KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
(Like Mother Like Daughter)
⚜⚜⚜♠♠⚜⚜⚜🌟
written by miemie👄
7⃣8⃣
"Saalihah wai dan Allah meh haka ne? Mesa kke wahalar da kanki akan Fudail? So kke ki kashe kanki da abinda ke cikinki? Ai da zebar gdan nan ba cemiki yayi karki fita ba, dan Allah kiyi hkr kodan darajan yaran dake cikinki, ki tausaya musu Saalihah, in shaa Allahu mala'ikun rahama barasu tsine maki ba ai asibiti zaki ba yawo ba." Kai kawai Saaly take kad'a mata "nikawai umma kiyi hkr baran fita ba, inma rashin lfyan ajali ne gomma ya d'aukeni kawai in mutu in huta." Umma ta mata tsawa "Toh maganan banzan nan ya isa, inke bakida hnkl ni inada, ina likitan data duba ki kwanaki? Ko ita se akira tazo ta duba ki ai." Saaly tace, "umma ni da kin bari kawai am fine."
"Saalihah banasan mgnan banza, ahakan ne you are fine? Kin ganki kuwa? Ina wayar taki? Maza kira likitan in mata mgn" badan Saaly naso ba takira family doctor'nsu dr Hassana bayan 'yan mintuna ta iso ba k'aramin razana tayi ba data ga yadda Saaly tayi bak'i ta rame ta canza kamanni gabadai, ta tausaya mata sosai acewarta duk laulayi ne. Tests da dama ta gudanar ma Saaly daga baya ta gano ulcer ne tattare da Saaly kuma badan komi ba ne se dan rashin cin abinci, gakuma blood pressure'n ta daya hau inhar bata rage yawan tunani ba toh definately zeyi affecting baby twins nata. 'Yan maguna ta rubuta ma Saaly tare da bata wasu medical advices.
Gdy sosai umma tayi ma dr Hassana haka Saaly ma. Har dr' Hassana tazo figa se ta tsaya ta tambaya, "ina ango neyau ban gansa ba? Lfy daiko?" Kafin Saaly tayi mgn umma tace, "ai yayi tfy ne saisa." Tare da k'irk'iro murmushin k'arya. "Toh Allah dawo dashi lfy yakuma bawa amaryar tamu lfya, sannu ko? Ki dage da cin abinci dan Allah in bahaka ba yaranki barasu fito da lfy ba" tana kaiwa nan ta fice.
Umma ce ta dawo ta zauna kusa da Saaly, kafin tayi mgn Saaly tace, "umma mesa kka mata k'arya? Mesa baki gaya mata zahirin al'amarin ba? Umma nayi ma Allah na alk'awari kan baran sake yin k'arya ba no matter the consequences ina wayata in kirata in gaya mata gaskian komai." Tsawa umma ta daka mata wanda itama kanta batasan sanda tayi ba "wai me haka ne Saalihah? Wani erin cutar da kanki kkesonyi, aiko a muslince akoi k'arerayin da aka halarta, ba kitanta kuma da zakiyi na gaya miki. Ai kindeji abinda likitan ta fad'a ki rage tunani BP naki ya hau gakuma ulcer'n dole da kka sama kanki na dole dan rashin cin abinci. Kinji dad'i ai ynzu, daman san kashe kanki kke gashi kuwa kin d'au hanya me kyau. Haba Saalihah kefa kke bani hkr time da abbanki ya bar min mgn kan nadena damuwa amman kuma segashi ke naki damuwan har yafi nawa. Yakamata wannan abu da kke yi ya tsaya, ki tausayawa 'yan biyunki mana. Kuma in kinayi wa Allah kibarni in shirya miki kayakin ki mu tafi gda, kibar nan, zama anan inbanda affecting naki ba abinda ze miki. Shi Fudail d'in ai dan yana son ya manta komi yasa yabar gdan mesa kema bara kibar gdan ba? Kid'an samu lokaci kiyi tunani hnklinki yad'an kwanta." Murmushin takaici Saaly ta saki
"Hankalina yakwanta umma? Ai nida kwanciyan hnkl mun raba k'afan wando se rananda Fudail ze dawo gareni. Wlh umma ni kad'ai nasan yadda nakeson Fudail, baran iya rayuwa bashi ba, rashin ganinsa kusa dani ba k'aramin tashin hnkl bane a tattare dani kema kin sani umma, sbd haka kima bar zancen in biki gda. Gara na zauna anan koda yaushe ina tunaninsa umma."
Tausayin Saaly a kowane second k'aruwa yake a birnin zuciyan umma "Tunda haka kkace Saalihah ba matsala ni zan tattaro kayakina inzo ina kula dake har se sanda jikin naki yaji sauk'i baran iya barin ki ke kad'ai ba bakida lfya ita kuma Ikleeman data raba masoya biyu, Allah isar mata. Barinje in siyo miki magunan, kinada kud'i awajenki?" "Nagode umma" tace "eh akoi acikin wardrobe din can ta k'asan." Nan umma taje ta zaro dubu biyu cikin mak'udan kud'ad'en dasuke wajen ta fice tabawa Habeeba kan tasiyo drugs d'in. Kafin Habeeba ta dawo umma har ta soya ma Saaly k'wai ta sake had'a mata wani tea me kauri. Tana fitowa daga kitchen Habeeba na dawowa amsar maganin tayi ta haura mata dashi sama ta zaunar da ita a hnkl take bata har tagama ci tana mata sannu, sannan ta b'allo mata drugs d'in tasha magunan. Ta sake kwanciya tare da rufe jikinta da bargo.
"Saalihah yakamata kiyi wanka, ze k'ara miki k'arfin jiki kinji?" Umma tace. Saaly na lullub'e da bargo tace, "a'a ni umma banasan wankan nan." Baki wangalau umma ta bud'e "karki gayamun kin kwana biyu bakiyi wanka ba eh Saaliahh?" Shiru tayi batace komai ba. Umma na salati tana tafa hannu "Saalihah! Kwananki nawa rabuwan ki da wanka, nace bakiyi wanka ba tun yaushe? Mgn nake miki." "Umma kwana hud'u nefa kawai..."
"...Ni Hajara nagama yawo, kwana hud'u bakiyi wanka ba? Ai rashin wankanki ma kad'ai ya isa saki rashin lfy, kuma a dalilin me barakiyi wanka ba bayan ga ruwa kota ina a gdan ki? Mesa kka k'i yin wanka Saalihah? Magana fa nake miki."
"Toh umma banida lfya, banasan ruwa yatab'ani saisa kawai..." Bata k'are magnar ba Umma ta katse ta "k'arya kke Saalihah yanzu kkacemin zaki dena k'arya amman gashi kinayi, kin k'i yin wankan ne sbd kina ganin yinsa bayida amfani tunda Fudail baya nan bale ya yaba wankan naki, ko bahaka ba?" Shiruu Saaly tayi batace komi ba aranta tace, "tabbas mgnan umma ba k'arya nabar yin wankan ne sbd aganina yinsa ba amfani, tunda bame yaba wa wankan, Fudail d'ina baya nan bale yace jan bakin yamin kyau, kokuma d'inkin yamin kyau kokuma nayi kyau, am damn missing you my Fudail. Akoda yaushe tunaninka nakeyi, duk abinda nakeyi ganinka nake kusa da ni, plz come back home..." Hannun umma data jiyo kan kafad'arta ne yadawo da ita daga duniyar tunanin data wula...
No comments:
Post a Comment