega emergency room d'in ya bud'u nan duk suka duk'ufa sukayi wajen kowa da abinda yake tambaya. Nan Dr'n ya musu bayanin komai yakuma tabbatae musu cewa cut d'in beyi affecting Radial artery nata ba in less than an hour zata farfad'o. Godiya suka masa sannan ya fice.

   "Daddy, Mummy I'm so sorry I'm terribly sorry nasan duk laifi na ne."

  "Ko kad'an Afzal" Daddy yayi saurin katsesa "you're not to be blamed for anything, idan har akwai mey laifi anan toh nine so kabar damuwa."

  "Mummy I'm sorry."

  "Don't be Afzal mungode da kulawanka in shaa Allahu zan sanar da Nazeefah zuwanka."

  "Thank you Allah ya bata lafiya."

  "Ameen mungode Khaleefah ka rakasa" cewan Mummy.

  "No don't bother" Afzal yayi saurin amsawa sannan ya fice. Gida ya wuce direct sede tun shigansa Amal ta karanci yanayinsa wani iri. Bayan ta mar sannu da zuwa ta d'auko masa ruwa ta zauna a gefensa. "Ya Omri lafiya?"

  "Babu" ya amsa sama-sama.

   "Kaman ya babu Ya Omri? Tell me kaji."

   "Nagaji ne kawai barin je in watsa ruwa in huta" hannunsa tayi saurin kamawa" kafin ya mik'e "Please tell me Ya Omri nasan akwai abinda yake damunka."

   "Rania I'm sorry."

  "Why what for?"

  "Rania it's Nazeefah tana kwance a asibiti yanzu haka as we speak."

   "Subhanallahi meya sameta?"

  "Yanke kanta tayi."

   "Nazeefan? Dalili?"

  "Batun takardan ta, yanke kanta tayi in attempt to kill herself."

  "I want to go and see her Ya Omri."

  "Rania-"

  "Please" tayi saurin katsesa "Ya Omri ji nake kaman duk laifi na ne, komin mey Nazeefah tayi laifi na ne."

   "Kar kiyi magana haka Rania, in har akwai wanda za ayi blaming anan mahaifinku ne and he's sorry mu taya Nazeefah da addu'a kawai Allah yasa ta gane gaskiya da wuri."

  "Ameen but I still want to go and see her please kar ka hanani Ya Omri." Hannunta ya d'au ya rik'e a cikin nasa "Okay zanyi wa Mummy magana se muje."

  "Thank you."

  "Don't mention so me kika girka mana? I'm hungry."

  "Spaghetti ne kawai nima ban dad'e da dawowa daga school ba."

  "Oh! Muje toh."

****
   Bayan Maghrib Afzal yayi wa Mummy waya inda ya tabbatar da cewa ba a sallamesu ba har anan sannan yace mata suna shigowa shi da Amal. Acikin k'ank'anin lokaci suka isa inda Mummy ta taresu ta k'arisa ciki dasu. Nazeefah na ganin Amal taji tsikan jikinta gabad'aya na tashi yayinda ta shiga yi mata wani irin tsananin tsana.

  "Mey wanann take mun a d'aki Mummy? Send her out send her out!"

  "Nazeef-"

  "Bana k'aunan ganinta a kusa dani ku fitar mun da ita daga d'aki" ta katse Mummy da hanzari.

  "Nazeefah please" Afzal ya sa baki. "Kiyi hak'uri."

  "Hak'uri Ya Afzal? Da abinda zaka sak'a mun kenan? Ashe for all these while k'arya kake mun? I never expected this from you, I thought you love me ashe ba haka bane, ka sani daga kai har matar taka bazan ta6a yafe muku wannan abu da kuka mun ba Mummy send them out."

 "Nazeefah dan Allah kiyi hak'uri" Amal tace da ita.

  "Ko da wasa karki kuskura ki sake kiran suna na Amal saboda keba 'yar uwata ba ce. You ruined my life, first you stole my father away from me and then now my husband, meyasa kike nok'e-nok'e? Ki fito fili kice kina son ki zama ni kina son ki sace nun rayuwa. Amal na tsaneki, na tsani duk wani mey sonki, ba kuma abinda ze fi mun nishad'i da jin dad'i kaman inga gawanki bana k'aunanki in har kina son kanki ki ficemun daga d'aki you have absolutely no right to speak to me get out." Hawaye Amal ta shiga yi yayinda Afzal ya janyeta jikinsa "Ku fice mun daga d'aki bana k'aunan ganinku duka."

  "Nazeefah meyasa bakida mutunci ne?" Mummy ta tambayeta tana mey tsananin jin takaicin abinda Nazeefah ta aikata.

  "Shikenan Mummy zamu koma" fad'in Afzal "Nazeefah Allah ya baki lafiya we mean you no harm" daga fad'in haka ya sauk'o da ganinsa akan Amal "Let's go Amal." Badan Amal na so ba ta amince ya jata waje se kallon Nazeefah take tana kuka itako Nazeefah ko sake kallon 6angarensu batayi ba.

   "Meyasa baku barni na mutu ba Mummy? I hate my life I hate Amal."

   "Nazeefah it pains me as a mother ace ni na tsuguna na haifeki, Allah ma shaida ne ni ba tarbiyyan dana baki ba kenan, bansan a ina kika d'auko wannan banzan hali ba dan bazan ce na mahaifinku bane saboda koda wasa be ta6a gigin d'aukan ransa da kansa ba. Kuma Amal da kike gani kika raina wataran zaki nemata hannu bibbiyu ki rasata kuma ko kin k'i kin so 'yar uwarki ce ba abinda zaki iyayi da ze canza hakan. Ki tashi ki ci abinci yanzu za'a sallameki zamu koma gida."

   "Wani gida?"

  "Ban gane wani gida ba gida gida mana."

   "Meya samu hotel da muke zaune aciki?"

   "Zamu koma gida gun Daddy'nku nide na fad'a miki."

  "No Mummy ni bazan koma gun Daddy ba, a dalilin mey? Bayan duk bak'in ciki da k'uncin da nake ciki shine sanadi."

  "So? He's still your father nothing can change that."

  "Ni gaskiya bazan bi ku ba."

 "Ni na fad'a miki" tana kaiwa nan ta fice had'e da rufo mata k'ofan.
 
****
  Tun da suka shiga mota har suka isa gida Amal take ta kuka.
   "Amal it's okay with time in shaa Allah Nazeefah zata fahimci komai kukan ya isa haka" Afzal yace da ita bayan sun k'arasa ciki yana mey share mata hawayenta.

  "Yaya I feel so responsible for everything Nazeefah is going through, Nazeefah tana sonka har yau har gobe tana sonka she can't ever stop loving you."

  "And you too Lily, you love me don't you?"

  "I do Yaya amma Nazeefah kuma fah? Yaya har ranta fa ta so d'auka akan soyayyar ka."

  "Amal you matter to me more than anyone morethan Nazeefah kibar tada hankalinki kinji? I love only you" rungumeta yayi a hankali itama ta zagaye hannayenta a bayansa tana mey lumewa acikin rik'onsa yayinda kalamun Nazeefah suke faman yi mata wasa a kai.

****
   Washegari...
  Dawowan Daddy daga gidansu Mami kenan amma sam babu walwala tattare da shi. Yana shigowa Mummy da ta karanci yanayin nasa tayi mai sannu da zuwa.
   "Tak'i amincewa?" Ta tambayansa a hankali.

  "Hjy Surayya ko bani dama in nemi tubansu sun hanani bale in sanar dasu k'udurina, Jameelah tana matuk'ar fushi dani haka ma mahaifinta. Ban san ya zanyi ba muddin tak'i yafe mun, alhak'in ta ya cigaba da bina kenan idan da ma akaina kad'ai ze tsaya da da sauk'i amma har ku baku tsira ba, bana k'aunan sake ganin ku cikin k'unci Hjy Surayya bana son abinda ze sake raba kanmu yadda na samu da k'yar Nazeefah ta amince ta biyoki kuka dawo mun."

  "Ka kwantar da hankalinka Alhj."

  "Ta yaya Hjy Surayya? Ta ina hankalina yaga ta kwanciya bayan rayuwan mu duka yana cikin gwagwarmaya."

  "Ni da kaina zanje in samu Jameelah gobe muyi magana in shaa Allahu zata yafe maka komai ta kuma amince da k'udurinmu."

  "Keda kanki?" Ya tambaya yana mey kasa 6oye mamakin da ya sha.

   "Baka yarda bane?"

  "Hjy Surayya a ina aka ta6ayin haka? Dan Allah karki baiwa kanki wahala-"

   "Kabar zancen nan Alhj" tayi saurin katsesa "Ai mun wuce haka yanzu try not to worry Allah kaimu goben."

  "Ameen Hjy Surayya banida bakin yi maki godiya, Allah saka ya biyaki da gidan Aljannah."

   "Toh kuma godiyan mey kake? Muje kaci abinci."

  "Ya jikin Nazeefah?"

  "Da sauk'i tana kwance a d'aki tana bacci."

  "Toh madallah".****

   Tamkar mey ta6in hankali haka Nazeefah ta zame musu a gidan ko abinci tak'i ci tun dawowansu daga asibiti jiya da dare har izuwa yinin yau. Allah ma yaso ana sa mata ruwa. Banda kuka ba aikinta a gidan, Mummy tayi mata nasiha tayi mata fad'a amma ina tak'i ji haka zata kafa hotunan auransu da Afzal tayita kalla ba fashi. Washegari kamar yadda Mummy ta d'au alk'awari ita da Daddy suka jesu gidansu Mami inda ya tsaya daga waje ita kima ta k'arasa ciki. Sallama tayi yayinda take sa kai cikin gidan, Mami dake gida ita kad'ai ce ta amsa. Kallo d'aya tayiwa Mummy ta tabbata mahaifiyar Nazeefah ce saboda tsan-tsan kaman da sukeyi.

   "Mahaifiyar Nazeefah?" Ta tambaya. murmushi Mummy ta saka had'e da gyad'a mata kai. "Bismillah ki shigo" tabarma ta shimfid'a musu inda suka zauna sannan suka gaisa.

  "Bari in kawo miki ruwa."

  "A'a 'yar uwa ba amfani."

  "Toh lafiya dai ko?"

  "Lafiya k'alau batun Abdallah nazo muyi magana."

  "Kiyi hak'uri maman Nazeefah amma in har abinda ya kawo ki kenan saidai ki koma."

  "Nasani 'yar uwa nasan abinda Abdallah yayi miki da zafi da ciwo amma abu ne ya riga ya faru ba abinda zamu iyayi da zai canza hakan saidai muyi gyara. Kiyi hak'uri ki yafe masa, shi yafiya ba kowa bane Allah yake basa iko da zuciyan yi amma na tambayeki ne saboda nasan zaki yafe masa saboda ko ban tambaya ba nasan a wajenki 'yarki Amal ta yo gadon kyawawan d'abi'unta. Idan muka ce zamu biye ta zuciyoyin mu toh wallahi ba abinda zamu tsinana wa kanmu na arziki. Ko ban fad'a miki ba nasan kinsan irin tsanan da ke tsakanin yaran mu Nazeefah da Amal. Duk yadda Amal ke son shirya tsakaninta da 'yar uwarta hakan ya gagara kuma ba wanda ze iya had'a mana kawunan yaran nan sama da ke."

   "Ban fahimce kiba Maman Nazeefah ta yaya zanyi hakan?"

   "Ki amince ki auri Abdallah."

 "Iyyeh?" Mami ta zaro ido wuru-wuru waje. "Kikace?"

  "Eh, ki amince ki auri mijina ta hakan ne kawai zamu iya gyara zuri'ar mu mu had'a kawunan yaran nan dan Allah ki amince."

  "Kiyi hak'uri Maman Nazeefah amma bazan iya cika miki wannan buri naki ba, bazan iya auran Khaleefah ba bazan iya ba."

  "Zaki iya 'yar uwa muddin kika yarda da hakan, dan Allah karki bari tsanan dake tsakanin yaran nan yayi tsamari iche tun yana d'anyensa ake iya tank'warasa, muddin ba'a sa musu a jiki cewa mun zama abu d'aya ba yanzu toh wallahi gaba tsanan da zasu tashi dashi a cikin zuciyoyinsu baze so yayi kyau ba ki taimaka."

  "Maman Nazeefah tunda nake ban ta6a jin inda uwar gida tazo taya mai gidanta k'aro aure ba ko da kuwa a radio ne, saboda haka ban san abinda ke cikin zuciyarki ba keda mijinki, bansan mey kuke shirin yi mani ba amma koma menene kuyi hak'uri ku janye ni daga cikin matsalarku tunda na samu auren 'yata be mutu ba Alhamdulillah koni na mutu a haka bazan damu ba."

  "Jameelah da zuciya d'aya nazo na sameki bada wata manufa ba, Jameelah har yau har gobe nasan Abdallah yana sonki, kema kin sani ba sena fad'a miki ba, ni kuma har ga Allah har cikin zuciyata tun cemin da Abdallah yayi bakida aure naji tausayinki ya shige min zuciya nasan ba komai ya hanaki yin aure ba illa idan kika juya baya kika ga abinda Adallah yayi miki, shi ya lalata miki rayuwa dan haka kuma shi ya tantanci yayi making everything right don haka na basa goyin baya na bashi shawaran ya auro ki. Kuma kinga ta hakan ne kawai zamu iya had'a kawunan yaran mu. Zan barki kiyi tunani anytime your mind is made up ga lamba na" ta fad'a had'e da ajiye mata wani gajeren paper data rubuta number'nta ajiki "Seki kirani, hope to hear from you soon ni zan wuce."

   "Toh bari in rakaki."

  "Ba amfani 'yar uwa yi zamanki nagode da wannan lokaci da kika bani se anjima." Tun fitan Mummy Mami ta shiga tunani, gabaki d'aya kanta ya d'aure se bata jikinta yake trap su Mummy suke shirin shirya mata in ba haka ba har a ina uwar gida ta ta6a aran bakin mijinta dan nema masa mata?

    Daddy kuwa a gida ya sauk'e Mummy ya wuce gidansu Amal, yasani it's now or never. Bayan mey gadi ya bud'e mishi gate ya k'arasa ya samu gu yayi parking sannan ya fito ya nufi entrane door inda yake ta knocking amma ba response kasancewar bacci da suke duka daga ciki. Ganin ba mahalicci se Allah kawai seya kira wayan Afzal. Kaman a mafarki Afzal ya soma jin ringing na wayansa dake ajiye akan side drawer'n kansa kafin ya mik'a hannu ya d'aga har Amal itama ta farka. Sorry go back to sleep" ya sanar da ita rik'e a hannunsa yana mey sake daidaita kanta a k'irjinsa sannan ya d'au wayan inda ya tarar da missed call na Daddy nan take ya kirasa back, "Halo Daddy?

  "Na'am Afzal gani a bakin k'ofan gidanku fa amma shiru ko bakuwa nan ne?"

  "Afuwan Bacci ne ya d'auke mu bari inyi ma mey gadi magana ya bud'e maka."

  "No already ina ciki ya riga ya bud'e mun ina bakin parlour ne."

  "Sorry bari ina fitowa yanzu" ya fad'a had'e da kashe wayan sannan ya sauk'o da kallonsa akan Amal "Rania bari in fita Daddy yazo yana waje." Kai zalla ta gyad'a masa sannan ta koma gefe ta cigaba da kwanciyanta. Jallabiyansa ya sanya ya fito ya bud'e wa Daddy yana mey sake basa hak'uri. Ruwa da juice ya d'auko masa inda suka gaisa yake tambayansa ya jikin Nazeefah.

   "Da sauk'i Alhamdulillah."

  "Toh Allah k'ara mata lafiya."

  "Ameen yaya Amal kuma?"

  "Lafiyanta itama."

  "Ina sake baka hak'uri game da abinda Nazeefah tayi muku ranan, ni kaina I'm having a hard time with her kuyi hak'uri kuyi mata uzuri."

  "Ba komai Daddy duka nan mun san what she's going through is not easy fatan mu Allah kawo mata sauk'i."

  "Ameen Afzal thank you."

  "Ba komai Daddy."

 "Yauwa dama batun Amal nazo ne Afzal, ina son muyi magana da ita in kuma bata hak'uri gameda duk wani abinda nayi mata, Afzal ka sani a addu'a I want to make everything right I want to marry Amal's mother." Mamaki da dad'i ne ya ziyarci zuciyan Afzal wanda ya kasa 6oyewa "Tabbas kayi tunani Daddy, Allah sanya alkhairi acikin hakan ya biya maka buk'atunka na alkhairi."

   "Ameen Afzal zan iya yi ma Amal magana."

  "Sure tana bacci bari in tayar da ita."

  "No no in tana bacci ka barta kawai ko gobe ina iya dawowa."

  "A'a don't worry." D'akin nasu ya koma yaje ya samu Amal ya shiga tada ita. "Rania?"

   "Uhmmm?"

  "Daddy yazo."

  "Uhmm?"

  "Yana son ya ganki kuyi magana." A hankali ta bud'e idanunta "Yaya I don't want to face him ban san mey zance mishi ba."

  "I know Rania, I know kiyi hak'uri kije kiji mey zai ce miki."

   "Yaya-"
   
  "Kar muyi haka dake kinji? Tashi hungo kayanki kisa" da kanshi ya mik'ar da ita zaune ya sanya mata kayan da hijabi suka fito suka zauna a kan two seater.

  "Ina yini Daddy?" Ta durk'usa har k'asa ta gaishesa.

  "A'a please Amal koma ki zauna Afzal ce mata ta zauna" duk da haka Amal tak'i mik'ewa seda ya amsa tukuna. Gaisawa sama-sama sukayi sannan ya fayyace mata dalilinsa na zuwa dan ya nemi tubarta.

  "Nasan na cuceki a rayuwa Amal, nasan nayi depriving naki duk wani right da gatan da kika cancanta a rayuwarki, nasan ban kyauta miki ba ban kuma kyauta wa mahaifiyarki ba amma gani yau nazo neman tubanki" ya k'arasa had'e da sauk'a k'asa akan guiwoyinsa. "Daddy please ka tashi" tayi saurin cewa amma yak'i. "I'm dearly sorry Amal, kiyi hak'uri ki yafe mun I'm here and ready to take full responsibility for everything ki bani dama in cika aiki na a matsayina na mahaifinki, ki bani dama in kula dake in soki a matsayina na mahaifinki da jini na ke gudana a jikinki. Amal I'm so sorry" Afzal be ji tashin Amal ba kawai ganinta yayi gaban Daddy tana k'ok'arin d'agosa "Don't be Daddy komai ya riga ya wuce ka kuma sani ni na riga na yafe maka komai da jimawa Allah ya yafe mana gabad'aya."

   Rungumeta tsam yayi a jikinsa cike da farin ciki yayin da duk suke zubda hawayen jin dad'i "Oh Amal thank you so much Allah cigaba da yi miki albarka  bansan da wani bakin zan yi miki godiya ba." Itama a hankali ta zagaye hannunta a bayansa "Ameen Daddy ka daina yimun godiya." Se murmushi Afzal dake ganin komi kaman a mafarki yake faruwa, this's all he's ever wanted, ranan da Allah ze bayyana musu mahaifin Amal ya nemi tubanta su shirya se gashi Allah ya kawo musu ranan.

    "Amal?"

  "Na'am Daddy" ta amsa.

 "Amal nasan kinsan yadda Mahaifiyarki ta tsaneni ko?" Shiru tayi bata ce komai ba. "Amal I need your help, Mahaifiyarki tak'i ta bani dama in bata hak'uri bale in nemi tubanta Amal a shirye nake da in auri Mahaifiyar ki in har zata amince."

   "Zaka auri Mami?" Ta tambayesa d'auke da d'unbun mamaki.

   "In har zata amince, eh."

   "Mummy kuma fa? Bana son abinda ya faru tsakani na da Nazeefah ya faru dasu suma, in har Mummy bata goyi bayan zancen nan ba babu amfani Daddy."

  "Hasali Mummy'nku nema ta kawo shawaran nan Amal, Mummy'nku batada matsala da hakan idan har keda mahaifiyarki kun amince."

  "Kayi wa Mami magana ne?"

  "Naso amma tak'i bani dama d'azu nida Mummy'nku mukaje tayi mata magana sede har yanzu bata shirya bamu had'in kai ba please help me Amal nasan bani da daman tambayan hakan daga gareki but Amal I love your mom, har yau har gobe ina sonta kuma ina son in aureta." Na matuk'a Amal taji dad'i ta juma tana mafarkin rananda Mami zata shiga d'akin mijinta itama koda sau d'aya ne taji dad'i a rayuwanta. Inde hakane kuwa se inda k'arfin ta ya k'are inshaa Allahu bazata gaji ba seta shawo kan Mami waya sani ko da haka Nazeefah zatayi accepting nata ta bata chance suyi working out relationship nasu.

  "Amal? Bazaki iya ba ko? Bakiya son mahaifiyarki ta kasance tare dani ko? Look I'm terribly sorry wallahi nayi nadaman abinda nayi muku please forgive me."

  "Ko kad'an ba haka bane Daddy hasali nayi murna da farin cikin wannan labari in shaa Allah kuma zan tayaka yima Mami magana."

   "Nagode sosai 'yata Allah miki albarka sak'a miki da alkhairi."
 
  "Ameen Daddy."

  "Toh ni bari zan koma."

  "Da wuri haka Daddy?" Fad'in Afzal "kabari mana muci dinner."

  "A'a karka damu."

  "Please stay Daddy" Amal ta sanya baki.

  "Tunda 'yata tasa baki na isa ince a'a? Se in jira d'in." Dad'i sosai both Amal da Afzal suka ji haka Daddy ya yini musu koda Mummy taji shiru ta kira ta tambayi dalili kuwa ce mata yayi se zuwa dare ze shigo, zeci dinner a gidansu Amal. Kafin su dawo daga masallaci Amal har ta gama tsara kan dining da had'ad'd'un dishes ta bi gidan da turaren wuta. Nan tayi musu magana suka k'ariso se yaba abincin nata Daddy yake Afzal na ta jin dad'i ana yaba girkin matarsa. Hira suka sha kaman ba gobe anan Daddy ya gano ababe da dama tattare da Amal, he's in every way submissive to be a great Dad to Amal. Da yazo tafiya kuwa har wajen motansa suka rakasa sannan Amal tace a gaishe mata da Nazeefah.

   Washegari...
   Wajajen sha d'aya Amal ta dawo daga school bayan morning lectures nata ya k'are. Tana dawowa ta kama shara bayan ta gama ta aza tukunyan tuwo sannan ta d'au waya ta kira Mami wacce ta d'aga a karo na farko.

  "Halo Mami."

  "Na'am Amal ya kike?"

  "Ina yini Mami? Ya kike ya Papi?"

  "Lafiya k'alau ya Afzal?"

  "Yana office."

  "Makaranta fah?"

 "Alhamdulillah ban jima da dawowa bama kinsan mun kusa fara exams."

  "Aww haba? Se part 4 kuma ko?"

  "Eh in shaa Allah."

  "Toh Allah sanya alkhairi ya bada sa'a mamana."

  "Ameen Mami."

  "Ba wata matsala dai ko?"

   "A'a ba komai."

  "Toh madallah."

 "Mami jiya Daddy yazo."

  "Wani Daddy d'aya?"

  "Daddy mahaifin Nazeefah."

  "Kuma mahaifinki ba."

  "Eh" ta amsa tana murmushi "jiya yazo muka yini se bayan Isha ya tafi."

  "Allah sarki."

  "Yazo ya nemi tuba na."

  "Kin yafe masa?"

  "Eh Mami."

 "Madallah toh yayi kyau."

  "Mami kefa?"

  "Baby-"

  "Mami kiyi hak'uri komi ya riga ya wuce Daddy yace min yana son ya aureki."

  "Baby ke kanki kinsan baze yiwu in auri mahaifinki ba ko?"

  "Dalili Mami? Hasn't it always been your advocate to get married someday?"

  "Yes Baby amma ba ga mahaifinki ba."

 "Meyasa Mami? Didn't you loved him? Dan Allah kar kiyi ma Daddy haka."

  "Baby bazaki gane bane."

  "Toh meneh Mami? Daddy yana sonki har yau har gobe kema kin sani."

  "Baby ba wannan bane matsalar."

  "Toh meye ne?"

  "Mahaifiyar Nazeefah."

  "Mummy? Me tayi?"

 "Baby bakiya ganin kaman wani muguntan suke shirin yi mun? In ba haka ba a ina ne kika ta6a ganin inda uwar gida tazo nema wa mai gidanta aure?"

  "Gaskiya ba a ta6a yin hakan ba amma kuma I trust Mummy na tabbata Mummy baza ta ta6a aikata abinda ze cutar dake ba Mami."

   "Wai meyasa kike biye wa Mahaifin naki ne haka?"

 "Because he loves you Mami and he's sorry mey aciki idan kin yafe masa kunyi reconciling? Duk mun san abinda Daddy ya miki da ciwo da zafi amma yayi nadama Mami please kiyi hak'uri ki yafe masa ki sauraresa."

  "Baby-"

  "Please Mami do this for me" rok'an kanta Amal ta rik'a yi amma ina Mami fa sam babu a ranta ta auri Daddy. Suna gama wayan Amal ta kira Papi ta irga masa komai mamaki yasha yadda har abu haka ze faru amma Mami bata sanar da shi ba. Chan dare bayan sun k'are cin abinci yayi gyaran murya had'e da kiran sunanta.

   "Na'am Abba wani abu ne?"

   "Tun shekaran jiya kika ce Khaleefah be sake shigowa ba?" Dum taji zuciyanta ya tsinke amma sam bata kawo a ranta har Amal zata kirasa ta sanar da shi komai ba dan haka se tayi masa k'arya "A'a wani abu ne?"

   "Meyasa kike yi mun k'arya Jameela? Yaushe kika fara haka?"

  "Abba-"

  "Ashe har matarsa ya turo da ta baki hak'uri amma kika k'i sauraronsu?"

  "Abba ba haka bane."

  "Dakata tukuna, shi fa d'an Adam ajizi ne kuma dukan mu nan ba wanda zece baya yi wa Allah sa6o amma kuma mey? Da zaran muka tuba kuma muka nemi yafiyarsa yana yafe mana ba wanda yace Khaleefah ya kyauta abinda yayi miki amma tunda ya gane kuransa yana son ya dai-daita komai meyasa bazaki basa had'in kai ba?"

   "Abba ba haka bane."

   "Jameelah har yanzu ke yarinya ce shekarunki dududu nawa ne? Kin kai arba'in ne?"

  "A'a Abba"

  "Toh haka kikeson ki k'are rayuwarki ba aure? Bakiya son ki bar yaran da zasu yi miki addu'a bayan kin rasu? Ko gani kike Amal ita d'ai ta isheki? Kisani fa dan ba na nuna miki bawai hakan na nufin ina jin dad'in zamanki a haka bane, kiyi wa kanki fad'a ki dubi tuban mutumin nan ku rufa wa junanku asiri." Shiru tayi batace ko k'ala ba "Ko baki ji ba?"

  "Naji Abba."

  "Toh tashi ki tafi."

  "Toh seda safe." Ko bacci Mami ta kasa yi ranan se tuna abunda Amal da Papi suka fad'a mata take gabad'aya ta rasa mey take ciki ita har ga Allah bata k'aunan abinda ze sake had'ata da Daddy saboda kasa mancewa da abinda yayi mata da take. Duk sanda ta kallesa se ta tuna da wancan mumunar ranan taji ta tsanesa. Amma ya ta iya yanzu tunda har Papi yasa baki? Bayan nan kuma kaman yadda Mummy ta fad'a ko ba dan tana so ba kamata yayi ta amince saboda su gyara zuri'a su had'a kan yaransu. Daga k'arshe de kawai ta yanke hukuncin yin Istikhara duk abinda Allah ya za6an mata shi zata bi.

  _One week later..._

    Cikin satin nan da aka shiga su Amal da Nazeefah suka fara exams har yau Mummy bata sake ji daga Mami ba shima Papi be sake yi mata magana ba as ya zuba mata ido yaga iya gudun ruwanta. Amal da Afzal suna zaune a parlour se faman kallo yake a laptop nasa yasa earpiece a kunne ita kuwa se karatu take kasancewar tana da paper k'arfe d'aya gobe. Wayanta dake gefenta ne ya shiga ringing dubawanda zatayi taga new number, without hesitation ta d'aga tare da yin shiru.

  "Assalamu Alaikum" akayi sallama daga d'ayan 6angaren.

  "Mummy?"

  "Ashe 'yar tawa zata gane muryan uwarta."

  "Mummy ina yini?"

  "Lafiya k'alau ya kike ya gida ya Afzal kuma?"

  "Alhamdulillah dukan mu lafiya."

  "Ya exams toh?"

  "Alhamdulillah Mummy ya Nazeefah? Jiya ma Khaleefah ya kirani muka gaisa."

  "Allah sarki ya Mami?"

  "Lafiyarta k'alau."

  "Kwana biyu shiru banji daga gareta ba nace ko zaki iya mun texting number'nta."

  "Sure Mummy bari in miki texting yanzu."

  "Yauwa 'yata thank you Allah ya bada sa'an jarabawa."

  "Ameen Mummy seda safe" nan tayi hanging take tayi mata sending numban Mami, itama Mumny tana gani tayi replying nata da 'Thanks.'

   "Lafiya dai ko?" Afzal da ya zare kunnen earpiece nasa d'aya ya tambaya.

  "Lafiya kawai tana son su gaisa ne."

  "Oh Rania I'm hungry."

  "Toh Ya Omri baga kitchen ba."

"Aww ma ni zanyi girkin da kaina?"

  "Toh Ya Omri karatu fa nakeyi" ta fad'a cike da shagwa6a.

  "Ni o'o" ya fad'a harda doke kafad'a wanda hakan yasa Amal dariya. "Toh mey kakeso kaci?"

  "Na fasa chin abincin ma I just want to sleep."

   "Tun yanzu?" Ta tambaya had'e da duban agogo "it's just 9 O'clock."

  "Yes Rania na gaji kallon ma na fasa."

  "Toh sekaje ka kwanta ai seda safe."

  "Ni kad'ai?"

  "Toh Ya Omri baka ga karatu nakeyi ba?"

  "Nasani anan nake nufi" kafin ta karanci abinda yake shirin yi kawai taji ya sauk'e kansa a k'irjinta ita ta rasa damuwansa, ga gado amma yace shi se a jikinta ze kwanta adjusting kansa yayi ya kwanta da kyau a jikinta "Toh goodnight" tace da shi.

  "Goodnight Rania I love you."

  "I love you too Ya Omri" ta amsa had'e da placing peck a cikin gashin kansa. Handout nata ta d'auka ta cigaba da karatunta haka har bacci ya d'auketa itama. Se chan wajajen k'arfe biyu Afzal ya farka se jin numfashin mutum yake a kansa shafawa da yayi ya gano Amal ce. Murmushi ya saki sannan ya rik'e kanta ya janye nasa a hankali. Handout na hannunta ya cire ya d'agata ya kaita d'aki suka kwanta.

   Washegari Mummy da Daddy suka jesu gidansu Papi kaman yadda Munmy ta sanar da ita cewan zasu shigo sede bata ce da Daddy ba sam Mami batayi farin cikin zuwansu tare ba amma ya ta iya? Sannu da zuwa tayi musu ta shimfid'a musu tabarma sannan ta kira Papi inda duk suka gaisa.

   "Toh ga Jameelah nan sama da sati kenan yau ina jiran ji daga wajenta amma shiru se jiya da daddare bayan da Surayya ta kira take fayyace mun cewa tayi Istikhara kwanaki hud'u da suka wuce za6i kuma Allah yayi mata" se kuma yayi shiru.

  "Muna jinka Abba" Daddy da ya kasa hak'uri ya tambaya.

  "Khaleefah zan d'auki amanar 'yata in baka ba wai dan ka cancanta ba se don yin hakan ne ya kamata kodan mu samu mu had'a kawunan yaran nan. Kai ba yaro bane ka riga kasan komai ba sena sake nanata maka ba seka taimaki kanka kayi abinda ya dace wannan duka matanka ne ka kwatanta yin adalci a tsakaninsu Allah ya baku zaman lafiya gabaki d'aya batun yafiya kuma duka mun yafe maka Allah yafe mana gabaki d'aya."

  "Ameen Abba nagode sosai in shaa Alalhu zaka sameni mey rik'on amana Jameelah nagode Allah sak'a da alkhairi."

  "Ameen" duka suka amsa.

  "Abba in ba matsala bana so a jinkirta auren."

  "Toh Khaleefah gaskiya seka d'an bamu lokaci mu shirya."

  "Wani shiri Abba? Ba shirin da zakuyi zan d'au nauyin komai da komai ni kawai kar mu jinkirta."

  "Toh madallah zamuyi magana duk abinda tace haka za'ayi."

  "Toh nagode, nagode sosai zamu koma."

  "Toh Surayya kekuma Allah ya sak'a miki da alkhairi ya baki riban hak'uri tabbas irinku acikin mata d'ad'd'aiku ne Allah ya baku zaman lafiya mai d'aurewa."

  "Ameen Abba nagode" ta amsa.

  "Toh zamu koma ga wannan" Daddy yayi maganan had'e da zaro wani bak'in leda daga aljihunsa wanda yake d'auke da kud'i.

  "Na mey kuma? Kaga kar mu fara haka da kai."

  "Abba dan Allah kar kayi rejecting mu tafi Hjy Surayya." Duk yadda Papi beso kar6an kud'in ba seda ya kar6a saboda yadda Daddy yayita insisting.

   Da Maghrib bayan Daddy ya dawo daga masallaci Nazeefah tayi sallama ta shiga d'akinsa inda ta tarar da Mummy aciki. "Ya Nazeefah lafiya?"

  "Daddy ina son bayan graduation namu inyi proceeding masters program d'ina."

  "Toh masha Allah anan Unimaid zakiyi?"

   "A'a a UK."

  "K'asar waje?" Mummy tayi sayrin tambaya.

  "Eh Mummy."

  "Ko meyasa?"

  "Achan nafi so inyi yafi sauk'i."

  "Toh shikenan se ayi making arrangements amma ai sekin jira results naku sun fito."

  "Zan tafi tun yanzu in results d'in ya fito seku amsa min a tura mun achan, Nagode" tana kaiwa nan ta mik'e ta fice. Bayanta Mummy ta biyo "Why the sudden decision Nazeefah? I thought ke kikace bakiyason fita k'asar waje karatu?"

  "I changed my mind Mummy."

  "Saboda mey?"

 "Babu."

  "Saboda kiyi nesa da Amal yeah???"

  "Mummy Amal ba matsala ta bace bani da damuwa da ita I'm doing this for myself."

  "Ke Nazeefah bakiya tunanin mutuwa ne? Rayuwan ma nawa take da har kike neman gujewa 'yar uwarki haka?"

   "Amal ba 'yar uwata bace stop referring to her as one."

  "Da kin k'i da kin so Amal 'yar uwarki ce yanzu maganan da muke da Daddy'nku ma shirin auro mahaifiyarta yake Jameelah."

   "What? Wa d'in?"

   "Mahaifiyar Amal, Jameelah."

  "Wannan wani irin abin kunya ne? Kuma kika amince?"

 "Hasali ni na kawo masa shawaran ma saboda mun riga mun zama abu d'aya yanzu."

  "What? Mummy are you okay? Taya zaki amince Daddy ya k'ara aure, auren ma wai mahaifiyar Amal of all people? Wallahi baza ayi abun kunyan nan da ni ba."

  "Ya kika iya? The earlier the better Nazeefah just accept it mu da su mun zamo abu d'aya."

   "No Mummy bazan ta6a accepting su Amal as one of my own ba duk abinda kuke shirin yi count me out cause I'll never welcome their kind into my family."

  "Yayi miki kyau."

  ****
  Acikin wata d'aya Daddy yagama had'a d'akin Mami, an sa rana nan da sati uku. Da ikon Allah kuma su Amal suka k'are exams nasu results yafito alhamdulillah duk sunyi passing. Ba yadda Mummy batayi da Nazeefah ba da tabari se bayan d'aurin auren tayi tafiyan nata amma tak'i. Ana saura sati d'aurin aure tabar Nigeria.

   ****
   "Rania lafiya?" Afzal daya kasa hak'ura dan jin meke faruwa ya tambaya.

   "Ya Omri" kawai seta rushe da kuka.

  "Subhanllahi!" da sauri yayo kanta hugging her in his arms yana bata hak'uri. "Ya Omri ta tafi" ta amsa at last.

   "Ita wa?"

  "Nazeefah" ta sanar dashi yana share mata hawayenta.

  "Ta tafi ina?"

  "UK tabar Nigeria tace bazata sake dawowa."

   "What? Meyasa?"

  "Ya Omri har yau Nazeefah takasa acepting d'ina da Mami tun kafin ma taji Daddy ze auri Mami tace ita zata wuce Uk tayi proceeding masters nata yanzu kuma dataji gaskiyan al'amarin jiya bayan sunyi landing ta kira Mummy ta jaddada mata cewa bazata sake dawowa ba."

   "Shhh it's okay sooner ot later zata gano gaskiya in shaa Allah kuma da k'afarta zata dawo."

  "I really do hope so Ya Omri bana son Nazeefah tayi nesa da gida the more she stays away from us the more lost she'll be."

  "I know but don't lose hope okay? Nasan Nazeefah she'll soon come around."

  "Thank you Ya Omri."

   "Anytime, still zamu fita d'in ko?"

  "Yes."

  "Alright toh."

***

   Mami ce zaune a d'akinta ta baje zannuwa da dama a gabanta tana za6an wanda zata kai d'inki. Tana cikin haka sega wayanta dake gefenta ya shiga ruri dubawan da zatayi taga Daddy ke kira. 'Yar murmushi ta saki sannan ta d'aga.

  "Amarya bakiya laifi koda kin kashe d'an masu gida ne."

 "Haka de kace" ta amsa tana murmusawa.

  "Toh ya kike?"

  "Lafiya k'alau ya 'yar uwata?"

  "Lafiyanta k'alau yanzun tace tasan kanki yayi zafi k'ila ma kina jin yunwa amma ba hankalinki."

   "Ai kuwa wallahi ina ta sorting kayakin nawa."

  "Toh mey kikeso ayi miki ordering wai?"

  "Laaa kace mata kar ta damu zan dafa taliya in ci."

 "A'a nikam kinga aikana tayi fad'a mun."

  "Toh inde haka ne kace mata duk abinda ya sawwak'a."

  "Toh shikenan ki gaishe min da Abba."

 "Zeji se anjima."

  "Yauwa" da haka sukayi sallama.

  "Mey tace wai?" Mummy dake gefensa ta tambaya. "Cewa tayi akai mata duk abinda ya sauwak'a."

  "Toh se a sai mata fried rice and chicken ai ko ya kace? Ita da Abba."

  "Se abinda uwar gida tace."

  "Kai Alhj bana son zolaya fa."

   "Ai gaskiya ce."

  "Nifa har yau fushi nake da kai."

  "Afuwan in uwar gida na fushi dani a ina zan sa kaina?"

  "Eh mana kak'i had'ani da 'yar uwata a gida d'aya."

  "Ba wai nak'i bane Hjy Surayya."

  "Kak'i ne mana tun yaushe nake binka ayi a had'a ginin nan kak'i."

   "Ai kinga har yau aikin ake kan yi in shaa Allahu ana kammalawa zan dawo da ita nan chan d'in temporary ne."

   "Promise?"

  "I cross my heart."

  "Toh Allah nuna mana ."

  "Ameen Hjy Surayya nawa na kaina, bari in je in siyo ma 'yar uwar taki abinci."

  "Gaskiya kam kar mu bar amarya da yunwa."

  "Toh a dawo lafiya."
 
 ***
  Ranar Asabar aka d'aura auren Alhj Abdallah da Jameela Muh'd akan sadaki dubu d'ari da sisin gwal arba'in. D'aurin aure kawai akayi da yammacin ranan aka kai amarya d'akinta. Se wani tattalinta Daddy yake, bayan sunci kajin amarcinsu Daddy yasa su sukayi raka'a biyu dan yima Allah godiya.




RANA D'AYA!
#RD

 King miemiebeeđź‘„

Thursday, 20 September 2018

RANA D'AYA!

BY MIEMIEBEE
PAGE 44



   "Ummi no, ba ita bace."

 "Then wacece, Nazeefah?"

  "Eh Nazeefah, Nazeefah ce Ummi."

  "Ni yanzu ka rud'a min kai, Nazeefah ce tafi kwanciya maka a rai kokuwa ita zaka saka?"

  "Ummi hankalina yafi kwanciya da Amal."

  "Toh Alhamdulillah in shaa Allah hakan shi yafi alkhairi."

  "Ummi Nazeefah kuma fah? Shikenan yanzu semu rabu?"

  "Toh ya zamuyi Prince? Rabuwa da ita ya zamo dole se inde zaka bijire wa za6in da Allah yayi maka ka saki Amal wanda nima ba barinka zan ba tunda har Allah ya riga yayi ma za6i."

  "I know Ummi kuma nima komin yaya bazan ta6a iya rabuwa da Amal ba but Nazeefah kuma fa? Na tabbata baza ta ta6a yafe mun ba, zan iya cewa soyayya na ne kad'ai ya bata wuya a rayuwa. Lokacinda ta soma jin dad'in aurena kuma na kama na k'ara aure nayi mata kishiya. Ban ta6a kyautata mata ba Ummi and now da abunda zan sak'a mata kenan bayan duk wannan wuya da ta sha? I need to treat her right one more time please ki taimakeni Ummi."

  "Hak'urin nan de shi zan cigaba da baka Prince, nasan da wuya Nazeefah ta kar6i bak'on lamarin nan da hannu bibbiyu kaman yadda ka fad'a amma as time progresses zata gano cewa za6in Allah shine mafi alkhairi a gareku gabad'aya kuma ba kullum bane muke samun abinda muke so. Don yanzu koda ka bijirewa za6in da Allah yayi ma ka saki Amal kabar Nazeefah, ba alkhairin da ze biyo bayan hakan se ma sharri. Se ka ga ma rabon ya zame mata ajali, kuma zancen wai baka ta6a kyautata wa Nazeefah ba kaima kasan k'arya ne. Duk kulawan da ya kamata ace mace na samu daga gun mijinta kayi mata kuma itama ta sani, so just calm down and do what's right Allah na tare da kai."

  "Thank you Ummi" da haka ya katse wayan yayinda kalamun Nazeefah suke ta yi masa yawo akai. Ji yayi gabad'aya baze iya sauwak'e mata ba. Dama seda ta fad'a mishi cewa tasan Amal ze d'auka akanta saboda baya sonta  se Amal se gashi kuma Amal d'in ze d'auka yanzu. Sede ba don baya son ta bane kaman yadda ta fad'a se don Amal ce za6in da Allah yayi masa kaman yadda itama Yayi mata lokacin da zata aureshi. Tsoronsa d'aya kar wannan za6i ya sake 6ata tsakanin wannan 'yan uwa. Dan kaman yadda Nazeefah ta sanar da shi ya tabbata muddin idan taji Amal ya bari ya saketa seta tsani Amal fiye da yadda ta tsaneta yanzu. Oh Allah shin ya zeyi yanzu? Idan da ace ze iya rabuwa da dukansu biyu da yayi dan hakan shi zefi wa kowa kwanciyan hankali. Gara duka su rasa sa da ya d'au d'aya yabar d'aya amma yaya ya iya? Zuciyarsa bazata iya jure masa rashinsu duka ba barin ma Amal tasa da yake ganin idan har ya rasata baze iya sake samun mace mey kyawun halatayya irin tata ba. She's just different.

  Mik'ewa yayi a hankali yabar d'akin ya nufi nasu inda Amal ke kwance a kan gado se tunani take. Har ya k'arisa kan gadon bataji shigowansa ba. Seda ya kira sunanta tukuna.

   "Rania?" Da mamaki cike da tsoro ta mik'e zaune tana kallonsa. Bazata iya tuna when last ya kirata da wannan suna ba, probably tun da ya gano cewa ita da Nazeefah 'yan uwa ne. Ganin bata da niyyan amsasa seya mik'a mata hannunsa da nufin ta sa nata a ciki. Bayan dogon nazarin da tayi daga k'arshe seta mik'a hannunta ta sanya cikin nasa inda ya mik'ar da ita tsaye akan k'afafunta. Na matuk'a kanta ya d'aure yayinda zuciyarta ta shiga bugun tara-tara barin ma da Afzal ya rungumeta a jikinsa.

   Shikenan ya tabbata ita zata tafi. Se bata kawai jikinta yake itace ze saka, tasani zamanta da shi ya k'are, ta sani Nazeefah ce tafi kwanciya masa a rai, ta sani Nazeefah ce za6in da Allah yayi mata. Tabbas tayi musu murna sedai kuma tayi k'arya idan tace bata ji zafin hakan ba because she loves him. No matter how hard she tried not to show how terrified she felt takasa saboda yadda take jin zafin rabuwa da shi. Kawai ji tayi hawaye na gangaro mata daga ido dai-dai wannan lokaci Afzal ya d'agota daga jikinsa da k'yar dan yadda ta kankamesa. Cike da mamaki ya tsaya kallon yadda take kuka sannan daga bisani ya shiga share mata hawayen nata "Please don't cry Rania."

   "I should really start packing my clothes" ta sanar dashi tana mey hana k'wayoyin idanunta had'uwa da nasa. "I'm really happy for you two Yaya, Allah ya baku zaman lafiya mey d'aurewa."

   "Mey kike cewa haka Rania? Zaman lafiya tsakani na da waye?"

  "Da Nazeefah."

   Murmushi ya saki kad'an "Meyasa kika ce haka? Why not you?"

  "Saboda bani ce za6in da Allah yayi maka ba Yaya. I know I'll be the one to leave and even though nima hakan ne ze fiye mun kwanciyan hankali I just can't deny the fact that I still love you so very much and I'll miss you so damn much."

   "But you don't have to miss me Rania because you're not going anywhere, this is your home anan kuma zaki cigaba da zama ba inda zaki."

  "No ba sekayi hakan ba Yaya, zanje in samu Mami a gida, chan d'in ze fiye mun kwanciyan hankali yaso ko haya ne se kasa a nan d'in." Dariya sosai ta basa wanda ya kasa dannewa yayinda ta tsaya kallonsa cike da mamaki da takaici. Mey yake nufi da hakan?

   "Rania listen to me, ba inda zakije nan ne gidanki kuma d'akin mijinki okay?"

  "D'akin mijina? Nazeefah kuma fa? Karka bijire wa za6in Allah saboda son zuciya Yaya. Idan kuma tsoron abinda Papi da Mami zasuce kake then ka kwantar da hankalinka kasani duk zasuyi maka kyakkyawar fahimta kaman yadda nima nayi maka. We all know you love me Yaya, please don't bother yourself."
 
   "Tsaya, kafin muyi aure mey kikayi? Kinyi Istikhara right?" Kai ta gyad'a masa a hankali cike da rashin fahimta sannan ya cigaba "Kuma bayan da kika gudanar se waye Allah ya za6a miki?"

   "Kai Yaya" ta amsa a takaice.

  "Kina ganin it is possible ace ni kuma nayi Istikharan yanzu se wata ta daban ta zame za6in da Allah zeyi mun bayan ke kuma ni Ya za6a miki?"

  "But Yaya-"

  "Ki sani Rania ko sau dubu mutum yayi Istikhara za6in Allah d'aya ne sedai idan shi yaso bijire wa hakan. Kaman yadda kikayi naki istikharan Allah ya za6a maki ni, nima haka ya za6a min ke yanzu. We two are meant to be Rania in shaa Allahu mutuwa ce kad'ai zata shiga tsakani na dake. Rania I love you so much kuma Allah kad'ai ne sheda game da irin son da nake yi miki, shi kad'ai yasan idan bake bazan iya rayuwa ba, shi kad'ai yasan muddin na rasaki bazan ta6a iya samun kamilar mace mey kyawawan d'abi'u da halatayya irin naki ba shiyasa ya za6an min ke ya sake bani daman da zan soki in kuma kula dake har ila k'arshen rayuwa na. I can't do without you Rania and I can't ask God for more da ya sake bani daman kasancewa mijinki, forgive me for all the times I've wronged you Rania, I'm terribly sorry please forgive me."

  Kuka Amal ke sosai yayinda ta kasa amincewa da abubuwan daya fad'a mata. Se gani take kaman a mafarki komai ke faruwa tabbas itama bazata iya rayuwa idan ba shi ba. Gani take kaman duk yadda yake jin yana sonta ita tafi sonsa, don dai kawai ita bata nunawa ne. Daga k'arshe kuma bazata iya yima Allah godiya ba da ya sake bata daman kasancewa matarsa, sai dai kuma bazata iya duba irin rayuwan k'unci da tashin hankalin da Nazeefah zata fad'a ba a rashin Afzal. Se gani kawai take inda itace Afzal yace ze sauwak'e wa. Tasan duk kalan rashin tawakkalinta tana bayan Nazeefah. Tasan Nazeefah na iya yin k'aramin hauka akan wannan dalili, she knows this is not going to be easy on her shiyasa take tausaya mata sosai.

  "Rania?" Ya kirata bayan shirun da tayi, jikinsa kawai ta fad' yayinda ta shiga yin kuka na sosai. "Bakayi mun komai ba Yaya don haka ka daina tambaya na yafiya I love you so very much." Ba k'aramin dad'i kalamanta suka sanyasa ba, matseta tsam ya sakeyi a jikinsa tamkar ana shirin k'watan masa ita yayinda wani irin sonta yake sake shiga zuciyansa. Sun dad'e a haka sannan daga bisani ya janyeta daga jikinsa sede har anan hawaye Amal ke.
 
  "Please don't cry Rania."

  "I wish I could stop Ya Omri."

  "But there's no need to."

  "There's every need to cry Ya Omri."

  "Saboda ban barki kin tafi gida kaman yadda kikeso ba kike wannan kuka Rania? Saboda Allah ya za6an min ke? Ashe ba haka kika so ba, I thought you said you love me" Kai ta gyad'a mishi take tana murmushin takaici.

  "Then meyasa kike kukan? A tunani na this is supposed to be the most happiest moment for us both."

   "Yes it is Yaya kuma hawayen nan da kake gani, hawayen farin ciki ne gani nake kaman a mafarki komai ke faruwa, I can't believe that we're still going to remain married to each other after hope has been gone."
 
   "I feel thesame way Rania, but tun farko tun kafin in gudanar da Istikharan nan nasan komin yaya akayi ni dake bamu rabuwa."

  "Ko meyasa kace haka?" Tayi saurin tambayansa cike da mamaki.

  "Saboda Istikharan da kikayi kafin mukayi aure Rania, idan da har ace akwai sharri a auran mu da Allah baze za6a miki ni akan Abdul daya kasance masoyinki ba. Idan har na rabu dake kinga kenan babu amfanin istikharan da kikayi. Ko ce miki akayi shi istikhara temporal decision ne na d'an lokaci? Hankali na ya tashi ne gabad'aya saboda Nazeefah. Ina matuk'an tausayawa halin da zata shiga idan har ta gano cewa I chose you over her, shiyasa nayi coming up da plan na cewa zanyi Istikhara kinga idan har nayi ita da iyayenta bazasuyi mun mumunar fahimta ba, zasuga za6in Allah nabi ba wai na zuciya na ba. Sedai kuma yanzu bayan dana gudanar da hakan nakega still Nazeefah bazata amince ta kar6i wannan bak'on lamarin da hannu bibbiyu ba. Nasan komin tayaya bazata ta6a fahimtar cewa Allah ne ya had'ani dake ba, bazata ta6a gane cewa ba komi mutum yake so a duniyan nan yake samu ba, gani take komai laifinki ne Rania and that is what hurts me the more knowing who you really are. Bana son a sanadin hakan ta sake tsanarki, ita gani take komai laifinki ne, ke kika janyo bayan ba haka bane. I wish Nazeefah could see this kind and selfless side of you.  Har yau kalaman ki na yinin ranan da na sanar dake cewa Nazefah k'anwarki ce suna kaina. Har yau na kasa mancewa dasu kuma bazan ta6a mancewa da su ba. Yadda kika cire son kai kikace kin yafe ni wa Nazeefah even though kina so na bawai bakiya sona ba se don cewa da Annabi yayi "La yu'minu ahadukum hatta yuhibbu li akhihi ma yuhibbu li nafsihi" [imanin d'ayanku baya cika har seya so wa d'an uwansa abinda ya so wa kansa] I get that you love me but you're willing to let your sister have me and ba kowa keda irin imanin nan naki ba Rania ko ni nan bazan iya aikata abinda kikayi ba ranan saboda haka kuma naji respect naki ya k'aru a idona yayinda sonki ya sake k'aruwa a zuciya na."

  Murmushin jin dad'i ta sakar masa tana mey share hawayenta "Ka sani ko da nace maka hawayen nan na jin dad'i ne k'arya nayi because zuciyata tausayawa Nazeefah take, I can't imagine the kind of hell she'll go through Yaya don haka har nakejin kaman mu hak'ura da juna sedai kuma bazamu iya yin jayayya da za6in Allah ba."

  "Hakane Rania, let just pray for her in shaa Allah as time progresses zata fahimci komai ta kuma nemi gafararki ayi zaman lafiya gabad'aya."

  "Da kuwa ba abinda zefi mun hakan farin ciki da jin dad'i Yaya. Inspite of how Nazeefah disperses me wallahi I still love her kuma zan cigaba da sonta ina yi mata uzuri har zuwa lokacinda zata gane gaskiya."

  "Allah yayi miki albarka Amal ya baki yaran da zasu kula dake ranan da buk'atan hakan ya taso Rania, I'll forever love, cherish and adore you."

   "Ameen Ya Omri I love you too."

  "Let's eat out ai zaki iya fita ko?"

 "Why not? Bari in shirya."

***
   Washegari...
 
   Dai-dai gaban gidansu Nazeefah yayi parking sannan ya zaro wayansa ya kira Daddy a karo na farko ya d'aga.

  "Halo Afzal ka iso ne?"

  "Eh Daddy."

  "Toh bismillah mana ka shigo." Harga Allah beyi niyan shiga ciki ba amma yaya ya iya? Gyara packing nasa yayi ya k'arisa ciki inda ya samesa a parlour ya gaishesa. Bayan sun gaisa ya zaro takardan daya ninke daga aljihunsa ya mik'awa Daddy "Kaman yadda nayi muku alk'awari cewa zanyi Istikhara, duk kuma wacce Allah ya za6ar mun ita zan d'au in sauwak'e wa d'ayan. Toh game da sakamakon dana samu bayan na gudanar da Istikharan na yanke wannan hukunci ba don son kai ko son zuciya ko makamancin haka ba, da fatan kai da iyalanka zakuyi mun kyakkyawar fahimta. Ga takarda nan na sakin Nazeefah, dafatan ze isa gareta zaka kuma bata hak'uri a madadi na ni zan wuce."

   "Dakata Afzal kar kayi saurin tafiya. Kayi hak'uri ka bani dama in baka hak'uri na jefaka da iyalinka cikin wannan rud'ani da tashin hankali da nayi. Kuma ka sani wannan hukunci daka yanke shine dai-dai koda ma ace bakayi istikhara ba bazan bari ka saki Amal ba saboda abinda nayi mata da mahaifiyarta kad'ai ya ishesu takaici da jarabawa. Dole nima in gir6e abinda na shuk'a. Da fari na d'au zan iya yi wa Allah wayo, na d'au idan har na aurar da Nazeefah shikenan bani da wani tsoro kuma ashe ba haka abun yake ba, ashe ita zina bashi ce idan har ka cita dole komin ta yaya ne ka biya. Kuma muddin ba a kaina ze ramawa Jameela abinda nayi mata ba dole se akan wanda nakeso. Dukda cewan Amal da Nazeefah 'ya'yana ne amma kaman yadda zanfi jin zafin sakin nan akan Nazeefah ba haka zanji ba idan da akan Amal ne saboda babu shak'uwan nan na uba da 'ya a tsakani na da ita. Allah ya za6an maka Amal ne saboda ya koya mun da 'yata darasi kuma saboda itama koda sau d'aya ne taji dad'in rayuwa. Ka sani wannan hukunci da ka yanke dai-dai ne kuma zanyi k'ok'ari in fahimtar da iyalai na, Allah ya baku zaman lafiya mey d'aurewa da Amal ya albarkaci rayuwanku in shaa Allah zan isar wa Nazeefah sak'onka."

    "Nagode sosai Daddy."

  "Ba komai, se kuma batun Jameela bazan gaji da rok'an kanka ba da kayi mun kwatance injeni gidansu in nemi tubarsu, idan ban samu sun yafe mun ba alhak'insu ya cigaba da bi na kenan, ka tausaya mun da iyalai na please Afzal."

   "In shaa Allah zanyi ma Papi magana karka damu."

  "Toh nagode sena ji daga gareka."

  "Ba komai ni zan wuce" ya fad'a had'e da mik'ewa "Ka gaishe da Amal ina da niyyan shigowa inzo in dubata nima in nemi tubarta amma ina son in d'an bata lokaci saboda nasan yadda zata ji ta tsaneni yanzu."

   "Zataji Daddy se anjima" yana kaiwa nan ya fice ya koma office har a yau idan ya gwada kiran layin Nazeefah bata d'agawa. Ba komai yasa yake son ya kirata ba se don so da yake ya bata hak'uri, baya son taga kaman baya sonta ne, har yau har gobe ze cigaba da sonta saboda akwai gur6in da ita kad'ai ce ta mamaye a zuciyansa. Ita ce macen da ya fara sani a rayuwansa, itace macen da ya fara sumbata itace macen da ya fara sharing wani abu nashi da ita. Shin har ze iya mancewa da ita a rayuwansa? He don't think so.

  ****
    Daddy be samu ya kaiwa Nazeefah takardan nata a ranan ba se a washegari. Bayan ya dawo daga sallan Azahar ya d'au wayansa ya kira Mummy sedai kaman yadda ta saba ignoring call nasa hakan ma tayi yau don haka ya tura mata sak'o.

  _Hjy Surayya kiyi hak'uri ki d'au wayan nan muyi magana. This is not about me it's about our daughter Nazeefah, thank you._
  Sak'on ya shiga bada dad'ewa ba Mummy ta karanta se contemplating take ta kirasa taji lafiya ne ko ta bari. Chan k'arshe de ta kira wanda ya d'aga a karo na farko. Bata basa daman yin magana ba tace, "Meya samu Nazeefan?"

   "Hjy Surayya wannan ba maganan waya bane gani nan tahowa yanzu."

  "Karka 6ata lokacinka bana nan na fita."

  "We both know k'arya kikeyi zanzo yanzu please" bata sake ce meshi komai ba ta katse wayan. Cikin mintuna da basu kai ashirin da biyar ba sega shi nan ya iso. Waya yayi mata akan ta fito nan da nan ta sanya hijabinta ta fice.

  Ba yadda Daddy beyi ba da su k'arisa koda reception ne su zauna suyi magana tak'i, tace ita idan har baze fad'i abinda yake tafe dashi ba zata koma ciki. Toh suje cikin mota su zauna nan ma tak'i. Yasan sam bey kyauta mata ba amma ba wai yayi hakan dan ya raina ta bane ko makamancin hakan, shi tsoron sanar da ita yake gudun kada ta gujesa kaman yadda takeyi yanzu.

   Hannu yasa a aljihunsa ya fito da takardan had'e da mik'a mata.

  "Mey wannan?" ta tambaya ba tare da nuna yunk'urin amsa ba.

  "Kedai bud'e ki gani." Kaman wacce bazata kar6a ba ta amsa ta bud'e had'e da karancewa.

   _A ranan Laraba, goma ga watan Juneru shekara dubu biyu da goma sha takwas na saki matata Nazeefah, saki d'aya, biyu, uku saboda haramta mana zama da shari'a tayi a sanadin ta na kasancewa 'yar uwar matata Amal na  jini._

  Ajiyar zuciya Mummy ta sauk'e dama tasan za'ayi haka. Dama tasan Nazeefah ce Afzal ze saka kawai bata so ta nuna mata bane don kar ta tayar mata da hanaki amma tasan haka za'ayi dama kodan ma Allah ya kama Daddy yasa shima yaji zafin da mahaifiyar Amal taji sanda yayi mata fyad'e. Tasani dole ne wannan k'addara ya fad'a akan Nazeefah saboda itama Amal ta samu farin ciki koda sau d'aya ne a rayuwarta. Idan harda ace wannan saki akan Amal ya fad'a da Daddy baze ji zafi kaman yadda ace zeji yanzu da ya fad'a akan Nazeefah. Ta hakan ne kawai Allah ze sanyasa gir6e abinda ya shuk'a, ta hanyar mayar masa da 'ya bazawara kaman yadda ya k'wace wa 'yar mutane budurci.

   "Shikenan ka huta ai yanzu Alhj, amma kasani nida 'ya'yana bazamu ta6a yafe maka wannan abun kunya daka aikata ba." Be bari ta shiga takawa ba yayi sauri ya rik'e k'asan hijabinta "Hjy Surayya bazan ma fara tambayan gafararki ba saboda nasan abinda nayi miki da 'ya'yanki is unforgivable but atleast give me a chance to apologize and tell you sorry. I'm gravely sorry for hiding the truth away from you, wallahi bawai don bana sonki bane kokuwa don bana mutuntaki yasa na 6oye miki wannan al'amari, sonki da nakeyi ne ya rufe min ido, bana son abinda ze shiga tsakani na dake Hjy Surayya, bana son in rasa ki. Dan son zuciya irin nawa se naga idan har na sanar dake gaskiya zaki gujeni kik'i aurena shiyasa na rik'e komai wa kaina. I love you so much Hjy Surayya and I'll never stop loving you, I'll wait. Zan jiraki koda kuwa zuwa k'arshen rayuwana ne amma bazan gaji da baki hak'uri ba dan Allah kiyi hak'uri ku dawo gida."

   "Babu wani abinda zaka sake fad'amun da zaisa in canza ra'ayina. Idan 'ya'yanka kake so kana iya shiga ciki yanzu ka ebosu amma nikam takarda na nikeso. Kaman yadda ka shiga tsakanin auren yaran nan kasa Afzal ya saki Nazeefah saki ba d'aya ba, ba biyu ba har uku nima haka nake so ka rubuta mun nawa. Idan har 'yata zata shiga k'uncin rayuwa ka tabbata kai m seka shiga ninki ba ninkin nata don haka ka rubuta min takarda na yanzun nan anan. Tunda rayuwan zawarci ka za6a wa 'yarka tayi nima mahaifiyarta shi zanyi."

   "Dan Allah kiyi hak'uri Hjy Surayya nasan nayi miki laifi, laifi babba amma dan Allah kiyi hak'uri ki gafirceni. Idan kika tafi kika barni ya kikeson in rayu?"

  "Bakayi tunanin hakan ba kafin ka danne 'yar mutane kayi mata fyad'e? Se kaje chan ku k'arasa da ita mahaifiyar Amal d'in that is idan har zata iya yafe ma zaluntar ta da kayi."

  "Kema kinsan bazan iya rayuwa da kowa ba bayan ke Hjy Surayya, kinfi kowa sanin yadda nake sonki tun ba yau ba."

   "Sam ba haka bane, I was a fool to believe you love me Alhj, yaci ace tun a lokacin chan na gane kud'in mahaifina kawai kake so ba ni ba. Wallahi Allah ne kad'ai ze sak'a mun. Duk kalan halaccin danayi maka na sa mahaifina yayi maka duk baka ga hakan ba you still chose to lie and cheat on me."

   "Dan Allah kiyi hak'uri bazan ta6a gajiya da baki hak'uri ba saboda nasan ban kyuata ba amma wallahi I love you Hjy Surayya I really do."

   "Shin anya ma kuwa labarin daka tsara min da iyayena na cewa kai maraya ne gaskiya ne kuwa? Shin anya kuwa ba k'arya ka shirya mana ba saboda ka samu kaci arzikin mahaifina Alhj?"

  Shiru Daddy yayi gun ya kasa cewa komai. Tabbas yayi mata da mahaifinta daya kasance hanshak'in mai kud'i bahaushe daga Kano k'arya lokacinda yazo aurenta. Saboda gudun da yake kar a nemi iyayensa kowani d'an uwansa a garin hakan asirinsa ya tonu na cewa yayi ma wata fyad'e a k'auye Mummy ta fasa aurensa ko iyayenta su hanata. Tun bayan da abin ya faru ya samu ya dawo makaranta be sake d'aga wayan iyayensa ba, duk lokacinda yaga kiransu baya d'agawa har ta tsinke saboda yasan akan mey zasuyi masa magana shi kuwa bayida abin cewa. Daga k'arshe ma da yaga kiran ya soma isansa se kawai ya sauya lamban wayansa gabad'aya, tun daga nan be kuma sake ji daga garesu ba se...
 
   "K'arya kayi mana ko? Why aren't you saying anything Alhj?"

  "Hjy Surayya yes, yes nayi miki da Abba k'arya batun iyayena amma wallahi ba don bana respecting naki bane se don tsoro da nake kar a garin hakan gaskiya ya fito in rasaki."

  "Wani gaskiya?" tayi saurin katsesa.

  "Batun abinda ya faru tsakani na da mahaifiyar Amal."

   "Wane irin mak'aryaci ne kai Alhj? Mey nayi maka a rayuwa da ka za6i ka gina duk wani abinda mukayi accomplishing tare akan k'arya?" Ta tambayesa hawaye na saurin ciko mata a ido. "All I did was to love you Alhj I'm so disappointed in you na tabbata da Abba yana raye a yau da shima baze ta6a yafe maka ba."

   "I'm truly sorry Hjy Surayya amma abinda ya faru ya riga ya faru idan da zan iya mayar da lokaci baya da nayi dan in gyara komai amma bazan iya ba please give me a second chance idan kika tafi kika barni taya kikeson in rayu? Tabbas idan ba ke su Nazeefah bazasu amince su dawo gida a gareni ba please kiyi hak'uri."

   "Bayan k'aryan nan se kuma wani k'arya ka sakeyi mun?"

  "Hjy Surayya a shirye nake da in sanar dake duk wani abinda kike buk'atan ki sani amma zaki galabaita tsaye a nan saboda labarina nada tsawo kiyi hak'uri mu shiga mota kokuwa mu k'arisa cikin reception." Bata ce da shi komai ba kawai ta shiga takawa yayinda yake biye a bayanta, a VIP reception suka zauna sannan Daddy yayi gyaran murya ya soma kaman haka.

   "A shekaran da na dawo hutun second year d'ina ne muka had'u da mahaifiyar Amal wato Jameela wacce nake kira da Jamee na. Jameela ta kasance itace mace ta farko da Allah ya fara sanya min soyayyarta a zuciya na, so kuma na aure bana lalata ba. We started off as friends amma cikin k'ank'anin lokaci soyayya mey k'arfi ya shiga tsakaninmu. Jameela was simply everything I could ever ask for, lokacin da muka fara soyayya kwata-kwata shekarunta goma sha shida ne, she was so beautiful, young and innocent. Tsaftacacciyar soyayya muka gudanar nida ita as ko zance naje wajenta iyaka muyi hira ba wani ta6e-ta6e bale makamancin hakan saboda Jameela yarinya ce kamila wacce take san addininta sosai take kuma k'ok'arin bin dokokin da ya kafa mata. Ahaka ne har nazo na koma makaranta wanda bada dad'ewa ba Jameela tayi mun waya cewa mahaifiyarta na shirin had'ata aure da d'an chairman na garinmu idan har ban hanzarta turo magabata na ba ana iya aura mata shi d'an chairman d'in. Hankalina ne ya matuk'an tashi se Allah-Allah nake session d'in ya k'are in dawo gida. Kasancewar a scholarship na samu karatun seya zammana banida gatan dawowa gida kowani hutu se shekara-shekara. Addu'a muka tsayar sosai nida Jameela cikin ikon Allah kuwa se har wata shekarar ta zagayo shi wannan yaro be turo ba. Na dawo bada dad'ewa ba na samu mahaifina nayi mishi maganan Jameela akan ina son a tura tambaya gidansu sede sam Abba yak'i amincewa akan cewa da baki na ne zan ajiye mata idan nayi aure yanzu ina karatu. Duk yadda naso fahimtar dashi cewa Jameela bata da matsala da hakan besides ma ina d'an yin business, makaranta kuma shekara d'aya ne ya rage sedai hakan ya gagara Abba yak'i ya amince ya bani goyin baya. A sanadin haka nida Jameela muka shiga tashin hankali sedai bamu cire rai ba, muka mik'a komai ga ubangiji. Ban san ya akayi ba de amma wataran mahaifiyar Jameela ta jiyota muna waya bayan kuma ita ta riga tayi mata miji a sanadin haka tayi ma Jameela duka tayi seizing wayarta sannan ta horeta da kada ta sake kulani. Kwana biyu na daina ji daga gun Jameela ko na kira layinta baya shiga gashi sun k'are makaranta lokacin bale inje mu had'u a chan d'in. Rana d'aya kawai na jajirce na jeni gidansu dan yadda shirun yayi yawa, dukda cewan ta haneni da taka bakin k'ofan gidnasu saboda yadda ta nuna mun mahaifiyarta bata sona. A farko da naje mahaifiyar ta kar6eni da fara'a kasancewar bata gane waye niba a lokacin da nayi mata bayanin kaina kawai ranta ya 6aci ta sauk'e duk wani haushin da takeji a kaina tayi mun koran kare harda muciyan tuwo ta bini waje. Hakan ba k'aramin 6ata mun rai yayi ba dan dole na hak'ura da Jameelah saboda a rayuwa na washi walak'anci na kuma d'au alwashin sena rama cin mutuncin nan da tayi mun ko ta yaya ne. Rana d'aya ina zaune kawai sega kiran Jameelah ban 6ata lokaci ba na d'aga inda take sanar dani tana son mu had'u. Chan na kaita bayan gari da siyasan cewa abu nake so in nuna mata, ina son Jameelah amma abinda mahaifiyarta tayi mun ya tsaya mun a wuya ko kallonta nayi se na tuna da abin. Haka kawai shaid'an ya soma raya mun in d'au fansa akanta sedai kuma sonta da nake yana rik'eni. Amma haka shaid'an ya rinjayi zuciyana ta hanyan raya mun ai tunda mahaifiyarta tana sonta idan na ta6a lafiyarta kaman na ta6a na mahaifiyar ne don haka idan na lalata mata rayuwa abun seya fi wa mahaifiyar zafi. Ana cikin haka ne sega abokai na guda biyu dana basu labarin abinda mahaifiyar Amal tayi mun nan suka sake k'arfafamun guiwa suka bani had'in kai nayi ma Jameela fyad'e ba tare da d'igon imani ba."

   "Koda mahaifinta ya kai k'arana dana mahaifina gurin mey unguwa k'aryata komai nayi na samu abokaina suka rufa mun asiri shima Abba ya goya mun baya saboda baze ta6a kawowa a ransa zan iya aikata abinda nayi ba. Acikin satin ko na gaba na samu na koma makaranta ban sake ji daga garesu ba. A karon chan ne na had'u dake Surayya, kika yi mun erasing duk wani bad memory'n dana bari da a k'auyen Askira. Tunda na sameki komai ya canza Surayya, soyayyar da kika nuna min ta dabance. Banida komai, Baki sanni ba, baki san wani nawa ba amma kika so ni kika kuma amince dani regardless. Ko a mafarki ban ta6a tsammanin cewa wataran zan iya mallakan 'yar babbar gida kamar ki ba mey hankali da tausayi. Lokacin da kika ce mun muyi aure ne nashiga tashin hankali badon bana sonki ba se don banason hakan ya tono mun labarina dana bari a garin Askira. Ban san da wani idon zan sake kallon iyayena da na shafesu a doron k'asa saboda selfish interest d'ina ba na kusan shekara. Rud'ani na matuk'a na shiga yayin da na rasa ya zanyi gashi bana son in rasaki saboda da in rasa ki gara na rasa komi nawa koda kuwa raina ne. Don haka nayi miki da Abba k'aryan cewa ni maraya ne. A tunani na hakan ne kad'ai zaisa Abba ya amince ya aura min ke Surayya. Ba abinda Abba beyi mun ba bayan dana aureki, abinda ya kama kayan da zansa, gidan da zamu zauna, motan da zan hau harta sadakin ki shi ya biya mun, komai da na sani na mallaka a lokacin na Abba ne. Harta aiki shi ya samo mun bayan da ya biya mun kud'i na gama masters d'ina muka dawo gida nan Nigeria idan ban manta ba kina da cikin Khaleefah."

   "A lokacin da muka dawo ne bayan na tafi yin service d'ina na koma k'auyen Askira dan d'auko su Abba in nemi tubansu in basu hak'uri ake tabbatar min da cewa sunyi hatsari shekaru biyu da suka wuce a hanyansu na zuwa k'auyen Dambuwa. Shi Abba a take ya cika ita kuwa Umma tayi jinyan wata shida sannan mutuwa yayi halinsa. I felt hopeless and useless Surayya, iyayena sun mutu amma seda shekara biyu nake sani. Ji nayi kaman in soka wuk'a wa kaina in mutu wani irin d'a ne ni? Na sosai nayi nadaman abinda na aikata na d'au alk'awarin yin sadak'atul jariya da sunayensu Allah ya kai musu ladan kabari. Nasan rashin kyautatawan da nayi wa iyayena yasa nima Allah ya jarabce ni da gagararriyar 'ya kaman Nazeefah.l

   "Daga gida na wuce gidansu Jameelah inda ake sanar dani suma sun tashi sun k'aura sun bar garin gabad'aya. Ba wanda ya sanar dani cewan rabo ya shiga tsakani na da ita bayan faruwan abun shiyasa ban ta6a sanin Amal 'yata bace se recently. Wallahi ba k'arya nake yi miki ba Surayya please believe me, taya zan so in had'a 'ya'yan cikina kishi Surayya bayan na san yin hakan haramun ne?"

    "Yanzu ina ita mahaifiyar Amal d'in take Jameelah?" Mummy data amince da duk wani abinda ya fad'a ta soma da tambayansa.

  "Tana cikin garin nan da zama amma bansan inda take ba, rannan Afzal ya taho da ita da mahaifinta gidan Nazeefah inda mukayi magana duka akan yadda za'a 6ullowa al'amarin nan nasu."

 "Baka san inda take ba kace?"

  "Wallahi ban sani ba Hjy Surayya ai kinsan bazan miki k'arya ba."

  "Bawai ina k'aryata ka bane Alhj I just want to be certain, tana da aure?"

   "Wallahi banda masaniya akan hakan amma base on abinda Amal ta ta6a fad'amun kaman mahaifiyar nata bata da aure."

  "Ka aureta Alhj" ta sanar dashi. Da mamaki ya tsaya yana kallonta yayinda ya kasa amincewa da abinda tace.

  "Eh?" Ya tambaya.
 
  "Nace idan har Jameelah bata da aure kuma bata niyyan yin wani auran anan kusa ka aureta."

  "Hjy Surayya kin ko san abinda kike cewa?"

   "This's the only way zamu iya samu mu had'a kan yaran nan Nazeefah da Amal mu gyara zuri'ar mu. Ka fini sanin halin Nazeefah, yanzu da Afzal ya d'au Amal a kanta ba k'aramin tsanar yarinyar nan zatayi ba dama already ta riga ta tsaneta."

  "Toh mey auro Jameelah zeyi ya gyara wannan lamari Hjy Surayya?"

  "Tabbas auro Jameelah zaisa Nazeefah ta shiga hankalinta ta nutsu ta sani cewa mu dasu mun riga mun zamo abu d'aya yanzu ta kuma sani cewa shi kishiya na akan kowa ne idan har da tanayin kwatance dani tagani toh yau nima gashi anyi mun kishiya."

   "Tabbas kinyi gaskiya Hjy Surayya amma bana son in had'a soyayyarki da kowa ke kad'ai nakeso."

  "Karka damu dani kuma ma ai nasan kana son Jameelar taka har yau ko ba haka ba?"

  "Amma ba kaman yadda nake sonki ba Hjy Surayya ni tausayin Jameelah kawai nake yanzu."

  "Karka damu ai ni nace ka aurota."

  "Hjy Surayya nifa banga amfanin yin hakan ba. Ba sena auro Jameelah ba."

  "Ka aurota Alhj ni na baka dama karka damu."

   "Surayya-" hannunta ta aza akan nasa cutting him off "Don't worry nima ai zama ni d'aya tal d'innan ya isheni ka kawo mun abokiyar zama tana tayani hira na tabbata kaman yadda Amal bata da matsala itama mahaifiyar tata haka ne."

   "Wannan ba sekin fad'a ba Hjy Surayya Jameelah sam batada hayaniya."

  "Toh kaga komi ya zo mana da sauk'i kenan, ka auro ta kaji?"

   Hjy Surayya what can I say? You're the reason behind who I am today and everything I've achieved, banida bakin yi miki da Abba godiya. Allah saka da alkhairi ya cigaba da sanya miki albarka a rayuwarki ya kuma ci gaba da kai rahama kabarin Abba."

   "Ameen Alhj tare da iyayenka kai ma."

   "Kin hak'ura zaki biyoni gida?"

  "Har sena amsa tukuna zaka tabbatar da hakan?"

  "Gani nake kaman mafarki nake Hjy Surayya, Allah yabar min ke tabbas irinku acikin mata d'ad'd'aiku ne."




RANA D'AYA!đź’•
#RD

 Love... King Miemiebeeđź‘„✨