Friday, 16 December 2016

‘YAR GATA CE!

BY MIEMIEBEE
PAGE 14



    ~* ~* ~*
  Da Asubaah Mama da kanta tazo tada Zeezee daga bacci don yin Sallah ‘cause anytime ta tura sauran bata tashi. Gbam! Gbam! Gbam! “Zeezee bazaki tashi ki bud’e k’ofar bane?” Murya cike da gyangyad’i tace, “waikam ba naji ba? Ai zan tashi.”
  “Shine nace ki bud’en k’ofan.”
  “Toh wai ki shigo kiyi meh Mama? Ai zan tashi.”
  “In baki tashi ba ma keda Allan ki” daga nan ta wuce d’akinta. Jin shiru hakan ya tabbatarwa Zeezee Mama ta tafi, “ai wallahi bazan tashin ba” daga fad’an haka taja comforter ta cigaba da baccinta se 7:00AM ta tashi tayi sallan ta sake komawa bacci, kasancewar yau Sunday ba school. Se 10:30AM ta tashi tayi wanka tasa wani A-shaped gown nata ta fito, a parlour ta tarar da Baba ta gaishesa sannan ta wuce kitchen dan neman abin karin kumallo chan taci karo da duka sauran ‘yan gidan nasu Mama kad’ai ta gaisar, dama on normal basis tana gaishe da Ibraheem ma amman data tuna da dukan daya mata jiya se ta fasa.
  “Ina breakfast d’ina?” Banza da ita duka sukayi Mama ce ta mik’a mata flask natan tace, “in bazaki gaisar da sauran ba Ya Ibraheem fah?” Baki ta turo sannan ta watsa mai harara dan ko kallonta baiyi “ina kwana?” Tace chan k’asa-k’asa almost like whispering, ganin yak’i amsawa yayi banza da ita tace, “tafi nono fari karka amsan” dai-dai zata karb’i flask nata Mama ta rik’e “amman fa yau akwai aiki kinga Baaba bata ji dad’in jikinta ba so bata samu daman zuwa ba yau adalilin haka na rabawa kowa aikin da zeyi, naki aikin share site nasu Ya Ibraheem da musu mopping neh” seda tabari flask na abincin nata ya shiga hannunta tace, “chabd’i! Ni ce zan share musu d’aki meh sauran kuma zasuyi? D’akina kawai zan share kowa ya share nasa.”
  “Haka kika ce?” Mama ta tambayeta.
 
   “Eh mana ni ba abinda zan share musu, Allah yayi wa kowa hannu” ta kama hanyan fita daga fad’an haka.
  “Tsaya ke! Kika gama breakfast d’in kizo zan aike ki shago” Ibraheem yayi maganar in a serious tone. Shiru tayi kamar bata jisa ba, “ko baki jini bane?”
  “Naji” ta watsa mai harara ganin bai kallonta nan ta juya ta hau gun-guni “shikenan shi baida aiki se aikan mutum shago wallahi bazan jeba.”

  _Back in the kitchen..._
  “Wai Mama kinajin yarinyan nan bazaki buge bakinta ba?” Cewar Yasmeen.
  “Barta tanayi wa kanta ne ai ba inda rashin kunya ze kai mutum se halaka Omar Baba na kayi hak’uri ka share muku kaji? Yi hak’uri.”
  “Mama wallahi haushi kike ban in kince tana yi wa kantan nan duka ne be isheta ba.”
  “Barta de ba muna nan tare da ita a gidan nan ba? Zan gyara mata zama” Ibraheem yayi maganan tare da miqewa haka ranan kowa na aiki banda Zeezee dake kallon disney channel,  ita gabad’aya ma tama manta Ibraheem yace ze aike ta shiko yana sane time ya bata inhar takai 12noon bata zo ba ita da shi ne!

   11:56AM aiken da Ibraheem ze mata yayi ringing a kanta firgit ta mik’e duk kalan rashin kunyan Zeezee tana d’an shakkan Ibraheem sanin halinsa.
  “Gani” tace alokacin da ta shiga d’akin nasu bata damu da miyar wa Omar shara bayan da tayi ba, gindin tsintsiyan ya seta k’afafunta ya rabga mata “bakiga shara nake bane da zaki shigo kina miyar min da aiki baya?”
   “Wayyo Allah! Allah ya isa na ni nasan kana sharan ne” kunnenta ya kama “meh kika ce?”
  “Babu dan Allah kayi hak’uri” murd’a kunnen nata ya shiga yi tana ihu Ibraheem dake zaune yana kallonsu ko k’ala bece ba “ni kike jawa Allah ya isa?” Tana hawaye tace, “a’a na tuba dan Allah kayi hak’uri.” Se anan ya saketa ta shiga share hawayenta N2000 Ibraheem ya mik’a mata “siya min Glo na 2k.”
   “Ya nima ka bani N500.”
  “Da uban rashin kunyan kin zan baki N500? In kinason kici arziki na ki dena yimin rashin kunya now b’ace min daga gani” bata ce dashi komi ba ta zarce d’akin Baba takai k’ara nan ya turata ta kira Ibraheem d’in.
  “Uhm Ibraheem Baba na kanada N1,000 kabani?” Baba yayi maganar cike da dabara.
  “Eh Baba” nan ya zaro wallet nasa ya mik’a mai “shikenan?”
  “Eh shikenan nagode koh?”
  “Ba komai Baba kekuma kije ki siyomin ina jiranki.”
  “Wai toh ba na jiba haa’a!” Bayan ficewan Ibraheem Baba ya mik’a mata dubu d’ayan, “saura kuma kije kice dubun daya banin na baki ba ruwa na.”
  “Barin fad’a ba Baba nagode” nan da nan taje ta sai masa katin itama ta sai nata.****


    Da Azahar friends na Ibraheem suka zo bayan sun dawo daga sallan Azahar ya tura Yasmeen ta kira Zeezee, seda ta gama b’ata mai lokaci tazo tana tura baki, “meh?”
Kallo ya galla mata da kanta ta gyara zancen nata, “na’am Ya ka kirani.”
  “Se kuma dana kiraki baki iya gaisuwa bako?” Kallo tabi friends nasan dashi Allah yaso ba mumuna cikinku da kunga buro-uba tayi maganan a zuci.
  “Ina wuninku” tayi murmuring, k’asa-k’asa suka amsa.
  “Kije ki kawo musu drinks sannan Yasmeen tayi guiding naki ki dafa mana indomie tunda ba ayi abinci ba tukuna.”
  “Ni? In dafa muku indomie? Gaskia a’a Ya, ni ban ma iya dafawa ba kuma koda na iya ma sekace wata boyi-boyi.”
  “Magana kike? nace kice Yasmeen tayi guiding naki.”
  “Ni wallahi Ya...” ta hau bubbuga k’afa tana tura baki “ni bazan dafa ba ina kallon shake it up kawai kuyi hak’uri zan kawo muku snacks d’ina na school kusha da drinks d’in.” Dariya sosai ta sa friends nasan d’aya daga cikinsu yace, “Mazaa kabar baby sis nakan nan kawai dama ba yunwa muke ji ba, kawo mana ruwan kawai kinji?”
  “Yauwa Ya Suleiman” shide Ibraheem bece komi ba tunanin kalan dukan da ze mata kawai yake, haka taje ta d’ibo musu drinks da snacks nata ta jera musu kan tray dai-dai tazo ajiwa kenan Ibraheem ya cafke hannunta tare da sa mata nank’washi meh uban zafi aka, k’ara ta saki tare da jan Alah ya isa nan ya k’ara mata “meh kikace?” Tana kuka tace,
  “Nace kayi hak’uri wallahi sabon kitso ne a kaina.”

   “Mazaa let her be please” cewar d’aya daga cikin friends nasan.
  “No kubar ni da ita me kika gama cewa d’azu?”
   “Babu, Ya dan Allah kayi hak’uri wallahi bazan k’ara ba wayyo kaina.” Kunnenta ya kama ya murgud’a da k’arfi.
  “Argghh!” Ta saki k’ara “wayyo Baba na dan Allah kayi hak’hri.”
  “In sake saki aiki kice min baza kiyi ba kiga abinda zan miki marasa kunya kawai” ya saketa “get out!” Da sauri ta mik’e tana jan Allah ya isa har ta fice.
   
     *****
  Da daddare bayan su Baba sun dawo daga sallan Isha ya kirawo Zeezee d’akinsa, “K’anwata bana kema zanyi maki yanka kinji?”
  “Dagaske Baba?” Ta fad’a sounding thrilled.
  “Sosai ma K’anwata” rungumosa tayi tana meh jin dad’i ana cikin haka Mama ta fad’o d’akin “ya haka meke faruwa?”
   “Baba yace zemin yanka wannan Sallan.”
  “Yanka? Alhj yanka zakayi mata?”
  “Eh in shaa Allah tunda Allah ya hore min.”
  “Sauran kuma fah? Ai kamata yayi ka musu duka ka had’asu kan dabba d’aya.”

  “Nifa kinga irin halinki da banso kenan, taya za’a had’asu duka? Allah kaimu next year suma se ayi musu amman bana kam K’anwata kad’ai za’ayi wa yanka.”
  “Hmmm Allah ya shirya ka toh partiality a filin Allah haka, kullum ina ma wa’azi amman bakka ji.”
  “Kanki akeji jeki huta K’anwata gobe kuna da school.”
  “Toh Baba seda safe.” The next day Zeezee ta cika wa kowa kunne a gidan da waqan za’ayi mata yanka za’ayi mata yanka. Yayyun nata tun abin na damunsu ma har sun saba yanzu, hak’uri sukayi suka cire damuwan daga ransu in ba haka ba har ciwon zuciya yana iya kamasu.***

 
     ~* ~*  RANAR SALLAH  ~* ~*
 
  Bayan sun dawo daga Idi Baba ya biya ya siyo raguna manya-manya guda uku, ba tare da b’ata lokaci ba yayi layyansa rago d’aya nasa, d’aya na Mama d’aya na Zeezee. Nan da nan suka shiga aikin nama banda Zeezee dake mak’ale a d’aki tana kallo a laptop nata.
  “Shikenan Mama ita Zeezee ba aikin da zatayi tana zaune a d’aki sekace wata sarauniya.” Yasmeen tayi maganar.
  “Toh ya muka iya Yasmeen? Dama ace Babanku bai gida ne toh amman yanzu da ance Zeezee ta d’aga koda tsinke ne se ya hau kan mutum da bala’i ki barta kawai.”
  “Ai wallahi idan ku kun hak’ura ni bazan barta ba Zeezee! Zeezee! fito nan dan k’aniyanki” cewar Mariam. Jin shiru ta nufa d’akin tan da kanta, miqe kan gado ta sameta, “fito muje muyi aiki.”
  “Wai aikin meh?”
  “Aikin uwaki ‘yar banza kawai fito! Kin maida mutane boyi-boyin ki fito nace!”
  “Ni ban iya ba wallahi kika tak’ura min zan had’aki da Baba.” Seda Mariam tayi dagaske ta samu ta fito da Zeezee daga d’akin. Kujera ta nema ta bata ta zauna suka hau gyaran kayan ciki banda toshe hanci ba abinda Zeezee ke chan kashi ya tab’a mata jiki zumbur ta mik’e “ni wallahi na fasa yin aikin k’azantar nan ku bani wani aikin daban.”
  “Akwai wanke-wanke sekije ki kama.” Yasmeen tayi informing nata.
  “Ni bazan yi wanke-wanke ba sede wani aikin.”
  “Maza wuce kije ki kama wanke-wanken kona gaggaura miki mari maras kunya kawai,karki ga dan ina barin ki wallahi kika b’ata min zan illata ki wuce nace!” Mama ta bud’e mata “ba zaki wucen bane?”
  “Ba naji ba wai kam” baki ta murgud’a sannan ta k’arasa wajen da aka tara wanke-wanken ta hau yi for the first time, se kwab’awa take tanayi kuda suna mata yawo ajiki abinda tafi tsana kenan! “Ha’aah nikam kudena tab’ani mana” tayi maganan da kudajen wai. Dariya Yasmeen ta hau mata “daidanki kenan su cinyeki ma mu huta” ganin kudan basu bar bi mata jiki ba ta je ciki ta d’au insecticide ta feffeshe wajen wanke-wanken se anan tasamu tagama jagwal-gwala wanke-wanken tayi ciki bata sake fitowa ba seda taji an soma gashi “ni ina rago na? Duk wanda ya cimin nama ban yafe ba wallahi.”
   “Gashi chan achan ba wanda ya tab’a miki namanki keda kanki zaki soya” Mariam ta fad’a tana hararta.
  “Ke wannan Adda Mariam kin kusan tafiya ma amman bazaki d’an canza hali aji dad’inki kafin ki tafi gidan miji ba, kuma kar kowa ya tab’a min ragona.”
  “Saidai in baza ayi sadaqa ba, in ba haka ba cinyan gaba da na baya duk sena yi sadaqa dasu” cewar Mama.
  “Wallahi kikayi sena gaya wa Baba ai dabba na ne, kiyi da naki mana.”
  “Please Mama karki sake ce mata komi in aka zo yin sadaqan seta hana muga, banza kawai” cewar Omar yana cigaba da latsa wayarsa. Harara da murgud’a baki ta mai sannan ta koma d’akinta.

  2 weeks after Sallah akayi bikin Mariam, biki yayi kyau masha Allah sede ace Allah shi bada zaman lafiya. Chan Kano aka kaita.

  ★★★★★
  _10 months later..._
   Alokacin Zeezee na Jss2 tana neman shiga na 3 saboda sun ma gama exams na 3rd term nasu sakamako yayi kyau sosai. Zeezee fa ba sauk’i an zama ‘yan mata yanzu se palli da rawan kai, hali zanen dutse har yau bata fasa rashin kunyarta ba, infact sede abinda ya k’aru ma. A month back Mariam da mijinta suka dawo Bauchi da zama kasancewar an mai transfer a gun aiki, sosai Mariam tayi nauyi haihuwa nan da watan gobe in Allah ya yarda, tunda Zeezee ta gano haka ta d’aga k’afa daga gidan Mariam saboda sata aikin da take.
   Yau Monday Mariam ta kira Mama kan atura mata Zeezee tad’an tayata aiki zatayi bak’i, Zeezee najin haka tayi faking rashin lafiya ita sam bazata jeba seda Mama tayi dagaske sannan ta shirya akwatinta kaya biyu kacal tasa ciki dan batason ta jima, Ibraheem ne yayi dropping nata chan Fadaman mada inda gidan Mariam yake. Bayan isan Zeezee ta wuce guest room ta dire jakanta sannan ta fito ta tarar da Mariam zaune a parlour tana shan farin k’asa.
   “Ina wuni? Ya k’arfin jikin?” ta gaishe ta sama sama.
  “Alhamdulillah rice and stew zamuyi min Zeezee.”
  “Rice and meneh? Kinfa san inba farin shinkafa ba, ba abinda na iya in zaki saki jiki ki tashi kije kiyi stew naki toh in kuma ba haka ba se bak’in naki suci garau-garau (shinkafa da mai da had’i) wai ace Uncle Mahmoud (mijin Mariam) kullum baida aiki se kawo mutane gidansa chin abinci wallahi mijina be isa yamin wannan d’anyen aikin ba.”

   “Toh uwar fitsara seki bari idan Uncle Mahmoud d’in yazo ki fad’a masa.”
  “Ni meya kaini? Ke matarsa bakiyi complaining ba seni, ni dama kun cigaba da zaman ku a Kano wallahi.”
  “Jeki kwashe tomatoes da sauran kayan miyan dake fridge d’in ki gyara ina zuwa in d’iba miki albasa.”
  “Wai Adda Mariam ni zanyi komi ke kawai zaki zauna nan kina ture-ture?”
  “Inda da lafiya na ajinki ma zan ce kizo ki tayani ne?”
  “Nikam gaskia bazan yanka albasa ba kema kinsan inada ciwon ido.”
  “Se akace masu ciwon ido basu yankan albasa?” Haka suka ta drama har aka had’a kan stew d’in Zeezee ta dafa shinkafa.

                    *** ★ ***
   Kwana biyu Zeezee tayi ma Mariam taji duk rayuwan bayi mata dad’i, ita ke mata wanke-wanke wai harda shara ma. “Ni wallahi yau zan tafi ban iyawa sekace ni nace kiyi cikin.”
  “Meh kika ce?” Mariam tayi snarling at her.
  “Ni nayi magana neh?” Ta murgud’a mata baki. “Wallahi yau zan tafi, don ni ba jaka bace.”
  “Kanki akeji nide ki gama min shara da wanke-wanken kiyi duk abinda kika so yi.” Haka bayan tagama aikin da cuwa-cuwa kamar yadda ta saba ta shirya tsaf ta d’au wanka cikin purple lace, trolley’nta ta ja zuwa parlour inda Mariamke miqe a k’asa “zaki tafin ne?”
  “Eh” tayi maganan tana plugging earpiece nata.
  “Toh ki gaida su Mama” daga nan ta rufe idonta danyin bacci. Few minutes later ta bud’e idanun nata taga Zeezee tsaye inda take bata ko motsa ba. “Ya haka? Kin fasa tafiyan ne?”
  “Shamawai! Da zanzo inta miki bauta da mijinki ne bazaki sallamen ba! Lallai kuwa!”
  “Aww jira kike in sallameki?” Mariam tayi maganan a bit suprised tana dariya da k’yar.
  “Eh mana bake kad’ai ba har da Uncle Mahmoud ma.”

     Cike da mamaki Mariam ta tafe hannu sannan tace, “Ahh lallai Zeezee, kin rik’a toh nikam Allah yaga banida kud’in da zan baki seki tafi, Allah kaimu wani lokacin.”
  “Wallahi k’arya ne ni ki sallameni.” Zeezee tayi maganan stubbornly.
  “In d’ari biyun mota ne bazan rasa ba.”
  “Chab! Wallahi Adda Mariam ba wasa nake ba ki sallamen.”
  “Kisani na dole, ke wato baki aiki tsakani da Allah bama wannan ba jinki ban sane da sharan cuwa-cuwan da kike min neh? Duk dottin k’ark’ashin gado da kujera kike tura su koba haka ba?”
  “Wancan kuma damuwanki ai in kikayi bak’i ba leqa k’ark’ashin gadon ko kujeran suke ba, nide ki sallameni in tafi.”
  “Lallai kuwa you are not ready to leave inhar ni kike jira na sallameki, zama nan ya kamaki” Mariam na kaiwa nan ta juya mata baya da k’yar. Tsaye Zeezee tayi wajen if only tasan ina Mariam ke b’oye kud’inta, tana cikin wannan tunani ta jiyo k’aran motan Uncle Mahmoud robe dake cikin handbag nata tayi sauri ta ciro ta shafa k’ark’ashin idonta take ta soma hawaye dai-dai nan Uncle Mahmoud ke shigowa anan Zeezee ta soma magana cikin kuka, “wallahi baki isa ba sekin biyani 5k na, ai ba haka mukayi da ke ba wallahi kibani kud’i na” ta rushe da kuka. Mariam batasan alokacin da ta mik’e zaune ba tana kallon wonders kafin tayi magana Uncle Mahmoud yayi sallama, “wa’alaikumus-salam” ita da Zeezee suka amsa in unison “sannu da zuwa Uncle” tace tana share hawayenta kaman dagaske.
  “Yauwa sannu Zeezee ta, Hajiya Mariamu sannu da jiki.” Da ya lura da Zeezee seya kamar kuka take, “ya da kuka kuma? Wani abu ne?” A rayuwa Uncle Mahmoud nason Zeezee badan komi ba sede dan k’iriniyarta musamman inya tuna days back da inyaje zance gun Mariam itama tafito tace se anyi zancen da ita.




  *© MIEMIEBEE*
  👄👄👄👄

  www.beeenovels.blogspot.com

No comments: