Saturday, 3 December 2016

‘YAR GATA CE!

BY MIEMIEBEE


   *December, 2016*
PAGE 04



        ★★★
    A kwana a tashi babu wuya game rai, Zeezee nada shekara d’aya (1 year) tal a duniya yanzu! Yarinya son kowa k’in wanda ya rasa, sede Mama bata fita da ita unguwa ko gidan biki ba idon kowa na akanta, ga kaya masha Allah tun tana Baby se to-match ake sa mata kasancewar Mama ‘yar gayu ce ajin farko amma wani abu Zeezee se tashi take da uban k’uiya, banda ‘yan gidansu bata san kowa ba again, a cikin ‘yan gidan nasu ma wani sa’in zab’a take, atimes in tana hannun Baba ko hannun Mama batason zuwa.
    Tunda Baba yake be tab’a celebrating birthday’n yaransa ba se akan na Zeezee. Grand birthday party had’ad’d’e ya tsara wa Zeezee lokacinda ta cika 1 year. D’imemen cake ya sai mata akayi celebrating, families ne da ‘yan unguwan da basu fi a k’irga ba se friends nasu Mariam suka ziyarci party’n. Su Mariam se palli ake anje an gayyato friends gabad’ai ana ta rawan kai. Se a ranan suke marmarin Zeezee kan ba gobe saboda ganin yadda tayi kyau. Har dan haka suka so yin fad’a ita da Omar. Sosai Zeezee tayi kyau ranan, an gyara mata gashinta cikin colourful ribbons, bugu da k’ari kuma ga yadda glassy green princess ball gown nata ya mata kyau da silver crown nata. Pictures suka sha sosai, suka ci suka sha suka kuma chashe!  
Birthday girl (Zeezee)


  _Wannan ke nan!_
    Tun da Zeezee ta cika shekara d’aya da watanni biyar a duniya Mama ta soma zancen yayeta amman inaaa Baba ya hana wai sam se Zeezee ta k’ara watanni uku ko hud’u kamar yadda muslinci ya tanadar sannan ze yarda a yayeta.

    “Haba Alhj dan Allah! Yarinyan nan de tayi wayo ko a yanzu aka yayeta ba’ayi depriving nata komi ba, aiko a muslincen ma cewa akayi 18-20 months ba’a ce lallai se yaro ya cika 20 months d’inba tukuna kuma yarinyan nan is 17 months now me marabar 17 da 18?” Baba da yayi shiru yana sauraronta tun da ta fara wannan zuba yace;
    “Ki fad’i koma meh Hafsah, kin ga dama kita bayani daga nan har gobe but believe me wallahi se yarinyan nan ta cika watanni ashirin (20) d’innan ki yayeta.” Yayi maganan tare da miqewa da Zeezee a hannunsa.
   “Ai sede in kai zaka cigaba da shayar da ita, yarinya gata doguwa ina ma ace wacce bata girma ne! Ni wallahi har kunyan cireta nake cikin jama’a zan shayar da ita, mutane se gani suke kamar ma tayi girma a shayar da ita  saboda tsawonta.”
   “Awww! Yanzu Hafsah sabida bakin jama’a kikeson tauye wa Zeezee hak’k’inta? Da kyau ban yarda ki sake fita gidan suna ko biki ba har se in kin yaye Zeezee kuma ki shirya nan da anjima zan kawo ta ki bata mama seta k’oshi sannan kiyi wani harkan gabanki.” Be jira me Mama zata sake cewa ba yayi tafiyarsa.

   Anyi haka da kwana uku tafiya ya tasowa Baba zasa Lagos saro laces da zannuwa da sauran abubuwa, ranar Asabar tafiyar ta kama. Duk iyalan nasa suna a garriage suna jiran ya shiga mota su mai ‘Allah kare’ amman ina seya kama hanyan zuwa mota ya dawo ya karb’e Zeezee, itama data gane tafiya zeyi se kuka take tana ‘Baba’ duk jikin sa yabi ya mutu seji yake kan ya fasa tafiya if only an yaye ta da yayi tafiyan da ita. Da k’yar ya iya ya shiga mota yayi wining glass k’asa yana kallon yadda Zeezee keta kuka hannun Mama.
   “Toh ki lalasheta mana Hafsah!”
   “Alhj wani irin lalashi ne ban ma yarinyan nan ba? Ai inba wai tafiya kayi ba barata bar kukan ba.”
   “Zeezee na yi hak’uri kinji barin dad’e ba zan dawo.” Cikin kuka take ta fad’in “Baba... Baba... Baba.”
   “Toh wallahi Hafsah sauran bayan tafiya na ki yaye Zeezee ki jira kiga abinda zan miki.” Shiru tayi batace koami ba, “dake fa nake magana!”
 
   “Yanzu Alhj nace wani abu ne? Allah dawo da kai lafiya.”
   “Ameen, kuma kar ki barta da yunwa, Ibraheem, Mariam nabar Zeezee a kulawanku in wani abu ya sameta ban yafe ba.”
   “Toh Baba Allah ya kare hanya ya dawo da kai lafiya” yaran suka fad’i a tare. D’ari biyar-biyar ya bisu dashi sannan ya tada mota nan fa Zeezee ta fara sabon kuka ahaka Mama tayi ciki da ita. Yau Baba ya tafi washegari Mama ta yaye Zeezee, yarinya data saba kowani minti shan nono kam seji take duniyar ma gabad’ai ba dad’i tata kukan ‘mama... mama’ ina sede Mama ta d’au abinci ta bata haka zata k’i chi da yamma Mama ta aika Ibraheem kasuwa ya siyo cerealac aka fara bawa Zeezee sam tak’i sha ita wai se mama seda yunwa yaci k’aniyanta ta amince tasha cerealac d’in. Na yini biyu Zeezee ta saba dashi sede still atimes zata ta kukan mama ko tata sa hannunta cikin kayan Mama amman hakan bai sa Mama ta cire ta bata.

   Baba kuwa tun tafiyarsa kullum se yayi video call yasa a had’a sa da Zeezee ya tai mata wasa tana dariya. Sati d’aya cus Baba yayi kamar yadda Mama tayi addu’a dan kuwa inhar ace before a week ya dawo tsab zece beji abinsa haka ba se an mayar wa Zeezee nono amman yanzu da ya kai sati Zeezeen kanta ta manta da nonon. Pounded yam and eghusi soup me rai da lafiya Mama ta shirya wa Baba sannan duk sukayi wanka suka shirya tsaf bayan kintsa gidan da sukayi sannan suka fara zaman jiran shigowan Baba.
    Da misalin k’arfe 5:14PM Baba ya shigo Bauchi seda ya tsaya a Bauchi club ya siyo masu gashi sannan ya k’arasa gida duk sun yi murnan dawowan sa tare da mai sannu da zuwa sannan suka soma shiga da kayakin ciki, shide Baba Zeezee ya amshe yana ta mata wasa sosai itama taji dad’in dawowan Babanta.

  *~ *~ Zaune suke duka a parlour se cin tsire suke suna sipping cool Maltinan su hankalin kowa na ayi a gama ci abud’e kaya. Baba dake tauna naman yana bawa Zeezee yaga alaman kamar yunwa takeji dan yadda take taci har in be sa mata a baki da wuri ba ta soma kuka. “Hafsah anya kuwa yarinyan nan ba yunwa takeji ba?”
   “Yaushe ne ta sha cerealac natan?” Tayi maganan ba tare da tasan how and when ba.
  “Dawo baya meh kikace?” Baba yayi maganan cike da k’in gaskata abinda kunnensa suka jiye mai. Nan fa Mama ta shiga kame-kame tayi tsit ta kasa cewa komai. “Dake fa nake Hafsah, meh kikace?”
   “Alhj...” Ta kasa k’arisa maganan.
   “Yayeta kikayi koh?” Shiru... “Nace yayeta kikayi ko?!” Yayi maganar cikin sautin tsawan da yasa Zeezee cusa kanta jikinsa. “Wai mesa bara’a tab’a gaya miki magana kiji bane iyyeh? Mena gaya miki kafin nayi tafiyar? Kinsan ko gun Allah kinada laifi koh?”
   “Alhj kayi hak’uri” be sake cewa komai ba ya miqe ya bar musu wajen nan su Mariam duka suka dawo da kallonsu kan Mama. Ibraheem yace, “Mama wallahi da baki yaye wannan Zeezee ba a banza yanzu ran Baba ya b’aci d’an tsaraban da ya kawo manan ma seya fasa badawa.”
   “D’an banza abinda ke daminka kenan koh? Mschw!” Nan itama Mama ta miqe tabi sahun Baba, d’akinta ta fara dubawa bata gansa ba hakan yasa ta nufa d’akinsa direct, k’ofar tasamu a rufe tayi knocking shiru Baban dake zaune bakin gado  yana bawa Zeezee bobo yayi be amsa knock natan ba.
 
   “Baban Zeezee na shigo?” Bata jira amsar sa ba ta bud’e k’ofar ta shige, ko d’ago kai ya kalleta beyi ba se feeding Zeezee yake. A hankali tazo ta zauna gefensa a bakin gadon tana kallon yadda Zeezee keta shan bobon sekuma ta bata tausayi taji dama bata yaye tan ban. “Baban Zeezee kayi hak’uri nayi laifi.” Kamar wanda bareyi magana ba yace;
   “Ita ya kamata ki baiwa hak’uri bani ba” yayi maganar ba tare da ya d’aga kai ya kalle ta ba. Daga nan Mama bata sake fad’in komi ba seda Zeezee ta shanyen bobon sannan ta miqa hannu ta d’agota daga cinyan Baba ta aza ta kan nata. Hannu tasa ta ciro mamanta ta gwada kaiwa Zeezee duk Baba na kallonta bece ko uffan ba sede abin mamaki ko kallon nonon Zeezee bata son yi hasali kuka ma ta soma kai Baba ya kad’a yace, “tsami kika ringa shafawa bakin nonon seda kika kori hankalin ta daga kai ko ba haka ba?” Shiru Mama tayi duk kunya yabi ya kamata, “ko ba haka ba?” Ya sake tambayar ta. A hankali ta gyad’a kai.
   “Kin kyauta sosai bani ‘yata” ya miqa hannu ya amshe Zeezee.
  “Alhj nafa baka hak’uri we are humans we all make mistakes wallahi da zata kama maman yanzu na yarda zan cigaba da shayar da ita se lokacin da ka yarda a yayeta, kayi hak’uri kaji?”
   “Yaushe kika yayetan?” Chan k’asa k’asa tace, “washe garin tafiyar ka.”
  “Hmm! kin kyauta Hafsah.” Hak’uri Mama tata bashi da k’yar ta samu ta shawo kansa ya hak’ura. Bayan Sallan Maghrib duk ya tara yaran a parlour ya ciro wa kowa tsarabansa Ibraheem da Omar English wears qualitative jeans da T-shirts set biyar-biyar, Mariam laces uku masu tsadan gaske da atamfofi super biyu, se Yasmeen laces biyu da ‘yar kanti masu kyau guda uku. Mama kuma laces biyar da atamfofi super biyu sena uwa uba Zeezee wanda suke nan fiye a k’irga.

  ★★★
      Life couldn’t be better for Zeezee! Wato duk wani abinda take so shi ake mata a gidan sede in Baba bai gida, yarinya tana girma tana dad’a kyau da kuma dad’a kama da mahaifiyarta. Cikin rumfa da rayen Allah Zeezee ta kai har shekaru biyu da watanni goma a duniya (2 years 10 months) baki ya nuna ras se aukin surutu da kuma rashin ji da b’arna. Sede duk laifin da tayi komin girman sa Baba bai bari ko tsawa ayi mata bale wai amata duka koda wasa ba wanda ya tab’a d’aga hannu ya daki Zeezee harta Mama da kanta.

   *~ *~
     Yau ranar ta kasance Sunday as usual tin k’arfe 7:00AM Zeezee ta tashi ta d’ago babban teddy bear nata sannan ta sauk’o daga kan gadonta fuskan Mama da Baba ta leqa taga du bacci suke sannan a hankali ta fice daga d’akin ta sake ja musu k’ofar. D’akin su Mariam ta nufa ta bud’e ta tarar da su suma suna ta bacci kan gadon nasu ta d’ale ta fara tsalle-tsalle a kai, badan komi ba dan kawai ta tadasu. Cikin bacci Mariam ta soma magana tun bata bud’e ido ba tasan waye da d’anyen aiki haka.

     “Zeezee dan Allah kiyi wa Allah kiyi hak’uri ki koma d’akin ku Baba na kiranki.”
   “K’ayyan kine Baba na basshi.”
  “Toh muma ki bar mu mana muyi baccin.”
  “O’o ce kun tashi dan sha tea.”
   “Fisabilillahi Zeezee sau nawa kike shan tea a rana? Kibari se anjima.”
   “O’o ni yanzu nake sho” ta cigaba da tsalle kan gadon. A fusace Mariam ta miqe ta galla mata wani mugun harara aiko Zeezee dan munafirci tasa kuka sekace dukanta akayi. Yasmeen da k’aran kukan Zeezee ya tada ta tace, “Adda Mariam kin shiga uku me kika mata?”
   “Kibar munafuka ko tab’ata banyi ba.”
   “Zeezee dawo” cewar Yasmeen. Kafad’a Zeezeen dake bakin k’ofa tana k’okarin bud’ewa ta buga da nufin o’o. “Wayyayi chena fad’a ki da Baba.”
    “A’a Zeezee ta yi hak’uri kar kije zo abinki kinji?” Cewar Yasmeen trying to sooth her.
   “Ki barta tajen in ta fasa ai in taga ana tsoron takai k’aran mutum ne take jin dad’i yake kuma sake bata garab’asan cigaba da yin hakan, kije ba wanda ya rik’e miki k’afa.” Mariam na kaiwa nan ta juya masu baya tare da rufe fuskarta da bargo ta cigaba da kwanciya. Zeezee na barin d’akin tasa sabon kuka ahaka har ta isa d’akinsu Mama ta hau jijjiqa Baba. Jin kukanta take ya tashi ya zauna, “ya haka Zeezee keda waye?” Ya azata kan cinyansa. Cike da shakwab’a kan yadda ta saba tace, “Adda Mayyam.”
   “Ai kaman na sani muje mu sameta.”

**
   Banging k’ofar d’akin su Mariam yayi firgit suka miqe zaune dukansu. “Me kika mata?” yayi tambayar wa Mariam yana me hararta.
   “Nifa ba abinda na mata tazo muna bacci tana mana tsalle-tsalle kan gado shine nace ta bari take wannan kukan.”
   “Laaa! Baba wayyayi kayyan tane, mari na tayi a zuciya na.”
   “A zuciyanki Zeezee? Ni?!” Mariam ta nuna kanta. “Yaushe ma naga zuciyan naki bale in mara?”
   “Eh a zuciya na.” Zeezee ta kuma jaddada mata.
   “Sannu ko k’anwata” Baba ya shafa kan Zeezee “yi hak’uri” sannan ya dawo da kallonsa kan Mariam “Allah Mariam ki kiyaye ni in sake jin kin tab’a yarinyan nan kiga! Ke shikenan kullum kina cikin bin gindin yarinya kina sata kuka sekace ba babba ba, this should be the last time I’ll warn you again.”
   “Allah sark-”
  “Rufa min baki!” yayi saurin katse ta.

   “Shikenan Zeezee?” Kai ta gyad’a a shagwab’ance sannan tace, “zan sha tea.”
   “Tea? Ko a dafa miki Indomie kina jin yunwa ne?” Ya matse cikinta yana mata cakul-kuli, nan ta hau dariya.
   “Eh” ta basa amsa.
   “Oya Mariam miqe ki je ki dafa mata Indomie da k’wanta guda biyu akai kafin nan Yasmeen kije ki had’a mata tea sauran ki d’ibar mata madara kisha kuma.”
   Kamar wacce zatayi kuka Mariam tace, “wallahi Baba ko an dafa mata Indomie’n ba ci take ba haka jiya ma k’arshenta zubar wa akayi kawai dan tasa nutum aiki ne.”
   “Toh ina ruwanki ai bake kike siya ba, shegen rashin son aiki maza tashi yaso kuka gama seku koma baccin, ku tashi mana!” A sanyaye suka miqe suka nufa bayi dan washing up se gunguni suke.

~* ~* Tea’n ta me kauri Yasmeen ta kawo mata tana zaune kan dining table nata da chair ta shanye tas, a rayuwa Zeezee akwai son tea bayan 25 minutes Mariam dake ta kumbure kumbure har yanzu ta kawo wa Zeezee abincin. As expected Zeezee ta jagualgwala taci kad’an ta k’ara mai abinta.
 
_09:34AM_
     Su Mama na a kitchen suna had’a breakfast, bayan Yasmeen tayi wa Zeezee wanka ta saci jiki tayi d’akinsu Mariam daidai gaban dressing mirror ta tsaya ta fara bi ta kan cosmetics d’in tana applying ita a dole tana kwalya, kaca-kaca tayi da kayakin kwalyan, data kama sharpening eye pencil seda taga k’arshen shi, data waina jan baki seda ya karye, liquid eyeliner ta bud’e ta zana a saman girarta saura ta zagar a k’asa. Komi seda ta b’ata sannan ta masu wanka da turare, daidai tazo fitowa kenan tayi kacib’us da Mariam dake shigowa. Hannu bibbiyu Mariam ta aza kan bakinta da taga fuskan Zeezee.
    “Ki masha min in wuce” cewar Zeezee tana k’ok’arin kare fuskanta.
   “Da kayan kwalyan wa kika-” bata k’are maganan ba idanunta suka sauqa kan ta’addancin da Zeezee ta masu da kayan kwalya. Fincikota tayi da hannu takai ta gaban mirron.

   “Meh amfanin haka? Ban hanaki tab’a min kayan kwalya ba?” Ganin haka Zeezee tasa ihu wane ana cire mata rai, Baba da Mama ne suka shigo a tare a cewansu ma ko Zeezee ta fad’i ne. Zeezee na ganin Baba ta ruga aguje wajensa ya d’agata sama “Baba kaga Adda Mariam koh?”
   “Me haka a fuskan ki Zeezee?” Mama ta tambaya.
   “Mama dubi fa, kalli abinda ta min da kayan kwalya komai seda ta b’ata kuma da gangan take.”
   “Taya zaki ce da gangan?” Cewar Baba, “bakiga yarinya ce ba? A jinki in tasan whats right and wrong zata yi abinda tayin neh?”
   “Amman fa Baba this is not her first time kwanaki da tayi seda na mata magana” tayi maganan idanunta na cikowa da hawaye.
   “Toh Mariam kema seda na fad’a miki ki riga sa kayan kwalyan naki cikin wardrobe kina rufewa achan Zeezee barata iya tab’awa ba.”

   “Ahtoh! In har dagaske kike, kuma me kika ma Zeezee take ihu?”
   “Duka na tayi a zuciya na.”
  “A zuciyanki koh? Yi hak’uri, wallahi Mariam ki kiyaye ni sau biyu nake miki magana kenan yau na uku duka ne.”
  “Alhj amman Zeezee’n ma kai mata magana ta rage b’arna ko jiya a islamiyya seda ta yage wa Mrs. Bee littafi.”
   “Lokacin ta ne ba maganan da zan mata ke Allah kad’ai yasan kalan b’arnan da kikayi kema” yana kaiwa nan ya fice k’arisawa Mama tayi kusa da Mariam da har ta fara kuka tana bata hak’uri haka seda Mama ta bata dubu biyu tayi shiru.

   Su Baba suna zaune a tsakar gida da Zeezee’nsa se hayewa jikinsa take tana wasa wane d’an biri, Ibraheem ne ya dawo daga yawonsa, da wayansa riqe hannunsa ya bashi full attention nasa a haka har ya k’arasa d’aki Zeezee na ganin shigewan sa ta taso daga jikin Baba tabi bayansa. Zaune ta tarar dashi kan couch dake d’akinsu a hankali taje ta zauna gefensa ko uffan bece mata ba se chatting nasa yake yana murmusawa time-to-time, da Zeezee ta d’anyi observing nasa seta gane chatting yake a whatsapp. “Ya Ibyaheem da whashapp.” tace da shi.
    “Ya akayi Zeezee?”
  “Ya Ibyaheem zanyi game.”
   “A’a Zeezee ni gaskiya bara ki kashe min battery ba duk games d’in ma gogewa zanyi” ba tare da tace mai komai ba ta miqe ta kama tafiya “k’ara na zaki kai gun Baba koh? Zo in sa miki toh.” Ko ta kansa batayi ba taje ta samu Baba ta fara kuka “wa ya tab’a min k’anwa?”
   “Ya Ibyaheem ne.”
  “Meh ya miki shi kuma?”
  “Yak’i bani wayanshi nayi game.”
   “Ibraheem! Ibraheem!”
  “Na’am Baba!” ya amsa tare da goge dukka games na wayan nasa sannan ya fito. “Gani Baba” ya durqusa gefe guda.
   “Ina wayan naka? Bata tayi game d’in.”
   “Baba nifa ba game a waya na.”
   “Ka goge kenan?” Kafin Ibraheem ya amsa Zeezee tace, “eh Baba yace min zeyi deleting.”
   “Ni? Yaushe nace miki haka Zeezee?”
“A’a barshi Zeezee jeki amso wayan nasa.”
   “Baba me zaka min da waya?”
   “Downloading mata zanyi ba ka iya gogewa ba? In na sake installing seka sake gogewa kaine da asaran data dan ba shi ze hanani next in ka goge na kuma downloading ba, amso min wayan Zeezee.”
 
   “Baba in na fita anjima zan tura a wayan friend d’ina wallahi ba nida data nima managing nakeyi.”
   “Wannan kuma damuwan ka amso min Zeezee” haka Ibraheem naji yana gani Baba ya shiga playstore “wani game kikeso K’anwa ta?”
   “Shubway churfers da plincess salon.”
  “Zeezee har biyu Baba wallahi data na ze k’are.” Banza dashi Baba yayi yama Zeezee downloading duka sannan ta fara playing. “Kaje in ta gama zata kawo maka wayar.” Kamar wanda zeyi kuka Ibraheem ya kalli Baba sannan Zeezeen dake ta game nata ya miqe ya bar gidan ma gabad’aya.



   *© MIEMIEBEE*
  👄👄👄👄
  beeenovels.blogspot.co.ke

1 comment:

Anonymous said...

Allah yasaka