Thursday, 9 March 2017
‘YAR GATA CE!
"Toh Masha Allah, in shaa Allahu zaki dawo d'akinki Zeezee, Al'ameen ze dawo dake kinji?" Wani irin dad'i maras misanltuwa ne ya ziyarci zuciyan Zeezee wanda tuni hawayen farin ciki suka soma tsiyaya daga idanunta. Kasa 6oye farin cikinta tayi, "dagaske Mama? Kin yarda kuma Ya Al'ameen ya amince ze dawo dani d'akina?"
"Sosai ma Zeezee in shaa Allahu bade kuka kike ba?"
"Mama I have to, ban ta6a tsammanin zanyi witnessing rana makamancin na yau ba, indeed you and your family are special souls sent from heaven to me. Nagode sosai ban zata zaku yafe min haka har ki sake bani wani chance d'in ba. Allah ya saka muku da mafificinsa ya kuma farinta muku kamar yadda kuma kuka farinta min. In shaa Allahu zaku sameni me ladabi da biyayya da kuma kula muku da Ya Al'ameen da dukiyarsa in all thank you so much." Mama na murmushi ta amsa da "ameen" a rayuwa batada burin dayafi taga Allah ya kawo ma Al'ameen nata matar da zata sosa kamar yadda Zeezee ke nunawa tana son Al'ameen nata yanzu. "Allah ya baku zaman lafiya, ya kuma baku zuriyya d'ayyiba. Zanyi ma Mamanki magana in shaa Allahu in two weeks time Al'ameen ze dawo dake saboda inason muyi celebrating re union naku." Kunya sosai Zeezee ta jiyo, "Mama is that necessary please karku sa kanku wahala, bazawara dani ma."
"Yimin shiru nikam kede kawai stay beautiful komin da zaki sa Aysha da Salmah will take care of it."
"I will be lying to tell you just how grateful I am Mama nagode sosai, Allah yabar zumunci."
"Ameen" anan Mama ta katse. Ji Zeezee ke kaman a mafarki dukannin abubuwan nan ke faruwa wai ita da Major General Muhammad Al'ameen united again! She can't wait to witness their married life again yadda zatayi showering nasa da soyayya zallah, she'll love him with all that she have. Da gudu ta fice zuwa d'akin Mama domin sanar da ita wannan great news inda taji Mama ma na akan waya, d'an tsayawan da tayi ta fahimci da Mama Babba suke wayar. D'akinta ta koma ta kira Lubiee inda tayi ta mata hauka, Ya Al'ameen ze dawo da ita and akwai party celebration da za'ayi holding. Sosai best friend nata taji mata dad'i sosai suka yita murna.
Mama na gama waya da Mama Baba ta kirawo Zeezee, bayan Zeezee tazo ta zauna Mama tayi gyaran muryarta.
"Zainab?" Ta kirata.
"Na'am Mama." Ta amsa a nitse.
"Ki bud'e kunnenki da kyau ki saurareni kinji ko?"
"Ina ji Mama." Tayi maganan kanta a k'asa.
"Kinfi kowa sanin the kind of hell you went through a gidan Adeel, don Allah yana sonki ne shiyasa ya ku6utar dake daga hannunsa yakuma sake dawo miki da masoyinki wanda both you and I couldn't believe so. Mama Babba ta sanar dani yadda komi ya faru and tace she wants you back as her daughter-in-law again. Kinfi kowa sanin me hakan ke nufi Zeezee, inhar tun yanzu kinsan bazaki zo ki kula mata da d'a ba tun wuri ki sanar dani na fad'a mata. Kinfi ni sanin yadda matar nan ke son d'anta."
"Mama wallahi ina son Ya Al'ameen kuma am ready to sacrifice anything just for his happiness, ina sonsa sosai and I'll take care of him as his wife."
"Allah yasa toh ya kuma baki iko."
"Ameen Mama."
"So tace min mu saurareta nan da two weeks tace da ba don Al'ameen is a bit busy ba da a jibi anyi komi an k'are amman saboda yadda aiki ya mai yawa zasu ga nan da sati biyun."
"Ba komai Mama Allah ya kaimu, nima kinga senayi amfani da wannan dama na d'an yi gyaran jikina."
"Exactly" cewar Mama "kin kawo shawara." Nasiha sosai ta d'aura wa Zeezee akai.
****
Kamar yadda Mama Babba ta fad'a a cikin sati biyun suka samu suka had'a komi, gobe in Allah ya yarda zasu wuce Bauchi where the luncheon will take place. Abinda ya kama daga gown, takalmi, accessories duka da Zeezee zata sa Mama Babba tasa Aysha da Salma sun tanadarwa Zeezee. Al'ameen sam be goyi bayan wannan luncheon d'in tsiyan ba saboda how busy he is, da k'yar ya samu ya kar6i excuse nan ma don ana ganin girmansa ne aka basa just some few days. Shi bek'i kawai a d'auko mai matarsa ba a kai masa gida.
On Zeezee's side kuwa ba k'aramin gyara tasha ba, wani fari da kyau ta k'ara. Magunan gyaran jiki na ciki dana waje da take sha da kuma amfani dasu kuwa sam bata wasa dasu unlike before wani sa'in ma ita ke cewa Mama na gunta ya k'are a sake amso mata wani. Anan ne Mama ta sake tabbatar da cewa lallai Zeezee is willing to go back to Ya Al'ameen. 'Yan uwanta gabad'aya sun samu hallaro wannan taro, they are damn happy for Zeezee for finally getting back the love of her life again. Friends nata kap tayi inviting wannan re-union party inda suma suka ci ashobensu.
(Nima Miemiebee na gayyato manya-manyan bak'i na 'yan team Maj-Gen Al'ameen erinsu Aunty Sis, Maman Fadeel, Maman Sultan, Queen Bilqees, Safiyya Galadanci, H. jiddah, Mjay, Mrs. Muhammad, Ilhamerh, Shukrah, Fadeela Sagir, Bilkisu Babayo, Ummi Hambali, Sa'adah Umar, Zainab. A, Sugrah, Aysha me littafi, Miss Fancy, Aasmaa Isa Muh'd, Ummu Aysha, Biebiee dee, Ramlah Gokaru, and to all of members of team maj-gen Al'ameen in my most honoured group miemiebee novels 2, my blog followers, YGC fanclubs 1&2, miemiebee fans club 1,2 and 3 and to all members of Team Maj-Gen around the globe. Duk na ganku kuna kwaso shoki😅👍)
Black gown me torches da adon white taci da black head inda Al'ameen yasha farar babbar riga da aikin bak'i shima. Kallo d'aya mutum zeyi musu su tafi mai da imaninsa. They just nailed it, ba abinda ya sake k'ayata party'n nasu kamar fara'ar Zeezee ko wani juyi Mama Babba tayi sede ta kama Zeezee na murmushi unlike last dinner'n su da tunda aka fara har aka gama ko hak'waranta basu gani ba. Zeezee couldn't take her eyes off her man. Koda aka buk'aci couple da su tashi suyi rawa, bayan Zeezee ta tashi ita ta miqawa Al'ameen hannu she is proud to show to the world that this is the man, the love of her life. Sam ta kasa sake hannunsa, rawa sama-sama Al'ameen yayi haka Zeezee ma. Seda Mama Babba suka fiffita ne ta zage tayi rawa sosai dasu Lubiee tare da fans.
Indeed that day was an unforgettable one for Zeezee. Wane sabuwar amarya haka su Mama Babba ke tattalin ta bayan sun gama luncheon suka wuce wani d'an opening again inda sukayi bud'an kai suka yita wankan naira suna rawa, anan ne Zeezee ta tuna da Baba se kuma tasa kuka, tana farayi Yasmeen ta kar6eta, se kan Maryam har Mama sanda tayi kukan itama. Kafin a hankara suka maida gun wajen kuka, don dole aka rufe taron aka wuce da Zeezee gidanta da aka share, akayi mopping aka kuma turare se k'amshi ke tashi kota ina. K'arfe 8:24pm aka sauk'e Zeezee a d'akinta. Har anan ta kasa dena kuka, se dawo mata events na rasuwan Baba suke if only Baba was here, taso ace Baba zeyi witnessing re-union nata da Al'ameen, ya d'auketa kaman yadda yayi a da ya dank'a wa Al'ameen ita halak malak. She really miss her Dad.
Da misalin k'arfe 10:45pm, lokacin kowa da kowa ya watse daga Al'ameen se Zeezee se kuma guards nasu. Kuka take har yanzu takasa tsagaitawa. Da plate cike da kaji a right hand nasa, left kuma juice a cup Al'ameen ya k'ariso gaban k'ofan d'akin Zeezee inda ya ajiye cup d'in kan wani chess of drawer'n irin wall mirrors d'innan sannan a hankali yayi knocking bisa k'ofan. Ba abinda yake ji banda sautin kukan Zeezee wanda sam bayi k'aunan ji. Jin shiru ya kira sunanta "Zainab? Zainab? You there?"
"Ka shigo Ya Al'ameen" ta fad'a cikin murya me rawa. A hankali ya bud'e k'ofan ya k'ariso ciki tare da ajiye mata abinda ya taho dashin akan side drawer'n dake gefenta.
"Are you still crying Zainab?" Kai tayi saurin kad'a mai tana share hawayenta.
"Stop it kinji bana so." Maimakon ta jisa ta tsagaita kukan a'a se kaman k'ara volume na kukan naki yace da ita. Ai seta sake 6alle masa da wani sabon kukan shark'af-shark'af. Rasa nayi kwata-kwata ma yayi da k'yar sannan ya zaro hanky ya matso kusa da ita tare da d'ago wet face nata from tears ya shiga share mata hawayen. "Na sha gaya miki Zainab banason ina ganin kina kuka haka."
"I miss him so much Ya Al'ameen I've never been a good and proud daughter to him."
"Kiyi hak'uri kinji? Aduk inda Baba yake yanzun nasan he is damn proud of you." Jikinsa kawai ta fad'a tare da hugging nasa sosai tana me cigaba da kukan, chak ya tsaya kaman gunki ya kasa hugging nata back. Se daga baya a hankali sannan ya aza hannayensa both a bayanta yana bubbugawa a hankali "its okay kinji? Our prayers are with him zamu cigaba da yi masa addu'a Allah ya cigaba da kai rahama kabarinsa."
"Ameen thank you."
"Shhh! Kukan ya isa toh" yayi maganan yana d'agota daga jikinsa. Hannu tasa ta share hawayen nata tare da komawa gefe ta zauna "I'm sorry" ta mai apologising.
"You don't have to gashi ci ki samu ki kwanta kinji? You must have been exhausted."
"Thank you Ya Al'ameen kai fah?"
"Don't worry bana jin yunwa."
"Are you sure? You can have my plate."
"No Zainab ci ki kwanta ina zuwa."
Yana kaiwa nan ya fice, binsa tayi da kallo seda ya baro d'akin sannan ta shiga cin kajin a hankali don koran yunwa through out yau bata sa komi a bakinta ba banda malt da Lubiee ta bata.
Why isn't he calling me his princess again? Ta tambayi kanta. Ya dena sona ne yanzu? Oh na cuci kaina. Tayi tunanin haka a ranta. Bayan ta k'oshi ta nufi bayi inda ta watsa ruwa sannan ta fito tasa night gown nata ta sake feffeshewa da tuarare, har anan Al'ameen be sake lek'owa ba. Ji take as if ta fita taje ta duba sa ko lafiya, har ta kai bakin k'ofa sekuma ta fasa ta dawo ciki, ganin thats not the right thing to do kawai ta haye gado abinta ta kwanta, tun tana jiran shigowarsa har bacci 6arawo ya saceta be dawo ba.
Ba Al'ameen ya tashi dawowa d'akin ba se pass 12 inda ya tarar da Zeezee se baccinta take tasha. Sanye yake da knee length wando me pattern na soldiers da kuma farin T shirt. Tsaye yayi a kanta yana k'are wa innocent face nata data aza hannunta d'aya akai tana bacci. Tsugunawa yayi sannan a hankali ya sauk'e hannun nata aiko karap ta cafke hannun sa cikin baccin tare da aza kanta k'ark'ashi just like a pillow. "Oh God no!" ya furta yana tunanin ya zeyi ya k'wato hannunsa, sanin idan yayi da k'arfi tana iya tashi yasa ya shiga jan hannun nasa a hankali. Sede seya kusan gama ja se Zeezee ta sake miyarwa, da k'yar ya samu ya zare abinsa sannan ya gyara mata kwanciyarta ya rufeta da bargo ya fice tare da kashe mata wuta. D'ayan d'akinsa daya saba kwanciya aciki ya koma ya kwanta yau ma inda da tunanin Zeezee bacci yayi awon gaba dashi.
Da Asuban fari Zeezee ta farka don yin sallah. Gefenta ta soma shafawa inda taji wayan, toh ko de har ya fita masallaci ne? ta tambayi kanta. Wutan d'akin ta kunna inda ta tabbata cewa Al'ameen ba a d'akin ya kwana ba saboda ba ko alaman wrinkle a d'ayan side d'in. Hakan ba k'aramin breaking mata heart yayi ba, she thought yanzu they'll be back as how they were before. She miss him so much tayi wasa sa damarta, Al'ameen baya sonta yanzu.
Al'ameen kuwa bayan ya dawo from Masjid ya wuce d'akin Zeezee don tada ita yin Sallah inda ya tarar da ita har ta tashi ma ta idar da sallan, tana zaune kan sallaya tana azkhar. "Assalamu Alaikum" ya fad'a yana tsaye daga bakin k'ofan.
"Wa'alaikumus salam" ta juya tare da gaishesa "good morning Ya Al'ameen."
"Morning Zainab, har kin tashi?"
"Eh."
"Dama nazo tada ke Sallah ne."
"Oh ayyah thank you."
"You're welcome, ya gajiyan jiya?"
"Alhamdulillah, you?"
"Also, ki huta kinji? Get some sleep."
"You too." With a nod ya juya, har ya bud'e k'ofan ze fita Zeezee ta kirasa, "Ya Al'ameen?" hakan yasa ya tsaya tare da juyowa. "Na'am wani abu ne?" So take ta tambayesa dalilin daya hanasa kwana jiya a d'akinta amman kuma jin nauyinsa take.
"Zainab?"
"Na'am" ta amsa kanta a k'asa.
"Tell me meneh?"
"Bbb... babu, I just want to thank you, nagode."
"For?"
"For everything."
"You're welcome get some sleep." Yana kaiwa nan ya fice. Kanta ta jingina jikin gadon tana me sake tsanar kanta, da alama Ya Al'ameen baya sona yanzu, "ya manta dani, daga gani ma ya dawo dani ne saboda yana tausaya min bawai don yana sona ba, oh! Na cucu kaina a rayuwa, daman bature yace opportunity comes once in a life time, nayi wasa da daman dana samu a baya, taya zan sa Ya Al'ameen ya fara sona again?" Da k'yar ta kammala azkhar nata ta kom ta kwanta****
Tun wajajen 8am Al'ameen ya tashi yasa Saje ya siyo mishi breakfast yaci suma suka ci nasu sannan suka shiga training. Ba Zeezee ce ta tashi ba se pass 11 tsan-tsan gajiya. Bathroom ta fad'a tayi wanka tsaf abinta sannan ta fito tasa d'aya daga cikin sabbin d'inkunanta, ta tsara light makeup sannan ta fice parlour. Jin ba hayaniya a waje yasa ta koma baya don duban Al'ameen. Kasa kunnenta tayi a bakin k'ofan d'akinsa inda ta jiyo muryarsa yana kan waya. Dad'i sosai taji jin yana gida, a 360 ta d'au hanyan kitchen inda ta tarar da farar leda kan dining table. Bud'ewan da tayi taga chips ne da egg sauce, wani haushin kanta ta ji, duk laifin ta ne da bata saba masa da siyan abinci ba da kowani wayewan gari sede ya jira tayi musu abin karin kumallo. Duk da hakan bata hak'ura ba ta wuce kitchen tayi boiling doya sannan ta tsara had'ad'd'en kidney sauce. Bayan data sauk'e ta zuba a had'ad'd'un food warmers nata sannan ta jera a dining. Tunanin ya zata je ta fito dashi daga d'akinsa take amman sam ta kasa battada caurage. Ana cikin haka ne Al'ameen ya fito tsaf cikin sky blue kaftan da hula shirin ya mugun amsar sa ya kuma sake bayyano da how fit he is, tun daga bakin k'ofa Zeezee ke kallonsa ta kasa d'auke idanunta daga kansa, wai shin ko wani irin kaya ne ke kar6ansa shi? She can't tell how fascinating he is looking. Takowa ya soma izuwa parlour'n cike da k'asaita magestically. Ganin kallon bana k'arewa bane yayi gyaran murya which shook Zeezee back to reality. "Good morning Ya Al'ameen" ta fad'a tana kallon k'asa.
"Morning Zainab har kin tashi?"
"Eh."
"Good ga breakfast naki a kan table, kin gani?"
"Eh na gani, but na girka mana breakfast, you should have woke me up in mana ai a maimakon siyowan da kasa akayi maka. Its my obligation to cook for you."
"I know Zainab, karki damu you were sleeping shiyasa banso in tadake ba despite gajiyan da kika sha jiya."
"It stil doesn't matter, come over and eat."
"No thanks I'm full kici ke kinji?" Mood nata yaga gabad'aya ya sauya.
"Ya Al'ameen even if its a bite please kazo kaci."
"Zainab chill kinji? Zuwa anjima zanci but right now am full nayi breakfast d'azu."
"Ban iya girki ba shiyasa baka son kaci ko? I'll keep on practicing sena zamo best chef just for you."
"You are a best chef already Zainab." Kai zallah ta gyad'a mishi amman sam bata ji dad'i dayace mata he is full ba baze ciba. Ita kanta ta gane yanzu Al'ameen baya sonta kaman da. Bataso nuna mishi yadda ranta ya 6aci ba ta danne zuciyarta tace, "kayi kyau Ya Al'ameen, kaftan d'in ya kar6eka sosai."
Murmusawa yayi sanda dimples nasa suka lotsa ciki gabad'aya "thank you kema kinyi kyau."
"Thanks also, zaka fita ne?"
"Eh zan duba wani friend d'ina, I won't take long." Nan ma bata ji dad'i ba tasan avoiding nata kawai Al'ameen yake if not shi ba ma'abocin fita yawo bane.
"Toh Allah ya kare, be back safely."
"I'll in shaa Allah thank you, kina buk'atan wani abu?" A zuciyarta tace yes, you I need you. Amman a fili ta kad'a kai "babu."
"Okay then" Tana kallonsa har ya fice, hawaye kawai ta soma yi a hankali, me zata yiwa Al'ameen ya koma sonta as before? Da k'yar ta iya ta karya inda ta sake cooking musu spaghetti da yasha kayan had'i as lunch, wannan karan bawa ita kad'ai da Al'ameen bane harda su Saje ma da masu gadi duk tayi girkin dasu. Bayan ta kai musu nasu ta dawo ciki tayi sallah ta sake d'aukan wani wanka sannan ta zauna a parlour tana jiran dawowan Al'ameen. Kaman wasa Al'ameen har after 3 be dawo ba, bata san lokacinda bacci ya saceta kwance a gun ba.
Har La'asr yayi bata ji ba bale ta tashi tayi Sallah, da La'asr d'in Al'ameen ya shigo inda ya tarar da ita kwance a parlour, kayanta na yanzu har yafi nada amsanta se kawai ya tuna back then da idan har Zeezee tayi kwalya ko tasa kaya me kyau a gida is either zata fita unguwa kokuwa zatayi hoto ta tura wa Adeel ne amman kam on normal basis bata kwalya don mishi. Murmusawa kad'an yayi sannan ya wuce dining inda ya bud'e food warmer'n, spaghetti ya tarar had'ad'd'e ciki kafin yace ze rufe Zeezee ta tashi daga baccin tana kallonsa. "Har kin tashi?" Ya tambayeta a bit disgraced lokacin da idanunsu ya had'u beso ba ta kamasa yana bud'e flask. Kai tamai nodding, "yaushe ka dawo? Sannu da zuwa."
"Just now thank you."
"Oh sannu da zuwa, zaka ci abinci neh?"
"Nah am full I had lunch a gidan friend d'ina." Sad expression ne ya bayyana karara a fuskarta tasan sarai da gan-gan Ya Al'ameen yake k'in cin abincinta, halan gani yake kar ya saba ci tazo tace ta dena yimai girki,well he is wrong. Danne zuciyarta tayi da k'yar tace, "oh I'm sorry."
"Kinyi Sallah?" Ya canza topic d'in. Kai zallah ta kad'a mai.
"Tashi toh kiyi, and also Taheer yace min kin sa musu abinci, don't stress yourself out next time ina basu kud'i suna sayan kinji? No need."
"Ya Al'ameen you don't have to, am your wife hak'k'i na ne in ciyar dasu and you as well."
"But-"
"Please let me do this." Ta katse sa a hankali.
"As you wish Zainab tashi kiyi sallah." Ba musu ta miqe ta nufi d'akinta.
Da daddaren daya ce mata zeci abincin ma ba ci yazo yayi ba, ba kad'an abin ke daminta ba ta rasa ina zata sa kanta. All she know is that she'll never give up on him because she loves him. Bayan ta gama shirin kwanciyarta ta fito ta tarar da shi a parlour, "kin shiga zaki kwanta kenan?" Ya tambayeta yana sanye da vest da wandon kaftan na d'azu.
"Eh" seka shigo take son ce masa amman tasan ba shigowan zeyi ba. "Seda safe." Ta k'ara akai.
"Sleep safe and sound." Kai ta gyad'a mai ta koma d'aki. Tana kwance bisa kan gado kawai ta soma kuka, so take ta kira Lubiee ta sanar da ita but she wants to give Al'ameen some time ai yama yi k'ok'ari daya dawo da ita despite kalan rashin kyautatawa da rashin kunyan data mishi da a baya, yayi sacrificing virgin duk a kanta saboda haka zata basa some space. Da tunaninsa yau ma tayi bacci.
*MIEMIEBEE. Team #YGC!🎀*
Beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄👄
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
1 comment:
Allah sarki zeezee, just be patient and give our yaya Al'ameen some time. After all, he loves u. Tnx sis
Post a Comment