TANA TARE DA NI... PAGE 82
BY MIEMIEBEE
Anas besan lokacinda ya fasa glass cup dake hannun saba daga riqo tsantsan wani irin baqin kishin daya tokaresa jin abinda Farouq yama Flowersa, kasancewar fatar jikinsa bame k’arfi bane take glass d’in yamasa kaca-kaca da hannu. K’ara Ummie da Amal suka sakar ayayinda Abuu da Shettima sukayi kansa suna tattara broken glasses d’in. Idanunsa take sukayi wani irin wawan jaaa a yayinda zuciyarsa ke wani erin tafasa.
Amsar wayan Farouq yayi daga kunnen crying Fannah “Mr. Fauzi kaji ka gaskata zance na?” Cikin wani erin muryar da ban tab’a sanin Anas dashi ba yayi maganar “Farouq kaji na rantse I WILL KILL YOU WITH MY OWN BARE HANDS kawai kajira had’uwa na dakai.”
“Hohoho!!! Kafin ka kasheni nikuma zana kashe maka Flower I have to go kasan akwai aikin abortion gabana” yana kaiwa nan ya katse wayar koda Anas ya gwada kiransa back cemasa ake the number does not exist kasancewar Farouq ya karya sim d’in yakuma kashe wayar gabad’aya ya cire battery bare sake amfani dashi ba gudun kar ayi tracking nasa down. Haka yayi da wayar Fannah ma ya cire sim nata ya karya yakuma kashe wayan. Wasu erin zafaffun hawaye ne suka soma sauk’o ma Anas akan kumatu. Waje Ummie tayi da Amal ganin Anas na kuka again. Daidai Abuu ya bud’e baki zeyi magana kenan wayar Anas ya soma ruri Abuu nakai dubansa yaga Mami. Kafin ya d’aga ya kalli Anas ganin ko kad’an hankalinsa bai jikinsa ya d’aga wayar kawai.
“Hello Maman Fannah.”
“Assalamu Alaikum” tace.
“Wa’alaikis salam Abban Anas ne.”
“Ayyah ina wuni?” Ta gaishesa.
“Lafiya alhamdulillah” ya amsa.
“Ya kowa da kowa?”
“Duk k’alau.”
“Masha Allah nace ko Anas na kusa inason muyi magana ne da Fannah nayita kirar wayarta bata d’agawa.” Zuciyarsa yaji yayi dum! Ya buga yama kasa magana.
“Hello...?”
“Maman Fannah inason ki saurareni dakyau dan Allah kuma kisani muna kan bakanmu na neman Fannah baramu tsaya ba semun sameta.” Gaban ta taji yayi mumunar fad’i.
Bayan salatin data sakar cike da tashin hankali tayi k’arfin hali tace, “Abban Anas meya samu ‘yata dan Allah?”
“Ki kwantar da hankalinki please, ‘yar ki Fannah ta na wajen Farouq yanzu haka as we speak...” Nan ya kwashe labarin komai yabata. Salati take alokaci guda idanunta suka ciko da hawaye.
“Yaushe Farouq da mahaifinsa zasu fita harkar Fannah subarta taji dad’in rayuwa? Me tayi musu?” Hak’uri Abuu ya riga bata sannan daga bisani ya katse wayar.
“Anas ka kwantar da hankalinka kaji?”
“No Abuu I can’t.” Ya fad’a rai a b’ace. Hannunsa daya yayyanke Shettima yayi yunk’urin tab’awa “don’t touch me Shettima just leave please both of you dan Allah kufita min a d’aki am sorry please.” Kai kawai Abuu ya girgiza he understands exactly what his son is going through.
“We will Babana zamu bar maka d’akin just behave yourelf, Shettima mu fita.” Nan suka fice, hankalain Shettima ya matuqar tashi kasancewar yasan halin wan nasa sam be iya rungumar k’addara ba tsoronsa kar Anas yakoma shaye shaye irin na da. Bayan ficewansu Shettima Anas ya miyar da kallonsa kan hannunsa me zuban jini alokaci d’aya ya miqe yashiga bathroom sabon spirit ya bud’e ya bulbula kan hannun nasa k’ara ya saki sosai dan sharp pain dayaji,gritting teeth nasa yake dan azaba idanunsa matse gagam.
“Atleast I can feel kad’an daga cikin pain da kike feeling Flower, atleast you are not alone in this, atleast zan iya feeling koda half of your pain.” Fuskarsa ya d’ago yana kallon mirror instead yaga fuskarsa se fuskar Fannah kad’ai yake gani ciki, tunaninta duk yabi ya mamaye masa k’wak’walwa. Da tunanin abinda Farouq ya sake hitting masa k’wak’walwa kuwa besan a lokacin da ya shure kwalabai da robobin mayukan shafe-shafe da suke kan counter d’inba.
“Fannah *_TANA TARE DA SHI_* No! he can’t take away Fannah from me, Fannah is mine, Farouq I will hunt you down like an animal.” A fusace yabaro bayin besan a lokacin daya ciro wani dogon kara daga k’ark’ashin gadon sa ba yasoma fashe fashe daga kan TV, dressing mirror, hanged mirror ba abinda be fasa ba. Abuu dake parlour ne jikinsa yabasa ba lafiya ba agurguje ya bud’e k’ofar d’akin ya tarar da Anas d’auke da wuk’a yana kan tsaga tafin hannunsa se cize bottom lips nasa yake cike da azaba amman hakan be hanasa cigaba da gudanar da abinda yakeyin ba.
“ANASSSS!!!!” ya kira sunansa diabelievingly a yayinda su Ummie ke bayansa suna sakar da salati kansa Abuu ya nufa ya tsinka masa mari tas kukeju take Amal ta b’uya bayan Ummie. “Bakada hankali ne iyyeh? Whats all this?” Yayi maganar yana k’are kallo wa mess da Anas yayi wa d’akin.
“Ina ka kai hankalinka?” Hannu yasa ya k’wace wuk’an. Se anan Anas yayi magana;
“Abuu give me back kabani please, be kamata inbar Fannah kad’ai tana shan wahala ba kabani wuk’an kaga se muna feeling pain d’in tare.”
“Anas get your senses together kanajina koh?! What nonsense. Nasan wannan abu ne meh wuya amman hak’uri zakayi kamar yadda nayi nima da Ummiminku ta tafi ta barni, balle ma kai ba tafiya Fannah tayi ba kidnapping nata akayi kuma in shaa Allah zamu sameta meye amfanin wannan abubuwan da kakeyi iyyeh? It has to stop!” Ummie ce tasa baki;
“A’a Ya Ibrahim kamishi uzuri, wannan tsaka che me wuya shi kad’ai yasan yadda yakeji kaima kasan how it feels like. In zaku bani dama kufita ku barni dashi” nan ta k’ariso cikin d’akin da Amal biye da ita batare da Abuu yace komai ba yafice haka Shettima ma. “Amal kema bisu.”
“No Ummie please kibarni in zauna da Ya Anas” dagudu taje ta rungomoshi tana hawaye. “Ya Anas in shaa Allah zamu samu Fannah wannan mugun Farouq d’in bare mata komai ba, bare mana harming baby ba because we love our baby ba?” Sam be amsata ba kai kawai ya gyad’a mata daga baya a hankali nan da nan Ummie ta gyara masa kan gado suka hauro dashi ita da Amal. D’akin tashiga tattarawa ayayinda Amal ta aza kan Anas a cinyointa tana shafa gashin kansa a hankali bayan ta tare jinin dake d’iga daga hannunsa da tissue. Bayan Ummie tagama kimtsa d’akin ta taho da bowl d’auke da towel ciki d’an k’ananun yankan da Anas yajijji a jikinsa agarin fashe fahsen dayayi dakuma yankan dayaji wa kansa ta goggoge tayi treating masa cikin k’ank’anin lokaci ta kimtsa sa.
“Zakaci abinci Babana?” Ta tambayesa shiru yayi be amsata ba hakan ya tabbatar mata baya jin yunwa. “Amal taso mu basa waje kinji?” Seda ya bari Amal ta mik’e sannan ya rik’e hannunta “ki zauna kinji Angel, don’t leave me too.”
“Ya Anas I will never leave you *_INA TARE DA KAI_* kamar yadda Ya Fannah ma take *_TARE DA KAI”_* calming and soothing wors masu kwantar da hankalin d’an Adam Amal ta riga furtawa yayanta tana sake tabbatar masa dacewa Fannah tasa ce kuma zasu same ta, shi ya jasu sallan isha sam yak’i barinta ta fita daga d’akin cemata yayi a d’akin yakeson ta kwana ita akan gado shi kan couch***
Baa tare da b’ata lokaci ba Mami tasamu Baba ta gaya masa halin da ake ciki hankalinsa yayi matuk’ar tashi tuni Afrah da Aiman suka soma kuka Mami na mara masu baya. Ya Khaleel Baba ya kira sam munafikin Allah ya nuna masa besan halin da ake ciki ba ce musu ma yayi rabonsa da Farouq sati d’aya kenan yanzu.
Suna gama wayar ya kira Farouq ya sanar dashi. Dariyan bosawa Farouq ya sakar “barsu Baba basuda hankali ne karka damu inada miliyan 2 yanzu sauran miliyan uku daga nan se muyi proceeding plans namu”
“Kayi daidai Farouq danko Fannah taka ce tun kana d’an yaro kake santa.”
“Maganar ka dutse Baba will get back to you later” nan ya katse. Maido da kallonsa yayi kan crying Fannah cike da azaba ya d’agota daga saman hannunta, mijinki is trying my patience you will have to bear the burden janta yayi zuwa d’akin d’azu tana had’asa da Allah amman ko sauraronta beyi ba d’aureta ya kuma yi sede wannan karan be toshe mata baki ba. Wani samsung S5 yaciro ya d’auketa hoto sannan yabi ta whatsapp yayi sending takan Anas yasan sarai Anas ba shiga whatsapp zeyi ba dan haka yamasa sending SMS
_Hurry! Smart guy and check in your whatsapp_
Amal ce ke kusa da wayar alokacin da saqon ya shigo.
“Ya Anas you have a new message.”
“Barshi Angel am not in the mood.”
“Ya Anas inkuma ya shafi Ya Fannah fah?” jin ba k’arya a magananta ya miqe tare da amsar wayar bayan ya karanta hankalinsa ya sake tashi fiye dana da ba tare da b’ata lokaci ba yayi enabling cellular connection first message da yayi popping up ya bud’e ganin pictures na Flowersa hannaye da k’afafunta a d’aure kansa yayi wani erin mumunar bugawa, hannu yasa ya dafe kan nasa ta gefen migraine d’in. Cike da tashin hankali Amal ta matso kusa da shi tana dafe sa, “Ya Anas mene ne? Meya faru?” Kasa koda furta mata ‘A ’ yayi.
Ba tare da b’ata lokaci ba yakira layin karap Farouq ya d’aga. “Hello smart guy now what? Zakayi as I say kokuwa I need to let her suffer some more?”
“Farouq please let her go ka saketa dan Allah kai bakasan darajan ‘ya mace bane? Musamman ma me d’auke da juna biyu?”
“Bansani ba kuma banason sani do as I say and I will let her go.”
“You filthy son of a b*tch what the f*ck do you want? Meh kakeso?! ” Amal dake a gefensa seda taja da baya tsabagen firgita datayi dan kalan tsawan da Anas ya daka.
“Zamuyi magana if you are ready, I’m hanging up.”
“Kafad’a min meh kakeso and let her go.”
“Miliyan uku nakeso... For now.”
“Are you crazy Farouq?”
“Yes I am, zakayi transferring kud’in kokuwa haka kakeson Fannah ta kwana?”
“I will zanyi please ka saketa please.”
“Ka turon kud’in first.”
“Nace zan maka sending ka sake ta please.”
“Senaga alert” nan ya juyo yana kallon Fannah dake ta kuka ba sauti. Fuskarta ya shafa “Farouq please kadena tab’ani banaso.” Maganarta har kunnen Anas.
“Farouq me kake mata? Kadena tab’a ta please.”
“Meh aciki dan na tab’a wifey na?”
“Kai wai bakasan tab’a macen da muharramarka haramun bane?”
“Bansani ba kuma banason sani send me my 3 mil and I will let go your wife.”
“Son of a b*tch” cewar Anas sannan ya katse wayar nan da nan yama Kacallah magana aka mai transferring kud’in. Kacallah na sanar da Anas yayi transfer d’in yakira Farouq back sede sam layin yak’i shiga kodaya gwada trying na Fannah ma haka, hankalin Anas in yayi dubu be tashi ba he can’t wait gobe a fara investigating, fatan ranan had’uwansa da Farouq kawai yake.
****
“Mijinki d’an Amanah Fannah har ya turo kud’in” cewar Farouq alokacinda yake since mata hannu. “Muje muci dinner.”
“No way! Ya Farouq I have to pray first.”
“Ba matsala zaki iya yin duk wani abinda kikeso tunda mijinki ya cika min buri.”
“Burin meh?” Ta tambayesa tana shafa hannunta daidai wajen daya d’aure har seda yayi pink.”
“Karki damu sooner zan sanar dake shiga kiyi alwalan ina jiranki.” Tsuka taja sannan ta shige bayan tafito ta had’a Maghrib da Isha yana zaune yana jirarta ko ajikinsa ma beyi Sallah ba, bayan ta idar yajata da hannu zuwa dining room nasu achan sukayi having dinner.
“So wifey time to sleep koh?”
“Kamar ya time to sleep?”
“Ya kike kwana da Anas?”
“Ya Farouq shin wai bakasan Anas miji na bane? Kaikuma ba muharrami na bane saboda haka barin had’a kwanciya dakai ba.”
“Kinsan me nafiso? Nafison kina fighting d’ina haka ‘cause it gives me more and more reasons to fight you down, dani zaki kwana ko kinaso ko bakiso.” A fusace ya miqe ya doso gabanta tare da miqar da ita da hannunta. Hannun nasa ta hau bigewa “ka sakeni Ya Farouq let me go.” Ko saurarenta beyi ba haka yajata sama zuwa d’akin daya tanadar masu akan gado yayi wurgi da ita. Kuka take sosai. Kayan jikinsa ya hau cirewa boxers zallah yabari.
“Ya Farouq dan Allah na had’aka da Allah kayi hak’uri ka kaini wani d’akin in kwana dan darajan manzon Allah.”
“Zaki ajiye wannan mayafin agefe ne kokuwa?” Sake matse gyalen tayi ajikinta ganin batada niyyan cirewa ya nufeta tare da jan gyalen seda ya rabata dashi ihu tahau yi tana kiran sunan Anas. Dukiyar fulaninta ya cafko wani irin k’ara ta saki sannan daga bisani ta tsinke sa da marin da bai expecting ba. Cikin kuka take maganar “bakada hankali ne Farouq?” Yau ko yayan ma babu. “Wallahi the next time ka gwada yunk’urin tab’ani I wont hesitate to kill you mugu, azzalimi maras imani kawai wanda besan darajar mace ba Alla-” bata k’are maganar ba ya kawar da ita da mari.
“Ni kika d’aga hannu kika mara dan fitsara? Sa’arki ne ni? You are asking for it.” Hannunta ya ja be tsaya ako ina ba se wani d’akin da ba komaj ciki banda uban duhu da poles guda uku ciki. “Ya Farouq ka sakeni mugu, azzalimi kawai ka sake min hannu” wani marin ya sake kai mata anan seda gefen bakinta ya fashe. A k’asa kusa da d’ayan pole d’in ya yasar da ita sannan ya d’ago wani thick igiya ya d’aure mata hannayenta duka biyu daga baya ihu sosai ta rigayi dan yadda ya matse mata hannayenta bibbiyu a bayan pole d’in sannan ya k’ulle da k’arfi gabanta ya sha ya k’ulle k’afafun ma sannan ya matso da fuskarsa gab da nata bata bar kukan ba har yanzu “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri ka sakeni please.”
“Mu kwana lafiya kikace min a’a ba? Haka anan zakiyi spending night naki alone in this room.” Nan zuciyarta yawani buga tunda take bata tab’a kwana ita kad’ai ba se yau ita ina ma d’aki ne me fasali da dasauki.
“Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri.” Fuskarta ya riqo sannan yasoma laluban lips nata dawuri ta maqesu chiki haka yatayi amman tak’i barinsa yayi kissing nata, daya gaji ya d’auko cellotape ya manna mata a bakin “sleep tight wifey” yace mata tare da kashe wutan d’akin wani erin baqin duhu ne ya ratsa cikin d’akin alokacinda ya bankad’e k’ofar. Kuka take sosai tana ta murza hannayenta ko zata iya sinche igiyiyin amman takasa haka yadda taga rana taga dare seda gari ya soma wayewa ne tasamu wani wahalallen baci yayi awon gaba da ita.
Shegen se 9:30AM ya tashi ko Sallah baiyi ba, bashin da ake binsa jiya ya sauk’e Asuba da Azahar kad’ai sauran se anjima in ya samu time. Bayan yayi wanka ya shirya cikin black top da jean trousers sannan ya nufa d’akin Fannah har a lokacin bacci take, tsugunawa yayi a gabanta fuskarsa d’auke dawani murmushin tsiya. Ba abinda yake kalla a fuskarta banda lips nata tsabagen k’azanta ko brushing Fannah batayi ba amman ahakan yakeson yayi kissing nata. Fuskarta ya shafo a hankali ganin batako motsa ba ya sake matsoda fuskarsa gab da nata ta yadda nishinsu ki tinkling. Abu k’iris ya rage yayi owning lips nata ta bud’e idanunta lokaci guda. Wani irin nishi taja tare da warwaro idanunta, baya yayi kad’an alokacin dayaga ta maqe lips nata.
“Good morning wifey da alama you had a wonerful night” ya k’are maganar yana since mata igiyoyin. Ganin batada niyyan masa managa ya cigaba “muje kiyi wanka ina neman shawararki.”
“Kayi duk abinda kakeso daman ka tab’a neman shawara na game da abu?”
“Wifey mesa kike min haka ne? Kullum bakida abinyi banda fad’a dani mijinki?!”
“Niba matarka bace kamar yadda kaima kake ba mijina ba.”
“Nasani ai shiyasa nakeson muyi aure, auren sunnah.” K’irji ta dafe “aure? Ya Farouq dan Allah ka rufa min asiri taya zaka aureni bayan inada igiyan aure akaina??”
“Wannan duk ba komai bane, zamu bar Nigeria zamu koma ko Ukraine ko Ghana seki zab’i k’asan da kika fiso.” Hawaye ne suka soma ambaliya kan fuskarta... durk’ushewa tayi har k’asa a gabansa jin ya ambaci barin k’asa gabad’aya.
Rok’ansa ta soma “Ya Farouq dan girman Allah kayi hak’uri dan soyayyar da kake ma manzon Allah kayi hak’uri kaji k’aina karka kaini wani k’asa daban karka rabani da iyayena dan Allah Ya Farouq...” Ta k’are maganar cikin sautin kuka.
*Ina me baku hak’uri da posting da bana samunyi kwana biyu my phone is having a problem, ku k’ara hak’uri I love you guys so much*
*© MIEMIEBEE*
beeenovels.blogspot.co.ke
9 comments:
Hmmmm thanks dear
Haba farook this is too much let anas kidnap yaya khaleel baban farook every body have a weakness his father must be his weakness too
I hate farouq passionately 😭 Allah sarki fannah💕 keep the good work miemie🌹
Ni kaina that's what I believe. If they don't get his fathere there's no way za a samu Fannah
Hmmm
I don't know wat to say at all
why Anas????? go and catch his f**k father too ....that's the only way to bring your flower back to in easy way
Faruq ya taka rawar gani he had his time sauran kiris ya gama nashi har ya fara ban tausayi don definitely zai kamu
Gaskiya his father za su kama Zai fiti
Post a Comment