(Like Mother Like Daughter)
⚜⚜⚜♠♠⚜⚜⚜🌟
written by miemie👄
7⃣7⃣
★★★★★
Haka fa rayuwar Saalihah da Fudail ya cigaba da kasancewa, abu kamar wasa yau k'imanin sati d'aya kenan rabuwan Fudail da gdnsa. K'imanin sati knan be sa Saalinsa a ido ba, talkless of ya tab'ata missing nata yake kamar yayi hauka, duk yadda yayi ya mance da ita yabi amman ya kasa, duk yadda yayi ya cire santa daga zuciyarsa tunda ita batta sansa ya kasa. Acikin satin nan kuwa ba k'aramin rama yayi ba har hasken sa ma ya ragu, kullum cikin tunani yake baya cin abinci baya komai, baya zuwa office se tunanin Saalinsa. Ilkleema tayi suratanta har tagaji har ta soma nadaman aikata abinda tayi dan bata zata Fudail ze shiga wannan yanayin da duk sanda tagansa se zuciyarta ta mata k'ona ba, ta had'a sa da Allah kan yasaki Saalihah halan ya mance da ita amman still yak'i. Hasali ma anytime tayi coming up da maganar sece mata yake ze tattara kayakinsa yabar gdan.
Ta fannin Saalihah ma abin hakane, saidai har gwara shi Fudail d'in akanta. Bata cin abinci se in yunwa yaci k'aniyanta, nanma intaci kad'an ne dan lfyr abinda ke cikinta. Habeeba na iya k'ok'arin ta dan kwantar ma Saalihah da hnkl amman ina abin is not helping at all. Kullum cikin kuka take tashi ta yini dashi ta kwana dashi kuma sam bata fasa sallan dare ba, kullum tana cikin neman gafarar Allah.
Cikin wannan sati Saalihah ba k'ramin rama tayi ba tayi bak'i duk tafita daga kamanninta cikin nata ba k'aramin azabartar da ita yake ba, sometimes ko miyau batta iya had'ewa ga wani uban laulayin dayake damunta yanzu, koda yaushe cikin amai take ga rashin cin abinci bale shan magani. Haka takoma wani abu daban a gdan nata. Bata kuma fasa kiran Fudail nata ba dukda kuwa kullum takira sa seyayi hanging kokuma ya kashe wayar gabad'ai. Rayuwa de takoma upside down wa Saalihah dan wanda yake gdan yari ma yafita kwanciyan hnkl. Ko k'arfin zama batada kullum akwance take taje asibiti kuma tak'i koda sunyi waya da umma bata tab'a sanar da ita abinda ke faruwa ba.
Komin rashin imanin mutum da taurin zuciya yaga Saaly seya zubda hawaye.
T boi kuwa yasa Ikleema agaba shifa tasan yadda zatayi Fudail ya saki Saalihah cuz that was not their bargain.
★★★★
Da yammacin ranar asabar Saalihah na kwance a d'akinta tana aikinta na kuka, Allah sarki! Wlh mutum ya kalli Saaly bare so sake kallonta ba dan yadda takoma sekace ba mutum ba. Damuwan duniya sun isheta hawaye ne suke zuba daga idanunta wanda har pillown data d'aura kanta akai ya jik'e. Zuwan bazata umma ta mata, bayan ta danna doorbell Habeeba dake sharan yamma ta taho ta bud'e mata tare da gaisheta da mata sannu dazuwa, sannan tayi serving nata snacks. "Ina Saalihah?" Umma ta tambaya. "Tana sama a d'akinta. Umma gara da kka zo."
Cikin rashin fahimta umma tace, "kamar ya Habeeba? Wani abu ne?" Zama Habeeba tayi a k'asa kusa da umma sannan tace, "umma wlh anty ce batada lfya, yau k'imanin sati knan rabuwan uncle da gdan nan, ni bansan meyafaru ba amman ina kyautata zaton maman uncle hjy ce ta rabasu, tun tafiyan sa anty tadena koda cin abinci ne, bayadda banyi da ita ba yanzu haka wlh ko k'arfin tsayawa batada tana kwance a d'aki ga laulayi kullum cikin amai take dan Allah ki taimaka mata ko asibiti ne akaita."
Mummy dakejin wannan magana kamar a mafarki ta zabura tare da sakin salati "Habeeba? Dan Allah dgsk kke innillahi. Ina 'yar tawa? Wlh Allah ya ia tsakani na da Ikleema, dani tasamu matsala bada 'yata ba mesa zatana azabartar min da 'ya?" Bata jira jin me Habeeba zata ce ba ta haura sama zuwa d'akin Saalihah da gudu. Tana bud'e k'ofar taga Saalihah kwance kan gado tana kuka ta lullub'e jikinta da bargo. Umma batasan sanda tafara kuka ba da gudu ta k'arisa gun Saaly akan gadon. Tare da hugging nata, ji tayi jikinta kamar wuta dan zafi. Da k'yar Saaly ta iya bud'e baki takira sunan umma. Bayan umma ta sakota ne tasa hannu ta share hawayenta sannan ta share ma Saalihah ma. Tana kallon yadda 'yarta ta koma tamkar me ciwon k'anjamau. Wani sabin kukan ne ya faso mata haka tanayi Saaly nayi sanda sukayi me isarsu sannan umma ta share hawayenta tayi calming Saaly da k'yar tayi shiru.
"Zaki iya zama 'yata?" Kai ta kad'a mata da alaman a'a. Da k'yar ta iya ta danne sabon kukan dakeson faso matan. K'olla ma Habeeba kira tayi nan danan tazo ta umarce ta dataje ta had'o ma Saaly tea me kauri. Bayan 'yan mintuna ta dawo da tean a hannunta umma ta amsa tare da mata gdy. Da k'yar ta kishingid'ar da Saaly tasa mata pillow a baya sannan ta bata tean, har tasamu ta shanye bata kuma harar ba. Bayan ta ajiye cup dinne ta rik'o hannun Saaly dayayi zafi sosai. "Meya faru Saalihah? Meya sameki? Mesa baki gaya min abinda ke faruwa ba? Taya zaki bar Ikleema ta cutar dake haka bayan mahaifiyarki tana raye? Eye Saalihah?" Kasa fad'in komi Saaly tayi sekukan datakeyi.
Cikin kukan tace, "Umma dan Allah kiyi hkr, banasan saki cikin damuwa ne saisa..." umma ta katse ta "bakiyasan sani cikin damuwa? ai kap duniya ba damuwan da zaki sani ciki kamar yadda nazo na ganki cikin wannan mumunar yanayin. Saalihah kinganki kuwa? Tun yaushe kke wannan rashin lfyr. Wlh Allah ya isa tsakani na da Ikleema tacuceni ta cuce ki Saalihah. Taya zata rabaki da Fudail shikuma taya ze amince ya yarda ya bita? Ya kyauta knan in ita jahila ce yanzu, seya biye mata suyi jahilcin tare?" Cikin muryan Saaly da be fitowa dan yadda ya dashe tace, "umma karki zagi Fudail baida laifi, nice na jawo ma kaina umma ni na masa k'arya bayan nasan baya san k'arya. Ikleema kuma ta tozartani, bata tsaya ga haka kad'ai ba sanda tayi making dina nayi looking bad a gaban Fudail." Wayarta dake cikin side drawer tasa umma taciro mata nan tashiga mssgs d'in ta karantawa umma sbd umma bata iya karatu ba. Kuka sosai umma tayi jin wannan d'anyen aikin da Ikleema tayi ma 'yarta. Batadamu su surikai bane su ynzu ji take kawai taje gdnsu Fudail ta cukume wuyan Ikleema ta mata tsinannen duka. Mik'ewa tayi tana huci, "yimin kwatancen gdansu Fudail d'in inje inci ubanta Saalihah, abin nata ya wuce gona da iri taya zata mki sharri haka? A dalilin me? Wlh bata isa ba nace kimin kwatancen gdan nata yanzu inje in gyara mata xama dan ubanta, nakega tamanta ko wace hajara, wlh dukda na d'au alk'awari ma ubangiji na kan baran sakeyin fad'a dawani mahaluk'i ba amman na Ikleeman nan yayi yawa."
"No umma dan Allah kiyi hkr kibarta, wanda yayi mekyau yayi ma kansa, ita tayi haka ne sbd tana ganin shine the right thing to do banasan tayarma Fudail hnkl nasan sarai yanzu kka illata masa uwa dole hankalinsa ze tashi nikuma abinda banaso kenan, already yanzu haka tashin hnkln abinda na masa na damunsa. Umma abu d'aya nikeson kimin ki riga sani cikin add'arki plz, Allah sassauta min. Kka min wannan kin gama min komi mummy" ta sa hannu ta share 'yar k'ollarta.
Wani sabon tausayin Saaly ne yakama umma. Dawowa tayi ta zauna tare da hugging nata "'yata kiyi hkr, in shaa Allahu Allah ze saqa miki Ikleema setayi nadaman abinda tamiki tun nan aduniya base munje lahira ba. Kalli abinda tamayar min da 'ya? Yanzu ta rabaki da Fudail din knan? Ya sakeki ne?" Kai Saaly ta kad'a mata. Umma tace, "ni dama sakin kin yayi wlh akan yadda yabarki anan kamar kayan wanki." Saaly tace, "ko kad'an umma karkice haka nasani Fudail ba'a san ransa ya barni ba evidence da Ikleema ta nuna masa is way too strong ace yayi watsi dashi umma. I can still feel it Fudail yana so na kamar yadda nakesonsa."
"Allah sarki Saalihah 'yata inda zan iya karb'an duka pain da kkeji danayi, zuciyata tana min k'ona matuk'a ace baran iya miki komi a erin wannan yanayi da kke ciki ba. Amman shi Fudail bekamata yabarki dukda erin wannan abubuwan da Ikleema tace kinyi ba sbd kina d'auke da cikinsa Saalihah. Bekamata ba, yakamata ya daraja cikin dake jikinki." Saaly tace, "Umma karki manta Ikleema made it clear to him kan cikin dake jikina ba nasa bane, cikin Tasleem ne taya ze daraja cikin?"
Umma tace, "To ke mesa baki masa bayani ba kka bar tsinanniyan can ta riga miki k'arya haka." "Umma koda na masa ba ganewa zeyi ba, bayan ga mssgs rubuce a wayata kan nace cikin dake jikina ba nasa bane. Umma kisani a addu'a, addu'ar uwa karb'ebb'iya ce a koda yaushe" ta k'are magnar da k'olla cike a idanta.
Sake rungumota umma tayi bar kuka 'yata, in shaa Allah 'yata zan saki cikin addu'a. Ina nan zanyi iya k'ok'arina inkula dake. Saalihah duk alifi na ne, daba dan erin hali na kka d'auko ba da yanzu kina nan tare da Fudail naki, kiyafemin dan Allah. Yanzu barin shirya miki kayakinki mu koma gda zakifi samun kulawa acan sbd bakida lfya Saalihah kin ji yadda jikinki ya d'au zafi kuwa? tafukan hannunki sunyi sanyi." Nan ta mik'e.
Hannu Saaly tasa ta rik'o ta dan haka ta kuma zama. "A'a umma kiyi hkr ni baran biki ba baran fita daga gdan mijina ba bayan ban tambayi izini daga gunsa ba, banasan tsinuwan mala'iku umma. Bareyi in biki ba..."
No comments:
Post a Comment