Wednesday, 7 December 2016
‘YAR GATA CE!
BY MIEMIEBEE
PAGE 07
*December, 2016*
Lunch Mama da Mariam suka shiga had’awa nan da nan suka gama aka d’iba ma kowa nasa da nama d’ai-d’ai akai. Ihu Zeezee ta k’urma “ya haka Zeezee wani abu ne?” Mama tayi saurin tambayarta.
“Ni banashon nama d’aya, banasho!”
“Jimin ‘ya da guda nawa kikeso? Bakiga plates na yayyun naki bane?”
“Baba! Baba!” Tashiga k’wala mai kira a gigice ya fito “K’anwata meya faru haka?”
“Mama ne!” Tasa kukan da anayin sane amman ba hawaye.
“Wai Hafsah shin yaushe ne zaki koyi son yarinyan nan? Kullum ace bakida aikin da yafi sata kuka?”
“Seka gayamin mena mata ai, daga sa mata abinci seta hau min kukan banza Mariam mik’on plate d’ina in d’iba in bar musu kitchen d’in.”
“Meya faru K’anwata?”
“Nama d’aya Mama ta shamin.”
“D’aya kacal? Adalilin meh?” Wabje serving spoon d’in yayi ya kwashi ragowar naman tas ya zuba wa Zeezee a plate nata ido kawai Mama ke binsa da “ni kuma me zan samu inci?”
“Inba keda abinki bama me zakiyi da cholesterol a jiki? Jekici abincin ki K’anwata.” Kafin su Ibraheem su soma cin namansu Zeezee har ta cinye 15 meats dake kan plate natan ko tab’a tuwon batai ba, ahakan tana neman k’ari wajen Ibraheem ta nufa ta zauna “Ya Ibyaheem nama.”
“Naman uwaki, ki gama cinye na miyan duka ki wani ce in baki nawa, bazan bada ba.” Su Mariam najin haka suka b’oye nasu cikin tuwonsu ihu ta k’urma daga ciki Baba yace, “wa kuma ya tab’ata yanzu?”
“Ya Ibyaheem ne yaban nama wai o’o.”
“Kai Ibraheem kaci girma ka bata mana.”
“Baba ni shikenan kullum sede ban d’ibi abinci ba seta riga cinye min nama.”
“Ka bata nace karka bari in fito.” Dogon tsuka yaja sannan ya d’au naman ya cusa mata a baki cike da mugunta “seki cinyen ai Mumu kawai.”
“Kaima Mumu” ta murgud’a mai baki.
Fitan su Baba sallan Azahar Zeezee ta fito da had’ad’d’un throw and doghnurt shaped pillows na Mama wanda take jerasu kan gadon d’akinta waje ta baza kan varenda tana wasa dasu. Mama na idar da Sallah tafito ta hau ta da masifa, “maza tashi ki mayar min su d’aki, iskancin naki har ya kaiga fito min da pillows waje mayar dasu nace!”
“O’o balin mayal inba.”
“Bazaki mayar ba?”
“Eh ni ki banni” mari Mama ta sakar mata a baya nan tasa ihu “Allah ya ishana!” ana cikin haka su Baba suka dawo “ya haka tun daga waje nake jin hayaniya.”
“Sekazo kayi mata magana, kace ta miyar min da pillows na d’aki tunda bata jin maganan kowa se naka.”
“Yanzu Hafsah meye aciki dan yarinya tafito da pillows tana wasa dasu.”
“Alhj kalli a k’asa fa take gurzasu.”
“Yi wasan ki k’anwata kinji?” Yayi maganan yana shiga ciki binsa Mama tayi tana k’orafi “wallahi ka cigaba da goye wa k’arya gindi ace yarinya duk abinda tayi dai-dai ne a idonka wataran da kanka zakayi kuka wallahi mu zuba mu gani.”
“Kanki akeji” yace da ita lokacinda ya mik’e kan gado “muddin ina gidan nan kam keda yaranki bazaku tak’ura wa K’anwata ba.”
Futu-futu Zeezee tayi da pillows na Mama sannan ta barsu gun ta zarce tsakar gida ta hau wasan banza da ganganci, koda Mama tafito ta ganta tanayi bata ce mata komi ba saboda there is no point doing so, koda tace mata ta bari ba barin zatayi ba. Kan turmi ta d’alle tana wasa daga bisani kawai ya juye da ita ta fad’i nak! A k’asa se ihu malam!
“Ai ga erinta nan kita wasan banza sekace na miji kad’an kika gani ai.”
“Eh kad’an tagani muguwa kawai ‘yarki ta fad’i amman ko kiyi yunk’urin d’agata” Baba wanda sanadiyan ihun Zeezee yafito dashi yayi maganar yana d’ago crying Zeezee daga k’asa. “Sannu koh? Sannu K’anwata” d’an hannu da gwiwa ta gurje amman se kuka take wane kanta ne ya fashem
“Sosai ne taji ciwon?”
“Ban sani ba kina zaune achan kaman kayan wanki shiga ciki kid’au min first aid sannu ko K’anwata yi shiru.”
A sannu a sannu ya samu ya shafa mata dettol wajen sede har yanzu bata bar kukan ba ita zafi “toh K’anwata me kikeso ayi miki?”
“A kila Ya Ibyaheem ya hula min.”
“Shi kikeso?”
“Eh da Ya Omal.”
“Ibraheem! Ibraheem!”
“Na’am Baba.”
“Kazo kai da Omar” bayan isowan su sukayi tsaye gun not minding halin da Zeezee ke ciki, “bakuga k’anwarku taji ciwo bane? Can’t you tell her sorry? Banason sakarci fah.”
“Sannu” sukayi murmuring in unison.
“Oya Ibraheem zo ka mata blowing air a wajen yana mata zafi.”
“Ni kuma Baba?” Yayi maganan yana pointing kansa.
“A’a ni dan k’aniyanka zo ka mata blowing air nace” haka yana kumbure-kumbure ya iso ya tsuguna gaban Zeezee k’afan nata ta mik’ar ta aza kan cinyansa take ya tunkud’e k’afar “meh haka zaki wani samin k’afanki me dottin nan kan kaya, bakiga farin kayane a jikina ba.”
“Bata gani ba sa k’afan naki Zeezee” nan ta miyar “ayyi Baba kayan fa zeyi dotti.”
“Ungo naka nan kai da farin kayan naka maza! hura mata iskan kaima Omar turn naka na zuwa in wan naka ya gaji.”
By 3:00PM as always yaran suka hau shirin islamiyya Mama dake neman hutu in any way possible ta kalli Zeezee dake mak’ale jikin Baba tana game nata hankali kwance tace, “Zeezee shin ke se yaushe ne zaki fara zuwa islamiyya wai kam? Mates naki duk sun soma zuwa” Kai Zeezee ta d’ago ta galla wa Mama harara sannan tace, “ban shani ba.”
“Ya miki kyau, ina Alhj kana ganin irin abinda nake yi maka magana akai ba? Yanzu ina zan iya shiga cikin jama’a da maras kunyan yarinya haka.”
“Ke shikenan bakida aikin yi a gidan nan se yiwa Zeezee baki?” Baba yayi maganar a fusace. “Gaskiya banaso, baki tashi zagi a gidan nan se akan Zeezee, islamiyya ne barata shiga ba seta k’ara girma haka kawai barin kai ‘yata islamiyya a jibgeta a banza ba.” Hannu Mama ta tafe tare da sakin salati.
“Su Yasmeen da suke zuwa ai ba haifan su akayi ba.”
“Yasmeen daban Zeezee daban.”
“Kuma bokon da zaka satan shi ai ba’a duka koh?”
“A LYS? Kin tab’ajin inda akace miki an daki d’alibi a LYS? Ai rashin dukansu is the number one reason da yasa zan sa Zeezee school d’in.”
“Lallai kanada aiki toh ko su basu dake taba ni nan zan dake ta sede bata sake zagina ko min rashin kunya ba.” Ba tare da ta jira me Baba ze sake fad’i ba ta fice masu daga parlourn.
“Shareta kinji K’anwata? Karki kula Mama and anytime ta tab’a ki tell me kinji? Zan rama maki da kaina.”
“Yeyy! Baba ni duk nan gidan nafi shonka.”
“Ai nima na fi sonki Zeezee ba a gidan nan kad’ai ba a duniya gabad’aya.” Ya shafa dogon sumanta.
***
Da fitan yaran bada jimawa ba Baba ya yi alwala ya fice Masjid shima. Bayan Mama ta idar da Sallah tajiyo sallama daga waje, ba tare da b’ata lokaci ba ta fita, Sultan yaron Aunty Sis ta tarar da ‘yar basket a hannunsa bayan ya gaishe da Mama ya mik’a mata basket d’in tare da fad’in “Mama nane tace in kawo miki.”
“Allah sarki Aunty Zainab, toh Sultan d’an albarka kace mata na gode sosai kaji?” tayi maganan tana bud’e flask d’in. Miyan ganye had’ad’d’e taga ciki (her favorite.) “Maman Zeezee zan tafi ina Zeezee?” Kaman ance Zeezee leqo tafito daga d’akin tana kallonsa wane yau ta soma sasa a ido. “Baraka jira kuyi wasa da Zeezee ba zaka tafi Sultan?”
“Zeezee!” yace da ita yana mata murmushi.
“Kazo gidan mu dan ka d’auke min ipad k-” bata idda maganar ba Mama ta bige bakinta “ce maki akayi yana d’auke-d’auke? Toh in baki sani ba shima Sultan nada ipad nasa d’an gatan Baban sane shima.”
“Allah ya isha” tace tana kuka.
“Ni kike jawa Allah ya isa?” Mama ta sake bige mata baki, volume na kukan nata ta k’ara “kuma wallahi shena fad’awa Baba” data ga Mama bata kallonta ta d’aga hannu ta zageta se anan taji ta huce.
“Zeezee bar kuka kinji?” Cewar Sultan warmly ko ta kansa batai ba ta nemi gu ta zauna tana ciccire ribbons da suke kanta tasan sarai Mama ta washi ta ganta tana yin hakan.
Kai kawai Mama ta kad’a da taga abinda Zeezee ke tasan sarai on purpose takeyi.
“Maman Zeezee zan tafi tunda yau Zeezee tak’i kula ni.”
“Share ta Baba na tsaya in d’an d’auko maka koda juice ne.” Nan tayi ciki, Zeezee na jin an ambaci juice hankalin ta ya tashi, sahun Mama tabi taga Mama na k’ok’arin bud’e mata sabon carton na juice nata. Wani irin shegen ihu tasa sannan tayi gudu ta cafko hannun Mama. “Ni wayyayi ki aje min jush d’ina ai nawa ne ba naki ba ki ajiye!” Ta rushe da kuka.
“Sake min hannu marowaciya kawai, da Uwarsa tazo ta baki dubu biyu kin iya karb’a ke kice baza a bashi juice ba? Wallahi kinyi k’arya sake min hannu!” Sake dandameta Zeezee tayi tana ihu kaman ana cire ranta, ko ta kanta Mama batai ba ta d’iba juice uku wa Sultan da sauran chocolates and snacks komi uku-uku sannan ta sa mai a leda. Uwar rowa tayi kuka har nishinta na wani sama-sama dan kanta tayi shiru ta fice varenda taje ta kwanta flat wajen tana birgima only if ace gun da k’ura da tayi putu-putu da kayan jikinta ko k’ala Mama bata ce mata ba ta juyo abincinta a plate ta samu waje ta zauna tana ci. Sarkin rowa ga kwad’ayi tuni kwad’ayinta ya shiga abincin, ba kunya bale tsoron Allah taje ta samu Mama “nima zanci.”
“Ba abinda zaki ci.”
“Wayyayi sena ci” ta miqa hannunta zata sa cikin plate d’in.
Bige hannun Mama tayi, “da hannu du dottin zaki sama min a plate? Bud’e bakin marowaciya kawai” haka suka yita drama har suka k'are abincin.
Bayan da suka gama cin abinci Zeezee ta nemi wayan Mama qirar Samsung galaxy S4 ta nufa chan ta side nasu Ibraheem inda ake ajiye manya manyan roba cike da ruwa ta jefa wayar ciki, se da ya kusan minti biyu sannan ta cire ta basa few seconds ta sake miyarwa tana murmushin jin dad’in abinda takeyi tace, “nan gaba jaki shake d’auka min jush kibawa Sul-” sunan da bata gama k’arisawa ba kenan due to lafiyayyen marin da Mama ta sakar mata a baya. Ihu ta saki Mama ta fisgota zuwa main tsakar gidan “bakida hankali ne iyye? Da wayonki da komai zaki d’au min waya ki jefa a ruwa?” Hannunta taja zuwa kitchen sannan ta zari tsintsiyan kwa-kwa guda biyu ta tattara kayan Zeezee sama ta shiga shwad’eta. Zeezeen da tunda tasan kanta ba’a tab’a mata duka ba se yau ta ringa kuka kaman ba gobe ana cikin haka Baba ya dawo gida. Tun daga bakin k’ofa yake jin kukan K’anwarsa a hanzarce ya k’ariso only to see the biggest suprise of his life.
“HAFSAHHH!!!” Ya kira sunanta da wani irin kakkausar murya amman hakan be hana Mama cigaba da aiwatar da abinda take ba, seda ta sake shwad’e Zeezee sau biyu again sannan ta barta alokacin har Baba ya iso inda suke yasa hannu ya d’aga Zeezeen da ko kukan arziki ma ta kasa yi don azaba. “Meh haka? Kashe ta kikeson yi komeh? Wani erin sakarci ne haka? Amman Hafsah da hankalin ki kuwa?” duk wannan tambayoyi jerosu yayi da numfashi d’ai. Hannu yasa ya fisge tsintsiyan dake hannun nata, har ayanzu Mama bata ce komai ba hannu yasa ya kwantar da crying Zeezee a jikinsa yana bubbuga bayanta.
“Kinsan baki fi k’arfin in d’au belt in zaneki ba kema koh?”
“Ka fad’i koma meh, kekuma kad’an kika gani ki sake d’aukar min waya kisa a ruwa kigani,” tayi maganan tana huci.
“La’ila!! Yanzu Hafsah akan waya kika daki yarinyan nan haka se kace zaki kaita lahira? Ina wayar?”
“Gashi nan” ta miqa mai. Abinda ya aikata ne ya mugun bata mamaki, to her suprise taga ya nufi wani daron dake cike da ruwa wajen wanke-wanke ya sake tsunduma wayar ciki baki Mama ta sake in disbelieve.
“Ansa a ruwan an kuma sawa, akan banzan wayan da be kai ya kawo ba zaki kashe min K’anwa? Nace ansa a ruwan maganan banza kawai!” ya watsa mata harara sannan ya wuce da Zeezee d’aki. Binsa tayi da kallo tace, “wallahi se ka sai sabo.”
*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment