Saturday, 3 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 61
BY MIEMIEBEE


★‡★‡★‡
      PRISON HOUSE MAIDUGURI, BORNO STATE.
 
    K’aramin gate ne ya bud’u Ya Khaleel ya sa kai ciki, be tsaya ko ina ba se wajen da aka tanada dan masu visiting prisoners. Da zamansa befi minti biyu ba aka bud’o wa Farouq k’ofa sanye yake da orange T-shirt na ‘yan prison meh ‘32’ rubuce a ta bayan. Sosai ya rame yayi bak’i, ta gefen bakinsa yanka ne alaman fad’a dawani yayi har yasamu injurin. K’arisowa yayi a kasalance ya zauna a kujera opposite Ya Khaleel.
 
   “Subhanallahi Farouq meya sameka anan?” Ya Khaleel ya tambaya cike da damuwa yana tab’a gefen bakin Farouq. Hannu yasa ya kawar da hannun mahaifin nasa “ba komai.”
   “Kamar ya ba komai Farouq da wanne kakeson inji ne? Da rashin ka kokuwa da rashin jinka? Cikin nan d’in ma baraka bar fad’a ba?”
    “Baba niba fad’a nayi ba” ya fad’i cikin murya cike da takaici.
    “Allah shirya min kai Farouq” hannu yasa ya d’ago wata leda tare da azawa kan table d’in yana bud’ewa. Abinci ne mai rai da lafiya, ga kaji kota ina. Ba makawa Farouq yasoma chi dan ko rabuwansa da abinci me kyau about a week now tun komawar Babansa Bama. Seda yayi dam ya kora da cool malt drink sannan yajisa d’an dadai.

    “Baba ya batun kud’in bailing nawan? Nagaji da zama anan.”
    “Farouq kasan kud’in bailing nakan ba abu neba na wasa, gun aikinka nayi masu bayani ko zasu d’an ji k’anka, albashin ka suka yanke sunce ba ruwansu dakai. Banki kuma sunk’i bani loan saboda ba aiki nakeyi ba, bakuma wani abu nayi possessing ba.”
    “Baba amman wannan abu is not fair, menayi da wannan Fauzin zesa a rufe ni?”
    “Saboda kai talaka ne Farouq shikuma yanada kud’i. Kai baka gani bane? Ba lawyer’n dayakeson tsaya mana kan case d’innan da zaran sunji Mr. Fauzi ne opponent d’in se su soma mana wasa da hankali.”

    “Bawani Mr. Fauzi dan ubansa, Fauzi kawai in bare amsa bakuma chan masa, uwarsa da Mr d’in. Wallahi na fito he must rule the day he was born.”
     “Ai fitowanka ba nan kusa ba Farouq.” Cike da rashin fahimta Farouq yace, “what do you mean Baba? Ina dubu d’ari biyar da muke dashi a k’asa?” Kai kawai Ya Khaleel ke girgizawa. “Baba talk mana, ina yake?”
    “Farouq a hanya na, na komawa Bama b’arayi suka tsare mana mota suka k’wace duka d’ari biyun danayi aiki na samu da k’yar sesa kajini shiru through out last week.”
   “What?!” Ya fad’a a tsawace tare da zabura. “Farouq yi hak’uri ka zauna.”
   “No! No! Baba this is unacceptable wallahi nagaji da zama anan. Nagaji, I can’t take it anymore. Yaushe ne zaka samu miliyan d’ayan da suke buk’ata ka cireni anan? Mschww!”
   “Calm down Farouq-” katse Baban nasa yayi.
  “No! I can’t calm down.” Mik’ewan shima Ya Khaleel yayi yace, “in har dan wannan baraka iya calming kanka ba then inaga there is no point ma in sanar dakai main abinda ya kawoni, ai wannan jaririn tashin hankali ne aganga da wancan.” Cike da rashin fahimta yace. “wanne kenan Baba?”
   “A’a barin fad’a maka ba tunda wannan ma yayi freaking naka out there’s no need in sanar dakai wanchan.” Hannun Baban nasa ya rik’e suka zauna atare. “Mene Baba please tell me. Ba abinda ze tada min hankali se lafiyar Fannah. Baba ina ba wani abun bane ya sameta?” Shiru Ya Khaleel yayi hakan ya bawa Farouq daman sake magana, “Baba talk mana please.”
 
    “Farouq inason ka kwantar da hankalinka ka sauraren da kyau.” Kai kawai ya gyad’a duk yakasa samun sukuni. “Jiya na je gidansu Fannah nake tambayan ‘yan gidansu ina take sabida ban ganta ba duk sukamin shiru ba wanda ya amsani I had to ask their neighbours nan ne suke sanar dani cewa Fannah tayi... Tayi...”
   “Tayi meh Baba?? Tell me!” yayi demanding
    “Farouq, Fannah tayi aure.”
    “Tayi meh?” Ya tambaya disbelievingly.
    “Tayi aure Farouq.”
   “No... No” kai yake girgizawa ba makawa. “Baba halan baka gane bane, Fannah is mine, she belongs to me no one can take her away. Whats mine is MINE, FANNAH  TAWA CE Baba.” T shirt nasa ya yaga daga gefe d’aya tattoo ne d’an babba ya bayyana a saman hannunsa anyi zanen heart ciki kuma an rubuta ‘F&F’ ma’ana ‘Farouq and Fannah.’ Cike da mamaki Ya Khaleel ke kallon hannun d’ansa totally speechless.

   “Subhanallahi Farouq dan girman Allah me wannan? Tattoo ka zana a hannunka? Kana muslimi?”
  “Eh Baba” ya amsa sa confidently “and I mean it I will never rest se ranan da Fannah tazamo TAWA sabida TAWA CE dama. Koma waye ya aureta seya sake ta inkuma hakan be yuwu ba, I don’t care koda zanyi spilting blood. Fannah tawa ce, ba mahaluk’in daya isa ya k’wace ta.”
 
   Kai Ya Khaleel ya kad’a “koda kuwa mutumin Mr. Fauzi ne? Koda  Mr. Fauzi ne mijin nata?”
    “Mr. Fauzi? Kana nufin shine ya auri Fannah matata???”
    “Shi ya aureta Farouq, Mr. Fauzi shine mijin Fannah, hak’uri ya zama 2 Farouq you can’t fight with Mr. Fauzi he is too powerful.”
     “Baba abu d’aya nakeson kamin, kawai kasan ya za’ayi in fita daga god forsaken place d’innan. Wallahi kaji na rantse sena koya wa Mr. Fauzi @ whats mine is mine and mine alone!” ya buga kan table d’in.

  ★★★★★
MAIDUGURI INTERNATIONAL HOTEL LTD.
 
     Kwance Fannah take bisa gado se kuka take duk tabi ta tadawa Anas hankali yarasa meke masa dad’i. “Fannah to muje asibiti mana” yace da ita cike da tausayi yana a zaune kan bediside drawer’n kanta.
     Kai kawai ta girgiza masa “zuwa gobe ze dena we don’t have to.”
    “Har se gobe? Tun safe ba abinda kikeyi banda kuka ko breakfast kink’i chi haka lunch ma. Ni ban zama care giver ba na gaji da kula dake, kimutu kika ga dama.”
    “Ai banche ka kula dani ba nima, tun farko ma banche ka zauna nan ba, kaje office abinka.” Ta juya masa baya.
    “Ai da kin fad’a hakan tun d’azu seda aka tashi a office d’in zaki wani cemin da ban zauna dake ba? Mschw!” Banza tayi dashi ta cigaba da kukan ta tana juye-juye. Ignoring nata yayi ya koma kan couch ya zauna tare da ciro wayarsa yana latsawa.

    Chan da kwanciyan kan gadon ya gagareta ta sauk’o k’asa se juyi take tana kuka, sekuma ta basa tausayi shi aduk lokacin da baida lafiya zata bar duk wani abinda takeyi takula dashi, why can’t he do thesame? Ajiye wayar nasan yayi ya taso zuwa inda take a kwance ya tsuguna. “Fannah” ya kira sunanta. Baya ta juya masa. “Fannah okay I’m I’m...” sekuma yayi shiru bayajin ze iya ce mata sorry.
   “Tashi kinji?” Nanma banza dashi tayi. “In had’a miki coffee?”
   “Don’t bother, banaso.”
    “Fannah bakici komai bafa since in the morning.” Shiru tayi bata ce komai ba. “Okay Fannah I’m sor-” be k’arasa fad’a ba yayi shiru. “Kinji?”
  “Banji ba.”
    “I just apologised to you, you have to accept it.”
    “Ni haka nake baka hak’uri ne? ka rik’e hak’urinka banaso.”
   “Okay I’m sorry kinji? Tashi ki koma kan gado.” Ba gardama ta mik’e ta koma gadon. Nan ya had’a mata yakai mata seda ya tabbata ta shanye yabarta ta koma ta kwanta.

  ****
        Washegari Fannah ta tashi garau masha Allah taji sauk’i sosai. A farko ma cewa Anas yayi bare je office ba, Fannah ce tasa sa a gaba saboda tasan halinsa duk wani alkhairin daya ma mutum seya k’arisa da tsiya, dan haka kawai tasa sa a gaba seyaje, shikuma dan nuna mata be damu da ita ba ya shirya yayi tafiyarsa ko breakfast yak’iyi. Yana ji tana kirar sunansa ya dawo su karya yayi banza da ita.
        Isarsa office ya baje kan kujera nan Kacallah yashigo masa da files ba adadi yasoma bi one-by-one yana signing, by 10:00AM yafita meeting sede tunda aka soma yakasa gane me akeyi kwata kwata hankalinsa bayya jikinsa yana chan yana tunanin Fannah for sure yasan ta samu sauk’i but he can’t stop himself from being worried, ana fitowa daga meeting d’in ya kirata a waya a lokacin tana bayi tana wanka seda tafito taga missed call nasa k’waya d’ya. “Shegen girman kai, ko kiran mutum sau biyu ma be iya ba” nan ta kirasa back bada dad’ewa ba ya d’aga. Shiru tayi bata ce komai ba shima haka sun kusan minti biyu shiru sannan yakira sunanta “Fannah.”
   “Na’am” ta amsa.
    “Aww dama kina kai? Shine bakiyi magana ba tun d’azu?”
    “Toh ai kai ka fara kira na.”
      “Ya jikin naki?”
   “Da sauk’i.”
      “Okay...”
     “Shikenan can I go ba k to what am doing?”
    “Me kikeyi?” Ya tambaya haka kawai yaji yanason cigaba da sauraron muryarta.
    “Yanzu nafito daga wanka zan shafa mai.”
  “K’azama se kusan to twelve na rana zakiyi wanka.”
   “Toh ai bacci nayi.”
   “K’azama ba.”
    “Niba k’azama ce ba, excuse me zan shafa mai nan ta katse.” Murmushi dukansu suka tsaya yi suna kallon wayoyinsu musamman ma Fannah. She can’t deny it anymore ta fad’a tarkon soyayyar Mr. Fauzi sede batason soyayyar yaje ko ina saboda batasan ayi hurting nata daga k’arshe ‘cause muddin Anas yasan sirrinta he will run away and leave her, aduk lokacin data tuna da wannan seta yayyafa wa zuciyarta ruwan sanyi dan huchar da zazzafan son Mr. Fauzi. Haka har tagama shirinta tana tuna jiya yadda Anas ya riga mata hidima ko da daddare da take kuka ya hana kansa bacci ya zauna da ita yana pompering nata, haka kawai taji tana murmusawa.

    Shima Anas zaune yake cikin one of hotels daya saba chin abinci, ga abincin agabansa amman yakasa ci se murmusawa yake musamman ya tuna rananda take tsaye da towel a gabansa dakuma lokacinda cinyoyinta sukayi tsami yake shafa mata muscle pain reliever. Da k’yar ya iya ya kai spoons biyar yaji yama k’oshi tunanin Fannah kad’ai ya ciyar dashi. Be jira aka tashi ba yabar office ji yayai kawai Fannah yakeson sawa a idanunsa, it hasn’t been long amman seji yake like shekara da shekaru ne.
 
    _K’arfe 3:00PM_
      Tsaye Anas yake bakin hotel room nasu ya kasa shiga dan girman kai. “What if tace mena dawo yai since before lokacin tashi yayi, me zance mata? That I miss her I want to see her? No! No way ai seta raina ni ta d’au ko sonta nake.” Ya juya ze koma kuma yaji bare iya ba Fannah yakeson gani and no one else. Seya d’aga hannu zeyi knocking seya sake maida hannun nasa baya.

     Fannah kuwa tayi waya da Afrah ta buga game, ta kalli pictures na bikinsu, tayi kallo, tagaji zaman shirun ya isheta. Sanin ba kowa a floor dasuke daga ita se Anas, Anas kuma baya nan ba wanda ze hauro ta d’au wayarta kad’ai. Atamfa ne d’inkin fitted riga da skirt ya mugun mata kyau a jikinta, kayan ya zauna tip tip. D’aurin ta ta daidaita sannan ta bud’e k’ofar, baki ta sake ganin Anas tsaye jikin k’ofar.
    Mutuwan tsaye sukayi duk a wajen suna kallon juna sun kusan minti biyu suna abu d’aya sannan ta kawar da kanta zata rufe k’ofar dan komawa ta d’auko mayafinta kenan Anas ya rik’o hannunta. Be d’aga idanunsa daga kan k’irjinta ba har ayanzu se kallonta yake.

    “Uhm Anas kasakeni in d’au mayafi na please.”
     “Why?” Ya tambayeta se anan ya dawo da kallonsa kan kyakkyawar fuskarta data sha d’an light makeup.
     “Anas hakan ba kyau-” katseta yayi.
   “No I like it this way, kinfi kyau haka kar ki rufe jikin ki kinji?”
    “But Anas-” katse ta ya kuma “Fannah I’m your husband nace nafison ganinki haka” se yanzu ya tuna da kalamun ta na ranan cewa batason tsinuwan mala’ikun rahma.     “Ko ki zauna haka kokuma inyi fushi dake mala’ikun rahma suyita tsine miki.”
    “A’a dan Allah don’t talk like that kaji karkayi fushi.”
    “Zaki zauna hakan?” Kai ta gyad’a a hankali. “Good” ya saki brightest smile nasa.
       “Da ina zakije ahakan?”
   “Babu kawai nagaji da zaman cikin ne nace barin d’an lek’o waje.” Ta basa amsa tana k’oka’rin raba hannunta da nasa. “Shine zaki fito ahaka ba hijabi ba mayafi?” Ya fad’a a little bit pissed off, daga yadda yake magana za’a san kishi ya motsa.

    “Toh Anas naga ba kowa a floor d’inmun, mu kad’ai ne.”
     “I know what of room services? Insuka hauro alokacin da kike k’ok’arin fitowa ahaka fah? Se suganki?”
    “Yanzu fa kace nafi kyau a haka kar insa mayafi.” Hannu yasa ya hargitsa gashinsa cike da haushi. “For goodness sake Fannah I’m your husband, taya zaki had’ani da room service? Nine kad’ai am aloud to stare at your body and not them.”
   “I’m sorry” tace dashi tana kallon k’asa.
   “No you are not Fannah, daga yau karki sake fitowa koda bud’e k’ofa ne ba hijabi ko mayafi do you get me? Banason mayafin ma hijabi constant kinji?”
     “Haba mana Anas ai dan bud’e k’ofa kam mayafi ma yayi.”
   “Ni bemin ba banaso, Fannah I’m serious.”
   “Okay naji barin k’ara ba.”
   “Better” yace yana hararta. “Matsa min in wuce.”
    “Ka wuce ina? Anas lokacin tashi daga office fa beyi ba, meka dawo yi?”
     “Me ruwanki? Ko kin d’au wai dawowa nayi saboda nayi missing naki? Hell No nadawo d’aukan wasu files ne, mema zan kalla a fuskarki ko jikin naki, excuse me?”
    “Niba abinda nake nufi ba kenan” gefe ta matsa masa ya shiga tabi bayansa. Briefcase dayake adana files nasa ya ciro shi a dole yadawo ne dan d’auko abu tana tsaye akansa se dube-dube yake yakasa koda d’aukan d’aya ciki. Ganin har yaci minti biyar be samu ba Fannah tace, “Anas anya kuwa files d’in kazo d’auka ba wani abu daban ba?” Da biyu tamasa tambayan dan kuwa hankalinta ya bata ba file yazo d’auka ba wayasani ma ko missing nata yake dagaske tunda har ya bud’e baki yafad’a d’azu indirectly.
 
    “Mind your business mana meh ruwanki da abinda nakeyi kin wani zo kin tsaya min akai sekace soldier (soja.)”
      “Allah baka hak’uri niba abinda nake nufi ba kenan, I was thinking ko kanaso in tayaka nema ne.”
   “Neman meh?”
  “File da kake neman, koba file kace kana nema ba?” Shi se yanzu ma ya tuna eh file yazo nema.
     “Toh banaso, zan nemi abu na dakaina.”
    “Yi hak’uri in taya ka” tace dawani mocking smile tattare da fuskarta.
   “Fannah yaushe na soma wasa dake? Mind your business.” Juya baya tayi tasoma tafiya zata kan couch ta zauna. “Mutum bare fito fili ya fad’a meya kawo sa ba se shegen zurfin ciki” tace chan k’asa k’asa almost kamar da kanta take maganar.
    Bejita gabad’ai ba amman yaji some part. “Ke! Me kikace?” Take ta juyo dan bata tsamman yajita ba.

     “Babu kawai cewa nayi Allah sa kasamu file d’in.” Harara ya galla mata tare da cigaba da nan file dayayi qarya yana nema. Chan ya d’ago kai yaga se lastse wayarta take, tsayuwa yayi yana kallonta ko kyafta ido baiyi data d’ago kai seya juya daga k’arshe ya ciro wani file yayi hanyan fita ai dagangan ya sakar da k’ara “awwchh! My ankle.” ya tsuguna yana rik’e k’afar. Da sauri ta nufa wajen “Anas meya faru?” Ta tambaya tana dubansa.
     “My ankle nakega nayi spraining. Awcchh!”
    “Ya Salam! But how?” Ta tambaya.
   “Nima bansani ba, argh!!” Hannunta ta zagaye ta bayansa tayi assisting nasa ta kwantar dashi kan gado. Se faman “awch!” na k’arya yake, sam yaji bayason rabuwa da ita koda na second ne shiyasa yayi coming up da wannan plan na spraining ankle nasa.

     Takalmasa ta cire masa da socks d’in, da ta tab’a k’afan hagun nasa seya sa ihu. ”Sorry, d’an tsaya in gani.”
    “A’a barshi.”
    “Anas kasan fa bareyi abar k’afar haka ba, nida cinya na sukayi tsami kwanaki ba haka kasani a gaba ka riga shafa min man zafi ba? Ka tsaya inga.”
    K’afan nasa ta aza kan cinyarta tana d’an mammatsa wajen ankle nasan. Sekuma abin yasoma masa cakulkuli, dariya yakeson yi amman ya matse se faking “awch!” Yake tayi.
   “Amma Anas banga alaman koda b’ullowan muscle bafa, kuma kace kayi spraining.”
    “Aww maqaryaci kikeson cemin komeh?”
    “A’a kawai de da abun ban mamaki ne.”
    “Sakemin k’afa ba sekin zagen ba.” Nan ya d’aga k’afarsa daga kan cinyar tatan.
   “Anas ba abinda nake nufi ba kenan I’m sorry.”
   “Banaso, tashi kibani waje.” K’afar nasan ta mayar kan cinyarta. “I’m sorry kaji?”
     “Naji” yace ba tare da ya kalleta ba.     “In shafa maka magani awajen?”
       “No you don’t have to.”
   “Anas in ba’a shafa ba baraka iya taka k’afan bafah.”
    “Don’t worry just come lets sleep.”
   “Sede inkai ni banjima da tashi daga bacci ba.” Nan ta mik’e ta rage masa kayan jikinsa ta juya kenan ya rik’o hannunta “lets sleep kinji?” Be jira amsarta ba ya jata ta fad’a jikinsa.

     “Anas me haka?” Ta fad’a a lokacinda take k’ok’arin tashi.
   “Lets sleep.” ya sake matseta jikinsa.
   “Ahaka? Ai namaka nauyi barin kwanta a gefe kaji?”
  “No I want it this way.” Bata sake cewa komai ba sede sam ta kasa samun sukuni, wani erin baqon yanayi ta tsinci kanta ciki.

_20 minutes later..._
      “Anas” ta gwada kiran sunansa jin yayi shiru, ta d’aga hannunsa daya zagaya akan bayanta a hankali sannan ta taso daga jikinsa ta yadda bata tadashi daga baccin nasa ba.

     *© miemiebee*
   

No comments: