TANA TARE DA NI... PAGE 67
BY MIEMIEBEE
Buga k’ofar take tana hawaye. “Anas please open up kaji? Kayi hak’uri dan Allah... I’m sorry Anas pleaseee...” Yana mik’e akan gado ya zura wa ceiling ido, idanun nasa sunyi ja zir yana sauraron duk k’aran da takeyi amman baijin ze iya bud’e mata ya saurareta. Why does love hurts? Tunda yake Fannah ce macen daya fara so mesa zata masa haka? Was he too quick? Even still be kamata tayi shunning nasa haka ba it was just a kiss bawani abu nayi niyyan mata ba was she too afraid? Oh no!
“Anas please ka bud’en kaji? Yi hak’uri dan Allah” Tagaji da tsayawan ta koma zama, k’arfin jikinta har ya k’are buga k’ofan ma takasa yanzu se hawaye kawai take. Da k’yar ta tattara kanta ta koma d’aki layin Anas ta kira yana gani har call d’in ya yanke yak’i picking ta dad’a masa 5 missed calls akai ganin he is not ready ya d’aga tayi texting nasa
_Anas please pick up your phone koda baraka bud’e k’ofar ba pick up the call kaji? I’m sorry we need to talk._
“We have nothing to talk about Fannah” ya fad’i a fili tare da miyar da wayar nasan ya ajiye a gefe. Sake trying layin nasa tayi yana ji yana gani nan ma yak’i d’agawa. Bayan kamar minti talatin daidai 5:30PM ta dawo k’ofar d’akin san. “Anas bakaci abinci ba ka fito kachi kaji? Karka zauna da yunwa please yi hak’uri.” K’ofar ta buga “Anas? Anas nasan kanaji na please ka bud’e” nan ma haka tata suratan duniyan ta befito ya bud’e ba.
_7:40PM_
A hankali ya bud’e k’ofar d’akinsa ya fito sanye yake da ¾ wando ash da farin vest. Yunwa ne ya fitine sa, tafiya yake yana addu’a Allah sa kar ya had’u da Fannah. Zaune a parlour yaganta ta had’a tagumi ko noticing nasa batai ba seda ya k’are mata kallo nakusan minti biyu sannan ya nufa dining area ya bud’o fridge anan ne tagansa. “Anas!” ta kira sunan sa ganinsa kad’ai taji damuwanta sun d’an ragu barata iya jure shirun Anas ba, baro inda take tayi ta nufa wajensa. Roasted chicken yaciro danko bai tunanin ze iya chin abincinta. Ganin haka tace, “Anas yanzu baraka chi girkin dana maka ba?” ta tambayesa idanunta na cikowa da hawaye. “Kayi hak’uri dan Allah, please ka zauna kaci abincin kaji? Wannan kazan ba rik’e ka zeyi ba.” so take ta rungumosa amman tana jin tsoro tasan Anas da banzan zuciya inba wani ikon Allah ba bare sake mata magana ba yanzu, babban tsoron ta kenan. Wata zuciyar ce tace mata to ki fad’a masa gaskia mana he will understand you, kai ta girgiza. Ko saurarenta beyi ba yaciro coke ya fice binsa take tana roqonsa har suka shiga d’akinsa amman ko sauraranta baiyi.
“Anas wai baraka min magana ba? I said I’m sorry bawai nayi hakan bane saboda inada wanda nakeso, Anas I have no one apart from you, you know that koba haka ba? Dan Allah Anas talk to me” ga hannunsa nan tana son ta rik’e amman tsoro bare barta ba da zaran ta tuna irin warning daya kashe mata d’azu haka tana ganinsa yagama cin kazan sa ya kora da drink ya miyar da plate d’in kitchen.
Bayan dawowansa ya zauna kan gado tare da juya mata baya, laptop nasa ya ciro ya soma soma aiki akai. “Anas I get it you are mad at me amman kayi hak’uri ka tashi muyi Sallah kaji?” Dadduma ta shimfid’a musu. “Anas lets pray ka tashi.” Bema san tanayi ba duk suratan da takeyin nan besan tanayi ba hankalinsa ya tattara ya miyar kan laptop nasa. Zama tayi daga bakin gadon chan ta d’an tattara kayansa daya cire d’azu tasa a laundry basket dawowanta ta jeta ta tsaya akansa. “Anas wai baraka min magana ba? Anas I’m talking to you” ganin baida niyyan koda kallonta ne tasa hannu ta rufe laptop d’in ita kanta bata yi tunanin zata iya hakan ba. Anan ne ya d’ago kai ya aza blue eyes nasa akanta.
“Anas I said I’m sorry lets talk please wannan sharenin da kakeyi ba abinda ze haifar mana please kaji lets talk.”
Kamar wanda bareyi magana ba chan ya nisanta yace, “we don’t have anything to talk about sabida banida abinda zan ce miki.” Yana kaiwa nan ya d’au laptop da wayoyinsa yabar mata d’akin. “Anas dan Allah karka sake tafiya...” ta sauk’a har k’asa tana kuka tafi minti ishirin zaune a k’asa sannan ta tattara duka k’arfinta ta tashi if only zata iya fad’a masa da tayi amman batta tunanin zata iya, tsoro kad’ai bare barta ba gani take kamar inta sanar dashi LABARIN TA (littafin pherty) ze guje ta abinda barata iya jurewa ba kenan. Parlour ta lek’a tagansa yana Sallah hawayen dake k’ok’arin fito mata ta matse sannan ta koma d’akin itama ta idar da nata. Kayan baccinta tasa ta haye gadon ta kwanta badan tana jin bacci ba dan de batasan nayi ba tunanin Anas nata kawai take.
Jiran shigowar sa take tun d’azu amman shiru har kusan 11:40PM Anas be shigo ba koda ta leqa parlour taga bayya chan. D’akinta ta duba chan ma bata gansa ba sauran d’akunan ta bi one by one kap bata ga Anas ba hankalinta in yayi dubu be tashi ba guest room taduba a k’arshe a hankali ta bud’e k’ofar ta tsince sa kwance kan gado yana bacci wani sabon kukan taji na k’ok’arin fito mata. Bayan ta shiga ta miyar da k’ofar ta rufe kan gadon ta k’arisa ta kwanta agefensa bayan ta had’a musu pillow. Hannunsa ta d’aga ta had’a da nata sannan tasa a k’ark’ashin kumatunta data kwanta akai. Kallonsa take ayayinda idanunta ke cikowa da hawaye “Anas I’m sorry if only I can tell you da nayi I love you so much” matso da fuskarta tayi tare da pecking nasa a kumatu sannan ta koma ta kwanta ahaka har tasamu tayi bacci ko data soma mafarke-mafarkenta sake matsowa tayi kusa da Anas ta dandame hannunta da nasa.
Asuban fari Anas ya tashi sosai yasha mamaki ganin Fannah kwance a jikinsa a hankali ya raba jikinta da nasa, hannunsa data matse cikin nata tak’i sakewa yayi qoqarin rabawa amman ya kasa daga k’arshe tapping nata yayi seda ta tashi daga baccin. Da sauri ta sake masa hannu “I’m sorry” ta fad’i bece mata komai ba ya mik’e yabar d’akin zuwa nasa achan yayi alwala yayi Sallah yasa alarm nasa da ze tada shi dan shirin office.
_7:10AM_
Cike dining table nasu ke da abinci daban daban iri-iri bata tab’a shirya masa breakfast me yawa kamar na yau ba. Lab’e take a kitchen tana jiran fitowar Anas 7:23AM ya fito yayi shiri all in black meaning he is in a bad mood today, yau akwai firing mutane a office kenan. Binsa da kallo take, hararan foodwarmers na kan table d’in yayi sannan ya nufa fridge yaciro ragowar kazan sa na jiya nan tafito daga wajen b’uyan nata. “Anas good morning” ta gaishesa ko kallonta beyi ba. Coffee data had’a masa ta tsiyaye a cup. “Anas take your coffee” nan ma banza da ita yayi chin kazansa yake a hankali ganin batada niyan daina damunsa ya mik’e a fusace batasan lokacin data rik’o hannunsa ba. Wani irin wawan kallo ya watsa mata da kanta ta miyar da hannun nata baya. “Anas I’m sorry atleast kabani chance inyi explaining kaina please.” Bece da ita komai ba ya d’au jakar laptop nasa ya kama hanyan fita binsa tayi da lunch data had’a masa ba rok’an duniyan da bata masa ba ya amshi lunch d’in amman yak’i har parking lot ta rakasa amman ya bonsa ta yayi tafiyarsa. Ciki ta dawo tana kuka batasan me zata ma Anas ya saurareta ba.
Rabinta nace mata ta tsaida sa ta fad’a masa reason dayasa tayi shunning nasa kamar yadda sauran rabin nata ke ce mata karta fad’a masa. Kwata-kwata batasan nayi ba wanka ma dak’yar tayi wedding photos nasu ta d’au tana sake kallo daidai kan wanda take kallonsa har yake mata dariya lokacin, ta tsaya ta d’au hoton a wayarta ta masa sending a whatsapp tare da adding caption
_Anas I will always look up at you. I’m sorry please come back home and I’ll explain everything banida kowa banda kai please and kar kayi firing workers naka saboda laifin danayi please... Kaji?_
Alokacin daya gama sanar da Kacallah yaje yayi firing mutane biyar kenan sak’on Fannah ya shigo bayan ya karanta seyaji jikinsa yayi sanyi, Kacallah ya kira a waya yace yadawo wa mutanen da aikinsu.
Fried rice me rai da lafiya Fannah ta girka musu yasha kayan had’i sosai, bayan tagama ta jera dining table sannan ta sake wanka taci kwalya sosai. Wata shegiyar english gown taciro daga cikin akwatin english wears nata. Kaya ne had’ad’d’en k’arshe gown ne har k’asa amman an tsaga shi daga k’asa zuwa har wajen guiwa ta gefe. Hannu d’aya garesa shima spaghetti hand ne seta sa seta sake cirewa kunya bare barta ta bari ba. Haka ta tayi ganin lokaci na k’urewa ta dage tasa bata sake cirewan ba, kallon kanta tayi a mirror yadda kayan ya tafi da surar jikinta ita kanta tasan tayi kyau amman kayan yayi tsireci mata da yawa bata tsammanin zata iya fitowa gaban Anas ahaka.
Gashinta tayi oiling ta taje da k’yar seda ta kusan hawaye sannan tasamu ta kama gu d’aya kamar ranan ta zaro kad’an a gaba ta kitsasu sosai tayi bala’in kyau sede duk wannan uban kwalya ta d’aura hijabi akai. Ganin k’arfe hud’u ya buga in less than 20minutes Anas ze k’ariso taji bugun zuciyarta ya tsananta tayi niyyan a yau zata bayyana masa sirrin dake zuciyarta itama ta fad’a masa tana sonsa takuma sanar dashi dalilin dayasa tayi shunning kiss nasa jiya. Ido ta rufe a sannu a sannu tacire hijabin ta koma gaban mirror ta k’are wa kanta kallo, d’an k’irjinta daya fito daga kayan ta dannesa ciki, tana dannewa yana sake fitowa data gaji tabari. Parlour ta koma ta zauna kan kujera se fad’i gabanta yake a yayinda take ta matse tsagun dake jikin kayan. 4:23PM Anas ya dawo gida k’ofar na bud’uwa Fannah ta bayyana a bayansa. Baki ya sake tare da zaro blue eyes nasa in shock yana kallonta, wace wannan kyakkyawar halittan dayake gani a gabansa? Kallonta yake daga k’asa har sama yayi haka kusan sau uku still yakasa yarda Fannah ce everything about her is perfect seji yake kamar yau ya soma sata a ido bebar kallonta ba har yanzu ga wani murmushin dake d’auke fal a fuskarta wanda ya k’ara mata kyau ji yake kamar ya had’iye ta dan kyau. Shin mesa bata sa masa irin kayakin nan kullum, dama haka Fannah take da innermost kyau? Masha Allah gaskia yayi sa’ar mata, matar da bata sonsa matar da take son wani na daban ba shiba. Wannan tunani na tab’o sa yayi k’arfin hali ya kawar da kallonsa daga gareta da k’yar.
K’ofar ya miyar ya rufe seda yazo wucewa ta gefenta tasa hannu ta dawo dashi baya da k’arfin da Allah ya bata. Jakarsa ta amshe kafin yayi magana tace, “welcome home mijina.” Kallonta ya tsaya yi danko bata ishesa da kallo ba idanunsa da suke kai kansu kan k’irjinta yake ta k’ok’arin miyar dasu kan fuskarta. “Anas we need to talk ko seka chi abinci?”
“Bani jaka na” yace da ita.
“No Anas I will not let you go this time around you must listen to me Anas, nagaji da wannan sharenin da kakeyi I can’t take it anymore, kad’au dan inaso ne nayi shunning naka iyyeh? Kuma kamar ya zakace ina da wani wanda nakeso sanin kanka ne banida kowa sekai.” Tad’anyi shiru hakan yabawa Anas daman magana “kin gama? If yes bani jaka na in wuce.”
“Anas wai dan Allah baraka bari ba? Look at me! Look at me Anas!” Ta fad’a a tsawace for the first time “I dressed in this alluring (attractive) manner just to impress you inda dagaske inada wanin da nakeso ai barin bari kaga jiki na haka ba.”
“I should have guess, excuse me” ya watsa mata kallo sannan yabi ta gefenta hannunsa ta kama ta dawo dashi baya. “Fannah bance miki karki sake tab’ani ba? Ban-” katse sa tayi;
“I don’t care! I don’t bloody care Anas” ta fad’a a tsawace. “You are my husband addini na be haramta min tab’a ka ba.” Hannun nasa ta sake kamawa “Anas na tab’aka na rik’e maka hannu so what? Why are you giving me such a hard time? Can’t you also see? Anas I love you. I love you Anas Ibrahim Fauzi and tab’aka yau na soma haka kawai baraka sa min hauka ba tun jiya nake binka kak’i min magana kona maka girki baka ci for what? Saboda nayi shutting naka? Ban barka kayi kissing d’ina ba? Is that it? Well here I am kiss me Anas if it will ease your anger kiss me. Haba mana! I love you Anas shirunka agareni babban tashin hankali ne. Yanzu wuce muje kachi abinci mucigaba daga inda muka tsaya.” Ta k’arasa maganan a tsawace tana masa nuni da daining area. Ita kanta batasan ta iya masifa haka ba inma ta iya bata tab’a tsammanin zata iyayiwa Anas masifa ba har ya tsaya yana sauraronta be zubar mata da hak’waranta a k’asa ba.
Mamaki ne sosai yacika Anas anya kuwa wannan ce Fannar daya sani wanda ko magana bata iyayi da k’arfi shine take wannan uban masifan daya d’an basa tsoro shi kansa? Hannunsa taja ta katse masa tunani. Kujera taja mishi tare da zaunar dashi nan tayi serving nasa abincin.
“Eat” ta fad’a masa. Ba musu bale gardama ya soma chi juice ta tsiyaye masa haka tana tsaye akansa har ya gama chi. “Zaka k’ara?” ta tambaye sa Kai ya kad’a mata kamar d’an yaro. Yana gamawa ya mik’e gabansa tasha.
“We are not done yet Anas.” se a yanzu bakin sa ya bud’u.
“Yes we are” ya fad’a a tsawace. A tsawacen itama ta mayar masa “no we are not because I love you Anas dan Allah ka dena wahalar dani haka I’m sorry for what I did to you yestarday. I’m so sorry please.”
“No you are not Fannah.”
“Anas I am wallahi I am, I love you.”
“Then prove it Fannah inhar dagaske kike you love me prove it to me.” Taku d’aya tayi tare da rufe gab dake tsakaninsu. Hannayenta biyu ta aza a side na fuskansa. “I love you and I will prove it.” D’agel d’in kafa tayi ta d’an kamo sa a tsayi. Ya bud’e baki zeyi magana kenan tayi shutting nasa dawani hot kiss. Mutuwan tsaye Anas yayi sosai Fannah ta basa mamaki yama kasa d’aukan abinda ke faruwa a k’wak’walwarsa be tab’a kawo wa a ransa Fannah zata iya kissing nasa ba, ita da kanta bata tab’a sanin zata iya aikata abinda ta aikata yanzu ba all she know is that she wants to prove to him she loves him.
A hankali ya d’aga hannayensa ya zagayesu a ‘yar k’wank’wasonta tare da sake pulling nata closer to him. Hannunta ta d’aga itama daga fuskarsa ta miyar cikin gashin kansa me uban yawa sun d’au tsawon lokaci suna abu d’aya sannan a hankali tayi pulling out nishi suke dukansu da k’arfi. Ba wanda ya iya yace ko uffan cikinsu they are both still shocked. Kanta ta sunkuyar har yanzu ta kasa believing abinda tayi sede kuma she enjoyed kissing Anas it was worth it. Kallonta yake na kusan minti d’aya ganin batada niyan d’ago kai ko cewa wani abu yasa hannu k’ark’ashin hab’anta ya d’ago fuskarta har ayanzu tak’i barin su had’a ido lips nasa ya lasa yana wani irin shegen murmushi.
“Flower...” Ya kira sunan ta cikin wani irin salon dake sosa mata zuciya.
*© MIEMIEBEE*
beeenovels.blogspot.co.ke
32 comments:
Thanks miemie
Wayyooooo......😗😍😚 love tin tin
Thanks alot
wow really LUV dis story more especially if u believed LUV only exist in book(LOL)
Lovers thing eager to see how he will react Idan yaji gaskiya
Thnx durln
Tnx sis
Dat was awsome
Really luv dis novel!!! More grease to ur elbow, Allah ya qara basira sis Miemie. Luv tinx!!
Really luv dis novel!!! More grease to ur elbow, Allah ya qara basira sis Miemie. Luv tinx!!
Hmmm
Really love dis novel Allah yakara Basira CNT wait for NXT episode to come
Thank you very much mimi 😘 Pls a karo 😫 This chapter ta hadu💃
Hmmmm lovers of no sorrow,i cnt wait to see d conclusion.i seriously like reading ur books because is interesting,more grace to ur elbow
���� this story is life! Please more , tnx fr ur hardwork
I l'île it. Thanks!.
I like it. Thanks!.
Dan Allah a qara mana koda kadan ne.... Mungode da irin qoqarin da kike Allah ya saka. ��
Aunty beee we r waiting ooo Allah yasa dai lafiya
Muna jira yar uwa😢
Book yayi sosai
Wallahi kam sosai
Muna jira yar uwa😢
Allah dae yasa lfy ☹️ Tnx alot
Yau shiru, hope it's fine muna jira
omo dis ur wndrful novel swt oh, e dey do me sey na correct film i dey watch, dis wndrful romantic drama btwn Miss Aliyu and Mr Fauzy no be small thing oh, chaii abeg nima i don enter wireless ntwrk oh. i dey hail u gsky. u dey over try.......
Tnks Sista.Mungode Allah ya kara basira da hikma.Amma pls kidan kara mana wani pls.
Tnks Sista.Mungode Allah ya kara basira da hikma.Amma pls kidan kara mana wani pls.
KAMI SEKELUARGA MENGUCAPKAN BANYAK TERIMA KASIH ATAS BANTUANNYA MBAH , NOMOR YANG MBAH BERIKAN/ 4D SGP& HK SAYA DAPAT (350) JUTA ALHAMDULILLAH TEMBUS, SELURUH HUTANG2 SAYA SUDAH SAYA LUNAS DAN KAMI BISAH USAHA LAGI. JIKA ANDA INGIN SEPERTI SAYA HUB MBAH_PURO _085_342_734_904_ terima kasih.
KAMI SEKELUARGA MENGUCAPKAN BANYAK TERIMA KASIH ATAS BANTUANNYA MBAH , NOMOR YANG MBAH BERIKAN/ 4D SGP& HK SAYA DAPAT (350) JUTA ALHAMDULILLAH TEMBUS, SELURUH HUTANG2 SAYA SUDAH SAYA LUNAS DAN KAMI BISAH USAHA LAGI. JIKA ANDA INGIN SEPERTI SAYA HUB MBAH_PURO _085_342_734_904_ terima kasih.
KAMI SEKELUARGA MENGUCAPKAN BANYAK TERIMA KASIH ATAS BANTUANNYA MBAH , NOMOR YANG MBAH BERIKAN/ 4D SGP& HK SAYA DAPAT (350) JUTA ALHAMDULILLAH TEMBUS, SELURUH HUTANG2 SAYA SUDAH SAYA LUNAS DAN KAMI BISAH USAHA LAGI. JIKA ANDA INGIN SEPERTI SAYA HUB MBAH_PURO _085_342_734_904_ terima kasih.
Sist Allah ya kara basira Tnx alot
Post a Comment