Saturday, 25 August 2018

RANA D'AYA!

BY MIEMIEBEE
PAGE 39

_Barkan mu da Sallah darlings, da fatan kowa tayi sallah lafiya Allah ya maimaita mana ameen.😘 Ina kuke 'yan gida na *MIEMIEBEE NOVELS?* wannan pejin naku ne, thank you for all the love, support and care, Allah cigaba da had'a kawunanmu yabar zumunci, I love y'all fisabilillah❤️💕



   


   _Labari na ya fara ne lokacinda na had'u da Abdallah wanda ake kira da Khaleefah, lokacin ina matakin form 5 (ss2) da karatu a Government Girls College dake garin Askira inda muke da zama a da kafin muka dawo nan. Umma (mahaifiyata) ta kasance mey buri akaina kasancewar ni kad'ai Allah ya azurta ta da, tunda ta haifeni har ta koma ga mahaliccinta ko 6atan wata bata sake ba. A dalilin haka ta d'au burin duniya ta sauk'e akai na, na cewa se mey kud'i ko d'an wane zan aura. Lokacin da samari suka fara lek'o kai suna nemana se Umma ta hanani kula kowanne daga cikinsu acewarta se mey kud'i. Duk yadda Abba yaso ya ganar da ita cewan shi fa miji na gari ake nema ba se mey d'ankaren kud'i kaman yadda take buri ba hakan ya gagara, acewarta taya 'yar shuwa kaman ni zan fara auren d'an talaka. Dan inyi ladabi a gareta se na hak'ura ban kula kowa duk wanda yazo guna da sunan zance se in ce masa ni an riga anyi mun miji ana cikin haka ne na had'u da Khaleefah watarana a hanyana na dawowa daga Islamiyya. Acikin duk manema na ba wanda ya ta6amun ya kuma burgeni ya kwanta mun a rai kaman Khaleefah, duk yadda naso sharesa lokacin da ya fara mun magana hakan ya gagara kawai na tsinci kaina ina mishi fara'a, har gida ya rakani ranan na basa lamba na a karo na farko da ya tambaya. Khaleefah saurayi ne kyakkyawa san kowa k'in wanda ya rasa, lokacin da muka had'u yana matakin part 2 ne a karatu a wata jami'a a chan k'asar waje inda ya samu scholarship. Khaleefah ba d'an babban gida bane amma saurayi ne mey zafin nema saboda tun a lokacin yana d'an sana'a haka, kafin ya koma makaranta soyayya me k'arfi ya shiga tsakanin mu amma ban ta6a nunawa Umma ba sanin bazata ta6a amincewa dashi ba. Ko da yazo ya koma makaranta hakan bey hana mu cigaba da gudanar da soyayyar mu ba, ze kirani mu wuni muna waya nima ranan da nasamu kud'i kuma nakan sa kati in kirasa muyi hira. Ana cikin haka ne d'an Alhj Iro Chairman na Askira ranan da suka zo makarantar mu kawo ziyara ya ganni yace yana sona ni kuwa ban basa fuska ba nace masa ina da wanda nakeso dukda haka be saurareni ba seda yazo har gida ya samu Abba ya sanar da shi k'udirinsa akaina da kuma abinda na fad'a masa na cewa ina da tsayayye. Umma naji ta hau ni da surutu akan bata yarda in kula kowa ba se Faisal d'an Alhj Iro. Niko a lokacin ba wanda na tsana kamansa, daren ranan na kira Khaleefah na irga mai halin da ake ciki inda ya rok'eni da in kwantar da hankalina idan ya dawo next hutu zeyi ma Abbansa magana ya turo magabatansa. Na sosai na tsaya da addu'a dan kar Faisal yayi gaggawan turo magabatansa cikin ikon Allah se har wani hutun ya sake zagayowa Faisal be turo ba. Lokacin ina matakin ss3 da karatu har mun soma rubuta WAEC._
   _RANA D'AYA ina cikin waya da Khaleefah Umma ta jiyoni, fisge wayan tayi ta jawoni tsakar gida tun daga d'aki sannan ta shiga duka na tana huci._
  _"Ban ce ba ruwanki da wani d'a na miji a gidan nan ba se Faisal?"_

  _"Umma dan Allah kiyi hak'uri" na shiga bata hak'uri cikin tsananin kuka._

  _"Rufa mun baki maras kunya kawai ce miki akayi ban san mey nake bane da nace se Faisal zaki aura? Ana neman miki sauk'i da jin dad'i anan gaba kina shashashanci."_

  _"Umma dan Allah kiyi hak'uri wallahi bana son Ya Faisal ni Ya Khaleefah nakeso."_
   _Zazzafan mari ta sauk'e mun a fuska. "Ina fad'a kina fad'a? Mey za'ayi da talaka da talauci idan ba Allah ya d'aura ma mutum ba? In ba rashin wayo irin naki ba ma taya a matsayin ki na 'yar shuwa zaki hau auran talaka? Kin ci sa'a har d'an chairman yace yana sonki amma kike sokancin nan? Naira na kiranki kina cewa baki so? Jakar ina ce ke? Wallahi idan har kinga kin auri Khaleefah yake kowa toh a bayan raina ne. Ma tukun waye shi? D'an gidan waye ne?"_
 
  _"Umma kiyi hak'uri."_

  _"Tambaya nake miki waye shi nace?"_

  _"D'an gidan Malam Ilu ne."_

  _"Wani Malam Ilu? Na bakin titi?"_

  _"Eh shi."_

  _Wallahi ban ta6a sanin bakida wayau ba se yau, ashe rashin wayon naki ya kai matakin da har zakiyi sha'awan aure a wancan matsiyacin gidan."_

  _"Amma Umma ai nagari ake nema ko musuluni bece se mai kud'in bala'i ba bale ma fa yana karatu bazamu rasa na rufin asiri ba."_

  _"Uwarki da karatun da kuma rufin asirin nace, chin kwalin degree d'in zakiyi kokuwa, kuma ni zaki gaya ma musulunci? Toh naji musulunci bece se me kud'i ba amma ai al'adar ki bata amince ki auri talaka ba."_

  _"Umma amma-"_

  _"Dakata idan kuma kina ganin ya akayi na auri Abbanki kike bayan bayida komai kisani Abban ki d'an uwa na ne, auran had'i akayi mana kuma nima muddin zaki amince ki auri wani nawa koda baida kud'i zan amince miki amma muddin bare zaki aura toh wallahi se mey na hannu kiji ki sani."_
 
  _"Umma bana son Ya Faisal dan haka bazan aureshi ba" na sanar da ita cikin 6acin rai. Amsana ba k'aramin tunzirata yayi ba, kafin in hankara kawai naji ta rufe ni da d'an banzan duka ana cikin haka ne Abba ya dawo daga kasuwa ya kar6eni. "Haba Awatif! Meyayi zafi haka zakisa yarinya a gaba kina dukanta kaman ganga? Meya faru?"_

  _"Yo ba gara gangan ba dama an san ba mutum neba bale yayi wayo, kuma ba ruwanka Malam wannan tsakani na da 'yata ne ehe! Bana son shisshigi."_

  _"Shisshigi fa kikace? Ni da 'yata kice shisshigi?"_

  _"Eh shisshigi ne mana kana na miji ina ruwanka da harkan daya shafemu." Abba be sake kulata ba ya juyo a gareni "Yayata ta kaina yi hak'uri" ya shiga bani hak'uri "Mey ya faru?" Bayanin komai na mishi Umma na tsaye tana hararata cike da takaici._

  _"Haba Awatif! A ina akace se mey kud'i za'a aura? Tunda yarinyan nan tana son yaron nan kuma yana da shirin turo magabatansa me zey hana muyi mata abinda takeso?"_

  _"Aww biye mata zakayi kai ma? Toh wallahi kunyi k'arya dukanku 'yar nan bazata auri matsiyaci ba se Faisal mu zuba daku mu gani" tana kaiwa nan ta janye hijabin ta daga kan igiya ta fice. Kuka na cigaba da yi a wajen Abba yana ban hak'uri._

  _"Abba dan Allah ka bawa Umma hak'uri Abba bana son Ya Faisal bana sonsa."_

  _"Yi hak'uri Jameelah zanyi mata magana in shaa Allahu zata sauk'o kinji? Kukan ya isa haka."_
  _Haka nan Umma ta k'wace mun waya ta hanani waya da Khaleefah ko fita ta hanani in ba Islamiya ko boko ba kullum ina rufe kup a gida gashi duk yadda Abba ya so fahimtar da ita gaskiya hakan ya gagara saboda Umma ta kasance mace mey zafi ko Abba wani sa'in tana fin k'arfinsa daga k'arshe Abba yace sede in hak'ura inyi yadda takeso saboda yayi-yayi ya ganar da ita gaskiya amma tak'i fahimta niko nak'i amincewa da hakan, ranan paper'n mu na k'arshe bayan mun gama naje na samu Khaleefah na sanar da shi cewa Faisal ya kusa turo magabatansa da yayi ma iyayensa magana su riga sa turowa idan har akayi haka toh dole Umma ta yarda amma sai dai shima koda ya kai maganan gida iyayensa suka k'i amince mai acewansu ya bari seya gama makaranta tukun. Na sosai na shiga wani irin yanayi bani da wata sana'ar data fiye na kuka acikin gida. Ba waya gashi ko fita Umma bata bari na inyi kusan sati biyu kenan banji daga Khaleefah ba rana d'aya kwatsam kawai mukaji ana sallama, amsawan da Umma tayi sega Khaleefah. Da fari da bata gane waye shi ba ta kar6esa da fara'a ta k'arisa dashi ciki bayan ya zauna yayi mata bayanin kansa ya fayyace mata k'udurinsa akaina Umma ta ci mai mutunci tayi mai koran akuya a idona ta kuma nuna masa ni Faisal zan aura. Ranan na kasa bacci dole washegari da yamma na saci idonta naje duban Khaleefah. Wannan yini shine mafi munin yini a rayuwa na, ban ta6a tsammanin Khaleefah ze iya mun abinda ya mun ba, ashe abinda Umma tayi masa ya mugun ci masa rai dan haka yayi tunanin k'untata mata ta hanyan 6ata mun rayuwa, yana ganin idan ya cuceni kaman ya cuceta ne, a tunaninsa Umma na sona d'inda har idan abu ya shafeni zata shiga damuwa saidai ba haka bane. A yinin ranan ne Khaleefah ya mun fyad'e ba irin rok'o da hak'urin da ban basa ba amma haka seda ya aikata abinda yayi niyya ba ko d'igon imani tattare da shi had'e da taimakon abokansa k'waya biyu. Bayan faruwan abun ban sake sanin inda nake ba se bayan kwana biyu dana farka na tsinci kaina a gadon asibiti. Abba na fara tararwa nan take na shiga zubda hawaye yana bani hak'uri shigowan Umma ta shiga zagina na tana kira na da 'yar iska. Duk yadda Abba da likita suka so ganar da ita fiyad'e akayi mun tak'i amince tana ganin gaskiya amma ta take. Ba irin sunan da bata kirani da shi ba harda ja min Allah ya isa. Har aka sallameni daga asibitin kuma bata sake koda lek'oni ba, Abba ne ya zauna akaina har aka sallameni. Ranan da muka dawo gida Abba ya shirya zuwa tinkarar iyayen Khaleefah akan abinda d'ansu ya mun dan k'watan mun hak'k'i amma haka mahaifin Khaleefah ya bushe ido yace sam shi d'ansa be aikata wannan mumunan abu ba sharri kawai ake son yi masa. Shima Khaleefah koda aka kaimu gaban mey unguwa rantsuwa ya ringa yi shi ba abinda ya ta6a had'amu ko sani na ma beyi ba haka muna ji muna gani aka tauye mana hak'k'i. Faisal kuwa tun da yaji wannan magana ya d'auke k'afa daga gidan mu hakan yasa Umma ta sake tsanata, dama chan nasan ba sona yake har zuci ba, kyau da jiki na kawai yake bi. Bayan wata biyu da faruwan abun ne kwatsam rana d'aya na tashi da zazza6i da amai. Ko kallon kirki Umma batayi mun ba, ina cikin aiki a kitchen da rana kawai amai yabi kaina na fito na shiga kwararowa a tsakar gida ana cikin haka Umma ta dawo gida daga unguwa, salati ta shiga yi tana tafe hannu amma ko agaji bata taimaka mun da ba seda na gama na kishingid'a jikin bango sannan ta tako ta shiga dubata._
   _"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ciki! Wayyo jama'a! Shikenan tayi cikin shege" ihu ta shiga yi tana kururuwa seda ta tara mana jama'a a gidan kafin ace mey magana ya zagaye gari akan cewa 'yar Malam Muhammad tayi ciki alokacin kuwa har Khaleefah ya koma makaranta, koda nazo na samu waya na kirasa layin nasa bai shiga ba shakka ya canza. Tun daga ranan da aka tabbata ina da ciki Umma ta sauya mun a gidan tokari na safe daban na yamma daban tamkar ba 'yar da ta tsuguna ta haifa ba haka ta tsaneni take kuma gaba dani. Sau dayawa nakan zauna in sha kuka ina kokonton anya kuwa Umma ce asalin mahaifiyata? Se daga baya Abba yake sanar dani dalilin daya sa ta tsane ni. Tun farko bata so ayi mun takwaran Baaba Jameela ba yar Abba wacce jininsu sam be had'u ba, sam babu jituwa a tsakaninsu tun ma kafin ta auri Abba, bayan auran nasu kuma se abun ya sake lalacewa tamkar annabi da kafiri haka suke ji da juna, toh tunda aka samun sunan Baaba Jameela Umma ta tsaneni. Shima Abba bawai yaso yasa sunan bane sedon mahaifiyarsa da dama akayi niyan yi mata takwaran tace ta yafe ayiwa Baaba Jameela kasancewar tunda tayi auri sama da shekara ashirin ko 6atan wata bata ta6a ba, dalilin da yasa aka sa min sunanta kenan._

   _Ba yadda banyi da Abba ba da ya barni in zubar da cikin amma yak'i acewansa yin hakan haramun ne bayan nan kuma nima ina iya rasa raina ta dalilin hakan. Ko fita ban isa inyi ba haka ina ji ina gani na daina zuwa islamiyya bayan nayi nisa sosai a karatun, shima Abba kaman wasa duk inda yaje se an ringa binsa da kallo ana nuna sa da yatsa, harta kasuwa gun aikinsa. Umma ce kad'ai ke fita freely ta dawo gida bawani fargaba ko tashin hankali saboda ko zagi na ake seta tsaya ta sa baki ayi da ita. K'arshe de haka zaman garin Askira ya gagaremu amma Umma ko a bakin zaninta hasali itama ke yad'a wa mutane nayi cikin shege. Alokacin da Abba ya gir6e gonansa lokacin cikina na wata hud'u ya kawo shawaran mubar garin Askira idan ba haka ba ko nazo na haife cikin nawa ba bar min d'an za'ayi ba shi kuma abinda yake gudu kenan, baya son laifin Khaleefah ya shafeki Baby._

  _Koda Abba ya sanar da Umma cewa zamu bar Askira ita tace ba inda zata tunda ba ita ta turani inyi abun kunya ba. Ganin Abba dagaske yake ko ba ita shi zeyi tafiyarsa yasa ta amince ta biyo mu. Gidan mu da komai da muka mallaka Abba ya siyar muka dawo nan Maiduguri bada sanin kowa ba dan ko Umma ma Abba be sanar da ita inda zamu ba kawai ganin kanta tayi anan cikin garin Maiduguri. Mun dawo bada dad'ewa Umma ta kamu da ciwon nono wato breast cancer, ina da shekara sha tara na haifeki Baby, bamu ta6a neman abu gun Abbanki mun rasa ba, komi yi mana yake, damuwa na tun kafin in furta yake yaye mun. Tamkar 'yar cikinsa haka ya d'aukeki yake kula da ke. Kina da shekara biyu mutuwa yayi halinsa ya tafi da Umma sede har ta mutu bata ta6a rik'eki a hannu ba. Tsanan duniya gabad'aya ta d'au ta aza mana ni da ke ko kallon arziki ban ta6a ganin tayi miki ba, batun Khaleefah kuwa har yau ban sake ji daga garesa ba. Sau dayawa manyan 'yan kasuwa masu aure harma da samari su kan nuna suna son su aureni amma tun kan abinda Khaleefah ya mun naji na tsani na miji a rayuwata shiyasa kika ga har yau ban sake yin aure ba, dan kuma gudun kar wataran yaran dana haifa su nuna miki banbancin 'yan uba, bana son abunda ze ta6a farin cikinki Baby, bana so"_ ta k'are cikin tsananin kuka.

    Kuka sosai Amal take itama, Afzal ma na sosai jikinsa yayi sanyi yana mamakin rashin imani irin na Umma marigayiya da kuma wannan Khaleefah mahaifin Amal.

  "Baby kiyi hak'uri na 6oye miki wannan sirri da nida Papinki mukayi dan Allah kiyi hak'uri."

  "Kibar bani hak'uri Mami, ni ya kamata inyi hakan na rashin fahimtar ku da banyi ba keda Papi please forgive me." A hankali Mami ta rungumeta yayinda suka cigaba da kuka shima Afzal seda k'walla ya ciki masa a ido dan tausayi. Be dad'e ba aka sallamesu Afzal ya dawo da su gida chan dare da Mami tashigo kawo wa Amal abinci Amal ta tsayar da ita.

  "Mami alfarma nake nema."

 "Fad'i ko mey kikeso Baby."
 
  "Mami ku raba aure na da Yaya."

  "Subhanallahi meya faru Baby? Wani abun ya sake miki ne?"

  "Mami sanin kanku ne kun cuci yaya tun farko da kuka san asali na be kamata ku had'a mu aure ba."

  "Baby wani irin magana kuma kike? Ya kike magana sekace mun zalunce shi? An fa fad'a mishi gaskiya kuma a hakan yace yana sonki Abbanshi ma na wajen."

  "Kina nufin Abba ma yasan asalina?" Kai Mami ta gyad'a mata a hankali.

  "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" ta furta cike da tashin hankali yayin da hawaye ya shiga ciko mata a ido. "Bayan su se suwa kuka sake sanar dasu asalina?"

  "Wallahi babu Baby daga su shikenan."

  "Nide na fad'a muki kuyi ma Yaya magana kawai ya bani takarda na bazan iya cigaba da zama da shi ba, zaluncin ya isa haka."

  "Baby dan Allah kibar magana haka, ya kike magana sekace laifinki ne kika kasance haka? Karfa ki manta wannan k'addararki ce haka Allah yaso ya ganki kuma ba wai yayi hakan dan baya sonki bane se don ya gwada k'arfin imanin ki."

  "Na sani Mami shiyasa nake son Yaya ya sauwak'e mun, Yaya be kamanci shegiya kaman ni a matsayin matarsa ba-"

  "Baby dan Allah kibar magana haka ki daina kwatanta kanki da wannan mumunar kalma" Mami tayi saurin katse ta yayinda ta saki murmushin takaici "Akwai k'arya ne acikin hakan Mami? Ko ba shegiyar bace ni?" A hankali Mami ta jata jikinta "Dan Allah ki bar fad'in haka, Baby tunda muna sonki mijin ki na sonki mey kuma kike nema? Wannan abu ya riga ya faru ba abinda zamu iyayi mu canza ko a tunaninki ni d'in dad'i nakeji na cewa bakida uba? Wallahi Baby na fiki takaici da zafin hakan shiyasa ni da Papinki muka d'au burin baki tarbiyya da ilimin boko da na islamiyya duka dan ki banbanta daga sauran 'yan matan da suka tsinci kansu acikin hali irin naki masu yawo akan layi suna barikanci saboda ganin da suke ba ta hanya madaidaiciya aka same su ba, Baby idan ba wai fad'a akayi ba bawanda ze miki kallon shegiya dan Allah ki daina fad'in haka" cikin kuka ta d'ago kanta daga jikin Mami tana share hawayenta "Godiya nake da ilimi da tarbiyyan da kuka bani Mami amma ban cancani miji kaman Yaya ba da yake da asali da mutunci da ma komai ba bayan ni inada akasin hakan, dan Allah ku mishi magana ku kuma basa hak'uri na zaman da mukayi tare."

  "Baby cikinsa da kike d'auke da shi fa? Ya zakiyi da shi? So kike ki haifi d'an shima ba uba?"

  "Sam Mami amma k'addara tariga fata cikin nan kuma zan raineshi, yadda Papi ya tayaki rainon cikina na tabbata ze tayani rainon wannan har zuwa lokacinda zan haifa in mayar masa da d'ansa."

  "Kekuma fa Baby? Haka kikeson ki k'arisa rayuwarki cikin k'unci da takaici ba miji kaman ni?"

  "Ya fiye akan in zauna da wanda nake ganin kaman ina cutansa ne Mami, wallahi gani nake Allah ma baze yafe mun ba."

  "Subhanallahi bayan shi yace kar a fad'a miki gaskiyan al'amarin ko bayan da yaji komai? Da ace mune muka 6oye mai gaskiya da seya zama yadda kike fad'an amma fa da saninsa da kuma amincewansa kafin aka d'aura muku aure."

  "It still doesn't matter Mami, Yaya deserves someone much better than me, he's way out of my league bazan iya cigaba da zaluntarsa ba." Duk yadda Mami taso fahimtar da Amal gaskiya hakan ya gagara ita sam hankalinta yak'i d'aukan maganar ita kawai Afzal ya sallameta, game da soyayyar da takeyi masa kuwa zata rok'i Alah ya cire mata shi daga zuciyarta du da cewan tasan hakan ba k'aramin abu bane. Da k'yar Mami tasamu kukan nata ya lafa ta sata taci abinci ta sha magunanta sannan tayi mata sallama ta janye k'ofar taje ta samu Papi take irga mai yadda su kayi da ita. Na matuk'a Papi ya tausaya wa Amal dama ranan da ya jina yana gudu kenan, ranan da zata gano gaskiya ta tsani kanta.

  Tana mik'e akan gado tana kukan zuci wayanta dake kanta ya shiga ruri dubawan da za tayi taga Afzal ke kiranta ba shiri ta 6arke da kuka. Tunda take a rayuwarta bata ta6a tsanar kanta da kuma k'yamar kanta ba kaman yanzu, gabad'aya ji tayi batada mutunci bata da daraja, bata jin zata sake iya sa Afzal ko Abbansa a ido waya sani ma ko sun sanar da Ummi hala itama Ummin ta sanar da Nazeefah. Amma ko idan da har Nazeefah tasan asalinta ta tabbata da ta yi mata gori da shi. Shin meyasa Afzal be bari an fad'a mata gaskiya ba? Ai idan da ta san gaskiyan al'amarin tun fari da bazata soma auren sa ba ma. Haka tana gani wayan ya tsinke bata d'aga ba har a karo na biyu ma k'arshe kawai seya tura mata sak'o. Sa6anin yadda ta saba goge sak'onninsa anytime ya tura mata yau se tayi tunanin ta bud'e inda ta fara karancewa kaman haka;

   _My Adorable Kitten please don't let what you found out earlier ruin you, you're still the beautiful, charming, elegant, intelligent, clever, and amazing Amal that I know, my wife and mother to my unborn kids. I love you regardless have a peaceful night rest, I'm missing you and our little one down here. Xx_ 😘

   Tana gama karancewa ta shiga wani sabon kukan haka ta kwana tana yi se kusan Asuba bacci mey nauyi ya d'auketa. Wajajen goma ta tashi bayan tayi wanka Mami ta kawo mata breakafst nata taci sannan Papi yayi sallama cikin d'akin nata. Zama yayi ya mata nasiha sosai amma inaaa Amal ta riga tayi making up mind nata ita sam bazata komawa Afzal ba. Daga k'arshe Afzal d'in Papi ya kira ya sanar da shi halin da ake ciki yana tashi daga office ya biya gidan nasu. Ba yadda Papi beyi da Amal ba da ta fito daga d'akinta Afzal yazo wajenta amma tak'i ta rufe kanta a d'aki se kuka take. Na sosai zuciyan Afzal yake k'una gabad'aya ya rasa ina zesa kansa. Kwana uku ya jera yana zuwa duban Amal amma ko yaje baya samun su had'u gashi koya kirata bata d'agawa, messages nasa ma bata replying tamkar sabon mahaukaci haka Afzal ya koma. Su Papi ma sunyi mata magana har sun gaji amma tace sam bazata cigaba da zama da Afzal ba tana cutansa, acewarta zalunci ne ace yadda yake d'an halak ita ko ga ta inda aka sameta ace sunyi aure. Tun sha biyu ya baro office yau yaje ya samu Ummi a gida kallo d'aya tayi masa ta gano yana cikin matsala.

   "Meya faru kuma Prince? Amal d'ince har yanzu bata sauk'o ba?"

  "Ummi things just got worse."

 "Subhanallahi kamar ya?"

  "Ummi kiyi hak'uri na 6oye miki wannan sirri da nayi nasani ko ba dad'ewa da jimawa gaskiya ze fito shiyasa nake son sanar dake yanzu."

  "Speak up already meya faru?"

  "Ummi gab lokacin da na kusan auren Amal iyayenta suka bayyana mun da Abba wani 6oyayyan al'amari wanda na buk'aci Abba da kar ya sanar dake bawai dan ban yarda dake bane se don ina gudun kar hakan ya canza miki ra'ayi akan Amal."

   "Ina jinka."

  "Ummi Amal batada asali."

  "Asali kaman ya kenan?"

 "Amal ba ta halatacciyar hanya aka same ta ba."

  "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un kana nufin Amal shegiya ce?"

  "I'm sorry but yes."

  "Kuma ka aureta Afzal? Baka da hankali ne?"

  "Ummi ki tsaya ki saurareni mana bawai abinda kike tsammani bane, k'addarar fyad'e ne ya fad'o akan mahaifiyarta."

  "Haka suka ce maka? Kuma ka yarda?"

  "Yes Ummi saboda ba k'arya sukeyi ba idan da har k'arya ne da bazamu ta6a jin sirrin nan daga bakinsu ba amma fa Papi da kansa ya sanar da ni da Abba."

  "Toh ai wayo suka maku saboda sun san ba a iya 6oye abin kunya ne."

  "Ummi kibar cewa haka, just calm down and listen to me ita kanta Amal bata ta6a sanin gaskiyan ba se last week."

  "Ita Amal d'in?"

  "Yes nida Abba suka fara fad'awa akan daga nan se su sanar da ita amma na buk'aci da a cigaba da 6oye mata gaskiyan saboda nasan halinta muddin har ta gano gaskiya toh zata iya k'in amincewa ta aureni gashi yanzu ta gaano gaskiya tace ita sena sauwak'e mata tana cewa she don't deserve to be with me I deserve someone better."

  "Ita Amal d'in? Ya akayi ta gane gaskiyan yanzu?"

  "Shine ai nake kaiki, ranan da naje gidansu muke sulhu ne taji komai" labarin duk yadda sukayi ya kwashe ya bata, Ummi can't help but to remain shocked. Tausayin Amal ne ya kamata na matuk'a.

  "Toh yanzu ya kenan? Zaku rabun?"

  "Kema kinsan bazan iya rabuwa da Amal ba Ummi."

  "Toh ya zakayi Afzal tunda iyayenta ma sunyi su ganar da ita sun gagara."

  "Even stil Ummi I'll continue to try my best."

  "Ko kana so inyi mata magana?"

  "Nooo bana son tasan kin sani."

  "Toh Allah baka ikon shawo kanta wallahi tabani tausayi matuk'a yarinya ga haddan Al~Qur'ani."

  "Ummi bakiga yadda take kuka ba ranan da gaskiyan ya fito."

  "Allah sarki Amal 'yar nan jarabawanta a duniya dayawa suke Allah de bata ikon cinyesu."

  "Ameen Ummi."

  "Ya batun Nazeefah fah? D'azu Mummy'nta ta kirani muka gaisa when do you plan on bringing her back?"

  "Ummi muddin Amal bata dawo mun ba bazan iya dawo da Nazeefah ba."

  "Zata dawo in shaa Allah Prince zan tayaka da addu'a."

  "Thank you Ummi barin wuce gida in huta idan Abba ya dawo ki gaishesa."

  "Bazaka jira lunch ba sauran kad'an fa."

  "I'm not hungry Ummi thank you." Rakasa tayi har gun mota sannan ta dawo ciki.

   Afzal be fasa zuwa duban Amal ba a rana na shida ne da yaje ya tarar da Mami kad'ai itama tana shirin fita, tana gama cin abinci ta basa hak'uri kan zata shiga nan mak'ota yin barka akan ya jira Papi shi ma ya kusa dawowa.

  "Ayya ba komai Mami sekin dawo zan jirasa."

  "Yauwa toh barin wuce." Bayan ta fice ya mik'e had'e da zaro wayansa daga aljihu sannan ya taka har izuwa bakin k'ofan d'akin Amal dai-dai gun ya tsaya ya shiga buga layin nata sede yana ji daga ciki yana ringing amma bata d'agawa.

  A hankali ya gwada bud'e k'ofan sa6anin kullum ya tarar da k'ofar a bud'e da mamaki ya bud'e mik'e akan katifarta tana bacci ya tarar da ita a tunaninsa gabad'aya tana ganin call d'inne kawai tak'i d'agawa ashe bacci take even though yasan koda idonta biyu ma ba d'agawa zatayi ba. Cikin d'akin ya k'arisa ya tsuguna a gefenta. A hankali ya aza hannunsa akan cikinta yana shafawa a hankula.

  "Kitten?" Ya kirata da k'aramin murya. "Kitten wake up it's me Afzal" ya sanar da ita kaman a mafarki take jin sautin muryansa, a hankali ta shiga bud'e idonta har ta sauk'esu akansa ba k'aramin razana tayi ba ganinsa da tayi akanta kad'an ya rage bata sa ihu ba.

  "Shhhhh it's just me calm down" ya buk'aceta. Kanta ta kawar ba tare da tace da shi komai ba.

  "Amal?" Ya kirata nan ma bata juya ba a hankali ya kewayo da fuskarta. "Babe please come back to me, dan Allah kiyi hak'uri mu koma gida I terribly miss you." Shiru ta mai ba tare da tace komai ba hakan yasa ya cigaba.
  "Amal fushi kike dani har yanzu da bazaki mun magana ba? Please forgive me I'm sorry, I'm terribly sorry."

  "Why did you do it?" Ta soma da tambayarsa tare da kewayowa.

  "Did what Sweetheart?" Yayi saurin tambayarta.

  "Mesa ka hana su Mami sanar dani gaskiya Yaya? Meyasa ka aureni bayan kasan yin hakan kaman ka zalunci kanka ne, sanin kanka ne iri na da bamuda asali bamu cancanc-" da sauri ya katseta ta hanyan aza hannunsa kan dry lips nata. "Please not a word Amal, I married you because ba laifinki bane da kika kasance haka, I married you because I love you Amal, I don't care koba ta halatacciyar hanya aka sameki ba and above all I married you because it's been destined you're going to be my wife and the mother to my kids Amal saboda akwai rabo a tsakaninmu" ya k'arashe maganan had'e da aza hannunsa akan cikinta. "Please come back home with me Baby please don't say no." By now kuka take sosai "I can't Yaya, I really can't" ta sanar dashi cikin tsananin kuka had'e da kawar da kanta.

  "So dagaske ne da Papi yace kince in baki takardanki?" Ya tambayeta cike da k'in yarda. Kai zalla ta gyad'a masa.

  "Lily ya kikeson in rayu in ba ke? Taya kike tsammanin zan iya rayuwa idan ba ke a kusa dani please don't punish me like this, by Allah my heart can't take it dan Allah kar kiyi mun haka taya kike tsammanin zan iya rubuta miki takardan saki wallahi koda wuk'a a wuya na bazan iya ba yaushe ne zaki gane cewa kece rayuwa na Amal idan kuma ba ke bazan iya rayuwa ba? When will you realize that?" A hankali ta shiga juyo da kanta tana mey mamakin kalan tashin hankalin daya bayyana a fuskansa tausayinsa kawai taji ya kamata har yanzu ta rasa gane soyayya ne ko kuma wani ciwon yake damun Afzal ace yasan asalinta amma be k'yamace taba bayan ita da kanta k'yamar kanta take.

  "I'm sorry Yaya I'm terribly sorry" ta basa hak'uri hawaye na tsiyaya daga idanunta.

  "I don't want you to be Amal just come back to me please ko ba dan ni ba dan wannan" ya fad'a yana sake mayar da hannunsa kan cikinta. Hannunsa tabi ta aza nata akai "Yaya you don't deserve me at all, you deserve someone better."

  "Dan Allah kibar cewa haka, I deserve no one other than you Amal please come back." Shiru tayi bata sake ce dashi komai ba.
    "Kinji? Dan Allah kiyi hak'uri kibar cewa in sawwak'e miki." Kai ta gyad'a mar a hankali. "Kin yarda zaki dawo?" Ya tambayeta eagerly nan ma kai zalla ta gyad'a mishi. Wani irin farin ciki Afzal ya tsinci kansa a ciki, hannunta ya d'aga had'e da placing soft kiss akai "Thank you Amal, thank you so much."

  "Yaya meyasa kake so na haka?"

  "Kitten ni kaina ban sani ba all I know is my love for yu knew no bounds a jinin jikina yake."

  "Yaya shin baka k'yamata ne?"

  "Subhanallahi Amal wace irin magana kike haka? Dan Allah kar ki sake cewa haka kinji?" Kai ta gyad'a mishi a hankali "Thank you" mik'awa yayi a hankali yayi kissing kumatunta "In shirya miki kayakin ki mu koma gida yanzu?"

  "A'a Yaya" tayi saurin cewa.

  "But Kitten why? Baki hak'ura ba har yanzu?"

  "Ba haka bane, I was never mad at you I was just angry."

  "Toh yaya ne?"

  "Yaya ai ni nace zan dawo kar ka damu nafi son in had'a kayakin nawa da kaina."

  "Toh ai bazaki iya ba hannunki da ciwo har yanzu."

  "Mami will help me kar ka damu."

 "Har yaushe kenan?"

  "Yaya don't you trust me?"

  "I do Amal morethan I do trust myself I just can't wait to see you back home." Murmushi kad'an ta sakar masa "You should go, Papi ya kusa dawowa kar ya tarar da kai anan."

  "Sure" ya amsa yana duban agogon dake d'aure a tsintsiyar hannun sa. "Kafin nan baki fad'a mun how many months is my baby ba Kitten" Wani kunya taji ya rufeta take ta kawar da kanta wanda hakan ya sanya sa murmushi "Kunya na kikeji Kitten?" Shiru tayi bata ce komai ba "Tell me kinji? In soma counting."

  "Yaya da saura fah."

  "Toh how many months ne?"

  "D'aya ne fa kacal" ta sanar da shi cike da kunya.

  "Wow! In conclusion saura mana 8 months kenan we have a long way to go don't we?"

  "Yaya ka tafi kar Papi yazo ya tarar da kai please."

  "Kori na kike haka Kitten?"

  "Yaya please."

  "Ba kiss ba komai kike son in tafi Kitten? Do you know how terribly I miss your sugary lips?" Bata kai ga juya mai baya ba ya rik'o hannunta "I can't wait to have you back Kitten" ya sanar da ita kafin ya matso kusa da kunnenta "Sena biya bashin duka kwanakin nan da muka d'auka bamu tare" kunya ne ya rufeta gabad'aya kawai ta matse idonta. Murmushi ya sakar sannan yayi pecking nata a kumatu "I'll call you later I love you" yana kaiwa nan ya ajiye mata envelope daya tanadar mata sannan ya mik'e ya fice ko jiran dawowan Papi beyi ba ya koma gida cike da farin ciki.

  Chan misalin k'arfe tara ya kira ta seda ya kusan tsinkewa ta d'aga.

  "Alhamdulillah I can't remember when last kika d'au wayana Kitten thank you for picking up."

  "You're welcome Yaya."

  "So how're you and my baby?"

  "Duka lafiya shine ka ajiye min kud'i d'azu Yaya?"

  "Take care of yourself Kitten I love you."

  "Thank you" ta amsa tana murmushi.

  "Yaushe zaki dawo toh?"

  "Zan dawo karka damu."

  "Toh shikenan zanga ko zan iya cigaba da jirarki nayi kewarki Kitten, there's no one to run to after coming back from home, no one to bath with or sleep together with ni kad'ai na na rage pity me and do come back soon please."

   "Nazeefah fa?" Kawai ta tsinci kanta yana tambayarsa.

 "Bata nan."

  "Tana ina?"

  "Na ce ta tafi gida Kitten muddin baki  dawo ba bazan iya dawo da ita." Mamaki tasha na sosai amma tayi shiru akanta ya tura Nazeefah gida? Wow!

  "Kitten are you there?"

 "Uhmm" tayi mumbling.

  "Kiyi ki dawo kinji? I miss you so much."

  "Toh mun gaisa I'm sleepy ina son in kwanta."

  "I can't ask for more Kitten, kwanta kinji? Sleep like a baby I love you."

  "You too seda safe" bata jira jin me zece ba ta kashe wayar. Murmushin dake d'auke akan fuskan Afzal ya kasa gushewa he can't wait to have his Amal back. Be kai ga ajiye wayansa ba sak'on gaisuwan Nazeefah ya shigo na goodnight bayan ya karance yayi replying nata da _Thank you I love you too_ 😘💕

   ****
   A kullum jira Afzal yake Amal tace masa ta shirya yazo ya d'auketa sede shiru ko yayi mata maganan kuma setace tana kan shiri ne gabad'aya ya k'osa ta dawo bayan kwana hud'u da yamma yana zaune a parlour yana kallon sports sega call nata yana shigowa hannu na 6ari ya d'aga baze iya tuna yaushe Amal ta d'au waya ta kirasa ba.

  "Halo Kitten?"

  "Yaya kana gida ne?"

  "Yes Kitten."

  "Zaka iya zuwa ka d'aukeni ko se gobe?"

  "Gobe kuma? I'm on my way right now." Wurgi da wayan yayi ya mik'e ya sa sabin kaya red buttoned sleeves shirt  me adon bak'i da black trouser sanin yadda Amal ke son red color. Combing gashin kansa yayi sannan yayi wanka da turare ya fad'a bayi ya wanke bakinsa da mouthwash ya fito ya d'au key ya fice. Nan da nan ya isa gidansu Amal yana k'arisawa ciki ya tarar da su zaune a tsakar gida Amal tayi wanka tsaf abinta ba bandeji ko d'aya d'aure a jikinta se yanzu ya gane dalilin da yasa tayita jan dawowa a garesa ashe so take se ciwonta ya warke. Masha Allah.

  Sanye take da pitch hijab mey hula wanda ya mugun mata kyau bayan sun gaisa duka Papi ya yi musu nasiha sosai itama Mami ta d'aura nata akai da kansa ya janye akwatin nata yakai mota ya kuma bud'e mata k'ofar bayan ta shiga ya rufe. Har yanzu da k'ingishi take tafiya a sanadin accident d'in, hannunta ma ba iya aiki take da shi sosai ba kawai de da sauk'i ne. Sallama yayi dasu Papi sannan ya tada motan suka fice se gida. D'agata yayi chak a sama ya kaita har ciki yayinda yasa mey gadi ya shigo da akwatin nata.
  Mamakin yadda ko ina yake tsaf Amal take bayan nan ga k'amshin turaren wuta.

  "Kai ka kunna turare?"

  "Kin tuna lokacinda na tambayeki yadda kikeyi?" Ya tambayeta da murmushi.

  Kai ta gyad'a tana mayar masa da murmushin "I'm impressed."

   "Let's go in ki rage kayan jikinki" bata kai ga mik'ewa ba daga kan kujerar daya ajiyetan ya dakatar da ita. "Let me."

  "Yaya kar ka damu I can manage."

  "No My lady allow me assist you."

  "Toh Yaya ai likitan ma kansa cewa yayi ina k'ok'ari ina taka k'afar idan ka cigaba da d'agani ai tsami k'afar zatayi."

  "Naji amma ki bari na yau" bata sake mai musu ba ya k'arisa ya d'agata suna kai corridor'n d'akin nasu tace "Ka manta chan ne d'akina?" Ta tambayesa da gan-gan tana mai nuni da d'akin data koma bayan daya korata daga d'akin nasu.

  "Kitten da gan-gan kike ko? Ai sede ni in bar miki d'akin ba ke kibar min ba, it was so wrong of me to send you out of your own room forgive me okay?"

  "It's okay Yaya" ta amsa tana mar murmushi, murmushin ya miyar mata sannan suka k'arisa ciki ya dawo ya ja akwatinta bayan ya sauk'e ta akan gado. Da kansa ya shirya mata kayakin acikin wardrobe nata. Ya so su fita cin abinci bayan sallan Isha amma ganin hakan ze bata wuya funda ga yadda take taka k'afara har yanzu se kawai yayi deciding ya musu girkin da kansa.  Kulleta yayi a d'aki be bud'e ba seda ya gama komai yayi arranging dining sannan ya d'auketa a hannunsa zuwa dining d'in yana bud'e flask d'in Amal taja wani numfashi "Hummm it smells so good."

  "Wait until it is served" ya amsa cike da jin dad'i. Da kansa yayi serving nata spaghetti d'in, da fari yaso suci a plate d'aya amma tuna condition nata se be sake sha'awan d'agata ba dan kar ya bata wahala. Na sosai Amal taci abincin harda neman k'ari wanda hakan ya mugun yima Afzal dad'i. Wani sabon soyayyarta yaji yana shigansa, tamkar k'wai kuma haka yake jinta baya sake k'aunan abinda ze had'asu har wanda zesa ta sake yimai yaji. Shi kad'ai yasan kalan tashin hankalin da ya shiga a rashinta. Bayan sun gama yatattare wajen dukda cewan taso yi amma ya hanata bayan ya dawo ya zauna kusa da ita inda ta kira sunansa a hankali.

  "Nazeefah fah yaushe zaka dawo da ita?"

  "Soon" ya amsa.

  "Ina Safiyya?"

  "Na sallameta har gida nan Mahaifiyarta tazo ta bada hak'uri tace ta riga ta mayar da ita k'auye dama tun farko bataso kawo su nan d'inba."

  "Allah sarki, Safiyya was innocent Nazeefah ce tayi manipulating mind nata ta kirani yayi sau uku tana bani hak'uri akan in yafe mata."

  "Dukda haka be kamata tayi miki abinda tayi ba Kitten kodan yadda kike kyautata mata kayakinki nawa kika bata?"

   "Yanzu kam ai ya wuce."

  "Nazeefah fa? Ta kiraki?"

  "Tace mun mey? Ba abinda ya sake had'amu."

  "Kitten I'm sorry nasan abinda Nazeefah ta miki da zafi kuma nasan bata kyauta ba but I would appreciate it if you'll find it in your heart to forgive her ni da kaina zan sa ta kiraki ta bata hak'uri."

  "No need Yaya godiya nake da Allah ya tozarta mana ita ka gane halinta bale ta sake tunanin cutar dani kawai ka barta."

  "But Kitten zan so ace you two are getting along ba abinda zefi min hakan farin ciki dan Allah kiyi hak'uri."

  "Yaya it's really okay" ta fad'a had'e da rik'e hannunsa. "In har Nazeefah ta gane kuranta ta kuma nemi tubana nikam me yafe mata ne kodan kai ma."

   "Thank you so much Amal Allah yayi miki albarka."

  "Ameen" ta amsa da murmushi.

  "Muje mu kwanta ki huta kinsan yanzu da da ba d'aya bane you'll be needing alot of rest now kafin nan kuma sena kar6i hak'k'i na ko bazaki bani ba?"

  "Yaya" ta ambata tare dukar da kanta cike da kunya.

 "Sarauniyar masu kunya toh wasa nake miki besides you're still sick I can wait until you get better" murmushi kad'ai ta iya ta sakar masa "So let's go bath" chak ya d'agata se a bayi ya direta inda ya fito ya d'auko musu towels nasu da kansa ya rage mata kayan jikinta. Bayan lokacin kansu da suka samu a bayin k'arshe ya tayata yin alwala dukda cewan tana iya yi da kanta amma yayi insisting shi zeyi mata. Daga nan ya tayata ta d'aure towel nata sannan suka fito tana rik'e a hannunsa. Kayan baccin ma yak'i ya barta tasa, bayan ya sanya mata yana cikin sa nasa ta mik'e a hankali ta nufi dressing mirror ta zauna ta shiga warware gashinta da hannunta d'aya ganin hakan ze bata wuya Afzal da ya gama sanya kayansa ya mik'a hannu ya rik'eta "let me help you" warwarewa ya k'arisa yi ya d'au comb ya shiga taje mata a hankali sannan ya shafa mata mai ya kama mata shi sakwa-sakwa yadda zataji dad'in bacci.

   "Thank you Habib Albi" ohhh how he misses her calling him with the name, baze iya tuna rabonta da ta kirasa da sunan ba. A hankula ya mik'ar da ita "Kikace?" Gano so yake ta sake nanata sunan se tace;
  "I said thank you" zalla.

 "No ba haka kikace ba" yayi saurin kad'a kai had'e da zagaye hannunsa a 'yar kunkuminta. "Yaya careful k'afana."

  "Sorry so say the name again Baby."

  "Wani suna?"

  "Kitten mana!" Ya had'e rai.

  "Ya Omri? Ya Amar? Ya Hayat? Mi Amor? Noorul qalb? Noorul ein? Wanne d'aya?"

  "Damn! My kitten is such a lover girl, all these sweet names for me?"

  "Yes Habib Albi so wanne kafi so? I'm giving you a new pet name."

  "Really why?"

  "Saboda we're starting a new life all over again, wannan karan ba fad'a ba komai se zallan soyayya da kulawa kawai."

  "Masha Allahuu I'm so proud of you Kitten Allah cigaba da yi miki albarka."

  "Ameen Habib Albi so wanne kake so?"

   "I think 'Ya Omri' sounds great."

  "Then you garrit Ya Omri."

  "How about I give you a new name too?"

  "Really?"

  "Yes Kitten."

  "Toh ina sauraranka" shiru yayi na d'an lokaci yana nazari, "How about Cherry? Peaches? Pearl? Flower? Rania? Snuggly? Cupcake? Which one?"

  "Cute names Ya Omri, Rania sounds arabic hakane?"

  "Yes Kitten it means Queen, my Rania my Queen" yayi mata bayani.

  "Uhmm na d'au Malikati ne My queen."

  "Rania is another form of it so wanne kikeso? Malikati ko Rania?"

  "Rania it's more fancy."

  "Really?"

  "Yes."

  "Toh shikenan starting today you're My Rania."

  "Thank you Ya Omri."

  "All the time My Rania."

  "So muje mu kwanta bacci nakeji." Kafin tace zata juya ya sake kankameta yadda ko k'wak'k'waran motsi bazata iya ba "Ya Omri lafiya."

   "I want to kiss you so badly Rania."

  "Ya Omri.." ta kuma furtawa tana k'ok'arin dukar da kanta, yatsa yasa ya d'ago fuskan nata sannan ya shiga shafawa a hankali "May I?" Ya tambayeta yana gangarowa kan lips nata. Wani irin kunya taji ya rufeta kaman ta nitse a k'asa ba k'arya aciki ita kanta she misses his tasty lips and minty breathe.

  "Rania may I?" A hankali ta gyad'a masa kai "No Rania it doesn't work like that answer me may I have a taste of this lips?"

   "Yaya mana" ta amsa a tak'ure tana kawar da k'wayan idonta daga nasa. "May I?" Ya sake tambaya yana mata murmushi "Yes Ya Omri you may kiss me" ta sanar dashi. Dad'i sosai yaji ya shiga matso da fuskansa kusa da nata a nitse seda ya had'e lips nasu, kissing nata ya shiga yi gently with tender touches yayinda take replying nasa itama a hankali dictating to him how much she missed him. Be bari numfashnta ya d'auke ba yayi breaking kiss d'in, a hankali ta sauk'e goshinta akan ha6arsa tana maida numfashi.
  "I love you Rania" ya sanar da ita yana shafe kan sajen fuskarta.
 
  "I love you too Ya Omri" daga haka ya d'agata ya kaita d'aki inda suka kwanta bayan ya kashe musu wuta.

  "Goodnight Raina I love you" ya sanar da ita had'e da sanya hannunsa k'ark'ashin rigarta yana shafa kan flat tummy'n ta.

  "Goodnight Ya Omri I love you too" ta amsa tare da sauk'e hannunta akan nasa.

 




RANA D'AYA!
#RD

Love... King Miemiebee👄✨

14 comments:

Unknown said...

Tnx miemiebee with this interested episode ,kai mun gode Allah ya kara karfin ido da basira.amin

Unknown said...

Enter your comment...godiya muke sis

Unknown said...

Oshey miemie more ink to ur pen,
Nazeefah auranki da Afzal yazo karshe, thank God ma baki da ciki

Unknown said...

Waiting 4 more update. To see how Nazeefa & her Father confronted the other house and their reaction.
More ink 2 your pen Miemiebee.tnx

Unknown said...

Double twalle to miemie bee joor. Allah na karo kwandon basira nd more updates I pray

Unknown said...

Uw

Unknown said...

❤️❤️❤️

Unknown said...

You're welcome

Unknown said...

Ameen you're welcome

Unknown said...

Hmmmmmm.... akwai sauran aiki. Tnx. We love you too

Unknown said...

Hmmmmmm.... akwai sauran aiki. Tnx. We love you too

Unknown said...

Weldone sis

Unknown said...

Allah ya kara basira

Unknown said...

Pls a cigaba