Sunday, 20 November 2016

HEEDAYAH!


                1⃣1⃣4⃣
   written by miemiebee👄



          "Mr romantic ynxu picture kake daukana bayan baby Rayyan na kuka", jakar laptop nasa ya ajiye kan kujera sannan ya karaso ya karb'a baby Rayyan kamar yasan hannun daddy'nsa seyayi tsit, murmushi sosai don moha yake heedayah takai masa bugi a baya, murmushin yake har ynxu "see? Yana zuwa gun awesome dad nasa yayi shiru" nan ya d'aga sa sama yana masa wasa heedayah se "kabari pls karya fad'i, kadena cilla sa sama wlh tsoro nakeji" tana mgnan tana goge hawayenta, don moha yace "oh! Passionate mother harda kuka baby na kuka momma nayi lol kinganki kuwa?" Wani bugin tasake kaimasa yace "Allah kka sake bugina zan d'aga rayyan sama" dagangan ta sake bugin nasa nan yahau cilla Rayyan sama, heedayah harda kuka ita xe jefar mata da baby kiss yabawa Rayyan dake ta dariya sannan ya jawo heedayah yayi hugging nata tabasa peck shima .
         A daren ranan don moha yama mummy  waya kan nanny fa setazo tana taya heedayah kula da baby rayyan sbd ranan har kuka take dan takasa sa rayyan shiru, cike da mamaki tace "haba dai! Lallai heedayah bata da dama" Kafin ya amsa heedayah ta fisge wayar "wlh karya yake mummy", mummy tace "ahh lalle wannan kece mother harda kuka" cike da shakwab'a tace "toh mummy kinga yadda yake kuka ne wlh nad'au ko wani abu ne yasemesa". Mummy tace "toh barin ma nanny mgn gbe xata shigo in shaa Allah", heedayah ta mata godia sannan ta katse wayar ta dawo da kallonta kan don moha dake tama Rayyan wasa takai masa duka a hannu yace "Allah baby ki sake bugina kiga in bansa picture'n ki na dazu a DP ba kowa yagani yayi dariya", shakwab'a ta fara masa "wlh mr romantic kana min wulakanci iya san ranka tun daxu nake rokanka ka goge pictures dinnan kak'i ynxu se wani yagani ne pls ka goge mana" ta k'are maganar kamar wacce zatayi kuka nan ta mik'e "bani baby na yau ba'a d'akinka zamu kwana ba" hannunta ya riko ta fad'o  jikinsa "haba my baby, meyayi zafi I was juat kidding yi hkr kinji kinsan barin iya kwana bake ba baby Rayyan beside me ba", turo baki tayi seka "kira 'yan matanka su dibe maka kewa ai". Yana murmushi yace "haka kka ce? Kinsan ni bana kwante", tace "eh din" nan ya ciro wayarsa ya soma dialing wani number da sauri ta fisge wayar tare da kai masa bugi "wlh bakada kunya wai ynxu kiran budurwa xakayi a gaban baby rayyan? ka b'ata min d'a tun kafin yasan me duniya". Jawota yayi suka tura baby Rayyan one side of the bed su kuma suka wula duniyar ma'aurata.
          Haka suke rayuwarsu cikin so da k'aunar juna. Washegary nanny taxo tunda taxo heedayah ta dena aikin komi illa kula da baby'nta nanny ke mata komi yan air har ynxu basu canza halinsu ba a gaban nanny suta romancing junansu. Su ummu jalila kuwa kowani after 3 days setazo taga lafyrsu ita da nafeesa tho itama takusa yin aure. Abu kamar wasa yau Rayyan nada 3 years se kyau yake yana girma yana sake kama da daddy'nsa sede kamar yanason fin daddy'nsan ma kyau ga gashin kansa tsantsi kamar na yaran turawa har yau bata masa aski koda kuwa low cut ne tara masa gashin take in yyi tsayi setayi trimming tana shafa masa mai, duk inda ta shiga dashy se an ta yabasa. Turenci a bakinsa kamar ruwa duda mgnan d'ai d'ai ga surutu wane parrot rayyan radio R² nanny ke kiransa. Koda yau yafara ganin mutane zagewa yake yata suburbud'a surutu ga gagara sekace d'an turawa komi a gdan destroying yakeyi, kayan wasan sa all over a gda ran harda sa wa nanny wani ball ta zame yana dariya.
       D'akinsa koda za'a shirya sau ishirin to seya wargaza sau ishirin d'in. Gashy ba me ko tsawatarsa masa as both heedayah da don moha sun d'au so da gatan duniya sun basa.This year suke da niyan sasa a sch. Koda heedayah ta tafi office nanny ke kula da rayyan ba abinda yake fad'o mata a rai se sanda take kula da heedayah gaskia time flies ynxu wai heedayah nada baby'n kanta itama, memories nata datake karama kawai ni da nanny muka zauna muna tinawa muna murmushi kamar yanda fans din littafin nan keyi right now.
             Umrah don moha keson suje wannan karan, ya ko gama duka processes da yakamta jirginsu a gobe ze tashy. Tas sun gama shirya kayakinsu, gda sukaje sukayi sallama da mama se wasa takeyi da jikanta haka mummy ma dasuka je gda, daga karshe gidan ummu jalila suka shiga last suka mata sallama sannan tace "ina Rayyan radio?" Heedayah tace "kai ummu jalila ynxu rayyan dinan ne radio? Ai zakuyi missing nasa wlh ze tafi umrah ya  barku", ummu jalila dake murmushi tace "aikam zanyi missn surutunsa ina yake?" Heedayah tace "yana mota yayi bacci", ummu jalila tace "ayyah to Allah kare hanya ya kuma tsare ya dawo daku lfy"... "Ameen" suka amsa ahaka sukayi sallama.
             Washegary safyan yakaisu airport sukayi sallama, Aesha ce ta kirata kam aurenta nxt month kwata kwata heedayah bataji d'adi ba gashi 2 months sukeson yi Saudi, bada jimawa ba jirginsu ya iso nan sukayi boarding. Kasancewar acikin 1st class zasui tafiyan, ya seke bama Rayyan daman yin gagara sosai harda kokarin bud'e window'n jirgi, ji bala'i fa kamosa heedayah tayi tace "sweetheart see, If you're not going to behave urself daddy nd I will are gonna take u back home, okay?" Shiru yayi ya had'e gira tare da zumburo karamin bakinsa "nooo I don't wanna go back home", heedayah tace "then behave urself don't you know there are doctors in here? They inject kids that dont behave denselves, do u want dem to inject you"  Jikinta yashiga yana rufe fuskarsa da mayafinta yana fad'in "noo momma I dont want injection". Don moha dake kallonsu kamar TV se murmusawa yake yace "uhn! Like mother like son rashin san allharanki ya dauko", ahaka suka samu rayyan yayi bacci can itama ta kwanta jikin mr romantic nata har tayi bacci, selfie yata daukansu both momma da rayyan suna bacci. Tafiya me nisa sukayi sannan suka iso saudiya inda suka sauka a Le meridien makkah hotel se tambaye tambaye Rayyan yakeyi. D'aki yamusu booking nan tashiga tayi wanka tama rayyan sannan don moha ya shiga yanayi nasa dinner kawai sukaci suka kwanta. Rayyan se aukin birgima daga ya wulla wa momma kafa se ya hau kan daddy haka suka kwanta a takure ranan

1 comment:

Unknown said...

Hmmm su hidaya mamabear