Wednesday 14 November 2018

RANA D'AYA!

BY MIEMIEBEE 
PAGE 47


   LAST AND FINAL CHAPTER DEDICATED TO EVERY SINGLE READER ❤️ 


    "Toh kai Afzal haka akeyi ne? Ka rik'e 'ya tun d'azu ka hana mu kakanninta rik'e ta?" Mami ta fad'a cike da wasa wanda hakan ya sanya su duka dariya a wajen. 

   "Mami sai de fa kuyi hak'uri dan wallahi duk yadda naso bayyana muku kalan farin ciki da walwalan da nake ciki a yanzu ba ganewa zaku yi ba, dan murna har gani nake kaman mafarki nake, I can't believe that this beautiful here is my daughter and that Amal is her mother, Alhamdulillah Allah abun godiya."

  "Tabbas Allah abun godiya ne Afzal" Mummy ta sanya baki.

  "Thank you Amal, Allah miki albarka."

  "Ameen Yaya" ta amsa da wahalallen dariya, tana wasa da canular'n dake hannunta. 

  "Toh shin za ayi wa Nazeefar tamu alkunya ne ko da Nazeefan zamu na kiranta? Naga ku iyayen zamani yanzu haka kuke yayi." Mami ta kuma tambaya inda Mummy ta gyad'a kai in agreement. 

  "Yaya?" Amal ta kira Afzal da ya kafa wa 'yar nasu ido ko kyaftawa ba ya yi. "Yaya?" Ta sake kiransa se anan ne ya amsa gabad'aya hankalinsa yayi nesa da shi. 

  "Na'am Rania?" Ya amsa yana d'ago kai. 

  "Baka ji Mami ba?"

  "Sorry meney?"

  "Za'ayi wa Nazeefah alkunya kokuwa?"

  Murmushi mey alfarma ya saki sannan yace, "Rania ni ai se abinda kikace."

  "But Yaya I'm asking you now."

  "A'a nikam se abinda kikace, don baze yi ace bayan wannan gaggarumin kyauta da kika mun in sake cewa ga abinda nake so ba, this's your moment live in it, idan kina son mu sanya wa Nazeefah alkunyan fine se mu nemi mey dad'i mu sa mata in kuma a'a we all good banida matsala." Kewayawa Mummy tayi ta kalli Mami cike da jin dad'in amsan da Afzal ya bada, inda itama ta juyo tana kallonta suka sakar wa juna murmushi. A gaskiya Allah ya amsa mata addu'an da ta dad'e tanayi wa Amal tun tana 'yar yarinya na cewa Allah ya bata miji nagari wanda ze darajata ya kuma kula da ita fisabilillah. 

  "Tuna mun wannan suna da kace yana maka dad'i."

  "Wanne d'aya?"

  "Wannan da muka gani a cikin littafi ranan."

  "Wai NIHAL?"

  "Yes shi why not muyi mata alkunya da shi you once said you like the name."

  "I really do but are you sure? In be miki ba, ba semun sa ba."

  "Of course Yaya duk wani abinda yake maka dad'i nima yana mun ko Mami?" Ta kewayo tana kallon Mami da murmushi d'auke a fuskanta. Murmushin Mami ta mayar mata had'e da amsawa "Eh Baby."

  "Toh kaga se mu sanya mata shi ko?"

 "Thank you so much Amal, Mami har yau bansan da wani bakin zan yi miki godiya ba na tarbiyyattar da Amal da kikayi kika raineta har izuwa lokacin da na zo nayi muku wayo na d'auke ta" dariya suka sa sannan ya cigaba "Allah ya sak'a miki da mafi alkhairi da ke da Papi gabad'aya."

  Mami na murmushin jin dad'i ta amsa da "Ameen. So kun yanke shawaran kenan yanzu? Nihal zamu na kiran jikar tamu da 'yar uwata?"

  "Yes Mami" yayi saurin amsawa. 

  "Toh Abban Nihal baka sanar damu ma'anar sunan ba" fad'in Mummy. 

  "It means gratified; delighted; happy; prosperous; and a blissful person just like she truly is."

  "Masha Allah gaskiya sunan yayi ma'ana Allah d'ayyiba ya raya mana Nihal" ta kuma cewa inda duk suka amsa da ameen. Mami ta cigaba "Duk yadda zan so cigaba da zama anan in kula da Nihal hakan baze yiwu ba yau girki na ne ko tukunya kuma ban aza ba, ni zan wuce Mummy seta bi ki kin gane?"

  "A'a baza ayi haka ba 'yar uwa" Mummy tayi saurin katseta. "Jikar fari ce fah? Ku ku tafi ni se in koma gida in yi ma Alhj girkin karki damu."

  "Wayyo 'yar uwa kin tabbata?"

  "Kar kiji komai Allah ya raya mana Nihal."

  "Ameen ya Rabbi kai nagode sosai sakillahu bil jannah."

  "Ameen wa iyyaki kuje idan na gama girkin se na sa a turo muku naku had'e da kayakin ki kema kokuma yanzu ina zuwa in had'o miki kayakin se insa driver ya kawo miki, wanne kika ga ze fi?"

  "Kinga dad'in da muke gida d'aya yanzu ko? In zaki iya had'a mun a yanzun nake ga zefi ga key na site d'ina nagode sosai."

   "Toh shikenan bari inyi sauri in had'o miki" ta amsa had'e da kar6an key d'in. 

  "Ermm Mummy?" Afzal ya kirata. "Na'am?" Ta amsa. 

  "Kiga ba sekin yi wani wahalan kawo abinci ba already munyi waya da Ummi tace zata kawo abincin so don't worry. 

  "Ji min d'a, ladan ma se mahaifiyarka ce kake so ta samu wato ko?"

  "Toh ai dukanku mummies d'ina ne Mummy" ya amsa yana dariya. 

  "Toh shikenan breakfast de gobe ni zan kawo ka fad'a mata na rigata."

  "Toh ba matsala Mummy thank you."

  "Yauwa barin wuce toh, mai jego sena shigo gobe ko?"

   "Toh Mummy thank you ki gaishe da gida." Har waje Mami tayi mata rakiya had'e da tuna mata kayakin da take so ta tattaro mata sannan ta dawo ciki. In less than an hour bayan kayan Mami sun iso aka sallami su Amal suka komo gida bayan tabbatarwa da likita yayi da ita da Nihal suna cikin k'oshin lafiya. Wanka me kyau Mami tayi ma Amal da kanta sannan ta had'a mata tea mey kauri ta sha dan samun ruwan nono. Afzal ko na zaune a parlour se pictures yake tayi wa Nihal chan idan ta fara kuka ya bata ruwan zamzam da suka tanadar. 
   Bayan Amal ta gama shiri Mami ta kira Afzal ya kawo Nihal dan a shayar da ita. Mutumiyar ku kam ta cire mama ta shayar da 'yarta ta kasa se tayi kaman zata sa mata a baki seta fasa, kan Mami da Afzal ne ya gama d'aurewa. 

  Chan Mami da ta kasa hak'ura ta tambayi ko lafiya "Ya haka Baby?"

  "Babu" ta amsa k'asa k'asa cike da kid'imewa. 

  "Toh ki bata mana baki ji tana kuka bane?"

  "Zan bata."

  "Toh mey kike jira? In taimaka miki ne?"

  "A'a zan iya zan iya" ta amsa cike da tsoro. 

  "Toh muna jiranki." Setayi kaman zata sa mata a baki seta fasa. "Wallahi Baby zan sa6a miki me ke damunki wai?"

  "Mami wallahi zafi zeyi, baki ji yadda yayi tsami ba, rik'e shi ma haka da nake zafi yake mun" Baki Mami ta hangame tana kallonta cike da d'umbun mamaki, Afzal da ya san kayansa kam se kad'a kai kawai yake. Ance aure na sa hankali toh ga har Amal tasa ta haihu amma shagwa6a da rashin hankalin nan nata na nan har yau, Allah taimake shi. 

  "Dan zeyi zafi se baza ki shayar da 'yarki ba? Ke d'in ba hak'ura nayi na shayar dake ba kema?"

  "Toh ai Mami ke kina da dauriya."

  "Kinga bana son shashanci kiba 'yar nan nono ta sha tunda ta shigo duniya fa banda ruwa ba abinda aka sake bata."

  "Ni wallahi zafi" ta sake cewa tana zum6uro baki yayin da ta shiga cika idanunta da k'walla. 

  "Ikon Allah toh wallahi inde haka zaki cigaba se Ummi tazo kuyi jegon tare na tabbata idan itace akanki zaki nutsu."

  "Ya Omri ina ruwanta a sake bata."

  "Ruwa?" Mami ta katseta kafin Afzal yayi magana. "So kike cikin nata ya fashe? Kai kuma Afzal kayi tsaye achan baza kayi mata fad'a bane?" Ta kewayo tana kallon Afzal dake rik'e da feeder'n Nihal a hannu. 
  
  "Zan yi mata Mami, Amal yi hak'uri ki bata kinji?" Ya ce da ita a hankali yana mey nufan inda take zaune. 

  "Aww ma hak'uri kake bata? Lalle kam banga laifin Baby ba kai kake d'aure mata gindi ko ka sata ta bawa yarinyan nan mama tasha ko in kira Ummi tayi mun maganinku duka" tana kaiwa nan ta fice daga d'akin. Se kuka Nihal take Amal na jijjigata, ta kuma bata maman ta sha ta kasa wai ita zafi. A nitse ya k'arisa ya zauna daga gefenta tare da dafe ta. 

  "Baby na?" Ya kirata, kai ta d'ago a maraice da k'walla cike dam a idonta tana kallonsa. Goshinta yayi pecking a hankali sannan yace, "Yi hak'uri ki ba Nihal ta sha kinji? Yi hak'uri."

  "Ya Omri wallahi yayi tsami ta6awa kad'ai nayi ma zafi yake mun" ta sanar da shi a shagwa6ance. 

  "I know sweetheart but kinga Nihal na kuka badan komai ba kuma se don yunwa help her out okay? I trust you na san ki da dauriya."

  "Mu sake bata ruwa zuwa gobe se in gwada breastfeeding nata nasan kafin nan tsamin ya d'an ragu."

  "Babe har zuwa gobe? Idan mukayi haka munyi ma Princess adalci kenan? Yi hak'uri kinji? I trust you I know you can do it" lalashinta yatayi yet still Amal ta kasa sawa Nihal mama a baki ita kuma da gajan hak'uri ta k'i yin shiru. Lalla6ata ya tayi har se da ya samu ta amince, rufe idonta tayi gam sannan shi da kansa ya saita kan Nihal ya ajiyeta, tana kama bakin Amal tasa wani d'ankaren ihun da ya mugun razana Nihal har da shi ma Afzal d'in. Sake nonon tayi ta shiga kuka cike da tsoro kaman ba gobe. Da hanzari Mami ta shigo d'akin a kid'ime se gani tayi Amal na hawaye, ita de ta na ganin shagwa6a yau, a hankali Amal ta mayar da bakin Nihal kai tashiga shayar da ita. Nihal bata yarda aka cire maman daga bakinta ba har seda tayi bacci. 

  Bada dad'ewa ba Ummi ta shigo da abinci, se rawan jiki take ta kasa zama gu d'aya da Nihal duk da cewan barci take, daga ta d'auketa suyi nan se suyi chan. Ita wai tunda take bata ta6a ganin fine baby ba kaman Nihal ba. 

*****

   "Ka ga hoton yarinyar?" Mummy ta fad'a had'e da mik'a wa Daddy wayanta across the table inda ya amsa. "Kaiii masha Allah Amal tayi k'ok'ari ita ta haifi wannan k'atuwar baby'n da kanta."

  "Wallahi ko Alhj da kanta, yarinyar tubarkallah k'atuwa."

  "Gaskiya Allah ya raya gobe in shaa Allahu zamu je mu dubata. Sun sa mata suna ko tukuna?"

  "Eh sunsa Amal ce ma ta sa."

  "Masha Allah ya sunan?"

  "Nazeefah, tayi wa 'yar uwarta takwara amma za ana kiranta da Nihal."

  "Alhamdulillah Alhamdulillah Allah sarki Amal, Allah ya cigaba da yi mata albarka yasa 'yar uwarta tayi koyi da ita."

  "Ameen Alhj wallahi addu'ata bata fin haka kullum."

  "Ya Nazeefar har yanzu tana kan bakanta na cewa baza ta dawo ba?"

  "Eh tun d'azu ma ina trying line nata amma baya shiga."

  "Toh Allah sa de lafiya."

  "Amin."

  "Jameelah zata kwana achan kenan ko?"

 "Eh kasan dake girkinta ne setace ni in taya Amal kwana amma ai kaga idan nayi haka ban kyauta ba tunda de jikarta ce ta farko shi ne nace suje ni zan kula da kai."

  "Hakan yayi Hjy Surayya Uwar gida a gidan Alhj Abdallah, Allah cigaba da yi miki albarka."

  "Kai Alhj ameen kayi ka gama muje ka watsa ruwa ko baka fad'a ba na san ka gaji."

  "Wallahi kuwa kaman kin sani meeting meeting baya k'arewa haka."

 Yana gama cin abincin ta sirka masa ruwan d'umi ya watsa suka kwanta. Washegari da sassafe ta tashi ta shiga had'a breakfast na nan gida da kuma wanda zata kai wa su Amal. Tana cikin aikin ne wayanta dake kan counter ya shiga ruri hannunta ta d'auraye tayi drying a jikin towel sannan tayi sauri ta d'aga duda cewan new number ne ke kira. 

  "Assalamu Alaikum" ta soma da cewa.

  "Wa'alaikumus salam" aka amsa daga d'ayan 6angaren. 

  "Nazeefah?" Ta ambata had'e da sauk'e wayan tana mey duban lamban da kyau. "Nazeefah is that you?"

  "Yes Mummy ina kwana."

  "Wani layi nake ganin kaman Nigerian number? Kin dawo Nigeria ne?"

  "Eh Mummy ina Abuja yanzu haka, zuwa anjima zan shigo in shaa Allah flight d'ina by 2 ne."

 "Toh Alhamdulillah Alhamdulillahi sannu da dawowa Nazeefah sekin shigo."

  "Ya Daddy?"

  "Lafiyashi k'alau me kike so in dafa miki?"

  "Anything will do Mummy."

  "Don't you miss my Eghusi?"

  "I really do Mummy amma bana son saki aiki ne."

  "Karki damu Allah kawo ku lafiya."

  "Ameen Mummy se mun sake waya."

  "Erm Naz-" sede har Nazeefah ta katse wayan. Dama so take ta sanar da ita cewa Amal ta haihu kuma tayi mata takwara but then seta ga it'll even be better idan Nazeefan ta shigo tukuna. She has a feeling everything is going to work out yanzu tunda yanzu ba tare da kowa ya mata fad'a ba ta duba taga ya kamata ta dawo gida. Ohh she can't wait ita da Amal su fara shiri. Nan da nan ta kammala girkin ta kai musu nasu dining, ta kai wa Papi da sauran masu aiki nasu sannan tasa nasu Amal kuma a flask ta shirya komi tsaf sannan ta shiga bayi tayi wanka ta shirya. Har ta gama karyawa Daddy na bacci seda tazo fita ne ta tada shi "Alhj ni zan wuce yaso ko daga baya seka shigo."

  "Ina zakije da safen nan haka?" Ya tambaya yana k'ok'arin bud'e idonshi. 

  "Gidan Amal zan kai musu breakfast."

  "Ba munyi zamu fita tare ba? Ina Abba?"

  "Ya na nan na kai mishi breakfast shima yana kwance yaso anjima seku taho tare naga baccin naka yayi nisa ne Alhj kaman stress yayi maka yawa."

  '"Yata ce fa ta haihu."

  "Shiyasa ai zaka iya zuwa duk lokacin da yayi maka, nasani 'yarka zatayi maka uzuri now go back to sleep idan ka tashi breakfast naka na jiranka akan dining ni na tafi."

  "Toh ki gaishesu."

  "Zasuji ba-bye." Acikin mintina k'alilan driver ya sauk'eta gidansu Amal inda ya shiga da baskets d'in ciki. Kasancewar ba kowa zaune a parlourn seta wuce ciki, ta inda ta jiyo hayaniya ta dosa had'e da yin sallama bakin k'ofan kamin ta bud'e. 
    
   "Yanzu k'ara ruwan sanyi kikayi akan wanda na sirka miki Baby?"
  
  "Assalamu Alaikum" Mummy ta sake yin sallama wanda se a nan sukayi noticing presence nata suka kewayo bakin k'ofan. "Ha'a 'yar uwa yaushe kika shigo? Bismillah bismillah sannu da zuwa."

  "Ya nake ta jin hayaniya haka?"

  "Ina kwana Mummy?" Amal dake d'aure da towel ta gaisheta tana mey k'ok'arin sauk'a k'asa. 

  "A'a 'yata yi a hankali kinsan k'asan ki ciwo ne ba sekin durk'usa ba hakan ma yayi, ina kwana ya jiki?"

  "Alhamdulillah da sauki'i ya daddy?"
  
  "Lafiyanshi k'alau na barosa yana bacci akan cewa anjima shi da Abba zasu shigo, ya jikata?"

  "Ayyah haka yace mun jiya Allah kawo su lafiya."

  "Ina Nihal tamu?"

  "Tana gun Yaya a d'ayan d'akin."

  "Har anyi mata wanka ne? Sannu da k'ok'ari 'yar uwa."

  "Sannu 'yar uwa ai da ma baza kizo ki same mu haka ba sede kizo kiga kowa yayi wanka tsaf amma wannan yarinyar" tayi maganan tana nuna Amal da yatsa "Nakega sede ke ko Ummi ne zaku tayata zaman jegon dan ni kam ta raina ni bata ko shakka na." Mummy na dariya ta tambayi meya faru inda Mami ta shiga irga mata, "yanzu haka ruwan dana sirka mata bayan nace kar ta k'ara na sanyi akai ta kama ta k'ara."

  "Toh Amal ai seda ruwa mey d'umi ake wankan ko so kike jikin ki yayi tsami ya rub'e shi ruwan zafin ai magani ne kar fa ki manta jikin naki du ciwo ne yanzu."

  "Mummy wallahi baki ji d'umin ruwan ba har fa hayak'i yake."

  "Rufa mun baki sangaltacciya kawai."

  "A'a 'yar uwa ke kuwa ya zakiyi ma maman Nihal haka? Kinga maman Nihal yi hak'uri ki shiga bayin kiyi wanka bari in sirka miki da kaina nawa baze kai na Mami zafi ba." Haka da k'yar suka samu Amal tayi wankan ta fito itama Mami ta shiga suka karya sannan Amal taje amso Nihal daga gun Afzal wa Mummy had'e da kai masa breakfast nasa. Sallama tayi bakin k'ofan bayan da ya amsa ta bud'e ta shiga. Tsince akan gado ta samesa da gajeren wando ajikinsa yayinda ya kwantar da Nihal akan k'irjinsa tayi tsit sekace ba ita ta fitinesu ta hanasu barci ba daren jiya. 

   "Toh kuma kinyi tsaye a wajen bazaki k'araso bane ko inzo in kar6e ki?" Yace da ita. 

  "Not at all Ya Omri I just can't believe my eyes, like you two are the most cutest beings I've ever seen."

  "Look at you cute thing come in." Murmushi ta sakar mishi sannan ta mayar da k'ofan ta k'arisa ciki ta ajiye abincin kan bed side drawer sannan ta zauna daga gefensa. "Good morning Ya Omri" ta gaishesa tare da kissing lips nashi a lokaci guda. 

  "Morning my sunshine" ya amsa "You're looking spectacular se kace ba ke kika haihu ba jiya ba, such a strong girl."

  "Kai Ya Omri" ta amsa tana murmushi.  

  "I'm damn serious kinyi kyau and above all you smell sooo good."

  "Thank you Love kai kam dan k'azanta ko wankan ma bakayi ba anyways you're still smelling good."

  "Aww dan ina mana raino kike so ki zageni?" Ya tambaya da d'aurarren fuska. 

  "Haba Sweetheart I was only kidding jazakallah kaji? Ya Nihal? Tayi bacci?" A hankali ya lek'a fuskan had'e da gyad'a mata kai "Sekace ba ita ta cika mu da kuka ba jiya."

  "Toh baku yi mata abinda take so ba ai dole."

  "Kaman ya ba ayi mata abinda take so ba Ya Omri? Ita wai kar in cire maman daga bakinta, a ina aka ta6ayin haka?"

  "Oho de se kiyi hak'uri after all dama nata ne."

  "Toh kawota in kaita wa Mummy she's so eager to see her."

 "Oh ayyah, ehemm before I forget, wai Mami yaushe zat tafi?"

  "Yaushe tazo ko yaushe zata tafi kake tambaya?" Ta sa dariya. 

  "Babe wallahi jiya da k'yar nayi bacci I miss your legs wrapped around me."

  "Same here Ya Omri, I miss sleeping on your broad chest amma ya muka iya? Se na fita daga arba'in Mami zata tafi."

  "What!! Wasa kike amma ko?"

  "Ka zauna anan."

  "Rania wallahi bazan iya ba gaskiya, if only you have an idea how I suffered yesterday alone."

  "Toh Baby ya zamuyi?" Ta tambayesa tana shafa gashin kansa a hankali "Kaman yadda ban iya wankan baby ba kaima na tabbata baka iya ba idan ba Mami wa ze nayi wa Nihal?"

  "Toh ba se ki koya ba, in fact ni zan ma koya."

  "Wa d'in wallahi baza ka iya ba."

   "Toh ke ki koya mana Baby?" 

  "Ni wallahi tsoro nake gani nake kaman zan karyata idan na rik'eta ba kaya a jiki."

  "God help me is just that I miss you Rania."

  "Me too Ya Omri" ta amsa had'e da kwantar da kanta a gefen na Nihal a k'irjinsa.

  "She's so beautiful" ta furta tana wasa da 'yar hannunta. 

  "Just like you" ya amsa had'e da zagaye hannunsa a bayanta. "Kinsan wani abu?"

  "Tell me."

  "Kinsan kin mun wayo ko?"

  "Da nayi meh?"

  "Da Nihal take kama dake ke kad'ai mana, ina laifin ko ido nane ta d'an d'auka."

  "Toh yi na ne Ya Omri? If it was my way ai sede tayi kama da kai tunda de kafi ni kyau."

  "Inji waye na fiki? Besides I was only joking, darling you're the most beautiful being I've ever known amma de ina son second child d'ina yayi kama dani kisan yadda zakiyi."

  "Wa ya fad'a maka ma zan sake haihuwa? Daga Nihal se Nihal."

  "Chab lalle ma! A dalilin mey?"

  "Da nace ka shigo labour room ina k'i kayi?" Tayi maganan tana k'ok'arin mik'ewa. 

  "Sweetheart ba haka bane" yayi saurin fad'a yana k'ok'arin dakatar da ita. 

  "Toh yaya ne? Ni ban ta6a jin inda mata ta kira miji labor room yak'i shiga ba."

  "Shine kikayi zuciya?"

  "Toh bazan yi ba?"

  "Baby ba haka bane I was so scared bana son jin kukanki."

  "But I needed you in there sweetheart."

  "I'm sorry okay? Next time in shaa Allah tare dani zaki shiga."

  "Ba wani next time d'innan daga kan Nihal na gama haihuwa na se inde zaka auro wata."

  "Ba watan da zan auro ked'in de zaki haifo mun masu kama dani har goma."

  "Sannu toh kad'au haihuwan wasa ne?" Cike da dabara ya sake miyar da ita jikinsa "Yi hak'uri baby na yi hak'uri kinji?"

  "Naji toh."

  "Then kiss me."

  "Dalili?"

  "Dama nasan ni kad'ai ke kewarki?"

  "Kaga bani Nihal in tafi nasan Mummy har ta gaji da jirana."
  Mik'ewa yayi ya zauna "you must kiss me first."

  "Or else?"

  "Or else bazan bada Nihal ba."

  "lol ba se inje in fad'a musu ka hana ni ba."

  "Toh kije d'in" ganin ta mik'e dagaske yayi sauri ya cafke hannunta wanda hakan ya sata fad'i kan gadon. Nihal ya ajiye a gefe yayi sauri ya haye kanta yana mata dariyan mugunta. 

  "Yaya mey haka? Ka d'agani wallahi banida lafiya." Wani killer'n murmushin dake tafiyar mata da imani ya saki "Let your dream boy kiss and take your sickness away baby."

  "Nikam ka d'agani Nihal dan Allah ki fara kuka."

  "Ai ita 'yar arziki ce ba kaman ki ba."

  "Au nice 'yar tsiya?"

  "Ni ban ce haka ba" ya amsa yana dariya. 

  "Wallahi Yaya nasan maganin ka, nikam d'agani" bata hankara ba kawai taji sauk'an lips nasa akan nata. Kissing nata ya shiga yi a hankali yana mey tafiyar mata da imani. A sannu a sannu yake kashe mata duk wani sassa a jikinta, Amal bata san lokacinda ta shiga mayar masa da martani ba a garin haka har d'aurinta ya kunce. Knock da suka jiyo daga bakin k'ofan ne ya dawo dasu daga duniyan da suka fad'a a rikice Amal ta ture Afzal daga kanta ta mik'e zaune tana k'ok'arin mayar da d'an kwalinta. "Baby??" Suka jiyo muryan Mami. 

   "Ermm na'am Mami" ta amsa cike da tashin hankali. 

  "Kar6o Nihal d'inne har yanzu?"

  "Ermm ermm na bata nono ne."

  "Ohh toh kiyi sauri Mummy na jiranki."

  "Toh Mami gani nan zuwa." Juyowa tayi ta danna wa Afzal dake ta faman kallonta harara yana wani lasan le6ensa, daga bisani kawai ta kai masa pillow fuska. "God help me! Ni kuma mey nayi?" Ya tambaya yana mata dariyan mugunta. 

  "Ma tambaya na kake ko? Fisabilillahi wani irin abun kunya ne wannan Yaya?"

  "Da nayi mey? Talking as if you didn't enjoy it too."

  "Aww ma haka zaka ce? Zaka gani" kafin tace zata mik'e yayi sauri ya rik'eta "Shikenan ke Rania abu kad'an zuciya."

  "Ni sakeni in d'au 'yata mu tafi."

  "'Yarki ko 'yar mu? Now that aside yi hak'uri Yaya is sorry."

  "Naji sakeni."

  "Kiyi hak'uri mana toh I said I'm sorry."

  "Nace naji."

  "Toh smile" murmushi cike da tsangwama ta sakar masa yayinda ya saketa ta d'au Nihal dake kwance a gefe, har bakin k'ofan yayi mata rakiya had'e placing gentle kiss a kan goshinta "See you around, I love you."

  "I love you too" ta sanar dashi sannan ta k'arasa wajen su Mummy. Bada dad'ewa ba Maamah, da sauran k'awayenta suka zo yi mata barka. Da Azahar Ummi da Abba suka kawo abinci inda Abba ya sawa Nihal albarka, sun kusan tafiya Papi da Daddy suka shigo suma. Wajajen 2:30 Nazeefah tayi wa Mummy waya kan sun iso dai-dai wannan lokaci Daddy suke shirin komawa da Papi dan haka suka ke6e inda take sanar da shi shigowan Nazeefah. Mamaki na sosai Daddy ya sha take suka wuce airpot suka d'aukota. Kuka sosai Nazeefah ta tsaya yi da suka had'u se faman neman tubansu take har suka isa gida. Bayan ta watsa ruwa ta sauk'o ta sami Mummy inda tayi serving nata abinci.

  Abincin take ci amma gabad'aya babu hankalinta a tattare da ita. 

  "Nazeefah lafiya?" Mummy da ta karance ta na d'an lokaci ta tambaya. 

  "Ermm babu" ta k'irk'iro murmushin dole, miyan yayi dad'i I've missed your cookings."

  "Thank you, fad'i tunanin mey kike?"

  "Babu fa kawai naga gidan ne ya canza site na waye wancan? Amaryar Daddy?"

  "Eh na 'yar uwata ce mahaifiyar Amal kuma amaryar Daddy'nku."

  "Oh" ta amsa sama-sama sounding not surprised. "Meyasa Daddy ya had'aku? Kuma harda mahaifinta suka dawo?"

   "Eh we're one big happy family down here, kuma ni na kawo shawaran a had'a mu."

  "Happy?" Ta nanata cike da rainin hankali. 

  "Nazeefah baki tambayi ya Amal 'yar uwarki take ba?"

  "Mey had'i na da ita? Please not this time Mummy."
  
  "Haba Nazeefah na d'au kin dawo saboda kin gano kuranki ne kina son ki gyara tafiyarki ko ba haka ba?"

  "Wani kuskure Mummy? Mey na aikata? I'm not back because of that so called Amal I'm back because I've missed you and unless kina so acikin sati in koma in da na taho zaki daina mun maganan Amal bana son jin maganan da ya shafeta."

  "Uh well tunda kince haka dama ina son sanar dake cewan ta haihu ne jiya ta samu 'yarta kuma tayi miki takwara." Chak ta tsaya da hannunta da take k'ok'arin kai loman tuwo. "What???" Ta tambaya out of disbelief. 

  "You heard me right Amal ta haihu ta yi miki takwara."

  "Ni tayi wa takwara?" Ta kuma tambaya had'e da sakar da wani dariyan rainin hankali "You're always good at telling jokes Mummy but not this time around."

  "Yaushe na zama playmate naki da zan na cracking jokes da ke Nazeefah? Amal ta haihu kuma tayi miki takwaraamma ita da Afzal sunyi deciing zasu na kiran 'yar da Nihal."

  "Mummy kinsan mey kike fad'i kuwa?"

  "Tabbas na sani kinga" tayi maganan had'e da d'ago wayanta kan pictures na Nihal ta kai had'e da mik'a mata "here swipe left ga yarinyar nan." Hannu na k'yarma Nazeefah ta amshi wayan ta shiga kalla da fari ma taso k'aryata komai sekuma taga irin tsan-tsan kaman da baby'n keyi da Amal nan ta sake tabbata da cewa eh 'yarta ce amma kuma se tayi mata takwara? Me ta ta6a yi mata mey kyau a duniya da har zesa tayi mata takwara? Shin Amal bata sane da irin k'iyayyar da tayi mata ne? Shin bata san cewa bayan shaid'an da fir'auna se ita tafi tsana fiye da kowa a duniya ba? Wow! Bata hankara ba kawai taji hawaye na tsiyaya daga d'ayan idonta wanda tayi saurin sa hannu ta goge had'e da mik'a wa Mummy wayanta sannan ta mik'e. 

  "Ya haka lafiya?" Munmy tayi saurin tambaya. Wanke hannunta tayi cikin bowl ta goge da towel ta shiga tafiya ko amsa Mummy batayi ba, tana kaiwa d'akinta ta fad'a ciki ta nufi kan gado inda ta kwanta. Kuka ta shiga yi kaman ba gobe tana mey tsanar kanta na d'aukan tsana da k'iyayyan duniya da tayi ta aza akan 'yar uwarta wanda suka kasance jini d'aya da ita. Ji tayi kaman ta kashe kanta dan irin munanan ababen cutarwan da ta ringa yi wa Amal baiwar Allah. Shin masu halayya irin na Amal guda nawa suke a duniya irin tamu ta yanzu? Ace duk irin sharratayyan da bita dashi amma ita ta sak'a mata da alkhairi haka har ta d'auki sunanta ta sanya wa 'yarta ta fari bayan ga mahaifiyarta dana mijinta a raye? Subhanallah ita kanta baza ta iya yafewa kanta abubuwan da tayi wa Amal ba bale ta soma neman yafiyanta. Gaskiya ne ta cuci kanta a rayuwa, da tun farko ta gane cewa idan abu rabon mutum ne ko ta yaya zai samu idan kuwa akasin hakan ne toh ko ta yaya ya buga baze ta6a samun abun ba koda ya samu ma abun baze yi lasting mishi ba. Da tun farko ta rungumi k'addaran cewa ita da Afzal are not meant to be da batayi hurting one and only sistee nata ba. 

  Tana cikin tsakiyan kuka Mummy ta bud'e k'ofan ta shiga da hanzari ta shiga share hawayenta. 

  "Nazeefah?" Mummy ta kirata had'e da dafe kafad'arta. 
  "Kukan mey kike haka? Tashi ki zauna muyi magana." Ba gardama ta mik'e zaune cikin tsananin kuka tace, "Mummy I've hurt Amal so much, ta ina zan fara bata hak'uri? She really did not deserve everything I put her go through Mummy nayi nadaman abubuwan da nayi mata."

   "Inde Amal ce na tabbata ta jima da yafe miki komai Nazeefah tunda de har ta d'au sunanki ta sanya wa 'yarta bayan ga mahaifiyarta a raye, inspite of everything Amal still loves you Nazeefah."

  "Abinda yafi ci mun rai kenan Mummy, meyasa zatayi mun takwara? Meyasa baza ta tsane ni ba kaman yadda na nuna na tsane ta? Meyasa bazata sak'a mun sharrin da nayi mata da sharri ba? Why is she making me feel like a bad guy?"
  
  "She only did what's right to reunite you guys."

  "Mummy I feel like a total crap ji nake kaman in kashe kaina Amal ta fini ta duk inda nake tunani" ta fad'a tana kuka sosai. 

  "Kar kice haka Nazeefah, life is a competition but we're not competitions amongst ourselves, yadda kike ganin Amal ta fiki da wani abun itama haka take ganin kin fita ta wani fannin, you guys are sisters Nazeefah you learn from each other okay?" Fad'awa jikin Mummy tayi tana mey cigaba da kuka yayinda Mummy ke lalashinta. 

  **** Washegari...
  "Har kin shirya ne?" Mummy ta tambayi Nazeefah dake sauk'owa daga kan stairs. 

  "Eh Mummy good morning."

  "Morning breakfast naki na kan dining."

  "Thank you Mummy ina Daddy?"

  "Ya fita office just a while ago."

  "Ohh kakan Amal fah?"

  "Yana nan zaki je gaishesa ne?" Kai ta gyad'a a hankali, dad'i sosai Mummy taji "sunansa Papi ba Kakan Amal ba kinji?"

  "Naji."

  "Muje in raka ki toh."

***
  Bayan sunyi sallama Papi ya tashi ya bud'e musu k'ofa, a parlour suka zauna inda Nazeefah ta sauk'a har k'asa ta gaishesa. "Ina kwana Papi?" Na sosai Papi yaji dad'i ya amsa da fara'a "Tashi mamana, tashi ki zauna ya karatu? Ya k'are ko da saura?"

  "Ya k'are Papi sauran graduation ne kawai."

  "Toh madallah Allah sanya alkhairi."

  "Ameen Amal tazo ta samu 'yarta kuma."

  "Eh mun samu takwararki."
   
 "Haka Mummy tace, toh Allah ya raya ya d'ayyiba."

  "Ameen ameen."

 "Dama nace barin gaisheka kafin in wuce chan gida in duba Amal kuma in baka hak'uri game da duk wani rashin hankalin da na tafka da a baya, please forgive me."

  "Ba komai 'yata nagode Allah sak'a da alkhairi ya miki albarka komai ya riga ya wuce kinji?"

  "Ameen Papi, thank you so much."

  "Toh Abba bari mu koma" fad'in Mummy har bakin k'ofa ya rakasu sannan ya dawo ciki. Nazeefah na gama breakfast ta jira Mummy ta shirya suka fice. Tun da suka isa gidan gabanta ke fad'i shin idan sun had'u da Afzal zatayi mishi magana ne ko kuwa? 

  "Mummy I can't do this" ta fad'a kafin su shiga ciki. 

  "Sure you can Nazeefah karki ji komai okay??" Kai zallah ta iya ta gyad'a sukayi sallama suka shiga. 

  "Ha'a Mummy sannu da zuwa" cewan Afzal dake zaune a parlour da Nihal rik'e a hannunsa yana mey k'ok'arin tashi. Mik'ewan da yace zeyi sukayi ido hud'u da Nazeefah ba k'aramin fad'i gabansa yayi ba for a second ya d'au ma ko hallucinating nata yake. 

  "Nazeefah?" Ya ambata bayan tsawon lokacin da suka d'auka suna kallon juna da sauri ta kawar da kanta daga kallonsa had'e da gaishesa "Ina yini Ya Afzal?"

  "Nazeefah yaushe kika dawo? Bismillah ku shigo" waje suka nema suka zauna ita da Mummy yayinda ya cigaba da rik'e Nihal. 

  "Jiya-jiya ta shigo" Mummy ta amsa. 

  "Oh ayyah ya karatu? Ya k'are ko da saura?"

  "Ya k'are Amal ta sauk'a lafiya?"

  "Lafiya k'alau Alhamdulillah an samu takwararki" ya amsa had'e da mik'ewa dan kai mata baby'n, a garin mik'a mata ita hannunsa ya goga nata kad'an. Mutuwan tsaye yayi waien yayinda itama tayi freezing inda take zaune, ji tayi duk wani rayuwan da sukayi da a baya suna dawo mata, ta d'au by now tayi moving on, ta d'au koda ta sake sanya sa acikin k'wayoyin idanunta baza ta sake ji mishi wani abu ba ashe ba haka bane, har yau akwai ragowan soyayyarsa a cikin zuciyarta. 

  "Masha Allah she's soo big" ta fad'a tana k'ok'arin 6oye bak'on lamarin daya ziyarce ta. "And soo beautiful ga shi kamanninsu d'aya da Amal."

  "Wane an raba kara" cewan Mummy. Bayan Nazeefah ta d'an rik'eta ta mik'awa Mummy sannan tayi gyaran murya. "Ya Afzal nasan komi ya riga ya wuce amma dan Allah ka yafe mun duk wani abinda nayi maka da wanda na sani da wanda bana sane da shi I'm really sorry."
  
  "Nazeefah there's no need to, mun riga mun zamo abu d'aya yanzu, Allah ya yafe mana gabad'aya Amal will be so thrilled to see you bari inyi mata magana." Knocking yayi bayan an amsa ya shiga a gaban dressing mirror ya sameta zaune tana taje sumarta. 

  "Ya Omri?"

  "Ina Mami?"

  "Wanka" ta amsa. 

  "Come there's something you need to see."

  "Menene? Meya faru?" Lokaci guda hankalinta ya tashi a cewarta wani abu ne ya samu Nihal. 

  "Kede kizo."

  "Yaya please speak up menene ya faru? Nihal ce?"

  "Just come" cike da fargaba ta mik'e tabi bayansa suna shiga parlour ya matsa gefe wanda hakan ya bata daman sanya Nazeefah a ido. Da fari ma k'in amincewa tayi, ta d'au ko wasa idanunta suke yi mata. 

   "Nazeefah?" Ta kira ta cike da k'in yarda. 

  "My sister" Nazeefah ta amsa idanunta suna masu cikowa da hawaye. 

  "Nazeefah kece??" Itama ba shiri idanun nata suka ciko da hawaye. 

  "Yes Amal ni ce" da gudu ta ruga taje tayi hugging nata inda suka fashe da kuka dukansu biyu. Mummy dake rik'e da Nihal itama bata san lokacinda idonta ya cika da k'walla ba. 

  "Amal I'm so sorry please forgive me." A hankali Amal ta janyeta daga jikinta sannan ta shiga share mata hawayen ta, "ki daina neman tuba na Nazeefah, har cikin raina na yafe miki komai duniya wa lahira kukan ya isa haka." Sake rungumeta Nazeefah tayi tana mey sake tsanar kanta na duk wani cutarwan da tayi wa 'ya uwarta. 

   "Amal ban san da wani bakin zan yi miki godiya ba" cewan Nazeefah bayan sun nemi waje sun zauna a gefen Mummy. "Amal you named your first daughter after me, duk kalan mugunta da bak'in halin da na miki hakan be hanaki aikata abinda kika fasa ba, da Mummy tace mun kin yi mun takwara na kasa amincewa sabida kasa gane wace irin mutum ce ke da nayi, instead ki sak'a mun da sharri kaman yadda nayita cutar da ke se kika gwammaci ki sak'a mun da alkhairi, alkhairin da ba kowa ne ze iya yin irinsa ba, Amal I hate myself for ever hurting you please forgive me."

  "Nazeefah komi ya riga ya wuce and I can't tell you how happy I am right now that you're back with us, addu'ata kullum bata fin Allah ya dawo mana dake cikin k'oshin lafiya and here you're in good health and shape Alhamdulillah."

  "Amal thank you so much, thank you."

  "Don't mention Nazeefah kuma dan Allah kibar kukan haka ya isa."

   "Allah ya raya mana Nihal gani nake kaman mafarki har yanzu wai kin yi mun takwara, 'yar uwata guda tayi mun takwra it feels like a dream." Murmushi mey k'ayatarwa Amal ta sakar wa Nazeefah "Ya karatu ya k'are?"

  "Eh saura graduation."

  "Ayyah congratulations Allah sanya alkhairi."

  "Ameen, Naki fah?"

  "Final year zan shiga nima."

  "Masha Allah Allah sanya alkhairi ina Mami?"

  "Tana wanka nakega ta fito yanzu."

  "Muje ki raka ni in gaisheta."

  Da murmushi kwance a fuskanta ta mik'e "Oya tashi muje toh." Afzal ya kasa daina murmushi, all he's ever wanted is to see his Amal happy and ya san ba abinda ze kai mata shiryawa da Nazeefah dad'i se gashi yau Allah ya shirya tsakaninsu, he can't ask for more. 

   Har cikin d'aki gun Mami Amal ta kaita inda suka gaisa sannan Nazeefah ta nemi tubanta na duk wani abinda tayi wa Amal wanda ta san yayi wa Mami zafi, a wajen duk sukayi reconciling. Kusan Azahar Mummy tace zata koma dan yin girki Nazeefah kam tace sam bata tafiya, se hira suke da Amal ta rik'e takwararta a hannu. Chan da zatayi sallah ta mik'a ta wa Amal dan yin alwala, tana cikin yin sallah ne wayanta dake gefen Amal ya shiga ruri lek'awa tayi dan ganin wake kira acewanta ma ko Mummy ce se gani tayi Baby❤️💕🔐 na flashing akan screen d'in da hoton wani kyakkyawan bawan Allah yana nan d'an bak'i da shi attatched to it. Murmushi ta sakar ta cigaba da rik'e Nihal har izuwa lokacinda Nazeefar ta idar. 

   "Wa ya kira?" Ta soma da tambayanta. 

  "Baby" Amal ta amsa. 

  "Oh!" Ta furta tana sunkuyar da kai. 

  "Baza ki kira shi bane?"

  "Ba matsala ko anjima zan kira shi."

  "Wai kunya na kikeji ne? Kinga baza ki shanya mun in law ba haka kawai, d'au waya ki kira shi kice mishi sallah kike, gashi" Mik'a mata wayan tayi sannan ta cigaba da shayar da Nihal. 
Kaman yadda Amal ta bui'aceta tayi ta kira sa back inda ya d'aga a first ring. 
  "Halo Babe?"

  "Belle how're you?"

  "I'm fine Babe? Ya kake?"

  "I also, just that I miss you." So take tace she misses him too amma kunyan Amal take ji "Ermm Babe kasan wani abu? I will call you later okay? Se anjima" bata jira jin me zece ba ta katse. "Iyyeee so tell me who is the handsome looking dude?"

  "Kai Amal kede kiyi focusing a abinda kikeyi kafin kisa nono ya bi mun kan takwarata."

  "Baki amsani ba waye shi?"

  "Wani ne."

  "Your man?" Gira ta d'age mata as yes. "Wow ina kuka had'u? A UK?" Nan ma giran ta sake d'agewa. 

   "Awwn am so happy for you sister tell me about him mana."

  "Nak'i."

  "Pleaseeeeee."

  "Sa'anki d'aya saboda Nihal."   

  "Haha naji ina sauraronki."

   "Sunan sa Ahmad A UK muka had'u naje yin masters d'ina whereas shi kuma PHD. He's a Nigerian, yana zama a abuja yana da aure da yara biyu."

  "Wow I'm really impressed in ba wai kin fad'a ba mutum baze ta6a cewa yana da aure ba."

  "I know right ko ni da ya cemun yana da aure ban yarda ba, ashe wai harda yara biyu, ko da shike auren wuri yayi when he was 22, he had his first son at 24 and his second daughter at 27 he's now 34 years old."

  "Impressive Nazeefah I'm so happy for you wallahi su Mummy sun sani?"

  "Not yet ke na fara sanarda ina son se ya gama karatunsa ya dawo se in yi introducing nashi to the family."

  "Hakan yayi Nazeefah wallahi nayi miki murna sosai ya uwar gidan ta shi? Ya had'aku ko tukuna?"

  "Ya had'amu, ai be jima bama suka je mishi hutu suka komo bari kiga pictures da muka d'auka da ya fita damu outing ranan" tayi maganan tana latsa wayanta "Here you go" amsa Amal tayi ta shiga viewing tana swiping "Goodness he's got such a beautiful family wallahi, da ke da uwar gidan ban san waye gaba a kyau ba gaskiya gata itama very young."

 "Yes she's 28 years old amma kika ganta wane tana early twenties nata."

  "Bata da wata matsala ko?"

  "Sam wallahi yadda kika san kanki haka take tamkar 'yar uwarta haka ta d'aukeni."

  "Such is life Allah ya baku zaman lafiya mey d'aurewa ya sunan yaran nasa?"

  "Fawwas da Fauzah."

  "Masha Allah I'm sooo happy for you sis."

  "Thank you Maman takwara."

****
  Ba Nazeefah ce tabar gidan ba se bayan sallan isha. Haka kusan kullum tana gidan Amal, kafin suna kuwa ta samu ta had'a akwati mey set uku wa Amal biyu na baby d'aya nata. Amal ta samu kyautuka sosai sede ace masha Allah. Seda Mami tayi mata arba'in sannan ta koma gida. 

   Nihal na da watanni uku Amal ta soma shiga school so anytime zata fita school se ta biya gida ta kai wa su Nazeefah raino. Atimes kuma wa Ummi. Da Khaleefah ya dawo hutu kuwa se su had'u suyita fad'a akan Nihal cewa sam d'aya baze ta6a ta ba. Yarinya san kowa k'in wanda ya tasa, ga fara'a ga murmushi, gata very plumpy, gashin kan nan tabarkallah. Haka nan rayuwa ta cigaba da kasance musu cikin kwanciyan hankali da so da k'auna. Na sosai Afzal yake ji da Nihal sau dayawa yakan riga Amal dawowa gida daga office da ya tashi seya biya gidansu Mummy ya amshi 'yarsa su dawo gida ya mata wanka yayi rainonta kafin Rania'nsa ta dawo. 
  Amal could not ask for more, this is indeed a dream she's living. A perfect daughter, a perfect husband and a perfect family. 


  _7 months later..._

    Ababe da dama sun gudana, da izinin Allah su Amal sukayi graduating bata da spill ko d'aya, ta d'ayan fannin ma Nazeefah har taje UK ita da Mummy anyi musu graduation nasu sun dawo. Shima saurayin nata Ahmad ya gama PHD nasa ya dawo gida har Nazeefah tayi introducing nasa wa su Daddy. Maganan da ake yanzu haka sa rana kad'ai ya rage. Kafin nan time to time yakan zuwa Maiduguri ya duba Nazeefah sannan ya koma, ko wani zuwansa kuwa da tsaraban da yake tanadarwa Nihal na musamman takwaran wife to be nasa. Na sosai yake son Nazeefah dan haka yake son duk wani nata tuni ya nemi Afzal suka k'ulla abotaka abinsu. Kullum sede be shigo gari ba se sun sa Sultan da ya kasa yin aure har yau a gaba. Maganan da ake yanzu haka Ahmad ya had'a Sultan da wata cousin tasa, abu kaman wasa wai Sultan ke soyayya. Na sosai yarinyar ta masa bayan ya kwana biyu haka yakan je Abuja ya duba ta. Afzal da Amal kuma sede abinda ya k'ari, soyayya suke zubawa kaman ba gobe sekace jiya-jiya aka d'aura musu aure even though suna d'an ta6a fad'ansu time to time amma hakan baisa sun daina son juna ba da kuma daina son farinta wa juna ba. 

   Yau ranan ta kama Asabar ranar da aka fi sani da ranar d'aurin aure. 

   Amal ce zaune akan dining table da Nihal dake da 10 months yanzu a gefenta tana feeding nata custards, tana sha tanayi mata wasa. Ba ruwanta ta sha nono ta sha madara ta ta6a custards gata nan k'atuwa gwanin sha'awa. "That's girl" Amal tayi praising nata tana k'ok'arin sake kai mata wani spoon d'in baki "shanye se mu tafi unguwa ko? Muje dinner'n Aunty Maamah da na Ya Abdool, ai zaki je?"

  "Dada" ta amsa wane taji abinda aka ce mata. 

  "Na Ya Abdool kikeso? Toh ai duka zamu je ko kin mance a venue d'aya za'ayi?"

  "Dada!"

 "Yauwa Princess d'ina shanye toh se mu tafi" Wayanta dake ruri ne tayi saurin d'agawa ganin Nazeefah ke kira tare da sawa a hands free. 

   "Mamman Nihal"

  "Na'am sis yane?"

  "Ina kwana ya kike?"

  "Lafiya k'alau ya gida ya Ya Ahmad?" 

  "Yana nan d'an wahala yaushe ne ya tafi ba last week ba?"

  "Amal na dariya ta amsa "eh wani abu ne?"

  "Wai ze sake zuwa he's missing me."

 "Shine zaki ce mishi d'an wahala?"

  "Toh mey ne? Sekace baya son kansa dan Allah, shi bai tunanin stress ne ai nakega cewa Fareeda (matar Ahmad) zan kar ta barsa yayi wannan tafiya."

  "Ji min 'ya! Ke baki san cewa garin masoyi baya nisa bane? Ko a tunaninki idan baya sonki zena zuwa ganinki akai akai haka ne?"

  "Toh ai ni tausayinsa nake I don't want him stressed out."

  "Ke bar shi ya d'an d'ana kafin ya kaiki gidansa, kinga fa da zaran kin shiga gidansa se yadda yayi dake."

  "lol toh uwar mugunta."

  "Eh mana enjoy your time while it lasts, kafin ya d'aukeki ya tafi dake."

  "Ya tafi da wa? Ce miki akai zan bishi Abuja?"

  "Yo eh mana" ta amsa tana dariya. 

  "Lallai wallahi anan zan zauna kinsan ni bana k'aunan zaman Abuja, gara nayi zama na anan kusa da takwara ta."

  "Lol toh zamu gani de."

  "Ina takwara ta?"

  "Gata nan ina feeding nata, Nihal ga Aunty Nazeefah kice mata hello."
  "Titi titi" ta soma cewa tana wasa wai Titi ne Aunty Nazeefah. 

  "My baby how are you?"

  "She's fine tana having breakfast."

  "Oh ayyah yanzu tailorn ya kawo mana gowns namu fa."

  "Haba yayi kyau?"

  "Wallahi sosai barin ma na Nihal sekinga yadda d'inkin ya fita."

  "Yaushe zaki shigo toh?"

  "Yanzu idan nayi wanka na karya."

  "Alright toh sekin shigo ki gaishe da kowa da kowa."

  "Zasuji ba bye." Ta kai ga ajiye wayan kawai taci karo da 6arnan da Nihal tayi, goran ruwanta ta kwantar se tsiyaya yake tana kalla tana jin dad'i. 

  "Haba! Haba Princess shikenan ke ba a isa a baki abinci ba se kin miyar da wajen k'azanta?"

  "Rania?" Afzal dake fitowa daga d'akinsu ya kirata, yana sanye da babban riga sky blue da ya sha aiki ya kuma mugun amsan sa ba shakka d'aurin auren Maamah da kuma na Ya Abdool zasa tunda se an d'aura na Ya Abdool za ayi na Maamah a different venue. 

  "Yes Ya Omri?" Ta amsa tana mey d'ago kai don kallonsa. "Dayyumm" ta furta a ranta dan wani irin kyan da yayi. "Kinga sabon cuff links da na siya last tafiyan da nayin nan? I'm running late" sede kaman ba da ita yake ba dan yadda hankalinta yayi nesa da ita. Nihal dake gefenta se faman kiransa take da "Dada" tana k'ok'arin mik'ewa daga kan kujerarta taje ta wajensa. Cike da tak'ama yake takawa har ya k'arisa dining aean, har anan binsa da kallo Amal take. 

  "Rania?" Ya kirata had'e da shafe gefen fuskanta wanda hakan ya sanya ta murmushi. "Ya Omri you look you look..." tama rasa abinda za tace. 

  "Handsome?" Ya d'age mata gira. 

  "Yes you look handsome, masha Allah" tsugunawa yayi had'e da pecking nata "Thanks Babe."

  "Dada Dada!" Nihal ta cigaba da kiransa. 

   "My Princesss" ya mik'a hannu ze d'agata "tukunah bari in d'auraye mata jiki kar ta 6ata maka kaya" murmushi ya sakar mata sannan ya ja kujera ya zauna daga gefeyana yiwa Nihal wasa har zuwa lokacinda Amal ta goge mata jiki ya d'agata. "So Kinga cuff links d'ina?"

  "Wanda ka taho dasu last tafiyan ka?"

  "Yep" ya amsa yana yiwa Nihal dake ta faman dariya wasa. 

  "Muje yana cikin wardrobe naka."

  "Na duba ban gani ba."

  "Kai dama ka iya duba abu ne? Yana nan a ciki muje."

  "Ni d'in ko? Muje zakig" d'akin suka nufa, Amal tayi gaba ta shiga neman pack d'min bada dad'ewa ba se gashi ta fito da shi. "Now tell me what is this?" Ta juyo had'e da tambayeshi. Shiru yayi na d'an lokaci "A ina kika samu? Bade a ciki ba."

   "Da a ina? Here of course" tayi nuni da cikin wardrobe d'in

  "But I j-"

  "Shhh literally Nihal is the only infant baby here but technically there are two babies tunda ko neman abu in ban sa hannu ba baka iya samu, here kar6i inje inyi wa Nihal wanka muma mu shirya." Hannunta ya rik'e kafin ta fahimci abinda yake shirin yi ya janyeta seda ta fad'a jikinsa. 

  "Thank you for handling my crazy ass Babe I love you very much" ya sanar da ita looking deep into her eyes. It's been almost 5 years but anytime Afzal ya sanar da ita cewa yana sonta se bugun zuciyanta ya dad'u. There's no lying, she's immensely in love with him. 

  "I love you much more my very own handsome" ta mayar mishi, adjusting height nasa yayi ready to kiss her, dai-dai lips nasa yazo sauk'a akan nata Nihal ta tsinka mata mari tas a kumatu

  "Wayyo Allah Mami na!!" Amal ta sa ihu Afzal be san sanda yasa dariya ba ganin haka itama Nihal ta bi sa se dariya sukeyi wa Amal. 

  "Nihal kika mareni? Kika mari Mamma? Kai kuma Yaya maimakon ka mata fad'a se ka tsaya kana dariya ko? Wallahi da zafi" ta k'arashe tamkar zatayi kuka. 

  "Nihal tell Mamma sorry" itako se ta d'aga hannu da niyyan k'arawa Amal wani marin. 

  "Wallahi kika mareni ba ke ba shan nono yau."

  "A'a yi hak'uri beyi zafi haka ba Nihal and Dada are sorry yi hak'uri kinji sweetheart."

  "Ni kayi sauri kar ka makara Ya Abdool yace nice ban shirya ka da wuri ba?"

  "Ko da nayi latti ma ai zey mun uzuri ko?"

  "Dalili?"

  "Because I have such a gorgeous wife."

  "Really?"

  "Yes baby" da wayo ya sauk'e Nihal a kan gado sannan ya zagaye hannayensa a 'yar kunkuminta yana mey sunkuyar da ita ta baya a hankali, "Now I really wanna kiss y-" bata bari ya k'are maganan da yake ba ta katsesa ta hanyan kissing lips nasa, a sannu a sannu har suka kai jikin bango suna manne da juna, chan Amal tayi pulling out, "Yaya you really have to go n-" shima nan be bata daman k'arisa abinda tayi niyyan fad'i ba ya kuma crashing lips nasa akan nata.

   Warin da suka jiyo yana tashi ne ya dawo dasu daga duniyan da suka fad'a. "Humm Princess is that you?" Afzal ya kewayo yana kallon Nihal data d'age d'uwawu a sama. 

  "Nihal sannu ko?" Fad'in Amal "Ya Omri ka san mey za ayi yanzu? Bari in tayaka cire babban rigan nan ka wanke wa Princess taka pupu ko?"

  "O my God Rania kiga it's almost getting to 10 ina hula na kar inyi latti."

  "Now you're trying to run away huh?"

  "Take care of yourself okay? I love you, Nihal I love you too."

  "Dada!!" Juyowa yayi ya sakar wa Amal murmushi sannan ya nufi gaban mirror ya sa cuff links nasa ya cakkwala hulan Zannan nan ya kuma feffeshe jikinsa da turare "See you around Babe." Murmushi Amal ta tsaya yi wa kanta admiring how gorgeous he is. "Be back safely, Allah kare mun kai Yaya." Wajen Nihal ta nufa ta d'agata sukayi bayi inda ta wanke ta da kyau sannan tayi mata wanka daga nan itama tayi nata. Tana cikin shafawa Nihal oil a gashi Nazeefah ta shigo nan Nihal tafara kiranta da "Titi Titi!" Nan da nan Nazeefah ta amshi Nihal ta gama shiryata itama Amal ta samu ta shiga shiri. Ana cikin haka Maamah ta shiga kiranta a waya. 

  "Maamah zata kasheni gashi har pass 11 bamu tafi ba" ta furta tare da answering call d'in. 

  "Haba Amal it's pass eleven already."

  "Amarya a gidan Mansoor yi hak'uri wallahi ankon dinner'n mu ne basu iso da wuri ba kinga yanzu da mun tafi se kuma bayan dinner mu dawo yi hak'uri we're on our way."

  "Toh se kunzo send my love to princess."

  "I will bye se mun shigo." Nan da nan suka gama shiri suka fita "Mamman Nihal wallahi kinyi kyau tsaya in d'aukeku da princess."

   "Sis bakiga munyi latti bane kam?"

  "Pleaseee mana Mamman Nihal bakiya son in tura wa Ya Afzal ne? Mu d'an birkita masa lisafi a gun d'aurin aure?" ta k'are tana mata signal da gira. 

  "Alright pose d'aya kawai fa amma."

  "Eh eh naji" nan ta ciro wayanta yayinda Amal ta tsaya gyara pose nata dana Nihal nan Nazeefah ta shiga d'aukansu bata tsaya ba seda ta d'auki a k'alla ishirin "Yauwaaa sauran selfie yanzu" da sauri tayi joining nasu ta musu selfies. "Bari in nemi wanda yayi kyau in tura wa Ya Afzal" tayi maganan suna masu takawa gun mota inda driver ke jiran su. Suna shiga driver yaja mota. 

   "Yauwa kinga Ya Afzal yana ma online, tsaya kiga yana bud'ewa ze kiraki." Cewan Nazeefah se kuwa tana mishi sending pics d'in yana bud'ewa in the next like one minute wayan Amal ya shiga ruri tana dubawa taga Afzal. 

  "Mena fad'a miki?" Nazeefah ta tambaya tana dariya itama Amal d'in dariya take sannan tayi swiping ta d'aga. 

  "Rania tell me I'm not dreaming how can you be soooo beautiful?? Masha Allah I have the most beeeyouteefull wife and daughter" se blushing kawai Amal take ko amsa sa ta kasa yi dan dad'i. 


  

   ALHAMDULILLAH Anan na kawo k'arshen wannan littafi nawa mey taken RANA D'AYA. Allah ya sa mu amfana da darusan da suke ciki inda nayi kuskure kuma Allah ya yafe mana gabad'aya. Ameen. 


  With love Mariam Anas AKA Miemiebee.❤️💕

8 comments:

Unknown said...

Wow masha Allah tnx allot hun Allah ya Kara basira more ink to ur pen Ameen ya rabbi

Unknown said...

Amin. A gsky Rana Daya tayi dadi ,Allah yasa mu amfana da abinda muka tsinta daga ciki na amfani. More ink 2 ur pen, tnx u once again

Unknown said...

Masha Allah tnx so much sist I really enjoy this novel in fact I always enjoy your novels

Unknown said...

Mashaa Allah yayi dadi

Unknown said...

Mashaa Allah...such a happy ending, RD yayi dadi sosai kuma ya fadakar,Jazakillah khairan sis. LYSM

Hafsy Hausa Novel said...

Dan Allah muna jiran new book dinki lovely sis muna jin dadin novel dinki.I ar de best always.

Blog27999 said...

Easy "water hack" burns 2 lbs OVERNIGHT

Well over 160 thousand women and men are losing weight with a simple and secret "water hack" to drop 2lbs each and every night as they sleep.

It's very easy and works every time.

Here's how you can do it yourself:

1) Go get a drinking glass and fill it with water half glass

2) Proceed to use this weight losing hack

so you'll be 2lbs skinnier in the morning!

Unknown said...

Masha Allah