Saturday 6 October 2018

RANA D'AYA!

BY MIEMIEBEE
PAGE 46




    Washegari...
Hayaniyan da Daddy ya jiyo a kitchen ne ya sanyasa fitowa daga d'aki inda yake kwance. Mami ya tarar tsaye gun sink ko mey takeyi oho.

  "Jamee na mey kuma kike yi?" Ya tambayeta tsaye daga bakin k'ofan.

   "Oh Alhj!" Ta juyo a d'an razane "Har ka tashi ne?"

  "K'aran kwanukanki suka tadani" ya sanar da ita.

  "Ayya yi hak'uri inzo in mayar da kai baccin ne ko zaka koma da kanka?"

  "Ko d'aya tambaya nake mey kikeyi?"

  "Oh! Doya nake ferewa Abba kasan bey karya ba."

  "Inji wa? Ai da kin tambaya, tare aka siyo mana breakfast d'in nasa mey gadi ya kai masa nasa se inde zaki site nasa ku gaisa."

  "Allah sarki nagode."

  "Jimin matan nan fa godiyan mey kuma kike mun? Dan na ciyar da Abban mu? Taho mu koma d'aki" ya k'are had'e da mik'a mata hannunsa murmushi cike da kunya ta saki sannan ta mayar da kayan aikin ta k'ariso ta mik'a hannunta ta sanya acikin nasa, janta yayi izuwa d'akinsu had'e da zaunar da ita kan gado. Cikin wardrobe nasu ya nufa ya d'auko wani package sannan ya dawo ya zauna a gefenta.

  "Hungo" ya mik'a mata.

  "Mey wannan?" Tayi saurin tambaya.

  "Kede bud'e ki ga" ba tare da yin gardama ba ta amsa ta bud'e d'an kunne ta tarar aciki k'waya d'aya. "Ko na waye wannan Alhj?"

  "Bazaki iya tunawa ba?"

  "A'a gaskiya" ta amsa tana kad'a kai amsa yayi daga hannunta yace, "Kin tuna rana na uku dana fara d'auko ki daga makaranta muna tsaye a k'ark'ashin makeken bishiyan chan muna hira muna shan rakke chan kika ta6a kunnenki kikaji ba d'an kunne? Muka ta nema amma muka rasa?"

  Murmushi take sosai cike da mamakin yadda akayi har yau Daddy be mance da wannan rana ba bayan ita da ba don ya tuna mata yanzu ba ta riga ta mance da shi shaf. "Toh ai bayan dana raka ki gida na dawo na cigaba da nema ashe ma ba a wajen ya fad'i ba tun a bakin makarantar ku ya fad'i."

  "Shine ka adana har yau Alhj?"

  "Kamar yadda na adana soyayyarki a cikin zuciyata na tsawon shekaru ashirin da biyu." Ya amsa nan take.

  Mamaki ne ya mamaye Mami gabd'aya ta rasa na cewa chan ta kira sunansa inda ya amsa a take "Alhj idan har kana so na haka toh meyasa ka gujeni? Na fahimci kayi mun abinda kayi ne saboda ka rama abinda Umma tayi maka amma meyasa ka kujeni? Meyasa ka daina d'aukan wayana?"

  "Duk da hakan ma be kamata inyi miki abinda nayi miki ba Jamee amma a lokacin shaid'an ya riga ya rinjayeni I'm terribly sorry."

  "Komai ya riga ya wuce Alhj ka daina neman tuba na."

   "Nagode Allah yayi miki albarka."

  "Ameen Alhj baka amsa min tambayan danayi maka ba."

 "Kinsan wani sa'in mutum baya sanin muhimmancin abinda yake da shi se idan ya rasa, da fari nak'i in amince da cikin Amal nawa ne saboda tsoro da nake kar in 6ata wa mahaifina suna acikin gari, kowa ya sani mahaifina sanannen malami ne ba k'aramin zubar masa da mutunci zanyi ba idan har na amince da cikin cewa nawa ne. Tsoro ne yasa na gujeki Jamee, na d'au bayan da nayi nesa daga gareki zan iya mancewa dake, na d'au yin hakan ne ze fiye mun kwanciyan hankali ashe sam ba haka bane. Tun bayan da nayi cutting off conact dake da duk wani nawa rayuwata ta dame, acikin k'unci nake kwanciya in tashi har seda Allah ya shigo mun da Surayya cikin rayuwata, wacce ta yaye mun duk wani bak'in ciki nawa take kuma bala'in tuna mun da ke ta kowani 6angare. Duk da hakan saide idan ban kwanta ba Jamee senayi mafarkin ki, lokacin da na fara neman layinki kuma se yayita cemun switched off."

  "Ba shakka nakega lokacin da muka bar Askira ne Abba ya buk'aceni da in yasar da sim card d'ina ze sai min sabo."

  "Tabbas ma hakanne, saide duk da hakan ban kariya ba kullum se na gwada layinki amma baya shiga, a wannan lokacin ne na tabbata da cewa guje miki da nayi shine babban kuskuren dana tafka a rayuwa na, a wannan lokacin na tabbatar da cewa akwai gur6in da kika mamaye a zuciya na, gur6in da se ke ne zaki iya cike mun shi. Lokacin da muka dawo Nigeria na koma Askira don nemanki inda ake tabbatar mun da cewa Allah yayi wa Abba da Umma rasuwa."

  "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un Allah ya jik'an su da rahama a tunani na gabad'aya wanda ka kaini gunsu sune iyayenka."

  "A'a wan Abba ne da matarsa."

  "Allah sarki."

"Daga chan se na wuce gidanku inda ake cemin kun bar garin Askira da dad'ewa kuma ba wanda yasan inda kuka dosa nayi cigiyarku har na gaji amma rana baya ta6a wucewa ban yi tunanin wani hali da yanayi kike ciki ba. Please forgive me Jamee."

  Hannunsa ta d'au ta had'a da nata tana murzawa a hankali "Alhj komai ya riga ya wuce wannan d'an kunne kuma zan cigaba da adana shi as a symbol of my love for you" Murmushi ya sakar yana mey jin dad'in abinda ta fad'a sannan ya janyo wayanshi "Bari in kira Hjy Surayya muji daga gareta."

  "Gaskiya ya kamata."  A karo na farko Mummy ta d'aga wayan inda suka gaisa. "Kun jini shiru ban kawo muku breakfast ba ko? Wallahi Khaleefah ne yamun tsiya na sa Alarm a wayana kawai ya saci ido na ya d'auke wayan sena makara."

  "Barka, dama waya aikeki? Karki damu mun riga mun karya."

  "Kai ina ruwanka? Idan na kawo se kar ka ci so ka fad'awa 'yar uwata kar tayi wahalan yin girkin rana I'll make it up to you guys."

  "A'a Hjy Surayya dan Allah karki sa kanki wahala."

  "Nikam ka had'ani da 'yar uwata mu gaisa" yana murmushi ya mik'awa Mami wayar "Assalamu Alaikum" ta soma da cewa. "Amaryar mu" Mummy ta amsa.

 "Kai 'yar uwa bazaki bar zolaya bade ya kike toh ya Khaleefah?"

  "Gashi se shiri yake ya kusan komawa school."

  "Allar sarki Allah kiyaye ya bada sa'a."

   "Ameen sena shigo anjima sauran kice zakiyi girki kuma."

  "Oh 'yar uwa kar ki sakaltani dayawa fah."

  "Ba ga Alhj ba yasan yadda zeyi dake ai."

  "Kai 'yar uwa."

 ""Ahtoh barin bar ku haka se na shigo anjima."

  "Toh muna godiya Allah kaimu."

  "Yauwa se anjima."

  Kaman yadda Mummy ta d'au alk'awari bayan sallan Azahar ta shigo da abinci kala-kala se sauk'e kuloli kawai ake tayi daga mota. Yini Mummy tayima Mami se kusan Maghrib da Daddy ya kusa dawowa ta koma gidanta. Zaman lafiya maras misaltuwa Mummy da Mami sukeyi sekace ba kishiyoyi ba wane wasu 'yan uwan jini, dai-dai da rana d'aya Daddy be ta6a jin kansu ba. Hasali har had'a kansu suke su biyu su waresa. Bayan ya k'are wa Mami kwana bakwai na amarchi ya soma yi musu kwana bibbiyu duka.

  ***
  Haka kwanaki suka cigaba da shud'ewa yayinda zama yake k'ara yima wad'annan abokan zama dad'i. Labarin Nazeefah kuwa duk sanda ta bugi iska takan d'au waya ta kira Mummy amma dai-dai da rana d'aya bata ta6an d'aukan waya ta kira Daddy ba ko da shi ya kirata ma se ta ga dama take d'agawa.

   9 months later...

  Abubuwa da dama sun gudana, Amal hutu ya k'are sun koma makaranta har sun k'are first semester suna second semester yanzu. Maamah kuma an kai goron tambayan auranta, labarin dawowan Ya Abdul kuwa shiru har yanzu ko su Mama sunyi mishi magana se yace shi ba yanzu ba. Sultan ko har yau labarin aure shiru ya tsaya rawan ido. Labarin k'awar Amal Falmata kuwa tayi aure abunta tabar Maiduguri ta koma a Azare take da zama inda mijin ke aiki. Har Azare su Amal suka kaita suka dawo. Tun tafiyan Amal wane akan allura Afzal yake zaune, minti-minti yake yi mata waya yaushe zata dawo. Sam baya iya jure rashin ta a kusa da shi.

***
  Amal ce zaune a d'akinsu da Afzal se faman karatu take gefenta kuwa plate ne cike da kayan k'walama ba abinda babu daga abinda ya kama kan tuwon madara, calanda, gullisuwa, tsamiyan biri, ba abinda babu ta d'au wannan ta d'au wancan. Haka kawai ta ke wani irin wawan kwad'ayi kwana biyu duk abinda tagani setaji tana so. Ba da dad'ewa ba wayanta dake ajiye a gefenta ya shiga ruri dubawanda tayi taga Afzal ke kira k'aramar tsuka taja ta cigaba da yin abinda ke gabanta. Yana tsinkewa ya shiga kira again nan ma tak'i d'agawa be dad'e ba sega sak'on sa.

  _Please pick up Rania I'm sorry._
  Tana cikin shawaran ta d'aga ne kokuwa sega call nasa again nan ma seda ya kusa tsinkewa ta d'aga had'e da yin shiru.
   ''Baby yi hak'uri mana."

  "Nifa ban ce kayi mun laifi ba."

  "Toh meyasa in na kiraki bakiya d'agawa?"

  "Karatu nake bana son distraction."

  "Baby Ya Omrin na kine kuma yau distraction? Yi hak'uri kinji Yaya is sorry."

  "Shikenan ni kayi ta mun wasa da hankali kenan kullum, yau kace gobe, jibi kace gata dan kawai kaga ina missing naka."

  "Haba baby yi hak'uri wallahi sune suka k'i sakemu saura mana trips biyu amma de yanzu."

  "Toh nikam se yaushe zaka dawo?"

  ''Zuwa next week in shaa Allah.''

  ''Har next week Ya Omri?''

  ''I'm sorry.''

  ''Promise?''

  ''I promise Baby.''

  ''Toh Allah ya kaimu.''

  ''Ameen kin daina fushin?''

  ''Ba dole na ba."

  "That's my Rania so ya kike? Should I FaceTime you?"

  "Okay." Nan ya katse wayayn ya yi mata video call inda ta d'auka suka cigaba da gaisawa. "Baby?"

  "Na'am'' ta amsa.

  ''Mey kikeci haka ba ni?''

  ''Oh tuwon madara ne.''

  ''Da kuma mey? Mey wancan bak'in abun?'' Plate d'in ta d'aga ta matso da shi kusa ''Tsamiyan biri ne.''

  ''Rania yaushe kika fara wannan ciye-ciye?''

  ''Ba ka nan ma ban tsira ba ko?''

  ''Toh ya Mami? Sun dawo?''

  ''A'a wai daga chan zasu wuce Dubai."

  "Oh ayyah Papi fa? Yana nan k'alau?"

  "Eh Mummy tana kula da shi."

  "Allah sarki toh yayi kyau."

  "Toh se anjima ko? Kaga karatu nake" tayi maganan tana nuna masa handouts nata.

  "Wait Rania d'an tsaya."

  "Yaya wai yau kai kake hana ni karatu?"

  "Not at all, Idona ne kokuma k'iba kika k'ara bayan tafiya na?"

  "K'iba?" Ta nanata tana duban jikinta

  "Eh mana kinga yadda kumatunki suka ciko."

  "Kai Ya Omri ka fa san bana son inyi k'iba."

   "Ai kuwa se kin fara slimming dan kin riga kin d'au hanya."

  "Omg! Dan Allah dagaske kake na k'ara k'iba?"
 
  "Kije ki duba mirror kiga" katse video call d'in tayi ta ruga gun madubi tana matse kumatunta. Kuma fa hakanne da gaske ta k'ara k'iba toh kode? Kai da k'yar tayi sauri ta kad'a kanta. Koda tayi missing period nata last month bata damu ba cause tunda ta samu miscarriage date nata ya rikice wani sa'in se yayi wata biyu be zo ba atimes kuma sati biyu zuwa uku ya dawowa. Amma kuma ai tabar shan planning pills nata there's possibility cewa tana da ciki. Toh amma wani irin ciki ne wannan ba laulayi ba komai? Ai wasu dama sunce  cikin fari ne yafi bada wuya na biyu da sauk'i yake zuwa. Ta shigesu Allah taimaketa ba ciki take d'auke da shi ba in bahaka ba zatayi bayani gun Afzal da yace su jira ta gama makaranta tukuna su fara bearing children kasancewar yadda cikin farinta ya mugun bata wuya. Da na sani ta shiga yi shin meyasa ma ta daina shan pills natan ta kuma cire implant d'in? Har ga Allah ba don rashin ji tayi hakan ba illa dan so da take ta azurta Afzal da yara, so take yaga jininsa shima bayan hak'urin da yayi na shekaru kusan biyar ba haihuwa. Bata son ta shiga hak'k'insa dan wani personal interest nata. Ko ba a tambaya ba tasan Afzal na son yara yadda kullum idan suka je gidan wani abokinsa da suke mugun zumunci yake wasa da yaran tamkar 'ya'yan cikinsa. Se kuma yanzu tsoro ya shigeta bayan alamomin juna biyu sun bayyana a  jikinta, ji tayi gabad'aya dama bata cire implant d'in ba. Ita de zata jira zuwa nan da jibi idan har period nata be zo ba zata asibiti a dubata.

   Washegari bayan lectures nasu ya k'are suka wuce restaurant dan chin abinci ita da Maamah sede Amal tak'i cin komai bayan kuma tana jin yunwan.

  "Wai toh mey zaki ci?" Maamah da abun ya isheta ta tambaya.

  "Ni wallahi ganda nake so."

  "Gan mey?" Maamah ta tambaya unbelievably.

  "Ganda wallahi."

  "Ahh gaskia kin so nishad'i ganda? Da ranan nan kuma acikin school?"

  "Wallahi shi nak so Maamah ki taimakeni."

  "Toh ya kikeson inyi Amal? Bawai ana siyar da ganda bane anan sede ki bari idan an tashi se driver'nki ya tsaya a kasuwa ya sai miki kije gida ki girka."

  "Toh ai yanzu nake so bazan iya jira har anjima ba."

  "Oh Amal! Ko mey sabon ciki sede hakan."

  "Nikam da Allah."

  "Kode cikin gareki?"

  "Kaman ya ciki sekace bakisan ina planning ba?"

  "Nasani ko kin cire."

  "A'a kam bayan Yaya yace kar incire."

  "K'arya kike."

 "Dagaske fah"

  Mak'aryaciya rantse muji! idan ma cikin ne da ke in Ya Afzal ya gano zakiyi bayani."
 
  "Maamah dan Allah ki taimakeni."

  "Aww cikin ne dake dagaske?"

  "Wallahi ban sani ba but ji nake kaman I'm pregnant jiya muna FaceTime da Ya Afzal yace wai na k'ara k'iba."

  "Ai gaskiyanshi kumatunki sun ciko."

  "Na shiga uku!"

  "Ya gane amma?"

  "A'a hankalinsa be basa ba."

  "Chab Allah ya taimakeki."

  "Da Allah ki daina tsorata ni nasan yadda zan sanar dashi idan har na tabbatar da komai."

  "Gara miki kam dan kinfi ni sanin halin ogan naki kikayi wasa se kunyi fad'a ma."

   "Kai Maamah ki daina razana ni."

   "Allah kuwa yadda seda ya ja miki kunne akan kar kije ki cire."

  "Nikam idan ba ganda zaki bani ba ki daina cika mun kunne."

  "Ganda kam sede unborn ya hak'ura dan babu inda zaki samu."
 
  "Ni bance miki ciki ne gareni ba" tayi maganan had'e da mik'ewa "Ina kuma zaki?" Maamah tayi saurin tambaya.

  "Out of school zanje in nemi ganda."

  "Lallai abu ya tabbata" Maamah tace cike da neman tsokana.

  "Kanki akeji" Amal ta amsa had'e da galla mata harara sannan ta fita. Nan da nan ta kira driver'nta yazo ya d'auketa, haka suka shiga bin restaurant by restaurant suna tambayan ko akwai ganda har seda suka samu.

   Na sosai hankalin Amal ya tashi bayan da tayi carrying pregnancy test a gida ya nuna mata positive sedai duk da hakan bata amince ba se da taje asibiti akayi mata tests da dama aka tabbatar mata da gaskiyan al'amarin cewa tana d'auke da juna biyu. Tirk'ashi! Yanzu mey abun yi? Tasan se sun haura sama idan Afzal ya gano gaskiya. Da fari tayi tunanin kwata-kwata ma kada ta sanar dashi amma kuma seta tuna idan har shi ya gano da kansa al'amarin zefi damewa. Yanzu what's the way out??

   Haka tana ji tana gani har Afzal ya dawo daga tafiya bata yanke hukuncin ko ta sanar da shi kokuwa a'a ba. Gashi koda ta gwada tambayan Falmata da Maamah shawara duk suka sake tsoratar da ita.

  "Rania k'iban nan naki lafiya kuwa?" Afzal dake mik'e akan gado ya tambaya yana mey k'ure mata ido yayinda take zaune akan kujera tana faman tsifan kanta. Zuciyanta taji ya buga, miyau ta had'iye sannan ta saki murmushin dole.

  "Kai Ya Omri dan Allah ka daina razana ni."

  "Aikam da alama kinji dad'in tafiyan da nayi tunda har kika yi wannan k'iba."

  "Ni dama tayani wannan tsifa zakayi."

  "In dawo daga tafiya kuma ki sani aiki Rania?"

  "Toh kayi shiru ka kwanta."

  "Zomu kwanta anjima in mun tashi se in tayaki."

  "Karatu nake so inyi anjuma."

  "Haba Baby na yi hak'uri mana."

  "Nikam barni inyi tsifa."

  "Toh zo kiji."

  "Mey?"

  "Kekam kizo mana."

  "Meneh ka fad'e shi daga nan mana." Ba salon da Afzal bebi ba amma haka Amal tak'i tasowa ta samesa gashi kuma baya son ya fito fili ya tambayeta saboda sarai yasan ta gane abinda yake nufi kawai bata son basa had'in kai ne. Mamaki ya sha sosai saboda wannan ne karo na farko da ya ta6a neman Amal tak'i basa had'in kai. Toh koma mey ne de Allah ya sa lafiya.
 
   Yau kwana uku kenan da dawowan Afzal amma Amal ta kasa mustering courage ta sanar da shi cewa tana da ciki se tayi kaman zata sanar da shi seta fasa.

   "Rania kiyi sauri mana I'm gonna be late for work."

  "Ermm ermm.." amma ta kasa yin magana se cin farcen hannunta take "Yaya"

  Anzo gurin Afzal ya furta a ransa dama duk lokacinda ta kirasa da Yaya toh laifi tayi ko ne mey yanzu?

   "Iyayen rashin ji mey kuma kikayi wannan karan?"

  "Yaya" ta furta cike da shagwa6a.

  "Rania speak up."

  "Kaga har past 7 hurry kar kayi latti."

  "Kin d'au na manta ne? Oya tell me what is it you want to tell me."

  "Dama so nake in ce maka I love you."
  Wani kallo ya watsa mata "We are not done Rania zamuyi magana idan na dawo." Kai zalla ta gyad'a mar tana turo bakinta. Tun fitansa har dawowansa Amal ta kasa samun sukuni.

   ****
   Fitowan Afzal daga wanka kenan ya nufi wardrobe nasa dan ciro kayan da zesa sede kap T shirts nasa Amal ta sanya tayi masa datti da su. "Huh! God help me Rania ina kika kai mun shirts d'ina?" Ya tambaya yana mey bud'e side na drawer'nta. Kaman a kyaftawan ido Amal ta mik'e dan dakatar da shi "Tsaya zan d'auko maka su da kaina kar ka d'aga chan" tayi saurin sanar da shi sedai ina tuni ya kai hannunsa wajen, paper ya ga wanda ya zaro waje. Hannu Amal ta mik'a zata k'wace amma ya janye "Yaya ka ba ni." Ta fad'a tana k'ok'arin yin tsalle amma ina ko kusa da hannunsa ta kasa kaiwa.

   "Yaya please dan Allah kar ka bud'e." Gabad'aya ta tsure tasan idan Afzal ya gani nata ya k'are.
 
 "Mey aciki?"

  "Babu ka bani please."

  "Babu? Toh in babu bari in bud'e inga."

  "A'a please Yaya ka bani" se k'ok'arin k'wata take amma ta kasa.

  "Dan Allah kar ka bud'e."

  "Mey aciki toh?"

  "Ermm ermmm script na test d'ina ne wanda na fad'i please kar ka bud'e." Dariya yasa "D'an tsaya toh muga zeron da kika ci d'in."

  "Yaya ple-" tana cikin yin magana ya bud'e sega pregnancy results na Amal da fari ma cewa yayi tun cikinta na fari ne sedai kuma da ya duba yaga data d'in ko sati be kai ba.

  "Amal?" Dum taji zuciyarta ta buga dama anytime ya kira ta da asalin sunanta toh tana cikin big trouble nata ya k'are.

   "Yaya-"

  "Mey wannan?" Yayi saurin katse ta.

  "Yaya-"

  "Wait! Is this true?" Ya kuma katseta "Are you really pregnant?"

  "Yaya-"

  "Just answer me Amal!" Ya fad'a a tsawace har seda ta razana.

  "Yaya yes amma kayi hak'uri I can explain."

  "Explain what exactly Amal?!" Ya kuna daka mata wani tsawan da ya mugun razana ta.

  "Yaya dan Allah kayi hak'uri."

  "Cire implant d'in kikayi?"

  "Yaya-"

  "I'm asking you for the last time Amal cirewa kikayi?"

  "Eh" ta amsa k'asa-k'asa.

  "Wow tun yaushe?"

  "Yaya-"

  "Amal answer me!"

  "4 months back."

  "Wow! Seriously? Ki ka kuma daina shan pills nakin?" nan kai zallah ta gyad'a.

  "Why? Mey na ce miki amma?"

  "Kar in cire."

  "Meyasa kikayi toh?"

  "Yaya I'm sorry."

  "Ba abun da na tambaya ba kenan meyasa kika cire?"

  "Yaya I'm sorry gani nayi kaman ina d'aukan alhak'in ka ne please don't be mad."

  "Tayaya? Tayaya kike d'aukan alhak'i na? Ni na kawo shawaran mu fara planning d'in kokuwa?"

  "Yaya kaine I'm sorry."

  "No answer me so kike kice kin fini sanin abinda nake so kenan komey?"

  "Yaya dan Allah kayi hak'uri."
 
  "Ban san meyasa bakiya ta6a jin magana ba koda nayi miki, seda na ja miki kunne nace miki this is my decision komin yaya kar ki cire implant d'innan se idan kin gama school amma kika k'i ji kika je kika cire saboda ni bansan abinda nakeyi ba ko?"

   "Wallahi Yaya ba haka bane I'm sorry."

  "Then yayane meyasa kika cire?"

  "Yaya-"

  "I'm not done" ya katseta "Answer me nace kin fini sanin ya kamata kenan ko mey? Kokuma ni da nace kar ki cire d'in bansan abinda nakeyi ba? Wanne d'aya?"

  "Yaya ko d'aya I'm sorry."

  "I'm very upset with you Amal sanin kanki ne last year result naki beyi kyau kaman yadda ya kamata ba, kinyi passing amma duk series of D ne dalilin da yasa nace mu fara planning d'innan kenan saboda ki samu kiyi concentrating a karatunki ba tare da wani distraction ba."

  "Amma wannan be bani wuya ba Yaya ko sau d'aya banyi amai ba."

  "I don't care Amal you're still not safe, and no matter what dole cikin nan zeyi miki causing distraction daga karatunki, abinda bana so kenan ni kuma I want you to focus on your studies just. Ko nid'in a jinki bana son inga jini na ne nace mu hak'ura se kin gama school? Na fiki damuwa Amal but haka nayi hak'uri because thsit is what is best for you for us all" ya k'arasa a tsawace.

  "Yaya I'm sorry bazan sake ba."

  "You're never sorry Amal bana ta6a gaya miki magana ki ji sede kiyi abinda ranki yake so bans-" sautin kukan Amal ne ya dakatar da shi, kuka ta shiga rera masa tsaye a wajen.

   Sedai Afzal be shiga yi ma Amal masifa ba kawai se ta yanki jiki ta fashe masa da kuka saboda tasan muddin ta fara kuka Afzal yana yin shiru. "Yaya I'm sorry" tace tana ta matso 'yar hawayenta. Kallo ya watsa mata kawai yabi gefenta ya fice izuwa d'ayan d'akin inda ya kwanta. Kukanta tasha a wajen seda ta gode wa Allah sannan ta mik'e ta je ta samesa a d'ayan d'akin Allah ya taimaketa ma be sa key ba. Akan gado ta tsincesa yana bacci, sid'ak-sid'ak ta taka taje tasamesa, jikinsa ta shige ta kwanta akan hannunsa haka har itama baccin ya d'auketa.

   Chan dab da goshin maghrib Afzal ya tashi se ganin Amal kawai yayi ajikinsa tana shar6an bacci. Ido ya k'ure mata yadda take ta baccinta cikin kwanciyan hankali da jurwayen hawaye a fuskanta. 'Yar murmushi ya saki tuna anytime ya fara mata masifa se ta rushe masa da kuka sanin baya iya jure kukanta. Ya rasa wani irin d'an banzan shagwa6a ne da ita kodan chan a gidansu ba a saba mata da masifa bane kokuwa da gan-gan takeyi ne oho shide amma shagawa6an nata na burgesa duk lokacin da ta fara kawai se yaji ya huce. Hannu ya aza akan cikin nata. "I'm sorry I got mad at you earlier, Rania bana son a sanadi na GP'nki ya sake sauk'a, I only want the best for you" tsugunawa yayi tare da pecking cikin nata. Daga haka ya mik'e yaje ya kama ruwa yayi alwala bayan ya gama shiri ya dawo ya tada Amal, yana tayar da ita ya fice ba tare da yace da ita komai ba. Sallah tayi ta tofe add'u'o'inta sannan ta zarce kitchen ta dafa macaroni da minced meat aciki ta dawo ta shirya kan dinning. Tunda take girkin take tsammanin shigowan Afzal amma shiru gashi ko da ta gwada trying numbanshi taga wayar ma a gida ya barta. Haka se chan kusan tara ya dawo Amal tayi jiran duniya har ta gaji. Yana shigowa ta zabura, mayar da k'ofan yayi ba tare da nuna ra'ayin yi mata magana ba so yake yaga ko zatayi masa.

   "Yaya sannu da zuwa" tace tana susan kanta yayinda ta kafe idanunta a k'asa.
 
  "Sannu" ya amsa sama-sama sannan ya shiga takawa gabansa tasha da wuri "Yaya I'm sorry dan Allah kayi hak'uri" ta sanar da shi idanunta suna masu cikowa da hawaye.

   "Ni ya kamata in baki hak'uri Rania I'm sorry kinji?" Cike da d'unbun mamaki ta d'ago kai tana kallonsa "Eh?"

   "I said I'm sorry for shouting at you earlier ki gafirceni."

  "Yaya-" dan mamaki tama kasa cewa komai. "Yaya ka daina fushi dani?"

  "Meyasa zan yi fushi da maman unborn d'ina? Na fahimceki Rania, and I appreciate your commitment to give me a family, to give us a family. Just know that I'll always be here for you if you needed me okay?" Hugging nasa kawai tayi tsabagen yadda takejin dad'i. "I love you so much Ya Omri."

  "I love you too babe" a hankali ya janyeta daga jikinsa. "How many months is my baby?"

   "Ko scanning banyi ba saboda tsoro da nake idan ka gano gaskiya zaka mun fad'a hala ma ka daina mun magana."

  "Be kamata in hau kanki da masifa ba d'azu Rania but I couldn't help it bana son saboda ni ki sake komawa baya a karatunki shiyasa nace mu fara planning I love you so much my Amal."

   "And I love you more Ya Omri a shirye nake da in rasa komi nawa saboda farin cikin ka, I'm willing to sacrifice my life for you Ya Omri. I've seen the way you so much love and adore kids shiyasa nima nake so in yi maka fulfilling this one wish."

  "And I appreciate that so much Baby, I can't believe I'm going to be a Daddy in anytime soon, Allah ya inganta ya cigaba da yi miki albarka."

  "Ameen Ya Omri."

  "So first thing gobe zamu je muyi scanning koba haka ba?"

  "Duk abinda kace my King Allah ya kaimu."

  "Ameen."

  "Muje muci abinci tun d'azu na sauk'e ina jiranka."

  "Har girki kikayi?"

  "Eh mana ba kayi mun fushi ba."

  "Yi hak'uri toh kinga ni bana son kina aikin wuya yanzu zan yi ma Ummi magana ta turo mana mey aiki d'aya daga gida."

  "A'a a'a nikam bana so bana so zan nayin komai nawa da kai na."

  "But Bab-"

  "Trust me Ya Omri koda zaka d'auko mey aiki ma kabari ba yanzu ba maybe idan nazo nayi nauyi amma yanzu kam da k'arfi na bana so."

  "What baby wishes she gets, fine se a bari se kinyi nauyi d'in amma fa karki na aiki sosai bana son ki galabaita mun baby."

  "Toh shikenan let's go and eat." Abincin su suka ci cikin kwanciyan hankali sannan sukayi wanka abinsu tare suka kwanta. Washegari kaman yadda Afzal ya fad'i suka wuce asibiti sukayi scanning ashe ciki har na wata biyu da sati d'aya ne tattare da Amal amma bata sani ba. Afzal dad'i kaman ze kashe sa se buge-bugen waya yake yana sanar da mutane Amal tasa is pregnant. Se tattalinta yake wane k'wai, idan ba abu yafi k'arfinsa ba sam baya barin Amal tayi aiki se inde shi yayi haka ta zama lalacacciya a gidan ko d'aga tsinke batayi sede tayita ciye-ciye tace tana son wannan tace tan son wancan. Wani irin d'an banzan kwad'ayi ta sake koyowa amma Alhamdulillah ba amai ba jiri ba ciwo ba komai. Haka Afzal ya cigaba da rainon cikin nata, kullum tare suke  zuwa yin scanning. Koda aiki yayi masa yawa ze buk'ace ta da ta jirasa seya dawo. Cikin na da wata biyar sukayi first semester exams nasu. Na sosai Afzal ya taimaka mata ta samu tayi passing with excellent results. Seda cikin ya kai wata bakwai tukun ya fara fitowa sosai acikin kaya, abinku da doguwar mace, tunda cikin ya fara fitowa Amal ta auri zama da hijabi a gida 24/7 saboda tsokananta da Afzal yakeyi sede bata cire hijabin ba seya nemi tsokananta. Har dan haka ma ta daina yin wanka tare da shi. Cikin nada wata takwas ya fito yayi k'ato tim, zama da k'yar tashi da k'yar kusan komai Afzal ne yakeyi mata. Haka kawi zata wayi gari rana d'aya tayita kukan banza in ya tambayeta dalili kuwa tace wai girman cikin ke bata tsoro.
   Bayan nan ga wani uban masifan da ta koya abu kad'an ta hau surutu da masifa.

   Da daddare wajajen goma Afzal na kwance yana bacci Amal ko se kuka cikinta yake sanadin yunwan da takeji, baccin ma ta kasa. Tun kafin su kwanta Afzal yake binta taci abinci amma tak'i saboda haushinsa da takeji har yanzu na hanata fita bikin sunan k'awarta da yayi. Shi kuwa dalilinsa wai saboda EDD nata ya kusa ne, it is more safe idan tana zama a gida kar labor yaje ya kamata acikin jama'a. Se harara take ta zuba masa shiko se baccinsa yake hankali kwance. Mik'ewa tayi da k'yar ta nufi kitchen ta bud'e fridge, jollof na shin kafa, macaroni, d'anyen awara, soyayyan kifi ta tarar a cikin fridge d'in sede duk ciki ba abinda ya gameta. Farin k'asa ta d'auko a inda take 6oyewa ta shiga tsotsa saboda Afzal ya haneta da sha tun lokacinda likitan ta tace musu abun baida kyau a jiki. Seda ta sha har biyu sannan ta koma d'akin, lokacin har goma da rabi yayi. Zama tayi daga bakin gadon tana tunanin ta yadda zata fara tada shi.

  "Yaya!" Ta ambaci sunansa. "Yaya ka tashi!" Cikin bacci ya amsa. "Mey ne Baby?"

  "Ni ka tashi" shareta yayi ya cigaba baccinsa.

   "Yaya ka tashi mana!"

  "Maman Baby na yi hak'uri mu kwanta kinga ina da office gobe yi hak'uri."

  "Toh ni yunwa nakeji."

   "Yaya ka tashi!" Tasa ihu, ba shiri ya mik'e zaune.

   "Dan Allah mey kikeso Baby?"

  "Ni pepper soup nakeso."

   "Toh ai akwai a fridge bari in miki micrwaving ko?"

  "Ni ba na kaza nake so ba na kayan ciki wanda ba thyme aciki nakeso."

   "Baby fisabillahi a ina zan samu pepper soup na kayan ciki cikin daren nan? K'arfe nawa ne?" Ya tambaya yana duban agogo. "Baby sha d'aya fa ake nema, sha d'ayan dare."

  "Toh laifi na ne? Ba baby'nka bace se kayi mata fad'a ba ni ba."

  "Ni ba fad'a nake miki ba yi hak'uri ki bawa baby hak'uri kice mishi gobe da safe zanje in siyo mishi."

  "Ni baby na ba na miji bane baby girl
ce ka daina canza mata jinsi."

  "Toh naji yi hak'uri Maman baby girl ki bawa baby girl hak'uri."

  "Ni wallahi shi muke so."

  "God help me naji toh naji zanje in saya miki."

  "Kuma in da thyme aciki bana so."

"Naji in shaa Allah ma babu." Nan da nan ya canza kayan jikinsa ya d'au key. "Toh sena dawo."

  "Allah ya kare I love you."

  "Ameen maman baby girl I love you too." Cikin sa'a kuwa a hotel na biyu da ya duba ya samu pepper soup d'in sede kuma da thyme aciki haka seda ya biya extra kud'i aka samu aka tankad'e masa romon aka yi getting rid of thyme d'in. Yana isa gida ya d'iba mata a saucer ya d'au mata ruwa. Sam bataji shigowansa ba kawai ji tayi karap an bud'e k'ofan. Kafin tace zata 6oye farin k'asan da take shan har Afzal ya gani.

  "Uhm uhm fito da shi na riga na gani fito da shi."
   "Yaya" kame-kame ta shiga yi. "Oya mik'a mun."

   "Yaya please"

   "Rania give it to me."
Bata sake yin gardama ba ta mik'a  masa.

  "Ina sauran?"

  "Babu wannanne na k'arshe."

  "One... Two..." ya shiga counting inda ta dakatar da shi da sauri. "Ka tsaya zan fad'a zan fad'a."

  "Oya a ina kika 6oye?"

   "Baby na" ta maraice fuska.  
 
   "Three... four..."
 
   "Yana cikin second cupboard a kitchen."

   "Kika sake saya se na kai k'aran ki gun Abba zance ko na miki magana bakiya ji ga shi zauna kisha an samu pepper soup d'in."

   "Na fasa sha ni awara nakeso."

  "Dan Allah kiyi hak'uri Rania bacci nakeji."

  "Ba zaka kai k'ara na gun Abba ba? Ni bazan ci ba."

   "Yi hak'uri wasa nake."

  "Nide wallahi awara nake so in ba haka ba inyi ma kuka."

  "Yi hak'uri Baby ta, ai bama haka dake kema kin sami, haba maman baby girl yi hak'uri ki sha mu kwanta ko? Gobe da kaina zan kaiki gidan k'awar naki kiga baby'n nata."

   "Daga baya kenan bayan an gama komai mey zanje inyi? Ni de awara nakeso."

   "Wannan d'in fa? In zubar?"

  "Ka sa a fridge amfaninsa ze taso wataran."

 "God help me!"

  "Ni de awara nake so." Haka dan dolensa ya juye pepper soup d'in a fridge ya fito da d'anyen awaran daga fridge dama already a yayyanke ne soyawa kawai za'ayi har ya shiga soyawa ya tuna da gardaman Amal ze iya kai mata yanzu tace ita mey k'wai ajiki takeso dan haka ya koma d'aki ya tambayeta. Ai kuwa tace mey k'wai ajiki take so cikin mintuna k'alilan ya gama soyawa ya kai mata nan ne ta zauna tacinye tas shide Afzal tausaya mata yake tun cewa da likita tayi idan ta fiye cin abinci sosai toh baby'n nata zeyi girma in akayi wasa ma ta kasa haifa da kanta se anyi mata CS. Amma inaa ita Amal ko a jikinta se aukin ci kaman  gara. Dam tayi sannan ta mik'e kan gado ta fara bacci. Se anan Afzal ya samu kansa ya kwanta shima.
   Haka yayi ta fama da Amal har zuwa lokacin da haihuwanta yayi. Dama likita ta basu tsakanin 12th-15th on the 14th Amal ta tashi da wani irin ciwon ciki mey tsanani, dama Mami tace mata anytime taji cikinta na ciwo ko bayanta toh tayi mata waya. Aikam Allah ya taimaketa ranan asabar labornta ya tashi bata fita school ba saboda ba wani serious lectures sukeyi ba, shima Afzal na a gida saboda ba aiki, tana zaune a d'aki ta nad'e k'afa tana tsotsan tsamiyan biri tajiyo wani irin sharp pain a mararta. Tuni tayi watsi da plate na tsamiyan birin ta sauk'a k'asa, da cikin nata ya sake murd'awa ta sa wani d'ankaren ihun da seda Afzal dake parlour ya shigo ba shiri, kanta ya yo da wuri yana tambayarta ko lafiya.

  "Yaya call Mami up I think I'm in labor."
 
  "Labor?" Ya sake nanatawa a razane. "Sure!"

  "Yaya kayi sauri wayyo Allah cikina zan mutu"  nan da nan ya kira Mami. Cikin mintuna k'asa da talatin ita da Mummy suka iso kafin nan ba irin yak'ushi da masifan da Afzal be sha ba. Amal se kuka da k'yar Afzal ya d'agata ya kaita mota Mummy ta biyo su da maternity bag nata duka suka yi asibiti inda akayi delivery room da Amal. Mutum d'aya aka buk'ata da ya shiga cikin d'akin da Amal nan su Mummy sukace Afzal ya shiga amma d'ankaren tsoro ne dashi atapir yace shi baze shiga ba sede cikin d'ayansu ita da Mami d'aya ya shiga. Baze iya jure ganin Amal tana kuka haka ba bayan ba abinda ze iya yi daze tsayar da azaban da take ji ba. K'arshe de Mami ce ta shiga, Amal se ihu take yi muryanta akeji ko ina a cikin asibitin Afzal ko zama ya kasa se safa da marwa yake a haraban d'akin yana mey rok'on Allah ya sauk'e masa matarsa lafiya. Bayan several pushes Amal ta samu kanta, ta haifo zankaleliyar 'yarta. Ana gama kimtsa su akayi ma Afzal magana.

   "Congratulations matarka ta sauk'a lafiya ta samu 'yarta both the mother and the baby are in good health zaka iya shiga ganinta." Dr ya sanar dashi da Mummy.

  Wani irin sanyi Afzal ya jiyo a jikinsa "Alhamdulillah Alhamdulillah thank you so much Dr." Ita Mummy dan farin ciki tama kasa magana.

  "You're welcome" daga fad'in haka yabi gefensa ya fice nan Afzal da Mummy suka k'arasa cikin d'akin. Wajen Amal tasa ya soma nufa had'e da placing mata peck a goshi. "Sannu da k'ok'ari my Rania, Allah yayi miki albarka sannu ko?"

   "Ameen Ya Omri" ta amsa a galabaice tana mishi murmushin dole.

  "Ga chan 'yar tamu achan" Mami tayi masa nuni da crib da aka sanya baby'n aciki. Nan da nan yaje ya d'aukota, baze iya kwatanta irin farin cikin da ya ziyarci zuciyansa ba a lokacin da ya rik'e baby'n nasa a hannu. Se kaman Amal kawai ya rik'e, yarinyan ba abinda ya rabata da Amal wane kakinta Amal tayi. Se masha Allah kawai Afzal yake ta furtwa har izuwa lokacin da ya dawo ya zauna a gefen Amal. Addu'a yayi mata Mummy ta mik'a masa zamzam da aka jik'a dabino aciki ya bata.

  "Rania she looks just like you" ya sanar da ita had'e da mik'a mata ita. Har kuka seda Amal tayi da ta rik'e yarinyar a hannu, yau Allah ya amsa mata addu'arta dan azaban data sha a labor room har cewa tayi ita mutuwa ma zatayi. Amshe baby'n Mami tayi ta mata addu'a itama sannan ta mik'awa Mummy itama tayi mata inda Afzal ya sake amsanta. "Gaskiya 'yar nan ta d'ibo Amal dayawa" cewan Mummy.

   "Nace miki kaman Amal kawai na rik'e a hannu ba abinda ya rabasu" Mami tace.

  "Alhamdulillah" Afzal ya sake mik'a godiyansa ga mahalicci. Ya rasa wani kyauta zeyi wa Amal wanda zey sanyata farin ciki kaman farin cikin da ta sanyasa a ciki yau. "Rania?"

  "Na'am?" Ta amsa mik'a mata baby'n yayi "Wani suna zamu sa mata?"

  "Yaya nice zan bata suna? Ai kaine mahaifinta kai zakayi deciding."

   "Na baki wannan dama, ki sanya mata duk wani sunan da kika ga ya dace." Shafe fuskan baby'n tayi a hankali had'e da placing mata kiss a kan hanci "Ina son mu sanya mata Nazeefah sunan k'anwata tilo." Gabad'aya wajen seda sukayi mamakin wannan ra'ayi na Amal, barin ma Mummy. Ina ma ace yadda Amal ke son Nazeefah haka itama Nazeefah take son ta? Da kuwa ba abinda ze fiye wa Mummy farin ciki. Duk sunyi murna matuk'a barin ma Mummy da har hawaye seda ta zubar taso ace ta iya ta bawa 'yarta tarbiyya kaman yadda Mami ta baiwa Amal, ta so ace Nazeefah tana da kyawun halatayya irin na 'yar uwarta Amal. Amsan yarinyan Afzal yayi ya mata hud'uba. "Welcome to the family Nazeefah, Allah ya albarkaci rayuwanki."

  "Masha Allah" fad'in Mami.

   "Allah miki albarka Amal, Ya k'ara muku lafiya keda Nazeefar mu."
  Ameen duka suka amsa a gun.




RANA D'AYA!
#RD💕

Love_ king Miemiebee👄

14 comments:

Unknown said...

Wow wow wow well done meimeibee am so much in Love with this page Allah ya Kara basira

Unknown said...

Osheey Miemie, Allah ya kara basira.

Unknown said...

Hlo, hope all is well, miemie munji shiru kwana 2 ba post. hpe lpia lau

Unknown said...

Hlo, hope all is well, miemie munji shiru kwana 2 ba post. hpe lpia lau

Unknown said...

Wlh kuwa Allah dai yasa komai lfy

Husna said...

Thank you darling.. an mana takwara thnk u... So what remains !book ya kare...more ink to your pen.

Unknown said...

Karewa kuma?

Unknown said...

Pls..miemie hope everything is normal

Unknown said...

Maybe she's writing exams

Unknown said...

Enter your comment...gsky baa kyauta mn koda kinada uxuri sai a mn bayani ai HB Jan rai yayi yawa

Unknown said...

Gaskiya kam

Unknown said...

Miemiebee hope all is well?

Unknown said...

Miyetti Allah ,da ftn lfy dai shirun nan ,don shirun yyi yw kuma ba lbr
More ink to your pen. Update soon pls

Unknown said...

Dan Allah miemiebee if there's something wrong let us knw please