BY MIEMIEBEE
PAGE 08
*December, 2016*
_9:46PM_
Kowa na a zaune a babban parlour yana harkan gabansa Mama ta shigo bata nufi ko ina ba se kan Baba dake riqe da Zeezee yana kallon NEWS. Gabansa ta sha “ya haka?” Yayi saurin tambaya.
“Kud’in wayata zaka bani.”
“In nak’i fa?”
“Nikuma inja Allah ya isa.”
“Toh Hafsah kija kinji? Kija please.”
“Ni gaskiya ka bani kud’in waya na ai ‘yarka ce ta b’ata.” Maido da kallon sa yayi kan Zeezee yace;
“Zeezee abawa Mama kudin waya ta sai sabo?”
“O’o” tace tare da make kafad’a “ba ta bawa Sultan jush d’ina ba ta kuma min duka.”
“Toh kinji?” ya d’ago kai yana kallon Mama “tace kar a baki kud’in, maganan K’anwata kuma ya zauna baza’a baida kud’in ba.”
“Allah ko? Wallahi Alhj kar ka bani kud’in wayana kaga aiki da cikawa gobe, ai nasan shagunan ka da suke Wunti zuwa zan in d’ibi duk abinda yamin.”
“Allah baki sa’a toh ni matsa min kallon NEWS nake” yace da ita. Rai a dak’ule ta koma gefe ta zauna ta hau taya Yasmeen tsefe kitson ta kasancewar jibi Monday zasu bud’e school.
Ana cikin haka k’ishin ruwa ya addabi Mama ganin Zeezee ce k’arama cikinsu kuma ita ke zaune ba abinda take tace, “keh Zeezee wuce ki d’auko min ruwa.”
“O’o” tace gatsau cike da rashin kunya.
“In aike ki kice min o’o? Tashi nace!”
“O’o bayin jeba.” Kallon Baba Mama tayi taga ko a jikinsa ma Zeezee na mata rashin kunya, “dole kayi pretending kaman baka ji ai dake bakada gaskiya” tace dashi. Se anan ya juyo ya kalleta sannan yace, “ai da gaskiyar ta ko wani aike kice se Zeezee, kika tashi kuma ba wanda kike duka kaman ta ba inda zataje, Yasmeen dake gabanki ba mutum ce ba? Ki aiketa ko ki tashi ki d’auko da kanki cigaba da game naki Zeezee na.” Kai kawai Mama ta girgiza “ka cigaba wallahi, Yasmeen Mama na jeki d’auko min ruwa.”
****
Washegari su Mariam sukayi wanka tsaf harda Zeezee suka shirya wai zasu gidan kitso for the first time Zeezee za’a gidan kitso. Baba da kansa yayi dropping nasu by tunda harda Zeezeen sa yau. Kitso me kyau sukayi kasancewar za’a koma school. Banda ma kiston Zeezee dayasha beads da ribbons kamar a sace kan a gudu. Da Azahar aka gama musu Baba yaje ya d’aukosu nan ma. Dawowan su gida suka tarar da kayaki sabi zube kan tabarma ta bakin k’ofa wajen duk suka nufa suka shiga duddubawa. Kayaki suka gani duk sizes nasu masu kyan gaske, suna cikin duddubawa Mama ta fito daga ciki tare da masu sannu da zuwa. “Iyye kitson autan nawa yayi kyau” ta shafa kan Zeezee.
“Batai kuka ba Mariam?”
“Batayi ba kasancewar game tayi ta bugawa a ipad nata.” ta amsata a takaice.
“Toh ko kefa? Kin ganki kuwa?” best smiles nata ta sakar wa Mama sannan tace,
“Mama kayan waye wannan?” Zeezee a rayuwa akwai son sabon kaya.
“Naku ne” nan ta rarraba masu se godiya suke shide Baba bece ko k’ala ba. Bayan da yaran suka wuce d’akinsu Mama ta matso kusa da shi tace, “kayi shiru tun d’azu baka ga kayakin bane ko basu ma kyau bane?”
“Tsakanin ki da yaranki meya kaini sa baki.”
“Hmm haka ne? Seka kawo kud’i dan duk a bashi na d’auka.”
“Bashi?!” Yayi exclaiming yana nodding head.
“Eh bashi Alhj da aiki nake da zan iya biyan wannan uban kayaki.”
“Shin wa kika tambaya ma kafin kikayi wannan karambani?”
“Karambani? Yanzu Alhj saiwa wa yaran nan kaya shine karambani?”
“Eh mana tunda bakida kud’in biya, nima banda kud’i seki jira in kika kwashe adashenki ki biya.” Dai-dai ze miqe kenan Mama tasa hannu ta zaunar dashi. “Wallahi Alhj baka isa ba sekace ni kad’ai na haifi yaran da zaka wani ce ni zan biya duka?”
“Da ni nace ki siya musu? Kaya de yara sunada tunda ba tsirara suke yawo ba sabida haka sake min hannu.” Sake dandame hannun nasa tayi, “ba kai kace ba amman ai ya kamata ne shiyasa kai bakasan rufin asirin ka bane ana ganin yaran ka da kayaki masu kyau ba?”
“Aww! duk wanda suke dashi be ishesu ba kenan? Sake ni nikam ko ki biya koki miyar wa Maman Fadeel kayakin ta.”
“Ka d’au wai barin iya miyarwan bane? Wallahi miyarwa zan.”
“Yauwa sakeni toh.” Fuska ta maraice sarai Baba yasan barata iya miyarwan ba da biyu ya fad’a hakan shima “Baban Zeezee dan Allah karka min haka, baka ma ji kud’in bafa kake wannan magana.”
“Nawa ne?”
“Dukan su ukun fa 35k ne kacal.”
“35k?” Ya zaro ido waje. “Shine kacal? Gaskia banida wannan kud’in yanzu sede in zamu biya rabi da rabi in biya 20k kibiya 15k.”
“In nayi hakan kuma da me zanyi ciko na sai sabon waya tunda kak’i bani kud’in duka.”
“In kinsan zance zakiyi ta tadawa toh kije kiyi duk abinda ya miki 20k d’inma na fasa baiwa.”
“Alhj mana dan Allah karka min haka.”
“Tsaya ma tukun d’an set uku-ukun ne har 35k nifa na lura kayan matan nan tsada ne garesu.”
“Alhj ai kasan kayan yara da tsada, Zeezee nan kad’ai taci 17K.” Hannu yasa a aljihu ya zaro kud’ad’d’e masu dimbin yawa sannan ya irga dubu sha bakwai (17) ya miqa wa Mama. “Ga na Zeezee nan, na sauran ki biya ko kuma ki jira in k’arshen wata yayi an bibbiya ni bashuka na se in gama biya.” Cike da mamaki Mama ta d’ago kai tana kallon Baba sannan tace;
“Lallai ma Alhj! wato in na Zeezee ne ka iya biya amman na sauran dake ba ‘ya‘yan ka bane baraka biya ba.”
“Wai ce miki akai barin biya ba? Nace maki banida kud’i” da hanzari ya miqe tare da adjusting hulan shi without giving ber a chance to speak yace, “zan wuce kasuwa.” Zeezee ya hau kira.
“Eh Baba!” Ta amsa daga ciki tana k’ok’arin fitowa. Daga k’asa-k’asa Mama tace, “wai ace yarinya in an kirata sede tace eh bata iya fad’in na’am ba, Allah ya kyauta deh.”
“Ina ruwan ki? Mschw! Zeezee na zan fita kasuwa kina son in saya miki wani abu?”
“Eh Baba ice cream da dambun nama.”
“Toh K’anwata sena dawo koh?”
Ba-bye ta mishi tare da komawa ciki.
“Ni matar gidan ba’a tambayeni ko me nakeso ba saboda banice a gabanka ba aiko?”
“Oh! Hafsah! Yanzu kishin Zeezee kike?”
“Ban sani ba nide a sai min gashi na kwana biyu ban motsa baki ba.”
“Seki kawo kud’i don ni banida.”
“Kaje tunda se na kawo kud’i na fasa cin” ba tare da yace k’ala ba ya fice.
_2:27PM_
Dai-dai nan Baba ya dawo gida bayan yayi parking ya kira Ibraheem yazo ya ciro wani babban kwalin da Allah kad’ai yasan meh a ciki faga motar. A varenda ya sauk’e se anan sunan dake jikin kwalin ya fito. “Washing machine?!” Ibraheem yayi excaliming da d’an k’arfi, jin haka Mama da yaranta suka leqo suma. Zeezee na fitowa ta d’ale jikin Baba.
“Baba ina aish clim d’ina?”
“Gashi anan K’anwata, Yasmeen ungo kai fridge na d’akina ki sa mata.” Baba yayi maganan tare da cire ma Zeezee ice cream d’aya daga cikin ledar. A sanyaye Yasmeen ta amsa sannan tace, “Baba nima zan sha”
“Wai ke wace irin kwad’ayayya ce?”
“Nima zan sha Baba” cewar Mariam.
“Kwad’ayayyun banza kawai! ku d’au d’ai-d’ai Yasmeen ki kai sauran d’aki.”
“Wannan kuma fah?” Cewar Mama tana me bin washing machine d’in da kallo.
“Bakida ido ne? Washing machine ne.”
“Ina da shi kuma nagani tambayata itace, washing machine na waye neighbours suka kawo a ajiye masu ko kuwah?”
“What do you mean? Ban kai in sai washing machine ba kenan ko meh?”
“Ni ba abinda nake nufi ba kenan naga d’azu ka gama cewa bakada kud’i.”
“Toh ba ruwanki bane, Zeezee K’anwata kinga wannan?” yayi pointing machine d’in da yatsa. Kai ta gyad’a as an answer. “Good, naki ne kinji? Ke kad’ai za ana yi maki wanki ciki.” Zeezee kanta seda tasha mamaki talkless of her siblings.
“Nawa Baba? Duka wannan?”
“Sosai ma K’anwata naki ne.”
“Yeyy!” Ta rungume shi tare da sauk’a daga hannunsa tana shafa jikin kwalin. Har a yanzu cikin Mama da yaranta ba wanda ya iya fad’in ko qala. Mama ta nisanta tace, “amman wallahi abin naka ya soma yin yawa Alhj, washing machine fa? Kuma kace na Zeezee kad’ai sauran ba yara bane? That aside d’azu anan nace ka bada kud’in kayan yaran nan kak’i kace ba kada kud’i, ka sai min gashi nan ma duk bakada kud’i amman ka iya d’auko washing machine da ke...” tayi pausing tana neman price tag na machine d’in. Kafin Baba yasa hannu ya tare ta karance “75k ka siya kuma wai ma Zeezee kad’ai.” Sosai Baba yaji a jikinsa ba dad’i amman ya dake yace, “toh se meh? Da tsofi dasu ne zan siya masu washing machine? Sabi’u na masu wanki me kyau shi kuma ze cigaba da musu amman de kam wannan na wanke kayan Zeezee ne kawai.”
“Ka kyauta toh Ibraheem zo muje ka siyo mana gashi.”
“Tsaya Ibraheem” Baba ya dakatar dashi da wuri, hannu ya sa a aljihu ya irga 3k ya miqa mai “gashi saya muku shikenan?”
“Nifa bana buk’atan kud’in ka” cewar Mama “miyar masa da kud’insa Ibraheem.”
“In ke bakiso yaran suna so wuce kaje ka siya muku sauran kuma kayita yawo a gari.” A sanyaye Ibraheem ya wuce.
*** _9:23PM_
Mik’e Mama ke kan gado da shirin baccinta a yayinda Baba ke other bedside d’in shida Zeezeen sa suna game, daga bisani Baba yace “K’anwata mu kwanta koh? Kinga akwai school gobe.”
“Baba gobe ne zanje school d’in?”
“Eh K’anwata.” Shiru tayi na ‘yan seconds sannan tace, “toh Baba banida uniform.”
”Karki damu zuwa next week zasu baki yanzu mu kwanta tashi in saki cikin gadon ki.”
“O’o ni yau anan zan kwana.” Kafin Baba ya amsa Mama tace, “kamar ya anan? Gadon kin kuma fah? Tashi da Allah.”
“Ke wai Hafsah meh matsalaraki ne? Anan d’in zata kwana.”
“Haba Alhj yarinyan nan ai tayi girman kwana tsakiyan mu.”
“Kanki akeji” ya miyar mata, d’aga Zeezee yayi tare da kwantar da ita tsakiyansu. Mama de bata ce komai ba, wuta Baba ya kashe yabar dim light zalla sede sam Zeezee takasa bacci ta juya nan ta juya chan da abin ya isheta ta miqe zaune “Baba!” ta kirasa yadda ta saba always.
“Na’am” ya amsa cikin bacci.
“Baba ni acile min beads d’in suna hanani basshi.” Nan Mama da batayi bacci ba tace, “kamar ya acire Zeezee? Ko kin manta yau aka miki kitson kuma kinada school gobe?”
“Ni acile min.” tayi maganan almost crying.
“Baza a ciren ba mschw!” Duk nan Baba besan me suke ba sautin kukan Zeezee yayi shooking nasa awake.
“Ya haka? Meke faruwa Hafsah?”
“Seka tambayi K’anwar taka ai.” Tayi maganan tare da juya masu baya.
“Meya faru Zeezee?”
“Baba ni acile min beads d’in suna hana ni basshi.”
“Acire kuma K’anwata? Kinsan gobe fa zakije school yara dayawa za’ayi musu kitso da beads.”
“Ni bana sho.”
“Toh an gama K’anwata, Hafsah!” Yasa hannu ya jijjiqata. Shiru Mama tai bata amsa ba. “Hafsah!!” Zeezee ta kira Mama da unanta da k’arfi.
“Lallai kam!” Mama tace tare da juyowa. “Rashin kunyar kin har ya kaiga kirana da suna na?”
“Toh ba kiran ki nake tun d’azu kika manna min hauka ba, karki tak’ura wa K’anwata please.” Baba ya kare Zeezee. Ba tare da Mama ta sake cewa abu ba ta koma ta kwanta.
“Hafsah! Magana fa nake miki.”
“Dan Allah kubarni inyi bacci ko na fice guest room.”
“Tashi ki cire mata beads d’in in kin gama yaso seki koma baccin.” Zama Mama tayi ba tare da tasan tayi hakan ba duk dan yadda kalamun Baba suka bata mamaki wato shima ya goyi bayan wannan rashin hankali. Ganin bata soma cirewa Zeezee beads d’inba se kallonsa take yace, “kefa muke jira ko a kunna maku wuta neh?”
Mik’ewa yayi ya kunna wutan d’akin sannan ya dawo ya zauna, ganin har yanzu Mama bata soma cirewa Zeezee beads d’in ba ita kuma bata bar fitinan acire ba, Baba ya d’aga ta ya azata kan cinyan Mama “oya ciccire mata su duka.” Kai kawai Mama ta girgiza ta hau cire beads d’in, na gaban tace Zeezee tayi hak’uri abar mata su amman ina sam Zeezee tace se an cire duka hakan ko akayi.
*** Washegari.
_Monday, 6:00AM_
On the dot Mariam tayi knocking bisa k’ofan d’akinsu Baba, yin haka sau biyu Baba yace, “come in.” A hankali ta bud’e tare da shiga, sanye take da wandon uniform nasu seda vest a jikinta bayan ta gaishe shi ya amsa tace, “nazo d’aukan Zeezee inyi mata wanka.”
“K’arfe nawa ne yanzun? 6 yayi neh?”
Eh Baba.”
“Toh ina zuwa” dawo da kallonsa yayi kan Zeezee tare d tapping nata. “K’anwata! K’anwata tashi kinji? Today is your first day at school.” Zeezeen da tayi nisa a bacci ko jinsa ba tayi ba, sake jijjigata yayi “tashi kinji yau zaki fara zuwa school tashi amiki wanka.” Cikin baccin tace, “yau ne Monday?”
“Eh K’anwata yau ne Monday tashi toh.”
“O’o ni abanni inyi basshi se anjima inje.” Haka da k’yar Baba ya iya ya tada Zeezee, Mariam na ganin kanta ba beads ta dafe k’irji, “Zeezee ina beads naki?” Kafin Baba ya amsa Mama ta juyo tana fuskantan su tare da fad’in “ba ga tanan ba fitinanniyar yarinya, haka ta sani gaba jiya seda na ciccire mata su.”
“Kuma se kika biye mata Mama?”
“Ke ina ruwanki? Mschw! d’auke ta kiyi mata wanka da Allah” Baba yasa baki.
“O’o ni ba Adda Mayyam bane zatayi min wanka.”
“Se waye kuma Zeezee?”
“Nishe Ya Ibyaheem.”
“Shi kikeso?”
“Eh” ta gyad’a kai.
“Toh angama, Mariam fice kije ki kiramin Ibraheem kice yazo yayi wa K’anwata wanka.”
“Toh” tace tare da ficewa.***
*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com
3 comments:
tnx
You're welcome
Post a Comment