Sunday, 4 December 2016

‘YAR GATA CE!

BY MIEMIEBEE
PAGE 05

  *December, 2016*


    _This page is in honour of *Fathooma Ali* a great fan I never knew I had. I have recieved your message, thank you so much for the love stay blessed Habibti #OneLove💕_


       Game Zeezee tai tayi kamar ba gobe, dan kanta ta gaji da bugawa ta shiga photos tata kallon pictures saura kuma ta rik’a gogesu a takaice seda tayi mai battery low wayar ta mutu gabad’ai sannan ta kai mai wayan alokacin yana zaune a parlour a side nasu yana assignment nasa na Technical Drawing “Ya Ibyaheem ga wayan ka” ta fad’i tare da ajiye mai a gefensa ko kallonta beyi ba ya cigaba da abinda yake chan tace, “Ya Ibyaheem zane kake yi?” Nanma ko uffan be ce mata ba feeding bottle nata da ke rataye a wuyanta wanda tea ne had’e ciki ta d’aga zata bud’e dan sha. A garin haka tean da yake ciki ya zube kan zanen Ibraheem, “shikenan ai kin huta yanzu! Tashi ki ficemin daga kallo!” ya daka mata tsawa.
   Lamo tayi tana kallonsa a yayinda hawaye ke ciko mata a ido, “baraki fita bane?! Ace mutum kullum se bad luck fice min! Yaso in Baban naki ya dawo ki fad’a mai, get out!” kuka ta soma ba makawa amman ko a jikinsa, kamar kyaftawan ido ya fisgota da hannu ya direta bakin k’ofar tare da rufewa harda kwad’o. Kuka Zeezee ta ringa yi wajen haka dan kanta tayi shiru sabida Baba yafita bai gida Mama kuwa nacan d’akinta tana kwance. Mariam dake tsakar gida ko a kwalan rigarta ta lalasheta daman acike take da ita for what she did to her makeup items earlier.

     Chan da ta gama kukan ta k’arisa wajen garriage inda takejin hayaniyan su Omar. Zaune ta tarar dasu yana ma Yasmeen homework nata na ‘paper mache.’ Waje ta nema ta zauna kusa dasu itama sannan tace, “Ya Omal meh kukeyi?” Kamar wanda bare amsa taba yace, “homework.”
    “Ya Omal paper ne kuka dafa?”
   “Eh da Allah shegen tambayoyi sekace ‘yar jarida kinga baraki iya yin shiru ba find your exit” daga nan Zeezee bata sake cewa komai ba sede duk abinda suke tana observing nasu.
   K’arfe uku suka gama shiri suka wuce islamiyya nan Zeezee ta samu kanta, da full confidence nata taje tana k’ok’arin bud’e k’ofa only to find it locked kamar Mama tasan b’arna data saba zatayi any moment yayyun nata suka barta ita kad’ai a gida, dalilin rufe k’ofan d’akin datayi kenan don restraining nata.

   “Mama ki bud’emin k’ofa.” Banza da ita Mama dake shirin bacci tayi.
   “Mama ki bud’e.” tayi maganan tana jijjik’a k’ofan.
  “Saboda kije kiyi b’arna ba taho mu kwanta in bara ki kwanta ba ga kayakin wasan ki can se kiyi wasa.”
   “O’o ni ki bud’e min.”
“Barin bud’en ba mab’arnaciya kawai.” Kuka Zeezee ta soma rusawa wajen tun Mama tana ignoring nata har ya soma daminta haka seda ta bud’e mata k’ofar bayan jan kunnen data mata na karta tab’a kayan yayyun ta. Like a good girl tace ita wasan ta zatayi. Mama na maida k’ofanta Zeezee ta zarce d’akinsu Mariam luckily yau sun mance basu rufe k’ofan su ba nan ta samu ta shiga. Bata nufi ko ina ba cikin d’akin se inda suke jera school bags nasu, na Yasmeen taja ta bud’e ta ciro notebook d’aya sannan ta fice izuwa kitchen inda ta nemo tukunya ta loda ruwa ciki sannan ta bud’e littafin Yasmeen wanda ya kasance Mathematics ta soma yagewa tana kacancanawa tana sawa cikin kwanon in aka tambayeta wai haka taga su Omar sunyi d’azu. Hakan ta cigaba da yi seda taci rabin littafin sannan ta ajiye ta d’au tukunyar ta aza akan charcoal stove, ashana ta shiga nema wanda bata samu ba saboda chan saman cupboard Mama ke ajiyewa. Dan kanta ta hak’ura bayan ‘yan mintuna ta sauk’e tukunyan sannan ta d’ibo cups da plates da saucers duk bibbiyu ta zauna tsakar gidan itama a dole zatayi paper mache.

    Moulding jikin cups d’in ta shiga yi tana manna papers d’in jiki amman ina se sumb’ilewa suke, haka ba fashi ta tayi sannan data gama taje ta jerasu layi d’aya da inda Omar ya ajiye wa Yasmeen nata.

_5:30PM_
    Anan yaran suka dawo daga islamiyya se Allah Allah Yasmeen ke ta ajiye jakarta ta duba home work nata ko yayi dan gobe Monday zasuyi submitting. Dad’i sosai taji ganin Zeezee bata tab’a mata abinta ba sede ganin wasu cups datayi a gefe bayan data gama duba nata seta d’au na Zeezee tana dariya “wai! Ji shirme itama wai a dole tayi pap-” maganan  da Yasmeen bata k’arisa ba kenan ganin handwriting nata jikin paper’n data lura da kyau kuwa taga Mathematics note nata ne. Salati ta saki sannan tasa gudu zuwa d’akinsu ta shiga neman Maths note nata sede its nowhere to be found. Dam idanta ya cike da hawaye ta kama hanyan d’akin Mama dan kai k’ara, tana fitowa taga rabin Maths note nata a k’asa gabad’ai ya canza kamanni tunanin irin dukan da Mr. Chika (Maths teacher’nsu) ze mata kawai take. D’akin Mama ta nufa tana kuka, Zeezee da tasan this was comig tuni taje ta lab’e jikin Mama.

   “Ya haka Yasmeen waya tab’aki?” Cikin sautin kuka tace, “Mama kalli fah, kalli abinda Zeezee tamin da Maths notebook d’ina” se kuma ta fashe da kuka. Amsan littafin Mama tayi ta k’are mai kallo sannan ta mai da kallonta kan Zeezee datayi tsit, daga bisani tace;
   “Mama bani bane.”
   “In ba keba ai nice, mesa bakiya ji ne iyye? Meh amfanin hakan? Wallahi ga ta Yasmeen kimata duk abinda zaki mata nan gaba ko cewa akai ta tab’a jakarki barata tab’a ba” da hannu Yasmeen ta finciko Zeezee ta nad’a mata na jaki, Mama na kallonsu batace komai ba se anan Yasmeen taji tad’an huce. Kuka Zeezee take wane dan shi aka kawota duniya. Chan ta wuce wajen garriage ta cigaba da kukan har tazo tayi shiru, tana jin k’aran motan Baba ta soma sabon kukan aiko parking na arziki Baba beyi ba yafito yana tambayarta ita da waye. Nishinta har wani sama sama yake tace, “Mam.. Mama ne tasa Yasmeen tamin duka.”

   “Duka?! A dalilin meh? Muje ina Maman naku?” tun daga gun ya shiga k’wala wa Mama kira.
   “Alhj lafiya haka?” Tayi maganan tana k’ok’arin fitowa daga kitchen.
  “Me kika sa Yasmeen ta mata? Yasmeen! Yasmeen! Kema fito nan.” Nan da nan ta fito rik’e da Maths note nata.
   “Ehen ina jinki kibani k’wararren dalilin da zaisa kice Yasmeen ta daka min k’anwa.”
   “Yasmeen mik’a mishi littafin naki” cewar Mama, nan Yasmeen ta miqa wa Baba bayan daya k’are wa littafin kallo yace, “wa yayi maki haka da littafin?”
  “Zeezee ce.”
   “Taya kika san itan ce? A idonki tayi ne?”
  “Alhj wani irin magana kake haka? Mu biyu da ita aka bari a gidan nan ko ni kakeson kace nayi wannan b’arna?”
   “Ba abinda nake nufi ba kenan abinda nake nufi shine ku dena zato tunda ba kamata kukayi in the process ba, ko ke kikayi Zeezee?” Kai ta girgiza alaman a’a. “Toh baga erin saba kun kama kun d’au alhak’in yarinya a banza.”

   “Baba wallahi Zeezee ce, ita tamin kuma Maths teacher’n mu duka na zeyi wallahi.”
   “Naji gobe zamu je makarantar naku na masa bayani amman koda wasa karki kuskura ki sake d’aga hannu ki tab’a Zeezee ever!”
   “Meh kake nufi da hakan Alhj? Baka yarda Zeezee ce tayi wannan tabargaza ba kenan ko meh?”
   “Taya zan yarda bayan ban kamata red-handed ba?”
  “Lallai kam!” Mama ta had’e hannunta biyu ta dafe a ciki “baka yarda bama bale ace ka ja mata kunne koh?”
  “A dalilin me zan ja mata kunne, ba abinda zan mata.”
   “Toh wallahi Alhj ka cigaba kai da kanka wataran zakayi nadaman abinda kakeyi, yarinya ace bata jin maganan kowa se naka Allah kyauta!”

~* ~*
    Da daddare bayan Sallan Isha’i Baba da Mama suna d’akinsu yaran suma haka a d’akinsu. Zeezee ne zaune a parlour ta baje kayakin wasanta se wasa take chan da taji ta gaji ta miqe ta nufa d’akinsu Mariam inda duk yayyun nata suke mik’e suna kallo a laptop na Ibraheem ba tare da tace dasu komai ba ta jawo k’ofan tayi d’akin Mama taje ta samu Baba.
   “Baba zan kayyi fyozen (Frozen.)”
  “Toh je kice wa Ibraheem ya sa miki.”
  “Toh” tace sannan taje ta samu Ibraheem. “Ya Ibyaheem Baba yace kasha min fyozen.”
   “Bara asa ba ke baki tashi kallo se kinga mutane sunayi toh bara’a sa ba, se mun gama za’a sa maki.” Ibraheem yayi maganar ba tare da ya kalli direction nata ba.
   “Dai-dai kenan” cewar Mariam “wai ita a rayuwa dan iskanci seta ga mutane suna kallo take fad’in zatayi toh bara a saba tunda ba laptop naki bane.”
   “Muguwa ba, naji ba nata bane amman naga ai ni na saya koh? Ni ke da iko dashi” atare suka d’aga kai suka ga Baba tsaye gabansu da alama tun d’azu yake tsaye gun.
   “Baba!” Cewar Mariam.
   “Eh ni, ai kaman nasan this was coming, ke bara ki tab’a barin halinki na muguntan nan bako Mariam? Oya sa mata frozen d’in.”
  “Allah sarki Baba sauran episodes biyu mu k’are season d’in fah.” Ibraheem said trying to explain calmly.
  “Se ku jira in Zeezee tagama ku k’arisa, sa mata ka kuma kai mata laptop d’in chan d’akina tayi kallonta ba tak’ura.”

    Se kumburi da gunguni suke Ibraheem ya sa mata frozen d’in yakai d’akin Baba ya ajiye. Bayan dawowansa d’akin ya d’au wayansa kamar ance ya shiga gallery yana shiga yaci karo da tabargazan da Zeezee ta mai almost half of his pictures are gone kuka ne kawai beyi ba.

   Washegari Monday duk yaran sun shirya school kafin nan seda suka kukkule d’akunansu suka bawa Mama key gudun kar uwar b’arna ta musu tabargaza. Aikuwa bayan Mama ta mata wanka ta karya ta nufa d’akinsu Ibraheem taji a rufe tayita jijjigawa ganin yak’i bud’uwa kawai ta je ta samu Mama tayita mata k’ananun b’arna a kitchen tana sata surutu. Da Azahar Baba ya dawo gida as always Zeezee taje ta mai oyoyo a parlour ya direta ya d’ago d’aya daga cikin ledojin daya shigo dasun ya bud’e sabuwar ipad ce pil ciki. Cike da murna Zeezee tace, “Baba ipad na waye?”
  “Naki ne k’anwata” daidai nan Mama ta shigo d’akin. Tsaye tayi in akinbo style tace, “Alhj menaji kace?”
   “Me ruwanki? Ipad na siyo mata.”
   “Ipad fa kace Alhj?” Kasa gaskata kunnenta tayi ta k’ariso ciki taga ipad d’inne dagaske hannun Baba.
   “Lallai Baban Zeezee ina jinka da Yasmeen last week take ce maka ka sai mata waya duk kusan kowa a ajinsu nada waya k’ememe kace wa yarinyan nan ba kada kud’i but here you are ka saya wa ‘yar Zeezee ipad bama tab ba ipad gabad’aya ko me zatayi dashi ban sani ba.”

   “Kinsan meh Hafsah in bakinki bare fad’i alkhairi ba seki fice min daga d’aki daman bani na gayyato kiba.”
   “Ai gaskia ne wallahi baka kyautawa, Yasmeen ya kamata ka sai ma waya ba Zeezee ba kaima kasani.”
   “Mschw! Ke dama kika kama surutu baki gajiya” hannu yasa a aljihunsa ya zaro dimbun kud’ad’e sannan ya irga dubu goma ya danka mata “sekiyi mata ciko ki siya mata.”
   “Ta rage hanya dai” tace tare da ficewa.
   “K’anwata karki kula Mama kinji? Kishi suke saboda basu da ipad” yace da Zeezee dake zaune kan cinyarsa. “Mu had’a miki a charging koh?”
   “Eh Baba akwai games a ciki?”
  “Sosai ma K’anwa ta kuma zan sake miki downloading sabi.”
   “Yauwa Baba nima barin bawa Ya Ibyaheem da Ya Omal ba tunda suna min rowan wayansu.”
   “Ai kuwa naki ne ke kad’an ki daga yau ba ruwanki da wayoyinsu tunda ga naki nan babba”
   “Yeyy Baba” nan ya had’a mata a charging, an hour later ya zaro yayi mata downloading games turum yarinya kam dama ta riga tasan kan amfani da torch screen. A waje ta zauna kan sallayanta tayi cross-legging legs nata ta hau buga game.

  2:30PM yaran suka dawo daga school. Da an gansu anga wanda suka kwaso gajiya from school  Yasmeen ce ta soma shigowa harta wuce Zeezee seta kuma dawowa dan gaskata abinda idanunta suke gane mata. “Ipad!” Tayi maganan tare da k’wararo idanunta waje disbelievingly. “Ya Omar kuzo kuga abin al’ajabi.”
   Daga nesa Ibraheem yace, “wai me neh kike wani tafe hannu?”
   “Kude kuzo mana!” A sanyaye suka k’ariso wajen duk baki suka wangale ganin ipad hannun Zeezee, itako yi tayi kaman batasan suna tsaye a kanta ba se game nata take tayi.

   “Zeezee” Ibraheem ya kira sunanta seda ta b’ata lokaci sannan ta amsa “meh?” cike da rashin kunya.
  “Kalleni” ya buk’ace ta. Nan ma seda ta b’ata lokaci sannan tasa pause ta d’ago sexy long eyes nata tana kallon sa, “meh?”
   “Ipad na waye a hannunki? Uncle Abdallah yazo ne?”
  “Nawa ne” ta basa amsa confidently. Dariyan rainin hankali suka hau yi dukansu especially ma Mariam da tanan tafi kauri dama. “Ipad naki?” Omar yayi maganan in between laughter.
   “Is good to dream big my sister” cewar Mariam harda hawaye dan dariya.
    “Uban wa ya siya miki?” cewar Ibraheem.
  “Ubanku ya siya mata” cewar Mama dake tsaye akansu tana kallonsu tun d’azu. Nan duk suka dawo da kallon su a gareta.

   “Mama jokes apart please ipad na waye?”
  “Gashi kuwa ta fad’a muku, nata ne Babanku  neya siya mata.”
  “Buro uba!!” Cewar Ibraheem “yanzu ipad Baba ya siya ma yarinyan nan?”
  “Eh cewa yayi kuna mata rowan waya and he can’t stand it kuna ma k’anwarsa rowa ya siya mata uwa uba gabad’aya.”
   “Amman shine last week nace Baba ya siya min waya yace min baida kud’i?” Yasmeen ta tab’e baki.
   “Karki damu nasa sa gaba seda ya bada dubu goma zan cika miki mu sai miki wayar.”
   “Yeyy!!” Ta hau tsalle. Dogon tsuka Omar yaja, “Banza mena murna? An siya wa k’anwarki ipad ke za’a had’aki da wayan da befi na 20k ba kuma kina murna.”
   “Yo naga kai ma Zeezeen k’anwarka ce kuma bakada ipad d’in.” tayi retaliating.
  “Wallahi barata saku ba wai bindiga a ruwa, nima se an canza min waya.” Mariam tayi k’wafa ta fice daga wajen. Ibraheem sarkin wayo ya k’arisa wajen Zeezee yana shafa dogon sumanta “My Zeezee taho muje d’akinmu yau na siya miki big bomb.”
   “Dagaske Ya Ibyaheem?”
   “Sosai ma taho muje” ba gardama ta bisa d’akinsu bayan ya canza kaya ya d’au mata sweet d’in as promised ya bata seda ya bari hankalinta yagama bin kan sweet d’in yace, “Zeezee zaki ara min ipad naki?”
   “O’o ba nima kana min rowan wayan kaba.”
  “Ai na dena yanzu, bakiga na baki sweet ba, so zaki ara min na ‘yan minutes ne kawai friends d’ina zasu so inason in nuna musu inada ipad da laptop ne kinji?”
   “Ni banasho su b’atamin ipad d’ina” tayi maganan tana lasan sweet nata.
   “Ai barin ma basu ba bale su b’ata miki so zaki bani?” Ta gyad’a mai kai. “Yauwa My Princess and one more thing please koda sunzo kada ki shigo nan side d’in kinji?” Like a good girl ta gyad’a mai kai.

    Bayan sallan La’asr friends na Ibraheem suka iso ina irin shi big boy d’innan gabansa mac book ne da ipad se palli yake musu yana wani feeling achan d’akin Mama Zeezee ce zaune se shan sweet da Ibraheem ya had’ata dashi take chan fa taga barata iya hak’ura da ipad nata ba ta miqe ta nufa BQ kaman yasan da haka yasa lock. Knocking ta shiga yi seda ya taso ya bud’e, ganinta da yayi ba k’aramin razana sa yayi ba murya chan k’asa k’asa yace, “Zeezee ya mukai dake?” Yana maganan yana leqan friends nasa da suke danne-danne cikin ipad d’in. “Kije ki jirani d’akin Mama kinji?”
   “Ina ipad d’ina?” da sauri yasa hannu ya toshe mata baki ai ta shiga shuresa, a garin haka taga ipad nata rik’e da friends nasa fisge kanta tayi da k’yar ta sa ihu “ku bani ipad d’ina!” ta fad’i da k’arfi. Ibraheem da ji yake kaman ya tone k’asa ya shige dan kunya ya gama yima friends nasa k’arya ipad nasa ne Zeezee tazo ta fasa mai tyre.

   Atare friends nasan suka juyo suna kallon Zeezee fuskokinsu d’auke da tambaya. “Wayyayi sena gaya wa Baba ka basu ipad d’ina.” Fuska yaci “wani erin ipad naki? Ke shikenan duk abinda aka saiwa mutum seki ringa fad’in naki? Mschw! In game kikeso ai seki fad’a a sa maki Auwal miqo min ipad d’in da Allah” yayi maganan a fusace erin baya son bullshit d’innan “gashi!” ya miqa mata “sauran kije ki b’ata min abu na” daga nan ya turata waje kafin ta sake sakar masa da wani bomb.
   “Phew!” Yayi sighing sannan yaje ya zauna ganin friends nasan basu bar binsa da kallo ba ya tuno da wata dabara “dudes kun kalli empire season 3 kuwa?”
  “A’a please kana dashi?”
  “Sosai ma!” yaja laptop nasa ya sa musu da haka ya samu ya gusar masu da tunanin incident daya farun daga brain nasu.

_9:12PM_
   Mariam ce tsaye bakin k’ofan d’akin Baba tun d’azu ta kasa gathering courage da zata shiga seta bud’e baki zatayi sallama se ta kasa ana ckin haka Zeezee tazo shigewa ko ganin Mariam ma batai ba dan yadda hankalinta yabi kan game da take. Dabara ce ta fad’o wa Mariam ta kira sunanta cikin wani irin salo, “Zeezee kyakkyawar gidan mu” se anan Zeezee ta d’ago kai tana kallonta “meh?” Tayi snarling at her
   “Haba *_YAR GATAN BABA_* meh nayi kuma kike b’atamin rai haka?” Tayi maganan tare da tsugunawa tana gyara mata ribbons na kanta. “Ipad naki yayi kyau sosai.”
   “Na sani ai.” ta fad’a mata gatsau da alama ‘yan rashin kunya suna kusa yau.
  “Allah baki hak’uri beauty meh kama da Mama, Zeezee nace zaki tayani yima Baba magana nima a canza min waya?”
  “O’o zaki ce a shiya miki irin nawa bana sho.”
   “Wane ni? Ai wannan naki ne ke kad’ai ni d’an k’arami za’a siya min kinji My Darling Sister?” Shiru Zeezee tayi tana nazari da k’yar Mariam tasamu tayi convincing Zeezee ta yarda zata yima Baba maganan.

   Bayan shiganta Mariam ta kasa kunne jin abinda Zeezee za tace. Gado ta haye ta samu Baba.
   “K’anwata zaki kwanta ne?”
  “A’a Baba a canza wa Adda Mayyam waya.”
   “Ita ta turoki ko?” Nan zuciyan Mariam ya buga Allah sa kar Zeezee ta tone ta.
  “A’a ba ita bace naga wayan ta ya shufa ne Baba.”
   “Are you sure K’anwata? Ba turoki muguwan chan tayi ba?”
  “Eh Baba zaka canza mata?”
  “Anything for you My Sister zan canza mata.”
   “Toh Baba zanje in kwanta gu’ night.”
  “Yauwa Zeezeen Baba sena shigo nima” ya bata peck a forehead ahaka suka rabu tana fitowa Mariam ta d’aga ta sama tana showering kisses all over her face. “Thank you, thank you, thank you, very very much.” Hannu Zeezee tasa tana goge kisses d’in “ni banasho Baba ne kawai yake kishing d’ina.”
  “Toh ‘yar autan mu yi hak’uri nagode kinji? Zaki sha tea ko in dafa miki Indomie?”
   “Eh Indomie.”
  “Taho muje toh Beauty.”

   Sab’anin kullum yau Mariam ce da kanta tayi feeding Zeezee tayi mata wanka sannan ta karance mata good night story ta nufa d’akinsu Ibraheem alokacin har sun fara shirin bacci. Bayan ta zauna kan couch tace, “chab Ya Ibrahem ashe de Zeezee nada advantage” nan ta labarta masa komai bayan dogon nazarin da yayi yace, “excellent! nima kod’ata zan gobe wallahi se an sai min machine.”
   “Ai kuwa de tanan za muna getting on Baba tunda yace komai shi Zeezee.” Hannu suka tafe da Ibraheem suna masu jin dad’in wannan cigaba da suka samu!

  *© MIEMIEBEE*
 👄👄👄👄

   www.beeenovels.blogspot.com

1 comment:

Anonymous said...

thank you