Tuesday, 30 January 2018

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
(Like Mother Like Daughter)
⚜⚜⚜♠♠⚜⚜⚜🌟
      written by miemie👄
                  8⃣7⃣



         Bayan zamansu da mintuna biyu wani yaro yazo ya mik'a ma Dr Hassana wani envelope amsa tayi tare da masa gdy ko bud'ewa batai ba ta mik'a wa daddy ana cirewa sega wani mp3 player. Kunnawa daddy yayi kawai sega muryan Ikleema. Exactly wayan datayi making last da Tasleem ne acikin mp3'n kowa se mamaki yake. Take daddy yaji idansa ya cike masa da hawaye hannu yasa ya share. Daga wani envelope kuma acikin babban envelope d'in ya bud'e sega hotan Ikleema  da Tasleem suna tsaye dagani suna mgn ne kan plan nasu. Wani envelope again ya sak bud'ewa Dr Hassana ta amsa ta mik'a ma Fudail "gashi Fudail listen to this and tell me ko dgsk ranan Saaly tayi waya da Tasleem." Sede tun da aka kunna recording d'in baka jin k'aran komi sena dariyan muguntan Ikleema harda cewa "ai shegya se Fudail ya sakeki wlh" ba abinda Fudail keyi se kuka. Yana me regretting duk wani missdoing dayayi ma Saalihah.

       Wayarta ce tayi k'ara nan ta d'aga "eh kashigo dashi. Muna emergency ward." Bayan 'yan mintuna sega wani d'imemen mutum ya shigo da d'an aikin gdan Fudail. Me share masu tsakar gda. Kowa kallonsa yake. Dr Hassana tace, "Fudail ina kyautata zaton kasan waye wannan ai ko?" Cikin kuka ya giad'a kai. Tace. "good kai gaya musu abinda kayi." Shiru yaron yayi. "Aww se an kaika police station zaka fad'a knan ko?"  "A'a dan Allah kiyi hkr zan fad'a." Tace, "Oya muna jinka."
   
      "Alhj (yana referring to Fudail) dan Allah kayi hkr sharrin shaitan ne..." Dr Hassana ta mik'a ma Fudail wani envelope yana bud'e wa sega pictures na Saalihah da T boi tun wancen d'in. D'an gdansan ya cigaba, "ni na d'aukesu wannan hotuna alhj, hjy ce (Ikleema) ta biyani dubu ishirin kan in kira matarka in ce mata kayi hatsari a daidai fed lowcost yanda in ta fito se shi Tasleem tsohon surayinta wanda har yau yake mutuwar santa ze cirota daga motar nikuma se in d'aukesu hoto. Haka akayi bayan da nagama d'aukawa muka kai muka wanke nabawa hjy daga nan bansan me tayi da pictures dinba, amman dan Allah kayi hkr sharrin shedan ne. Karku kaini prison dan Allah" Be k'ara furta word ba daddy ya tsinke sa da mari tas! Kukeji a kumatunsa. Kafin ya hankara ya k'ara masa d'aya "bakasan zuwa prison? Toh wlh jail zan kaika bama prison ba you'll regret what you've done to my daughter inlaw take him away." Nan aka fita dashi yana ihu yana had'asu da Allah.

         Dawowa daddy yayi ya zauna ya kalli abba sannan umma again back to abba da muryarsa na rawa yace, "dan Allah ku yafeni kuyi hkr, on behalf of Ikleema kuyi hkr ku yafe mata. Sbd abinda tayi tasa life na 'yarku in danger..." Fudail dayayi shiru tun d'azu se hawaye yake zubarwa kamar zararre yace, "daddy dan Allah kabar basu hkr I shud be the one to apologise" kneeling yayi gabansu umma da abba yana basu hkr. Dr Hassana tace "you're not Fudail, abinda kayi ma Saaly is unforgivable, kafi kowa sanin halin Saaly u shud know duk k'arya mummy take maka but you failed to. Bakayi kowani investigation ba kawai ka yanke hukuncin Saalihah taci amanarka da Tasleem"

        "Whatt?" Daddy yace "me kke fad'a Hassana. Wayaci amanan wani kuma da wa?"  "Gashi nan daddy ka tambayesa ze gaya maka komi, shiyasan me yayi ai..." Daddy ya dawo da kallonsa kan crying Fudail a fusace. "What did you do Fudail?" Shiru yay bece komi ba se kukan dayake tayi. Su abba da su umma kam dey are completely speechless barin ma abba da be tab'a sanin abu game da wannan al'amari ba. "Am talking to you!" ya daka masa tsawa take yafara mgn, tundaga sanda Ikleema ta kirasa a waya rananda yake dawo wa daga office kan yazo tanasan nuna masa abu. Bebar komi ba kuma beyi k'aryan komi ba full acct of everything ya basa he's reaady to face the consequences inde akan Saalihah ne. Yana gamawa yace, "daddy dan Allah kayi hku..." Be k'are maganar ba daddy ya tsinka masa tas! Kukeji.

        "This is the first time nake marinka Fudail, ban tab'a sanin kai shashasha bane se yau. How could you? Daman bakada hnkali shine nabarka kayi aure? Ka ringa cutar da Saalihah haka? You've had your time Fudail, believe me bakai ba Saalihah daga yau. Asma'u da kakeson ka aura ita zan aura maka. Itakuma Saalihah Allah bata hkr da lfya."  "Daddy dan Allah kayi hkr wlh sharrin shed'an ne dan Allah karka rabani da Saalihah."  "Ya isa! Not a word!  Banasan sake jin hak'urinka, ma iyayenta zaka bawa hkr bani ba, su ka cutar musu da 'yarsu kuma kasani kayi ma kanka..." Daidai nan wayarsa yayi k'ara yana d'agawa yaga new number nan ya amsa "hello waye ne?" Hon. Ahmad ne dan Allah?"  "Eh shine."  "Yanzu haka as we speak ana kai matarka hjy Ikleema TH, munsamu sumemmiyar jikinta ne a bayan gari da alama wasu group na maza ne suka mata duka wanda aka nemesu aka rasa su but ana kan investigation har ynxu." Salati kawai dady yake a hnkl ya sauk'e wayar daga kunnensa yace, "Allah ya isar ma Saalihah. An samu sumemmiyar jikin Ikleema a bayan gari ina kyautata zaton yaron dake kan hoton d'azun nan ne yamata duka dama saida na gaya mata inhar bata soya halayenta ba barata gama da duniya lfya ba. Kuma gashi tagani ai kaima Fudail in bakayi a hnkl ba kamar mummy'nka zaka k'are. Ban tab'a sanin bakada wayo haka ba se yau, abu haka yana faruwa a gdan ka baraka min mgn ba, to me amfani na? Ka gommaci ka gayawa Ikleema problems naka akan ni ko? Ba damuwa na gaya maka kafara shirin aurenka nan da months."

        Har ya juya ze fice se aka bud'e k'ofar d'akin Saalihah. Duk suka d'uru sukayi wajen. "Kune family'n patient d'in?" Dr'n daya fiton ya tambaya, "eh, eh, eh" kowa yake fad'i. "To mijinta na nan?" Murya na rawa Fudail yace, "eh yana nan gani, nine mijinta." Dr'n yace "a gaskia barin b'oye muku ba due to fad'uwan datayi tayi losing jini sosai. Amman cikin ikon Allah batayi bleading internally ba. Cikin tan nanan cikin k'oshin lfya. Saidai tana buk'atar blood transfussion wanda in da'ya daga cikin iyayenta suna nan zamu so a d'ibi nasu."  "A d'ibi nawa a samata plz dr. Fudail yace a takaice.

        Kowa ya juya yana kallonsa. Dr'n yace, "ai is not poaaible blood group naku yazama d'aya..." Katse sa yayi "am blood group O I can donate to any1, lets make it fast plz kar wani abu ya sameta." Muryan daddy suka jiyo yace, "no bara a d'iba naka ba na iyayenta za'a d'ba tunda kaine ka jawo mata duk wani abinda takeji yanzu, bata buk'atarka  anymore."  "Daddy dan Allah kayi  hakuri karka min haka, dan Allah."  "I said enough" daddy ya daka masa tsawa "banasan sake jin mgn daga gareka Mal Ibrahim bismillah plz." Sekuma Fudail yabawa abba tausayi yace xalhj Ahmad kayi hkr, tunda ya tuba yakuma yi nadama mijinta ne shi inhar jininsa ze iya mata shiya cancanta ya bata. Kuje Fudail, jeka ba wa matarka jini. Alhj Ahmad dan Allah kayi hkr ka barsa." Kai kawai daddy ya giad'a sannan ya fice  tare da cemasu "zan dawo anjima baran je inga Ikleema. Kaikuma Fudail karkaga dan kabata jini ka d'au it'll change something, ina kan bakata ba kai ba Saalihah." Duk suka masa "Allah kare." Nana akayi wata d'aki da Fudail aka gwada jinin nasa dan tabbatawa blood group O dinne shi.

       Sannan suka yi d'akin da Saalihah take a kwance ya ganta tayi pale kamar wacce bata da rai har oxygen sanda aka sama ta, ga kanta duk bandage ji yake kamar yaje yayi hugging nata yabata hkr, ji yake kamar ya kwace rashin lfyr tan shi yayi suffering ba ita ba. Take idansa suke cike da hawaye dr'n ne ya basa hkr sannan ya kwantar dashi akan wani gado kusa da Saaly aka harhad'a abubuwan jan jinin a hnkl jinin jikinsa ya soma fita yana bin siririn pipe d'in da aka had'a da hannun saalihah a hnkl har ya fara shiga jikinta. D'ayan hannunsa ya d'aga ya rik'o hannunta dashi yana murzawa a hnkl "am so so so sorry Saalihah, am terribly sorry I wish you could forgive me for the misdoings i've done to you, I should have believed ba k'arya kke min ba am sorry plz." Haka yata suratai abinsa. Leda biyu akaja daga jikinsa aka bawa Saalinsa sede dr'n yace har ynxu ya kamata a k'ara mata d'aya and bareyi aja daga jikin Fudail ba gudun kar rashin lfya ya kamasa shima za'a ja daga jikin mahiafiyarta ko Mahaifinta.

         Fudail yace, "no dr inhar kasan true meaning of love kaja daga jikina I don't care koda duka jinin jikina za'a bata inhar she's going to live. Am ready to risk my life. Plz do, take another bag." Dr'n yace. "sosai nasani kuma I can see kanason matarka sosai but medically be kamataba is not as if daman kasan za'a ja jini a jikina ka shirya ne kayi hkr ai da biyun ma kayi k'ok'ari."  "Dr plz nace, dan Allah." Ganin Fudail nasan masa kuka ya yarda haka aka sake zuq'e wani ledan daga jikin Fudail...

★★★★★
   
   A teaching hspital dake garin Bauchi room 18 Ikleema ce kwance kan gadon asibiti da goshinta duk bandeji, fuskar gabad'ai yaji rauni ko ina ciwo ne d'ayan idanma kam ya kumbura ya rufe. Hannunta d'aya akarye k'afanta kuma ya gurd'e abinde ba kyan gani. Hawayen nadama se gangara suke daga idanta zuwa kan pillon datake kwance akai. Daddy ne tsaye akanta wanda ya jima ahaka tun shigowarsa bece mata komi ba se kallonta dayekeyi cike da nadaman aurenta ma...

  Rangem rangem gem ga asirin Ikleema ya tonu fa. Rangem Ga t boi nan yamata duka fa rangem rangem gem😃😃😃

No comments: