Friday, 16 December 2016

‘YAR GATA CE!

BY MIEMIEBEE
PAGE 15
  *December, 2016*



      “Babu komai Uncle ni na tafi” taja jakarta kaman dagaske.
  “Kaman ya ba komai? Gashi ina gani kina kuka kice babu, Hajiya Mariamu na me kikayi wa K’anwar tamu take kuka?”
  “Wallahi Dear ban mata komi ba ni kaina bansan meke damunta ba.”
  “Ai dama haka zakice kin kama kin cinye min 5k kikace nazo tafiya zaki bani, baki ban ba dole kice ai baki san meke damu na ba ni zan tafi.”
   “Ni?!” Mariam ta dafe k’irji “yaushe na tab’a cin bashi gunki Zeezee?”
  “Wait... Wait Zeezee na, Adda Mariam ce ta ranta kud’i gunki bata biya kiba?”
  “Eh Uncle” ta fad’a tana gyad’a kai.
  “Wallahi Dear karka jita sharri take neman min.”
   “Tsaya mana Habibti muji daga bakin K’anwar tamu.”
  “Wallahi karka jita sharri take neman min.”
  “Wallahi ba k’arya bane Uncle Mahmoud if only Yasmeen was here data gaskata hakan, a idonta Adda Mariam ta ranta kud’in.”
  “Chab! Lallai Zeezee bakijin tsoron Allah.”
  “Ai nasan baki k’arya Zeezee, nawa ne kud’in nakin?” Dad’i taji sosai tasa hannu ta share hawayen ta “5K ne.”
  “Dear Allah karka bata.”
  “Ba ruwanki Hajiya Mariamu tsakani na da K’anwata” wallet nasa ya ciro ya irga 10k “gashi wannan duka naki ne” bayan ta amsa ta irga tsalle ta hau yi “duka nawa Uncle?”
  “Eh mana, stew na ranan yayi dad’i wannan tukuici ne.”
  “Fa ba ita tayi stew d’in ba.” cewar Mariam.
  “Wallahi nice ai Uncle ma yasani” pillow Mariam ta wurga mata “mak’aryaciya kawai” gwallo Zeezee ta mata ganin Uncle Mahmoud bai ganinta “toh Uncle ni zan tafi nagode Allah ya k’ara bud’i.”
  “Ameen K’anwata bazaki jira in having lunch nayi dropping naki ba?”
  “A’a Uncle karka damu zan tafi da kaina”
  “Toh ki gaishe da Mama and everyone” bayan ba-bye taja jakarta ta tafi.

   Isanta gida keda wuya ta wuce d’aki direct ta ajiye jakanta sannan ta fito tayi d’akin Mama “ya har kin dawo neh?” Mama dake zaune bakin gado tayi maganar.
  “Eh tace tana gaisheki haka Uncle ma kuma yabani 10k.”
  “Toh masha Allah zan kira sa na masa godiya ina kud’in yake?”
  “Me zakiyi dashi? Bade karb’ewa zakiyi ba!”
  “Yo dama ‘yar yarinya dake sena barki da 10k?”
  “Ni wallahi shiyasa banson fad’amiki ammin kyauta ni wallahi kibarmin kud’ina.”
  “Haka kika ce?”
  “Eh” ta amsa tana gyad’a kai “kinyi dai-dai, Allah kawo ranan da zakice na baki kud’i kiga in ban gaggaura miki mari ba.”
  “Allah bare kawo ranan bama ni zan fita gidan su Miss Rama sena dawo” bata jira jin meh Mama zata ce ba ta fice.

  *****
   Cikin sati biyu Zeezee ta gama kashe 10k d’in cikin k’ananun siyayyan da basuda amfani, ayau Monday suka koma school su Zeezee ‘yan matan Jss3. K’arfe 7:10AM ta gama shirinta Ibraheem yayi dropping nata kasancewar Baba yayi tafiya, yana dropping nata ya wuce office shima. Kasancewar yau ne first day at school basuyi wani abin arziki ba se hira suka ta sha ita da Lubiee and others 2:30PM Ibraheem yazo d’aukan Zeezee ko kad’an bata lura da  motansa ba as she was busy gisting with her friends, ransa ne ya mugun b’aci ya fito daga motar a fusace ya nufi inda suke tsayen da hijabinta ya jata. Ashar ta hau d’urawa ba tare da tasan waya mata hakan ba, tana juyawa tayi 4 eyes da angry Ibraheem.   “Ya yaushe kazo?”
  “Wa kike zaga?” Ya danna mata rank’washi a presence na friends nata “Allah ya isa ni nasan kazo ne kuma seka kama ka jani da hijabi ka sakeni”
  “Kinada bakin magana ko?” Kunnenta ya kama ta hijabin ya murd’a da k’arfi batasan lokacinda ta soma kuka ba amman hakan besa tayi shiru ba se Allah ya isa take ja mai a haka har yajata mota ya bud’e ya turata ciki se ihu take tana kuka a motan ganin ya faka gefe guda tayi kum da bakinta gudun karya karyi reshe ya mata kalan na kwanaki.
   “Nayi shiru wallahi nayi dan Allah kayi hak’uri.”
  “Marasa kunya kawai bari mu isa gida” yaja mota. Bayan isansu gida ta shiga bayi a guje ta danna lock tana ji yana kiranta tak’i bud’ewa seda ta tabbata ya fita masallaci ta fito ta nufa d’akinsu, wayarsa ta d’au ta shiga whatsapp ta tayi sending had’ad’d’en break up message cike da zagi da cin fuska wa Fateemah girlfriend na Ibraheem ta wuce d’akinta tasa lock tana me praising kanta.

   Koda Fateemah taga message d’in dariya sosai taci dan kuwa she’ve trust in her Ibraheem tasan sarai aikin Zeezee ne. Batasan me ta mata ba Zeezee ta tsaneta, Ibraheem na dawowa ya shiga whatsapp yaga d’anyen aikin da Zeezee ta mai ita dan sokanci ma bata goge chat d’in ba. Murmushin mugunta ya saki ta one side of his face sannan ya kira Fateemah tana d’agawa ta k’yalk’yale da dariya “aikin Zeezee koh?”
  “Barni da ita Babe.”
  “No Baby please karka tab’a ta kabarta.”
  “Kamar ya na barta! Baki karanta message d’in bane?”
  “I did but please let her be for me dan Allah.” Seda ya nisanta yace, “naji I won’t beat her amman she’ll have to serve some punishment.”
  “Eh better amman karka tab’a ta please” hira kad’an suka tab’a sukayi sallama d’akin Zeezee ya nufa direct daman gashi Baba bai gida bale ya d’aure mata gindi kamar yadda ya saba.
  “Zeezee!” Bata san lokacin da ta saki fitsari a panties nata ba jin kakkausar muryarsa, shiru tayi bata amsa ba.
  “Zainab!” Ya kira sunanta more tensed this time around “wallahi before the count of three ki bud’e k’ofan nan ko na b’ab’b’alki wallahi.” Safa da marwa take a d’akin ta rasa nayi chan tace, “Ya ina toilet nefa.”
  “I don’t care ki bud’e k’ofan nan nace kar kiyi pushing d’ina kisa na miki duka.”
  “Bazaka dake niba idan na bud’e maka?”
  “Nace ki bud’e!”
  “Ya dan Allah kayi hak’uri” a hankali ta nufi k’ofan ta bud’e take tayi kneeling “dan Allah kayi hak’uri” ko saurarenta beyi ba ya fincikota da hannu se side nasu yayi wurgi da ita a d’akin. Gabad’aya Zeezee ta gama tsurewa se faman hak’uri take basa “rufa min baki!” Ya daka mata tsawa “ce miki akayi dukan ki zanyi? Kuma koda dukankin ma zanyi, you think wannan hak’urin kin could stop me?” Dan sanyi taji a ranta, wajen laundry basket ya nufa ya fara fiddo da laundry’nsa duk anan kallonsa take bata ce komi ba bayan daya gama ya wurga mata sabulu da omo “oya pack them kije ki wanke min su tatas, isolate the white coloured ones from the rest and believe me in har be wanku me kyau ba zaki sake and don’t think wai da washing machine zaki wanke, uh-uh” yayi shaking kanshi “da bare hands naki now off you go.”

  “Chabd’i! Nice zan maka wanki kuma wai da hannu? Allah yaga ko panties d’ina ban tab’a wankewa ba seda machine, ko nama da washing machine kokuwa kayan naka su zauna da dotti.” Belt nasa ya zare “meh kikace?” Nan ta maraice fuska, “Ya dan Allah kayi min rai kayi hak’uri wallahi ban iya ba zan maka da washing machine.”
  “Nace banaso tattara ki bani waje! Now!” Tana b’ari ta tattara kayakin tayi waje da su waje ta nema ta zauna tana sharb’an kukanta tsakani da Allah tana sumbatu tana kiran sunan Baba, ko uffan Mama bata ce mata ba da ta ganta, bayan data gama shan kukan ta tsoma kayakin cikin bucket tana tunanin ya zata fara wankin. Ganin Ibraheem tayi ya fito da belt a hannunsa take ta fara wankin without knowing how. Kujera yaja ya zauna gefenta yana kallonta tare da instructing nata da zaran tayi pausing kuwa  ya d’aga mata belt tana kuka tana jan Allah ya isa ta samu ta gama wankin sukaje gun shanya ta shanyasu tas har takama hanyan d’akinta tana tafiya tana kallon yadda omon yaci mata faracu tana gun-guni Ibraheem ya kira ta “ke! Where do you think you are going? Baki fa gama aikin naki ba.”
  “Ni wallahi ba jaka bace, dubi wankin dana maka kawani ce ban gama ba” seta rushe da kuka “wuce site d’ina nace kinada minti d’aya kiyi hakan” banzan kallo ta bishi dashi “shegen jan fuska sekace tsuliyan biri, mugu kawai” tafad’a a hankali sannan a hankali ta soma bin bayansa suna isa d’akin ya jata toilet “so nake ki wanke mana bathroom d’innan tas! Banason naga slightest dotti ga harpic da hypo off you go.” Kuka tasa tsakaninta da Allah “bazaki tashi bane?” Still sprawled a k’asa tace;
   “Ya kayi hak’uri wallahi na tuba zan kira Aunty Fateemah na bata hak’uri.”
  “Aww kinsan dama abinda kikayi ba dai-dai bane?”
  “Eh nasani wallahi na sani sharrin shaid’an ne.”
   “Kinsan ba kyau mesa kikayi?”
  “Wallahi sharrin shaid’an ne na tuba.”
  “Zaki k’ara?”
“Wallahi bazan k’ara ba ko wayanka bazan sake tab’awa ba.”
  “Kai inaaa tashi kije ki wanke toilet d’in by then kayan da kika wanke sun bushe kihau gogewa ban yarda da tuban da kikayi ba.”
  “Ya wallahi na tuba bazan sake ba, na sake kamin duk abinda kaga ya dace.”
  “Maza tashi ki bani waje ki sake tab’amin waya kiga” har da cin tuntub’e agarin fita, d’akinta ta nufa straight taje ta mik’e kan gado.

  A week later Mariam ta haihu ta samu ‘yarta Zeezee najin haka ta hau had’a akwatinta zata gun me jego kodan cin kazan jego, itama Yasmeen na jin haihuwan Mariam ta hau had’a akwati. D’aukan abu ya kawo Zeezee d’akin Yasmeen ganin tana had’a akwati ta dakata, “Yasmeen ina zaki haka?”
  “Bakiji haihuwar Adda Mariam bane? Zanje tayata zaman jego.”
  “Chab! Ke asuwa? Wallahi na rigaki ni zanje mata.”
  “Se mu gani ai! Keda ko aiki bakison yinne zaki tayata zaman jego?”
  “Wannan kuma keya dama wallahi ni zanje dani za’a ci kajin jego ehe!” ganin Yasmeen ta cigaba da shirya kayakin nata ta fice zuwa d’akin Baba kai masa k’orafi ai kuwa ya goye mata baya just as expected, yace sam ita zataje ta taya Mariam zaman jego ba yadda Mama batai dashi ya bari Yasmeen meh son aiki taje ba yak’i, bayan Zeezee ta gama had’a akwatinta Omar yayi dropping nata a motan Baba.
  Mariam dake expecting Yasmeen kawai se ganin Zeezee tayi. “Ya haka ina Yasmeen?”
  “Tana gida” ta bata amsa a takaice.
 “Tana hanya ko tana gida? Ba ita zata tayani 40 days ba?”
  “Baba yace ni zan miki.”
  “Ke! God help me wallahi aiki zaki zage kiyi kina jina koh?”
  “Ai nasani ina baby’n take muga kota kwaso muninki.” Da yamma Mama da Yasmeen suka iso tayi ma baby wanka.

   Zeezee de tun daga ranan ba aikinta se ciye-ciye dake ba abinda Uncle Mahmoud bai siyowa kowani rana kuwa se Mama tazo tayi ma jikarta wanka atimes su taho da Yasmeen atimes nahh. Ba wani aikin arzikin da Zeezee ke yiwa Mariam banda in an kawo kaji ta baje taci ta had’a tean ta me kauri tasha se in taga Uncle Mahmoud ne tage zagewa tayi aiki saboda kud’in katin dayake bata anytime yaga tana aiki. Ahaka har aka samu akayi suna yarinya taci sunan Ramlah (mom na Uncle Mahmoud.)
   30 days Zeezee tama Mariam ta tattara kayanta tabar gidan saboda gajiya da tayi da wanke panties na kashi, Mariam se aukin barin ‘ya ba pampers dalili wai ana zafi ga Ramlah se aukin pupu any minute. Ganin haka Zeezee tace zata koma gida Uncle Mahmoud da kansa yayi dropping nata ya bata 3k ai kuwa mutumiyar ta raina ta manta d’ari biyu zuwa biyar da yake bata almost after every 3-4 days nasa kati a waya.
  D’akinta ta wuce direct tayi whats needs to be done sannan ta fito tayi d’akin Yasmeen, mik’e kan gado tana karatu ta tarar da ita “Yasmeen ina Baba?”
  “Har kunyi arba’in d’in ne?”
  “Su gama arba’in nasu lafiya wannan Ramlah take ko meh se aukin kashi minti-minti na gaji da wanke pant na gudo.” Dariya sosai Yasmeen ta tsaya yi da k’yar ta samu ta tsaida dariyan tace, “amman bakida mutunci wallahi sam!”
  “Niba wannan ba ina Baba ya bani dubu biyu in cika in sai wani porche dana gani a Jumia 5k.”
  “Baba yayi tafiya ai yau.”
  “Tafiya!” Tayi exclaiming “shine be fad’a min ba wallahi ya kyauta.”
  “Ji mata! matarsa ce ke da seya sanar dake in zeyi tafiya, lallai kam.”
  “Ni yanzu ki ranta min 2k, na gama sa rai Uncle Mahmoud ze ban 5k yakama yawani ban 3k mschw!”
  “Baki gode ba kenan.”
  “Iyi kuwa ko bakin kasuwa naje na zauna zan tara dubu ukun, ranta min 2k d’in kinji?”
  “Dalili? Ke d’inda baki biyan bashi.”
  “A da ba, da dabansan meye bashi ba amman Allah yanzu zan biyaki.”
   “Tsakaninki da wa?”
  “Da da tsuntsu ne? Da Allah mana.” Kallonta Yasmeen tayi taji kaifa bazata iya rantawa Zeeze kud’i ba. “Kai! Ban yarda ba kije kice Mama ta baki.”
  “Tana gida ne? Kai aiko tana gidan ma ba bani zatai ba ‘cause time da Uncle Mahmoud ya ban 10k ban bata ko k’wandala ba.”
  “Kinga erin halin naki ai, nide kije ki rok’eta kokuwa kije gun Ya Ibraheem ko Omar nide na koyi lesson ban sake baki bashi.”
  “Ya Omar? Wancan marowacin? Ko dubunsa ban tab’a ci ba, dama-dama Ya Ibraheem d’inma de shikuma yanzu da naje ze kama min suratai please ki bani Allah zan mayar miki nan da 2 weeks” da k’yar tasamu tayi convincing Yasmeen ta bata kud’in nan ta biya buk’atar ta.

   
     * ~ *~  _Few days later_...~ *~
   _Wednesday night 12:46AM_ Zeezee ce miqe kan gadon d’akinta tayi ruf da ciki se chatting take a wayarta not minding gobe tana da school ga kuma test da suke dashi a Maths. Bacci ne yazo yayi gaba da ita batasan when and how ba. 5:00AM as usual Mama tazo tayi knocking bisa k’ofar d’akintan gbam! Gbam! Gbam! “Zeezee tashi Sallah” shiru ba response “Zeezee!” Se anan ta amsa uhmmm.
   “Tashi Sallah ko kin manta da akwai school yau?”
  “Ni banayi.”
  “Yaushe ne kikace baki Sallah? Yauma kice bakiyi?”
  “Toh date d’ina ya rikice ne” tayi stating sleepishly.
  “Banson k’arya fa bud’en k’ofa!”
  “Mama dan Allah ki tafi naji zanyi.”
  “Kar ma kiyi ba yarinya ce ke yanzu ba ai” tana kaiwa nan ta fice Zeezee bata tashi ba se 6:00AM alwala tayi, tayi Sallah ta koma gado ta mik’e a cewarta wai 6:30AM seta tashi tayi wanka ta shirya.

    Kasancewar baccin da bata samu jiya ba tayi sleeping off 7:10AM Ibraheem ya gama shirinsa tsaf yazo fita ganin ba Zeezee yayi ficewarsa yaso seta bi su Nanah (maqotansu) bacci Zeezee tayi tasha se 9:06AM da Baaba tazo share mata d’aki ta tashi sanadin knock da Baaba ke. Firgit ta miqe se yanzu ta tuna tanada Maths test, agogo ta kalla taga 9:07AM “innalillahi! Maths test!” bayi ta fad’a tayi brushing ko wanka batai ba har a yanzu knocking Baaba ke.
  “Nikan dan Allah wa me cika min kunne? Koma waye ne ya koma seda na gama makara zaku wani zo kuna wani min knocking mschw!” Ta k’are maganan tana zipping school bag nata, drawer’nta ta bud’e taga ba uniform ciki duk sunyi dotti, jiyan daya kamata ta wanke batayi ba tana ta chatting. Ihu ta qurma ta zarce d’akin Mama, suprisingly Mama ta d’ago kai tana kallonta “ya haka? Ba school ne yau?”
  “Ai dole kice haka” tayi maganan almost crying “Baba kad’ai ya damu da naje school koko a’a wallahi sena kirasa na irga mai komai, tun tafiyansa nike tashi na shirya kaina baku assisting d’ina gashi a banza yau nayi missing Maths test kuma teacher’n bayayin make up test.”




  *© MIEMIEBEE*
  👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com

2 comments:

Anonymous said...

thanks a lot

Unknown said...

Thnks meemee