BY MIEMIEBEE
PAGE 40
_This chapter goes to Members of the prestigious group of *MIEMIEBEE FANS* thank you so much for the maximum support and love guys, I love y'all fisabilillah 💕_
Da Asubah alarm na Afzal yayi ringing yana kashewa ya tashi ya shirya bayan nan ya tayar da Amal sannan ya fice masallaci, tana idar da sallan ta koma bacci ko jiransa ta kasa sa6anin yadda ta saba. Murmushi kawai ya saki ya tu6e jallabiyansa ya kwanta a gefenta sannan ya saita alarm nasa. Shida na bugawa alarm d'in ya shiga ruri sa6anin yadda Amal ta saba rigasa jin alarm d'in harma ta tashi ta kashe ta tayar da shi se gashi yau se baccinta kawai take, lallai nauyin baccin masu ciki daban yake. Mik'ewa yayi a hankali gudun kar ya farkar da ita sannan ya gyara mata kwanciya ya shige bayi yayi wanka, breakfast nasa ya had'a da kansa yaci ya shirya sannan ya komo kan gadon ya mata placing gentle kiss a goshi ya fice. Ba Amal ce ta tashi ba se chan wajajen k'arfe goma. A razane ta farke had'e da duban lokaci a fankacecen agogon dake manne a sentan gadon d'akin nasu.
"Subhanallahi!" Tayi exclaiming "Yaya you're going to be late" ta furta cike da tashin hankali yayinda ta juya tana neman Afzal kan gadon sede wayam ba kowa. Mik'ewa tayi ta lek'a bayi nan ba shi wayanta ta d'au ta kirasa a karo na farko ya d'aga "Good morning My Rania" ya gaisheta yana mey barin duk wani abinda yakeyi focusing on the phonecall just.
"Morning Ya Omri where are you?"
"At work" ya amsa nan take.
"Kana nufin kana office?"
"Yes Rania."
"How? Yaushe ka tashi ka shirya? Baka sa alarm bane?"
"Kina bacci duk nayi hakan alarm kuma na kunna har ya gama ringing baki ji ba."
"Omg! Ya Omri I'm sorry yanzu ka karya?"
"No harm done Rania I prepared breakfast myself."
"Next time ka tayar dani in tayaka shiri kaji?"
"No Rania, you're pregnant and still sick, kina buk'atan hutu sosai so karki damu kinji? I can manage."
"Are you sure?"
"Yes Rania, yaushe kika tashi?"
"Yanzu ban san yaushe na soma bacci mey nauyi ba, daga cewa barin kwanta kafin ka dawo daga Masjid kawai se bacci ya d'aukeni ban kuma sake jin komai ba."
"Dama chan haka baccin masu ciki yake."
"Gaskiya bazamu shirya da baby'nka ba idan zena sani bacci kaman gawa haka."
"Toh da mey zakiyi mishi?"
"Punishing nashi zanyi."
"Ta yaya kenan Rania?"
"By starving myself."
"So kike yunwa ya addabe min baby na?"
"Toh ba yana sani bacci ba."
"Yi hak'uri Rania beyi zafi haka ba, ga breakfast a kan dining nasa driver ya saya miki je kici kinji?"
"O'o" ta amsa tana turo baki tamkar yana tsaye a gabanta.
"Yi hak'uri ko in dawo in baki?"
"Eh" ta amsa da gan-gan don jin mey zece.
"Toh shikenan I'm on way ki jirani."
"Lol Ya Omri yanzu dagaske office d'in zaka bari dan ka taho ka bani abinci?"
"Anything for you Rania."
"Wasa nake maka yi zamanka kayi aiki, zanci da kaina bari inyi wanka."
"Are you sure ba sena zo ba Rania?"
"Don't worry Ya Omri sekace wacce ba tada hannu."
"Alright I'm waiting for your dope pictures in kinyi wankan ayi mun kwaliya na musamman a turo mun."
"Anything for my Omri I'll hang up."
"Take care I love you."
"I love you too" da haka ta katse wayan. Bayi ta fad'a tayi brushing sannan ta fito ta karya bayan nan tayi wanka ta sanya wata doguwar jallabiya mey d'ankaren kyau sannan ta zauna ta tsara kwaliya ta taje sumarta da k'yar da hannunta d'aya ta kwantar a bayanta ta shiga snapping pictures tanayi wa Afzal sending ta Snapchat. Ko aiki ya kasa yi ranan se kallon hotunan nata kawai yake. Da azahar bayan yaci abinci ya kira Nazeefah a karo na farko ta d'aga. Bazata iya tuna when last ya kirata ba, ko ta kira baya d'agawa ta sak'o kawai suke gaisawa.
"Ya Rouhi?" Ta kirasa.
"Na'am Rabba'atul Bait" ya amsa.
"Ya Rouhi you callled!" Ta fad'a cike da k'in yarda.
"Yes Rabba'atul Bait ya kike?"
"Ya Rouhi I miss you, I miss you so much."
"I'm missing you too kina gida?"
"Yanzun na dawo daga lectures."
"Inzo?"
"Eh?"
"Nace inzo?"
"Ya Rouhi zaka zo gani na?"
"Yes Rabba'atul Bait baki yarda bane?"
"Ya Rouhi you're nomore mad at me?"
"Not anymore sweetheart so inzo?"
"Yes Ya Rouhi you're always welcomed."
"Alright I'm on my way" daga nan ya katse wayan. Kaman a kyaftawan ido Nazeefah ta fad'a bayi ta watsa ruwa nan da nan ta shirya cikin wani bak'in lace mey torches na pink. Na sosai d'inkin da shi kanshi lace d'in ya amshi farar fatarta. Light makeup tayi amma ta bala'in yin kyau kasancewar ta kwana biyu batayi applying makeup ba. D'auri irin na Zahra Buhari tayi ta cire gashinta ta k'asa sannan ta feffeshe jikinta da turare inda ta shiga zaman jiransa, chan bada dad'ewa ba Afzal yayi mata waya kan ya iso ta fito.
Mayafinta ta d'au ta yafa sannan ta fice daga gefen gidan nasu yayi parking motansa, wani irin sanyi ne ya ziyarci zuciyan Nazeefah na ganin Afzal kawai da tayi. Kishingid'a yayi daga jikin motan nasa yana sanye da black suits, sky blue shirt da red tie, ba k'aramin kyau yayi ba kaman a had'iyesa. Bata san lokacinda tasa gudu ta nufesa ba, hannunsa ya bud'e mata wide open inda ta fad'a jikinsa hugging him so tightly sun dad'e a haka sannan a hankali ya janyeta sede kawai yaga tana hawaye.
"Not the tears Rabba'atul Bait."
"Ya Rouhi I miss you so much" ta sanar dashi had'e da sake fad'awa jikinsa tana hugging nasa be sake d'agata ba, tsam ya rik'eta yana shafa bayanta ba k'arya shima yayi missing nata na sosai. Da kanta ta d'ago daga jikin nasa tana share hawayenta hannunta ya sauk'e had'e da zaro hanky daga aljihunsa ya shiga share mata hawayen nata da kansa. "Cry nomore Sweetheart" ya sanar da ita. Kai zalla ta iya gyad'a masa.
"Kinga yadda kikayi kyau?"
"You too Ya Rouhi."
"Toh ya kike?"
"Ka shigo ciki dan Allah."
"No not today."
"But ba kowa a gida dukansu sunyi tafiya sun tafi Umarah ni kad'ai ce se wata 'yar uwarmu kuma ta fita itama."
"Are you sure?"
"Yes Ya Rouhi please ka shigo." Hannunsa taja ta kaisa har parlourn Daddy, da tayi yunk'urin kawo masa ruwa da abinci kuwa seya hanata akan cewa yanzun ya baro restaurant. A gefensa ya zaunar da ita yana kallonta tabbas yayi kewarta shima, yana cikin binta da kallo idonsa yayi tozali da wani shatin belt a hannunta wanda har yanzun ya k'i gushewa. Sosai yaji zafin hakan, duk lokacinda ya tuna ya d'au abu ya zaneta seyaji ba dad'i. Hannun nata ya d'aga a hankali yana shafa wajen "Rabba'atul Bait I'm sorry, I'm sorry for bruising you like this."
"Please don't be Ya Rouhi, you have no reason to be ni na jawo komai wa kai na and I'm sorry please forgive me."
"I've forgiven you Rabba'atul Bait nazo ne don in jaddada miki ina shirin dawo dake d'akinki, zaki dawo?"
"Ya Rouhi zaka mayar dani gida?" Ta tambayesa cike da k'in yarda.
"Yes Rabba'atul Bait you're going back to your home."
"Ya Rouhi!" Ta ambata hawaye na ciko mata a ido yayinda ta fad'a jikinsa tana kuka, zagaye hannunsa yayi a bayanta yana calming nata "Ya Rouhi dan Allah kayi hak'uri na d'au alk'awari bazan kuma abinda na aikata ba please forgive me" a hankali ya d'agota yana share mata hawayen nata "Na fad'a miki I've forgiven cry nomore."
"Thank you so much."
"Baki tambayi ya jikin Amal ba." Alokaci d'aya yaga yanayinta ya sauya.
"Nazeefah na d'au kinyi nadaman abinda kika yi wa Amal koba haka ba?"
"Ya Rouhi nayi."
"Then why this reaction? In har Amal tana da niyyan yafe miki meyasa ke bazaki iya neman tubanta ba? Kinsan ko akwai hak'k'inta akanki? Kuma muddin baki nemi tubanta ba ta yafe miki Allah baze ta6a barin ki ba?"
"Ya Rouhi nayi nadaman abinda nayi mata, wallahi nayi."
"Then ki bata hak'uri I want you to call her and apologize." Shiru tayi bata ce komai ba tana tunanin ta inda zata fara kiran Amal ta bata hak'uri, wani irin k'ask'antarwa ne Afzal yake shirin yi mata haka?
"Bazaki iya ba?" Ya tambayeta yana mey tsamo ta daga tunanin da takeyi.
"Ya Rouhi ba haka bane" ta mai k'arya.
"Nazeefah yaushe ne zaki gane cewa Amal 'yar uwarki ce ba abokiyar gabanki ba? Yadda kike ganin ina son ta kema fa hakan nake sonki, in kuma kina ganin kaman nafi son ta ne then you're right saboda Amal na mun abinda zuciya na keso. Bata k'untata mun, bata sani surutu, kuma tana sonki saboda tasan ina sonki. Ta sani idan taso wani nawa kaman ni taso amma ke fah? You don't love her single bit. Why Nazeefah? Do you even love me at all? I doubt so because if you really do zaki so abinda nake so kema ki so Amal."
"Ya Rouhi dan Allah kar kace haka sanin kanka ne ina sonka, I do love you above of everything."
"No Nazeefah, idan da har kina so na da zaki so Amal ki guji aikata abinda ze 6ata mun rai but no, you keep on hurting Amal which is technically like hurting me, ita kuma zuciya mey kyautata mata take so ko baki san da haka ba?"
"Na sani" ta ambata kanta a duke.
"Good saboda haka nake son ki soma kyautata wa Amal, kin fini sanin yadda Amal ta d'aukeki da zuciya d'aya, kinfi kowa sanin cewa Amal bazata ta6a aikata kwatankwacin abinda kikayi mata ba saboda tasan idan ta ta6aki kaman ta ta6a ni ne why can't you do thesame? Yadda kike jin ni mijinki ne itama fa haka takeji you both have equal rights on me, I love you Nazeefah, I really do love you and bana son abinda ze sake shiga tsakaninmu but idan kika cigaba da wannan halin naki zakisa ki fita mun a rai kuma bana son hakan ya faru because I don't want to hate you Nazeefah please change your ways. Kece fa uwar gidana komin yaya matsayin ki daban yake dana Amal a zuciya na da kuma ma a idon jama'a, be kamata ace ke kike yin wannan rashin hankali ba kamata yayi ace Amal ce keyi kina mata wa'azi, ke bakisan da wannan abinda kikeyi ba Amal zata iya k'wace miki martabarki?"
"Ya Rouhi I'm sorry."
"Don't be Nazeefah, I just want you to change ki sauya d'abi'un nan kiso 'yar uwarki muyi zaman lafiya dukan mu please. Idan har kina sona zakiyi mun abinda nakeso."
"Naji Ya Rouhi in shaa Allah kuma zan canza, ko mey kakeso I'll do it."
"Ki tuba ki bawa Amal hak'uri, that's all I want."
"Ya Rouhi sena bata hak'uri ne? Ai na tuba."
"Toh bakiya son in dawo dake gida?"
"Ina so."
"Then kiyi hak'uri ki sauk'e girman kan nan ki bata hak'uri I kow it's not easy but do it for me okay?" Ya k'are had'e da d'aga hannunta ya rik'e acikin nasa.
"Naji zan bata."
"And promise me bazaki sakeyin abinda zeyi hurting Amal ba, promise me ko na mayar dake bazaki sake tada wa kowa hankali a gidan ba, zaki bawa Amal dama kuyi zaman lafiya." Hannunta ta aza akan nasa dake rik'e da d'ayan nata "I promise Ya Rouhi in shaa Allahu bazaka sake jin kaina dana Amal ba."
"Thank you Nazeefah thank you so much."
"Ni ce da godiya Ya Rouhi."
"So yaushe zaki kirata?"
"Bana son muyi magana ta waya nafison inje in sameta har gida in nemi tubanta."
"Masha Allah."
"Yaushe zaka mayar dani gida toh?"
"Yaushe su Daddy zasu dawo?"
"Next week."
"Suna dawowa zan zo in d'aukeki Rabba'atul Bait kinsan be kamata haka kawai in d'aukeki ba tare da sanin su ba."
"Hakane kam toh in yi mishi magana ta waya?"
"Still hakan beyi fasali ba kibari su dawo d'in ai nan da next week kaman gobe ne."
"I know Ya Rouhi is just that I miss you."
"I miss you even more darling" ya rik'o fuskanta "And I can't wait to have you back." Murmushi ta sakar masa sannan ya mik'a a hankali yayi kissing lips nata na lokaci kad'an. "I should get going."
"Tun yanzu Ya Rouhi?"
"I need to get back to work."
"Zaka gun Amal de."
"That is after I close from work."
"Toh tashi in raka ka" har gun motansa ta kaisa inda ya d'auko wani pack k'arami daga cikin motan ya mik'a mata "This is for you."
"For me?" Ta tambaya had'e da amsa.
"Open it" ya umarceta. Ba gardama ta bud'e wani Silver bracelet ne me bala'in kyau ta tarar aciki "Ya Rouhi this's so beautiful."
"Do you like it?"
"Alot, thank you so much Ya Rouhi."
"Alright ki koma ciki se mun sake waya." Da haka sukayi sallama ya koma office.
****
_9:36pm_
"Gobe zamuje muyi first baby scan namu ba? Ko bazaki iya zuwa ba?" Afzal dake kwance akan cinyan Amal a parlour ya tambayeta. Hannunta dake cikin gashin kansa tana wasa dashi ta cire "Mey ze hana Ya Omri? Allah kaimu."
"Ameen, d'azu naje gidan su Nazeefah."
"Oh how's she?"
"She's fine."
"Yaushe zaka maidota d'akinta?"
"Zuwa next week su Daddy sunyi tafiya so sai sun dawo "
"Allah kaimu:"
"Ameen" ya amsa had'e da d'ago kansa "I wish Nazeefah will be like you Rania."
"Meyasa kace haka?"
"Inda zata rage zafin kishinta ta sauk'o kaman ki ai kinga da mun samu zaman lafiya a gidan nan."
"Why?"
"Because bakida kishi Rania."
"Haka kake gani?" Ta tambayesa da murmushi kad'an.
"Yes Rania ban ta6a ganin kishinki ba."
"Saboda ina 6oye wa ne gudun sanyaka cikin damuwa kaman yadda kake ciki yanzu."
"Kina nufin kema kina kishi anytime na ambaci sunan Nazeefah?"
"Tabbas Ya Omri kawai dan ina 6oyewa ne ita kuma Nazeefah bata iya 6oye kishinta shiyasa kake ganin haka. If not ina matuk'an kishinka Ya Omri nakega fiye da yadda Nazeefah ma keyi, ma tukun tayaya ne ba zanyi kishinka ba bayan ina sonka?"
"Wow! So for all these while ranki na 6aci kema idan na kira sunanta?" Kai ta gyad'a masa "Amma bawai hakan na nufin na tsaneta bane saboda yadda nake jin inada iko da kai itama haka ne, we're both your wives Ya Omri and we love you."
"Rania you're just different in a unique way, Allah sa Nazeefah tayi koyi da halinki."
"Ameen" ta amsa tare da sakar da hamma.
"Baby na tana saki bacci ko?"
"Se kuma aka cemaka baby girl ce?"
"Toh mey ne da? Ai mace ce kyakkyawa kamar ki."
"A'a na miji ne, handsome kaman ka."
"Mu zuba mu gani."
"Eh mu zuba d'in, nida abu ke jikina kawani ce min na mace ce? Na miji ne let that sink."
"Wow ni kuma da nayi ajiyan kikeson kice bansan mey na ajiye ba?"
"Eh baka sani ba."
"Shikenan time will tell ba se munyi musu ba" cike da dabara ya mik'ar da ita kan kujerar had'e da aza kansa dai-dai saitin cikin nata kaman mey son sauraron abu "I wish I can listen to its heartbeat Rania."
"Not only will you listen to its heartbeat Ya Omri, one day zaka rik'e sa hannu" ta sanar dashi tana shafa kan nasa a hankali.
"Allah nuna mana wannan rana."
"Ameen" ta amsa.
"I can't wait have a replica of you calling me Daddy Rania, I really can't." Dad'i sosai taji ta sakar mar da murmushi "Thank you so much Babe."
"Godiyan mey kuma kake mun Ya Omri?"
"For everything Rania, for trying to give me a family Allah ya cigaba da miki albarka."
"Ameen Ya Omri everything for you yauwa d'azu ma Ummi ta kirani."
"Ayyah ya take?"
"Lafiya k'alau ashe ka fad'a mata I'm pregnant."
"A tunaninki zan iya yin shiru ne? Bank'i a buga a newspaper cewa kina da ciki ba Rania, you made me so proud and happy" hira suka ta6a sannan chan sukaje suka kwanta.
***
Lafiya k'alau suka cigaba da zama abinsu ba tashin hankali bale fad'a se zallan so da tsan-tsan k'auna amma kuma sey me? Kwana biyu zazza6in safe da na yamman nan ke son sake dawowa Amal, gabad'aya yabi yasata a gaba, kullum cikin amai take abin tausayi harta zube. Kaman kar Afzal ya fita office yau yakeji dan yadda jikin nata ya sake yin tsanani shi ya d'au sun riga sun wuce nan yanzu ashe rashin lafiyan mey tafiya ya dawo ne. Misalin k'arfe goma Maamah tazo dubanta. Ga laulayi ga targad'e a hannu da k'afan da be gama warkewa ba har yanzu.
"Sannu cikin nan na baki wuya Bestie."
"Thank you, anata lectures bani ko?"
"Gashi next week muna da tests har uku na Mallam Auwal biyu da na Malama Binta."
"Na shiga uku Maamah ko notes bani dashi gashi Malam Auwal baya bada handouts sede wani ikon Allahn kam in ba haka ba nasan inada carry overs wannan semester."
"Karki damu na miki photocopying nawa notes d'in na Malama Binta kuma gashi na sai miki" tayi maganan had'e da zaro su daga jakarta tana ajiyewa akan side drawer.
"Maamah bansan ya zanyi in ba keba, thank you so much Allah yabar zumunci."
"Ameen ba komai kede kawai ki samu time kiyi karatu in fever'n ya sauk'a. Ya Ya Afzal?"
"Ya fita office da k'yar wai ze zauna ya kula dani."
"Ayya meyasa kika hanasa?"
"Toh ba amfani Maamah zuwa sha d'aya haka zazza6in ze sauk'a."
"Ayyah ai ni na d'au kin rabu da zazza6in ashe da saura."
"Wallahi ko nima na d'au ya k'are kawai shekaran jiya ya fara mun kaman wasa fa se amai, komi naci hararwa nake."
"Sannu wata nawa ne yanzu?"
"D'aya fa da sati uku."
"Allah sauwak'e toh in shaa Allah kina fita daga first trimester naki shikenan."
"Ameen Maamah."
"Na gaya wa Ya Abdul fa."
"Mey d'in?" Amal ta tambayeta had'e da zaro ido.
"Batun kina da ciki mana."
"Innalillahi!" Ta dafe goshinta "Baki da hankali ne Maamah?"
"Toh mey? Ba abun farin ciki bane?"
"God help me wallahi baki had'u ba taya zaki fara sanar da Ya Abdul ina da ciki dan Allah? Mstw se yace mey?"
"Ya taya ki murna of course yace in gaisheki."
"Mstw wallahi ke banza ce wani sa'in ya yake toh? Se yaushe ze dawo?"
"Waya san masa ne kullum na tambayesa yace da saura da alama ya samu wata achan ne take d'ebe masa kewanmu."
"Allaha yasa toh wallahi da sena fi kowa yi masa murna."
"Wallahi ko, ameen deh." Hira Maamah ta tayata da se wajajen uku ta tafi sanin Afzal ya kusa dawowa. Saidai har shida Afzal yau shiru dan haka Amal ta d'au waya ta kirasa don jin ko lafiya, saidai da ya shiga seya katse yin hakan sau biyu se tayi tunanin ko yana meeting ne bada dad'ewa ba kuwa sega sak'onsa.
_Sorry for not informing you, I'm in a meeting be home in a moment I love you._
Murmushi ta sakar ta furta "Allah dawo daki lafiya." Sannan ta mayar da wayan ta ajiye.
Wajajen takwas Afzal ya dawo gida lokacin jikin Amal ya sake tashi se kakkarwa take k'ark'ashin bargo. Jakansa kawai ya ajiye ya nufi kanta yana shafa fuskanta a hankali "How're you feeling Rania?"
"Sannu da dawowa" kad'ai ta iya fad'a masa.
"Kinci abinci?" Ya sake tambayarta inda ta kad'a masa kai.
"Rania why? Bakiji abinda Dr yace miki ba jiya?"
"Ya Omri ko naci hararwa zanyi yana tayar mun da zuciya."
"I'm sorry kinji? Ko black tea ne ki dage ki sha bari in had'a miki."
"Please no bana so."
"Toh se mey? Bazeyi ki kwana akan yunwa ba Rania please."
"Koko nake so, idan nasha bana hararwa shi Mami ke bani lokacin da nike gida."
"Kokon dana sani kunun kamu?" Ya tambayeta da mamaki inda ta gyad'a masa kai.
"Toh Rania ina zan samu kamu? Ko da akwai ma ban iya had'awa ba kuma kinga dare yayi ba inda zan iya samu bale in siya miki."
"Don't worry zan sha ruwa kawai in kwanta gobe seka saya mun."
"Rania don't you get it? Bazan iya barinki ki kwana akan yunwa ba."
"I'm sorry" tace da shi idanunta na kakkafewa. Wayansa ya zaro daga aljihunsa "Wa zaka kira?" Tayi saurin tambayarsa.
"Ummi to ask ko zata iya had'a miki se in amso tunda gida ba nisa daga nan."
"Ya Omri ba seka sa Ummi aiki ba" saidai be saurareta ba ya kira Ummin bayan ta d'aga sun gaisa yake tambayarta ko akwai kamu a gida.
"Eh lafiya?"
"Ummi ban fad'a miki ba ko? Jikin Amal ya tashi."
"Subhanallahi bade laulayin ba?"
"Shi Wallahi gashi ko mey taci hararwa take se koko kad'ai kuma babu a nan gida shi'e nake tunanin ko zakisa su Esther su had'a mata yi hak'uri dan Allah."
"Kai kuma mey na wani bada hak'uri? Ai Amal 'yata ce bari in had'a mata yanzun ni da kaina driver ya kawo muku."
"Ko nima zan iya zuwa in kar6o kawai a had'a mata d'in."
"No ka zauna ka kula da ita tunda ga driver."
"Alright thank you Ummi."
"Kayi mata sannu bari in yi sauri in had'a mata" nan da nan ta wuce kitchen ta had'a kokon da kanta ta cika masu a wani k'aton flask yadda har gobe Amal zata iya sha sannan ta had'a musu da d'anye incase zata kad'a in ta samu k'arfin jiki. Zama yayi akanta yana ta yi mata sannu ko kayan jikinsa ya kasa cirewa kunun na isowa ya d'iba a cup yasa sugar kad'an yadda baze tayar mata da zuciya ba ya koma d'akin sannan ya kishingid'ar da ita jikin gadon ya shiga bata, na sosai yayi mamakin yadda tasha kokon sosai gashi ko hararwa batayi ba sa6anin duk wani abinda takai baki.
Ai ko idan haka ne ya zama dole ya koyi dama kokon dan yana yi mata. Bayan ta shanye ya buk'aceta da ta watsa ruwa zata fi jin dad'in jikinta amma tak'i, ba yadda beyi ba tak'i wai yau Amal tasa me son wanka wane kifi ce ake had'a ta da Allah tayi wanka take k'i? Tun jiya rabonta da yin wanka haka k'arshe se da ya d'iba ruwan d'umi a bowl da tsumma ya mammatse mata jikin nata da shi sannan ya samu ya sata tayi bacci. Nan shima yaci abinci ya k'arisa aikin daya rage masa daga office ya fad'a bayi ya watsa ruwa yana cikin fesa turare wayansa ya shiga ruri dubawanda zeyi yaga Nazeefah ke kira be 6ata lokaci ba ya d'aga inda suka gaisa.
"Su Daddy sun dawo ne?"
"A'a se next week kuma wai."
"Lafiya dai ko?"
"Lafiya kawai chan d'in ya musu dad'i ne."
"Ayyah se mun k'ara hak'uri sun dawo kenan ko Rabba'atul Bait?"
"Ya Rouhi ni kawai kazo ka d'aukeni."
"Bazeyi ba Rabba'atul Bait ki k'ara hak'uri kinji? Allah dawo dasu lafiya."
"Ameen ya jikin Amal?"
"Gashi nan Alhamdulillah deh."
"Allah sawwak'e toh."
"Ameen thank you."
"I miss you Ya Rouhi."
"I miss you even more darling it's late you should sleep by now."
"Goodnight toh."
"Sleep like a baby" nan ya katse ya gama abinda yakeyi yaje ya samu Amal suka kwanta. Duk yadda yaso kwantar da ita a jikinsa ya kasa sabida yadda jikin nata ya d'au wani irin zafi, sekace ba yanzu ya gama matse mata shi da ruwa ba.
Haka Amal ta cigaba da fama da zazza6in, da rana kad'ai take samu tayi karatu, ranan da zasuyi test d'in Afzal da kansa ya kai ta makarantar yayi magana da securities akayi cutting line aka shiga da ita ta gudanar da E-test suka komo gida. Haka duka sauran tests d'inma jiranta yake seta gama su taho gida tare. Kokon nan kuma shi kad'ai take sha ba tare da ta harar ba, da safe Afzal kafin ya fita office yake dama mata yasa a flask yadda da ta tashi sede tasha. Acikin sati Amal ta rame sosai tayi duhu sede jikin da sauk'i sosai yanzu zazza6in ya tafi se k'warnafi ko turare inba na wuta ko khumrah ba bataso, muddin tana d'aki Afzal be isa ya fesa turare ba se taji amai. Gashi sam bata son wanka yanzu, kwana biyu yau tak'i yin wanka matse mata jiki ma da Afzal yakeyi yau ta hanasa yi wai bata so. Alwala idan tayi na Azahar da shi takeyin La'asar wani sa'in har Maghrib. Shi de Afzal yanzu yake sake tabbatar da zancen cewa ciki nasa wasu matan k'aramin hauka.
"Rania yi hak'uri kiyi wankan kinji? Ni da kaina ma zan miki yi hak'uri." Ko tankasa batayi ba taja bargo ta rufe kanta, sauk'e bargon yayi "Yi hak'uri kinji? Karfa zama da dottin nan yayi miki illa."
"Wai wallahi inda kaine acikin halin nan ko alwala ma baza ka iya yi ba ka barni kurum in wari nake maka kaje d'ayan d'akin ka kwanta." Dariya sosai ta basa, mutumin da banda k'amshin turaren wuta ba abinda ke tashi daga jikinsa ne wai ze ce yana wari shi kawai gudun abinda zama da dattin ze iya haifar mata yake ba don wai tana wari ba.
"Yi hak'uri Rania beyi zafi haka ba."
"Toh ka barni in kwanta."
"Toh shikenan seda safe Allah k'ara sauk'i."
"Ameen" ta amsa tana rufe idonta sauk'an lips nasa taji a fuskanta "I love you."
"Ina da dotti ka manta ne?"
"I'll still kiss you Rania yi bacci kinji? Get well soon" Murmushi ta sakar masa sannan a hankali bacci ya d'auketa.
***
Da kwana hud'u Nazeefah ta kira Afzal akan su Daddy sun dawo, dad'i kenan he can't wait ya dawo da ita gida ta bawa Amal hak'uri su fara shiri, it's what he's ever asked for. Yana zaune a office yana aiki around 2:30 wayansa yayi beeping alaman shigowan sak'o. Message yagani daga Amal from snapchat da hanzari ya bud'e wayan ya bud'e, hotonta yagani wanda yake da tabbacin yau ta d'auka. Tana sanye da wani dogon rigan roba armless ba ko d'igon kwaliya amma tayi bala'in kyau da gashinta kame a tsakiyan kanta jelan na lilo. Be 6ata lokaci ba yayi replying nata;
_Triple A💦;_ Iyyeehh😍😍 yau baby na yabar min Rania tayi wanka kenan._
Bada dad'ewa ba sega reply nata.
_His Rania👑; 🙈 na cika ka da wari two days ko?_
_Triple A💦; dama shuwa suna wari ne? Ai ban sani ba don ni kullum na matso kusa dake k'amshin turaren wuta da khumra nake ji._
_His Rania👑; 😩 Ya Omri you're so sweeet_
_Triple A💦; 😁💕 Ya jikin naki toh? Da sauk'i?_
_His Rania👑; Alhamdulillah bakace nayi kyau ba😩😩_
_Triple A💦; Haba 'yar shuwata kema ai kinsan kinyi kyau 😍😍, send me more._
_His Rania👑: O'o ai baka ce mun nayi kyau ba seda na rok'a😕_
_Triple A💦; Rania please😩😩😭 Ya Omri is sorry._
Seda ta gama waina sa sannan ta d'au sabi ta tura masa inda yata yaba kyanta, na sosai yaso posting hoton amma tuna Nazeefah kan iya gani seya fasa, baya son abinda ze sake had'a kansu.
Sa6anin kullum yana isa gida Amal ta taresa yau harda hugging nasa.
"Yau turare na baya wari?" Ya tambayeta dan kuwa sede be matso kusa da ita ba seta toshe hancinta wai turarensa wari yake mata. Kai ta gyad'a tana masa murmsuhi "Welcome back Ya Omri."
"Jiki da sauk'i kenan."
"Alhamdulillah."
"You look so takeaway Rania."
"Thank you Ya Omri."
"Toh ya baby na? Kin bata abinci?"
"Mun sha kokon daka had'a mana kafin ka fita office har sau biyu."
"Mashaa Allahu, ya rage ko a k'ara had'a wani?"
"Ka bari seka huta besides na fara aiki mafa da hannun nawa kaga" ta d'ago hannun nata mey targad'e tana juyawa a idonsa. "Alhamdulillah, My Rania is such a strong woman Allah k'ara miki lafiya Sweetheart."
"Ameen Ya Omri mu k'arisa ciki" rage kayan jikinsa yayi ya ragar da shorts zallah sannan ya haura gado ya sameta inda take mik'i da handout rik'e a hannunta tana karantawa. Tamkar d'an yaro ya haye jikinta ya kwanta had'e da saita kansa dai-dai saitin k'irjinta da suka ciko tim. "Ya Omri zafi suke min kad'an gyara" tayi saurin sanar dashi.
"Ze daina Rania" yace da ita yana sake cusa kan nasa cikin k'irjin nata "Bacci nakeji na gaji daga aiki" murmushi ta sakar kad'an sannan ta zagaye hannunta a bayansa tana mey cigaba da karantunta, daga haka har itama baccin yayi awon gaba da ita. Da goshin Maghrib Afzal ya farka a hankali ya raba jikinsa daga nata ya fad'a bayi yayi alwala sannan ya tada ita itama.
Bayan da ya dawo daga sallan Isha ya had'a mata kokonta shi kuma ya had'a quarker oats yasha daga nan suka koma d'aki sukayi wankan su tare kaman yadda suka saba. Sede tun da suka kwanta Afzal keta tak'ura mata, itako tak'i barinsa chimma abinda yake da niyya se wani shusshuresa take shiko kaman maye ya kasa hak'ura.
"Ya Omri mana kana fa da office gobe."
"Rania yanzu duk hak'urin nan da nayi baki gani ba? I need you today hak'uri na ya k'are."
"Ni banida lafiya" ta amsa tana tattare bargon a jikinta.
"Na sani ai Allah k'ara miki lafiyan amma yi hak'uri ki barni kinji?"
"Ni gaskiya sena samu sauk'i."
"Haba My Rania yi hak'uri kinji? Kad'an kawai shikenan."
"Yimin wayo de" ta amsa tana cire hannunsa daya samu ya sak'ala cikin rigarta.
"Yi hak'uri kad'an nace I promise a hankali zan yi miki" rok'arta ya cigaba dayi har seda ya samu ya shawo kanta haka har suka gamsar da junansu. Tana rik'e a hannunsa bacci yayi gaba da ita. Shi kansa baze iya describing yadda yake son Amal yake kuma jinta a ransa ba, all he knows is that bayida irinta.
Kasancewar washegari Saturday ba aikin office se suka yini a gida abinsu, da safe sukayi breakfast tare, yau bayan kokon Amal har ta iya taci soyayyan k'wai da fries. Bayan breakfast ta rok'i Afzal da ya kaita salon ta wanke kanta. Shirayawa sukayi tsaf suka fice sede suka tarar da shagon a rufe, dawowansu Afzal yace ze wanke mata da kansa.
"Ya Omri yaushe ka iya wanke kai?" Ta tambayesa da mamaki.
"Da ke kike wanke min nawa?"
"Toh ai naka ba gashin kirki bane akai."
"Kede kam kizo mana kiga."
"A'a nikam gaskiya na yafe haka kurum ka jagwalgwala mun kai?"
"Rania I'm serious ki tsaya kiga in be wanku da kyau ba sekiyi complaining" wardrobe nata ya nufa ya d'auko mata vest da shorts "hungo sanya su."
"Amshi mana Rania kinga fa La'asr ya kusa" amsan tayi ta tu6e ta sanyasu ya jata bathroom d'in. Daga bakin tub d'in ya ajiye mata kujera ta zauna akai ta mik'a kanta ciki inda gashin nata ya sauk'a har k'asan tun d'in. Tsoro yawan gashin nata ya basa shi kansa yama rasa daga ina ze fara wankewan, maganin mey kaud'i kenan.
"Toh Ya Omri ka fara mana" tayi maganan had'e da tattare gashin nata ta d'ago kai tana kallonsa yayin da yake tsaye a kanta.
"Toh ki mayar da kan naki mana ai nasani" ya fad'a confidently sannan ya zauna daga gefenta a bakin tub d'in. Hand shower ya bud'e ya jik'a gashin nata da shi jak'ab sannan ya tsiyaya shampoo akai ya shiga massaging kan a hankali dan dad'i har wani bacci-bacci Amal ta soma ji a gurin. Wanke mata gashin yayi mey kyau shi kansa be tsamman ze iya ba bayan ya wanke ya d'aure mata head towel suka fito ta zauna gaban mirror sannan ta kunce towel d'in tana tsiyaye ruwan.
"Ya Omri zaka iya taimaka mun da jakan hand driers d'ina?" Ta tambayesa politely.
"A ina?"
"A k'asan wardrobe d'ina." Wajen ya nufa ya d'auko ya mik'a mata sannan ya cigaba da tsaye akanta yana ganin yadda take busar da gashin, na d'an lokaci shima ya gane yadda akeyi. Hannunta ya rik'e yana mey dakatar da ita. Da mamaki ta d'ago kai tana kallonsa "Kawo inyi miki."
"Ya Omri ai kayi mey wuyan zan iya yin wannan da kaina karka damu."
"No Rania kawo in miki" murmushi ta sakar masa sannan ya amsa ya shiga busar mata da gashin yana tajewa kaman yadda yaga tana yi har seda gashin ya bushe garau sannan ya jawo mai ya shiga shafa mata bayan nan yayi combing mey kyau sannan ya kama mata shi a tsakar kai sakwa-sakwa.
"Amazing Ya Omri you're just incredible."
"Yayi kyau?"
"Alot, thank you so much."
"Don't mention so you owe me big yanzu."
"Meyasa?"
"Nima wataran se kinyi mun aski." Dariya tasa na sosai "Ashe kuwa zaka ga disappointment har nice zanyi maka aski? Ashe wani ya kusa ya fara yawo da hula."
"Lool" dariyan yake shima '"Yar k'auye ko rik'e clipper ma bata iya ba hala."
"Toh akwai na miji ne a gidan mu da har zan koyan?"
"Ni d'in akwai mace ce a gidan mu har na koyi wanke kan?"
"Ai wanke kai da sauk'i yake akan yin aski barin ma irin naku na 'yan gayu da se an gyara saje, gaban kan ma a cire wani shape, spare me please ni bazan iya ba."
Dariya sosai ta basa amma ya cize, "Toh shikenan zan je Uni sex Salon (salon da maza ke zuwa mata ke zuwa) na Racheal tayi mun askin tunda ita ta iya."
"Gun mace zaka je?" Ta kewayo tana tambayansa da mamaki yayinda kishi ya bayyana karara a fuskanta.
"Toh ba kince ke baki iya ba."
"Toh ka je d'in zunubin ai ku biyu za a rubuta muku banda ni" ta sanar da shi had'e da juya mai baki sannan ta cigaba da harkan gabanta. Murmushin gefe ya saki nan da nan ya canza kayan jikinsa yasa wani bak'in half jamfan da ya mugun amsansa ya feffeshe jikinsa da turare ya zuba accessories nasa sannan ya d'au jakan askinsa ganin fa dagske yake ze fita Amal ta k'urma ihu kafin ya kai ga bakin k'ofan ta sa key ta k'wace.
"Matar Afzal ki bani guri in wuce."
"Wallahi bazaka fita ba."
"Harda rantsuwa?"
"Eh wallahi bazaka fita ba."
"Toh ni da gida na?"
"Eh naji amma bazaka fita ba."
"Askin ke zakiyi mun ne?"
"Ai gashin kama be yi wani tsawo ba fitina ne kawai."
"Nide matsa min."
"Seka rantse gun na miji zakaje tukuna."
"Why?"
"Taya wata mace zata ta6amun kai? Wallahi Nazeefah kad'ai na yarda ta ta6a ka."
"Really?" Ya tambayeta yana dariya.
"Sosai ma kuwa, bayan nan ga 'yan mata cike kullum a shogon so kake su yi mun snatching d'inka?"
"Toh laifin waye? Ba ke kika ce baki iya ba."
"Toh zan koya" dariya sosai ta basa amma ya moze. "Ni matsa min."
"Zan koya Allah zan koya amma kar kaje shagon Racheal dan Allah."
"Yaushe zaki koyan toh?"
"Ya Omri ai kasan ba a dare d'aya zan iya koya ba but zan sa kai."
"Promise?"
"I promise" ta amsa tana gyad'a kai dad'i sosai yaji ya jata jikinsa had'e da zagaye hannayensa a 'yar kunkuminta "Ashe kina sona haka dama?"
"Eh mana" ta amsa tana turo k'aramin bakinta. Bata hankara ba kawai taji yayi owning lips nata a hankali yake turata har suka fad'a kan gado ya shiga yi maya wasanni. Da k'yar ta iya k'watan kanta "Ya Omri yanzu na wanke kaina Allah bazan iya sake jure jik'asa ba."
"Karki damu zanyi miki drying."
"A'a Ya Omri da Allah kayi hak'uri ka bari" ko sauraranta beyi ba ya tu6e vest d'in daga jikinta. "Ya Omri stop wallahi zanyi maka ihu."
"Kiyi d'in se muga mey k'watan ki" haka ya cigaba da sarrafa ta har seda ya kashe mata jiki lissss ya biya buk'atansa.
a_An hour later..._
Amal ce kwance jikin Afzal yana shafa dogon sumarta yayinda wayansa dake kan side drawer ya shiga ruri. "D'an mik'i mun wayana Rania" ba gardama ta juya ta d'ago "Wake kira?" Ya tambayeta.
"Nazeefah" ta amsa had'e da mik'a masa, niyyan basa waje tayi har ta janyo vest nata zata sa seya rik'e hannunta ya sake kwantar da ita a jikinsa tare da zagaye hannunsa a bayanta sannan yayi receiving call d'in.
"Halo Ya Rouhi?"
"Na'am Rabba'atul Bait ya kike?"
"Lafiya ya gida ya Amal?"
"Alhamdulillah lafiyanta."
"Jikin nata da sauk'i?"
"Eh Alhamdulillah."
"Su Daddy sun dawo d'azu."
"Oh haba?"
"Eh."
"Sun dawo lafiya?"
"Lafiya k'alau yaushe zaka zo ka d'aukeni Ya Rouhi?"
"Tunda yau suka dawo mu bari mana gobe? Su huta yau ko?"
"Ya Rouhi anya kuwa you miss me?"
"You know right I do Rabba'atul Bait ki shirya kayakin ki yau kinji? First thing gobe zanzo in d'aukeki."
"Toh shikenan sekazo I love you."
"I love you too" yace sannan ya katse.
"Rania?" Ya kirata kai ta d'ago a hankali tana kallonsa. "I'm sorry kinji?"
"Why? What for?"
"For everything I said to Nazeefah that made you felt jealous."
"Karka damu Ya Omri, tunda nima kana fad'a mun daddad'un kalamu haka dan mey zanji haushi sabida ka fad'awa 'yar uwata? Wannan kishi dole ne amma bawai hakan na nufin naji haushi bane, so karka damu kaji?" Dad'i sosai kalamunta suka sanya sa ya sake rungumeta tsam ajikinsa "I love you soo veryy much Rania."
"So gobe zaka je ka d'auko ta?"
"Yes in shaa Allah har gida tace zata zo ta baki hak'uri."
"Allah kaimu toh."
"Ameen."
"I'll miss you for the 2-2days da zaka na yi mata."
"I'll miss you terribly too Darling" ya sanar da ita had'e da placing mata light kiss a goshi "Tashi muyi wanka toh muyi sallah kinga ana neman hud'u se muje muci abinci ba?"
"Sure Ya Omri."
"Karde har kin mance?"
"Dame fah?"
"Seriously Rania?"
"Yi hak'uri ka tuna mun na d'an sha'afa ne."
"Wato kin ma manta yau zamu fita first baby shopping namu ko?"
"Ya Omri beyi sauri ba?"
"Haka kullum kike cewa ai a hankali a hankali zamuna ragewa please don't say no, I'm so excited."
"Alright toh."
"Kin yarda zamu je?"
"Anything for my Omri." Nan da nan sukayi wanka sukayi sallah sannan suka shirya suka wuce shopping. Siyayya sukayi sosai, Afzal na kwasan kayan baby girl Amal na yin na baby boy se dariya masu shagon suke musu amma ko a jikinsu. Se after 6 suka dawo gida da goshin maghriba.
****
GIDAN ALHJ ABDALLAH.
RANA D'AYA!
#RD 💖
Love... King Miemiebee👄✨
19 comments:
Godia babu adadi miemiebee
Allah ya kara basira
Please update soon I can't wait inji abinda baban Nazeefah zaice.
Nazeefah sorry ooh aurenki da Afzal yazo karshe dan dole cikin keda Amal daya zata fita Kuma nasan kece.
Thanks so much sweedy... Godiya muke
Masha Allah, thx so much sis
Tenx so much .
Toh-toh-toh......ana wata ga wata
Amma nasan zaiyi wuya Bbn Nzf ya amince da komawarta .
Amma baridai mujira muga abinda zai faru....Miemie Allah ya kara basira. We luv u much .pls update soon
Sannu da kokari mamana. ..Amma kullun members of miemie grp sune yan gata kullun sai anyi musu dedicatin page😑
Thanks,dan Allah ana tunomu da wuri��
Thank you swtat Allah y Kara basira more update pls.
Thank you swtat Allah y Kara basira more update pls.
Hop our miemie is duin fyn de. ...Coz it is unlike u
Very unlike her kam shirun is getting out of hand gashi duk mun kusa muji yadda za a kaya
Very unlike her kam shirun is getting out of hand gashi duk mun kusa muji yadda za a kaya
Allah dai yasa komai lfy
Amin ya Rabbi
Amin ya Rabbi
Miemie hope all is well? Munjiki shiru.
Walhy fa
I pray nothing bad is wrong with our miemie😥
Hope all is well. Allah yasa lafiya
Post a Comment