TANA TARE DA NI... PAGE 59
BY MIEMIEBEE
Chicken chop ya wuce dasu dan siyo musu roasted chicken. Bayan yayi parking yafito ya bud’e mata k’ofarta, kamar d’azu haka ya matso ta jikinsa. “Anas yanzu kama hannun ma kadena? Se haka?” Ta tambaya a nitse.
“Eh na dena nan gaba ma I think d’aukan ki zan soma.” Bata sake che dashi k’ala ba suka shiga ciki d’aya daga cikin kujerun ya ja mata bayan ta zauna ya nufa wajen siyan. Shiru Fannah ta zauna tana ‘yan kalle-kalle kafin ta hankara ta jiyo sallamar sabon murya akanta. Data d’ago kai taga matashi ne jik’a a jini ko suyi shekaru d’aya da Anas koya girmi Anas da kad’an.
“Wa’alaikumus-salam” ta amsa sa d’auke da murmushi a fuskarta. “May I sit?” ya buk’ata in a calm way.
“Yes sure.” Nan yaja kujerar dake kusa da ita ya zauna. “Koban tambaya bama nasan bakida aure ko?”
Murmushi ta saki tare da girgiza kai ta bud’e baki zatayi magana kawai taga Anas from nowhere ya cukumo kolar rigar bawan Allah yakai masa punch a fuska take gefen bakinsa ya fashe. A firgice ta mik’e “Ya Salam! Anas meh hakan please? Taya zaka hau dukansa be maka komai ba, ka sake shi.”
“Bemin komai ba? Are you kidding me Fannah?” hannun mutumin ya murd’a ta bayansa cike da mugunta wanda har yasa mutumin sakar da k’ara.
Cike da azaba yace, “hey who are you? And meh na maka? Let me go will you? Taya zakazo ka kamani in public kana murd’a min hannu.”
“Awww tambaya ma kake meka min?”
“Anas everybody is starring at us dan Allah ka sake shi, its embarrassing” Fannah ta katsesa cikin salon da bareji haushi ba.
Juyawa yayi ya kalli jami’un wajen. “Mind your own god damn businesses! Now!” yace dasu a tsawace nan kowa yacigba da harkan gabansa.
“Barin maka warning, ko a lahira kaga Fannah karkayi yunk’urin mata magana ‘cause it might be the end of you, ba’a mutuwa a lahira but when it comes to toasting my wife I could kill you. Do you get me?” Ya sake murd’a wa mutumin hannu. Cike da azaba da mamaki mutumin ya d’ago kai yana kallon Fannah data tsure itama.
“Why didn’t you tell me you were married?” Abinda yace kenan. Wani irin gulity concious ne ya kama Fannah.
“You mean you didn’t know?” Anas ya tambaya cike da mamaki shima.
“Bawan Allah a tunaninka haka kawai zan hau toasting mace me aure ne? Seda na tambayeta ko matar aure ce ita sekuma ta min shiru. Da shigowa na garin nan sati kenan I know barely no one.” Take Anas ya sake sa “I’m so sorry please kaji? Accept my apologies.”
Seda mutumin ya k’are masa kallo sannan yace, “accepted amman nan gaba don’t just jump into conclussion” yana kaiwa nan ya waiwayo ya kalli Fannah tare da kad’a kai sannan ya fice. Hannunta Anas ya finciko cike da azaba ita kanta tasan she is in trouble ko d’ago kai taga ya yanayin fuskarsa take ma batai ba a iya sanin ta fuskarsa da idanunsa zasu iya fin jan kala yin ja saboda daga yadda yake nishi za’a iya kwatanta b’acin ransa.
K’ara ta saki tana k’ok’ari k’watan hannun nata. Bakin k’ofa yajata. “Sir your order is ready” ko jin mutumin beyi ba yajata suka fice daidai motarsa yayi wulli da ita kad’an ya rage bata fad’i ba. “Get in” yace cike da b’acin rai hawaye tasoma wanda batasan lokacin ba, a hankali ta bud’e k’ofar ta shiga ya kunna mota. Koda suka isa hotel d’in fitowa yayi tsaye yana jirarta bayan tafito yakuma kama hannunta irin na d’azu.
“Anas dan Allah ka saken da zafi.” Ko sauraronta beyi ba ahaka har suka haura d’akinsu. Banging k’ofar yayi da k’arfi tare da bugata jikin k’ofar. Ba abinda take banda kuka ba sauti dakuma b’ari. Dududu ratan dake tsakanin fuskarsa da nata befi inchi biyu zuwa uku ba. Wani irin kallo yake mata tsabagen yadda ransa ya b’aci yama rasa me ze mata. Cikin wani irin tsawacaccen murya yace, “bakida hankali neh?! Kina matar aure zaki zauna kusa da wani? For crying out loud harda k’in cemasa you are a married woman? Huh?!” Kai kawai take girgiza masa hawaye nabin k’uncinta.
“I’m talking you!” ya fad’a a tsawace tare da sake buga jikin k’ofar. B’ari take harwani sama sama nishinta yake, “Anas dan Allah kayi hak’uri, I’m sorry please.”
“You still haven’t answered my question. Why Fannah? Answer me!” Cikin sautin kuka tace, “Anas kaifa da bakinka ka fad’amin koda anyi bikin you can see any girl you want tunda contract marriage ne shine nima naga ai bawani abu ciki dan mutumin d’azu yamin magana.”
“Damn it!” Ya sake buga k’ofar. “Damn everything Fannah! What if na fad’a miki I don’t mean it, tunda akayi bikin kinga naje gun wata ko wata tazo min ne? I don’t mean any of those words kawai na fad’a ne.” Ya k’are maganar yana kallon k’asa.
“Anas I’m sorry dan Allah kayi hak’uri.”
“No Fannah ke kanki kinsan what you did was wrong, how could you not respect our marriage?” Yana kaiwa nan ya juya binsa tayi, tayi hugging nasa ta baya tana meh hanasa koda motsi. “Anas I’m sorry dan Allah kayi hak’uri I thought you meant what you said shiyasa, am sorry please.” Har a yanzu baijin he can forgive her. Hannunsa yasa ya raba jikinsa da nata. “Anas please...” Ta rok’esa se ambaliya hawaye ke a fuskarta.
Kayan jikinsa ya rage yabar shorts da vest zalla tare da hayewa kan couch ya kwanta. Kuka take har yanzu ba sauti ganin ba mahalicci se Allah ta mik’e ta nufa bayi, fuskarta ta wanke sannan tafito ta juye masa coffeen sa cikin cup tare da kai masa. Ganin haka ya juya mata baya. “Anas kayi hak’uri kasha please.” Banza da ita yayi. “Anas please, I said I’m sorry be isa ba?” Nanma banza da itan yayi.
“Anas koda contract marriage ne tsakanin mu you are still my husband kadena fushi dani banasan tsinuwan mala’ikun rahma please talk to me.” Nanne yayi magana.
“Ince miki meh?”
“Anas me zan maka ka yafemin please, stop being mad.” Juyowa yayi yana kallon yadda take ta zubda hawaye sekuma ta basa tausayi. Coffeen ya amsa ya kurb’e tare da miyar mata da cup d’in. “Nasha shikenan?”
“Anas bakace ka hak’ura ba.” Shiru yayi tamkar bejita ba. “Anas mana...”
“Naji, bacci nakeji yanzu allow me, will you?”
“To katashi ka haura gadon ka kwanta, kaji?” Shiru bece komai ba. Hannu tasa ta jijjik’a sa bece da ita komai ya mik’e ya nufa gadon ya kwanta. Mayafinta ta d’auka tayi bakin k’ofa. “Ina zakije?” Ya tambayeta.
“Akwatina zan d’auko.”
“Wait.” Nan ya d’au wayarsa yakira wani in less than 2 minutes aka kawo mata jakar tata. Amsa tayi ta bud’e ta soma jera wanda takeso da wanda battaso tun Anas yana kallonta har yayi bacci. Bayan ta gama taga still da saura Azahar. Kan couch d’in ta nufa ta mik’e nan itama tayi baccin.
*****
Sakamakon ihun da Anas ya tsala ne ya farkar da ita daga bacci a firgice. Ganinsa tayi zaune kan gadon ya had’a wani irin gumi da sauri ta nufesa. “Anas” ta kira sunansa, beko amsata ba se girgiza kai dayake. Remote na AC ta d’aga ta k’ara k’arfin. “Anas are you okay?” Ta tambaya a nitse. Nan ma be amsata ba. Tissue ta zaro tana goge masa gumin nasa bayan data gama ta yasar sannan ta dawo ta zauna kusa dashi. Hannunsa ta d’aga tayi interwining yatunsu su a hankali.
“Anas mafarki kayi?” Kai ya gyad’a mata.
“Want to talk about it?” Kai ya girgiza.
“Okay toh keep calm kaji, I’m here if you need someone.” Chan k’asa k’asa yache, “yarinyan ta dawo.”
“Yarinya kuma?” Ta tambaya cike da rashin fahimta. “Wace yarinya kenan Anas?”
“Yarinya from the incident. *_TANA TARE DA NI..._* haka tacemin kuma nima I can feel it. *_TANA TARE DA NI..._* Ina take?” Ya d’ago idanunsa da basu gama dawowa asalin colournsu ba yana kallonta.
“Anas bansan wace yarinya kake magana ba, its just a dream kaji? Inma wata yarinyar kake nema sooner or later zata bayyana maka, kaji?” Kai ya gyad’a tare da mik’ewa kan gadon, kansa ya aza akan cinyoyinta masu uban laushi da tsoka daidai ya kwanta. Bata ce masa komai ba ya daidaita position na kansa akanta yana kallon d’ayan direction d’in. Fannah kad’ai tasan irin electric sparks da suke going mata ajiki. Wannan ne karo na farko dawani d’a na miji ke kwanciya mata a cinya.
“Fannah kina ganin zata yafemin abinda na mata?” Yace da ita cikin wani irin salo. Shiru tayi danko batasan ina ya dosa ba.
“Wa ce kenan?” Ta tambaya.
“Yarinyar, kina ganin she can forgive me despite abinda na mata?”
“Me kama ta Anas?” ta tambaya cike da neman k’arin bayani.
“Its horrible I can’t say it, na cuce ta nasani shiyasa koda in mun had’u tace sena aureta zata yafemin zan aureta, I will do it” Bugun zuciyarta taji ya k’aru, meh Anas yana wannan yarinyar dayake fad’in ze aure ta na hak’ik’a? Shida bayason aure koda wasa yake cewa zeyi toh mesa? Kamarya ya cuce ta kuma? Toh kode ciki ya mata ya gudu? kai a’a Anas beyi kalan me bin mata ba har ace yama wata ciki, toh me ya mata? Shi ya tsamota daga duniyar tunanin data wula.
“Fannah kinaga zata yafemin in na bata labari na?” Hannu tasa cikin silky gashin kansa me uban tsayi da cika daidai ba kamar nata ba. Shafa gashin nasa take a hankali tana curling wasu a yatsunta. “I’m sure zata yafe maka Anas muddin kayi nadaman koma mene ka mata, dakuma in ta sake jin labarinka. Zata yafe maka kaji?” Kai ya gyad’a a hankali. Daga nan be sake cewa komai ba.
Bayan like 10 minutes takira sunansa shiru taji be amsa ba. Data lek’a fuskarsa setaga har yayi bacci no wonder taji ya k’ara nauyi. Dukda cewar idanun sa a rufe suke se ji take a jikinta ta tab’a sanin Anas a wani gun to a ina ne? Hannu tasa ta rufe fuskarsa tabar daidai wajen idanun nasa, nan kamannin nasa ya sake fito mata sede ta rasa gane a ina ta sansa. Maybe me kama dashi na sani ai wannan girman London yayi nikuma ban tab’a zuwa chan ba, theres no way zamu tab’a had’uwa. Ta tunatar da kanta a zuci.
D’an k’ara ta sakar sakamakon zogin da cinyarta na dama ke mata ta inda kan Anas yafi nauyi. “Anas” ta sake kiran sunansa.
“Uhmmm” yayi groaning cikin sautin bacci.
“Anas ka koma kan pillow naka kaji? Cinya na ya soma yin tsami.” Shiru yayi dan bema jita ba daidai kunnensa ta matso “Anas” ta kira sunansa.
“Fannah let me sleep mana kinji?”
“Toh Anas cinya na zafi.”
“Please...”
Badan tanaso ba ta amince. Gashin kansa take ta wasa dashi har gwada kitsawa take sede da ya kitsu se ya warware dan santsi ba kamar ta ta me uban tauri ba gara ma ace in tayi stretching. Chan cinyar hagunta ma yasoma ciwo. Hak’ura kawai tayi batasan seda ta fara gyangyad’i ba da taji zata fad’i seta farka ai haka bacci b’arawo yasata gaba batasan lokacinda ta fad’a kan Anas ba, kayinta kan nasa a yayinda nasa ke kan cinyarta. Bacci sosai duka sukeyi cikin kwanciyar hankali.
******
Se 2:30PM Anas ya tashi ko Sallah basuyi ba. Ji yayi nishin mutum a kansa gakuma alamun gashi kan fuskarsa wanda yanada tabbacin ba nasa bane. Hannu yasa yana tattab’ata har ya gano mace ce a kansa kuma Fannah ce. How comes? Ya tambayi kansa, nan ya tuna duk wani abinda ya faru. Gosh no! Why do I have to tell her? What if ta gane na tab’a raping wata a rayuwa na? God help me. Duk wannan magana da yake a zuci yayi su.
“Fannah” ya kira sunanta. Bacci take har yanzu bata ko motsa ba, “Fannah” yasake kira yana jijjiqa ta danko motsawa ya kasa duk nauyin ta na akansa. “Fannah wake up” nanne ta d’an bud’e ido. “Wake up kinji? Bamuyi Sallah ba.” Firgit ta tashi daga kansa tana sosa ido ita kanta batasan ya akayi ta fad’a jikinsa tana bacci ba.
“I’m sorry” tace masa.
“I too” ya miyar mata.
“You are sorry?” ta tambayesa cike da mamaki “for what?”
“For ealier, for making you cry.” Dad’i taji iya dad’i atleast koda be fito fili yayi spelling mata SORRY ba ya kwatanta.
“You are no more mad at me?”
“Yes I’m not, also nagode.”
“For...?” Ta tambayesa.
“For letting me sleep on your laps.”
“Ohh! bakomai you had a dream.” Shiru yayi kamar be jita ba dan bayyason ta tono da maganar. “Muyi Sallah first lokaci ya wuce.” Tsam ya mik’e ya nufa bayi ko motsawa Fannah batayi ba as se mik’a take. Bayan yafito yace, “you are next” tare da jawo wata bak’ar jallabiyansa yasa.
Ai tana gwada mik’ewa tasaki wani irin wahalallen k’ara cike da azaba da sauri ya nufo inda take. “Fannah whats wrong?” Take idanunta suka cike da hawaye. “Meneh?”
Cinyarta kawai take nuna masa se yanzu ya tuna time da take ce masa cinyarta yayi tsami yak’i tashi, seyaji guilty gabad’ai.
“Dan kwanciyan danayi akai ne koh?” Ya tambayeta cikin wani irin salo cike da tausayi. Hawayen nata yasa hannu ya share mata. “Don’t worry zafin ba sosai bane just help me in mik’e.” Da ya gwada mik’ar da ita seta saki k’ara, tausayinta sosai yaji ya kama sa musamman ma ya tuna shine sanadi, besan lokacinda bakinsa suka furta “ *I AM SORRY* ” ba. Words data juma tana jiran ranan da ze furta mata su se gashi yau yayi. “Anas karka damu I’ll be fine.”
“Taya barin damu ba bayan nine sanadi.” Da k’yar ya iya mik’ar da ita ya takata har zuwa bathroom d’in sannan yafito bayan data gama abinda zatayi ta kirasa yazo ya taimaka mata ya fito da ita tayi tayi ta fito da kanta amman takasa, ko yatsa ya tab’a cinyoyin nata zafi suke mata. Anas yayi tabari ya d’aga ta tak’i wai abin kunya ne taya da girman ta ze d’aga ta. Bayan ya tada Iqama ya juyo yana kallonta, yadda take ta yamutsa fuska cike da azaba. “Zaki iya yin Sallar a tsaye?”
“Eh don’t worry, lets pray.” Har hawaye seda ta zubar acikin sallar musamman suka zoyin sujjada da zaman tahiya. Bayan da suka idar ya juyo yana kallonta nan ya karanchi tayi kuka. Cikin akwatinsa ya nufa ya zaro wani man muscle pain killer ya nufo inda take. Kallonsa take cike da rashin fahimta. K’afanta d’aya yaja a hankali a yayinda ta sakar dawani irin k’ara dan azaba.
“Sorry” yace da ita. Ganin yana k’ok’arin kwaye mata abaya tasa hannu ta rik’e nasa.
“Anas lafiya me haka?”
“Fannah magani zan shafa miki.”
“A cinyan?” ta tambayesa tana zaro ido waje cike da mamaki.
“Eh” ya bata takaicaccen amsa.
“A’a’ahhh!” ta sake baki tana kallonsa. Taya ze gane mata cinya ana zaman lafiya ai ta gwammaci tacigaba da zama da cinyar haka har seda ze sab’e da kansa. Kayan nata ta matse gam a jikinta.
“Fannah me haka?”
“Banaso, kabari ze warke da kansa.”
“Kinga banson sututan banza yaushe nene ze warken? Harfa kuka kikayi da muke Sallah, bari na shafa miki.”
“Anas banaso please ka bari.”
“Dalili?”
“Dalili kuwa itace taya zan kwaye maka cinya na a waje? Gaskia ba kyau kabari kawai.”
“Toh ba mijin ki ne niba? Naga dama ko ba kaya ajikinki zan kalleki amman I’m not interested, cinyarkin ma dan yazamo dole ne. Bring it.” Kafad’a ta buga “o’o gaskia ni banaso.”
“Fannah kinason in miki na k’arfi koh? Ki kawo k’afar, mema zan gani ajikinki wanda bangani ba a waje.”
“Eh ni koma me banaso, kaje kata ganin na karuwai a waje amman banda nawa.”
“Haka kikace?”
“Eh mana taya ana zaman lafiya zan hau kwaye maka cinya na.”
“Okay you want it in a trouble way, you are gonna get it.” Ajiye maganin yayi gefe guda ya rik’o siraran hannayenta biyu cikin nasa guda d’aya...
No comments:
Post a Comment