KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
(Like Mother Like Daughter)
⚜⚜⚜♠♠⚜⚜⚜🌟
written by miemie👄
8⃣6⃣
★★★★★
Dr Hassana ta tambayi Saaly, "baraki bari ki kwana anan ba yaso gbe ki koma gda?" "A'a dr" ta amsa "banasan kwanan asibiti ga Habeeba zata kula dani, karki damu. Kema umma kije gda Sa'ad na neman ki." "Toh shknan" inji dr Hassana zaku iya tfya already Fudail yabiya kud'in bills d'in sim naki kuma na guna zanyi investigation dashi pictures d'inma duk nasa Habeeba takawo min d'azu. Allah k'ara lfya kinji Saalihah? Kuma dan Allah ki rage tunani nama Fudail d'in mgn and I won't rest se nayi finding justice miki." "Nagode sosai anty Hassana Allah bar zumunci." Suna kaiwa nan suka fice driver'n daddy Fudail ya turo ya sauk'e umma a gda sannan ya sauk'e su Saaly suma.
A parlour suka tarar dashi yana ganin sun iso lfy yasa ya tashi ze koma d'aki. Sunansa Saaly ta kira cak ya tsaya tace Habeeba tayi excusing nasu, a hnkl take tafiyan har takai gabansa kau da kansa yayi yadda bara ma su had'a ido ba. "Thank you" tace masa. Bece komi ba kawai kai ya giad'a mata tare da bin gefenta ya fice. D'akinta ta haura da rarrafe dan jirin datakeji. Tea Habeeba ta had'o mata tareda b'allo mata drugs nata bayan ta gama sha ta had'iye ta fad'a bayi tayi wanka sannan tafito tayi sallan isha ta kwanta. Da tunanin Fudail nata ta kwanta. Ta fannin Fudail shima hakan ne gabad'ai ya kasa gane meke faruwa, shide yasan yana san Saaly amman besan mesa anytime tazo kusa dashi yakeji bayasan ganin ta ba. Ahaka har shima yayi baccin.
3 days later...
Habeeba ce ta gama aikin komai tama Saaly breakfast haka Fudail ma, bayan data kai masa nasa ne ya tambayeta "ya jikin Saalihah?" "Da sauk'i uncle" ta fad'a. "Make sure tasha drugs nata kinji? Take care o her" "In shaa Allah uncle" sannan tafita. Haurawa sama tayi zuwa d'akin Saaly taga Saaly bata ko tab'a breakfast nata ba tayi nisa da tunani dafa ta tayi "anty tunanin ya isa kinga bakida lfy kuma ko a asibitin sanda akace ki rage tunani, ynxu uncle yace in tabbata kinci abinci kinsha maganinki, kiyi hkr kisha kinji?" Cike da mamaki Saaly tace, "yace ki tabbata nasha drugs d'ina? Kode wasa kkemin Habeeba." "Wlh anty dgsk nake kinsan duk da abinda yake faruwa uncle yana sanki kuwa? sosai wlh saisa nakeson ki rage tunani, uncle nasanki sosai, nan da d'an lokaci zaku shirya" ta k'are maganar tana mata murmushi. Dad'i sosai Habeeba taji ta matso da Habeeba kusa da ita tare da hugging nata sekace bame aiki ba ni miemie nace Saalihah anyi hnkl gaskia. "Nagode Habeeba, ngd sosai you're like a sister to me, Allah saka miki da alheri." "Ameen" Habeeba tace "baranje in kimtsa kitchen." "Tou sannu" Saaly tace.
Da misalin k'arfe 2:30PM Saalihah na zaune a parlour tai shiru tare da zura ma TV ido dagani tunani takeyi har Fudail yafito daga d'aki yaje dining space bata gansa ba bayan yagama shan ruwan ya taho ya haura sama zuwa d'akinsu dan d'auko wani briefcase nasa kasancewar yaga Saaly zaune a parlour. Ya shiga ya d'auko yana rifo k'ofar kawai yaganta kamar aljan a gabansa. Sanda ya ji tsoro seya ci fuska. "Excuse me" yace batareda ya kalleta ba. Ganin tak'i matsawa yasa ya gwada bin ta gefenta hannunsa ta cafke hannunta yaji yayi zafi sosai, gashi its not as soft as how it use to be before. Duk seyaji wani iri. "Let go off my hand Saalihah." K'in sake hannun nasa tayi "Fudail why are you doing all this?" "Ki sakeni nace, ai duk abinda nakeyi yau ke kka jawo Saalihah, let me go" a garin fisge hannunsa dayayi da k'arfi ne ya tureta sekuga Saaly na gangara kan stairs tundaga sama ta soma gangara sanda ta sauk'a har k'asa. "SAALIHAH!" Fudail ya k'olla mata kira k'ara kad'an ta saki sekuma tayi shiru. Da sauri ya sauk'a yabi kanta yana juya fuskarta yaga goshinta na jini gashi ga dukan alamu ta sume. Tapping nata yake a kumatu sam batayi responding ba. "Saalihah plz don't go and leave me, am sorry for mistreating you dan Allah karki tafi wake up plz." Hugging nata yayi duk ya b'ata kayansa da jinin goshinta.
D'ago hannunsa da zeyi daga k'asa kawai yaga pool of blood daga k'asanta ihu ya saki. Se kuka yakeyi, "innalillahi! Na kashe ki Saalihah, I've killed my own wife. Habeeba! Habeeba!" Habeeba dake waje tashigo a firgice ganin Saaly a k'asa ga jini ko ta ina yasa ta tsala ihu tuni itama ta fara kuka tana salati "un..uncl..uncle meya samu anty? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." "Jeki d'auko min waya na da key'n mota a d'aki" da gudu ta fice a yayinda ya d'aga Saaly dake ta zuban jini har ynxu yakaita mota daidai nan Habeeba ta iso da key'n ya bud'e yasa unconcious Saaly a baya Habeeba ma tashiga a 360 suka bar gdan se asibitinsu na kullum Reemee nan akayi emergency da ita. Dr Hassana ya kira Allah yaso tana asibitin nan take ta zo ta inda suke tashiga OR'n ba abinda Fudail yakeyi se kuka haka Habeeba ma. He can't forgive himself inhar wani abu yasamu Saaly ko babies nata. Daddy ya kira yana kuka duk hnkalin daddy ya tashi.
"Meya faru son? Wni abu ne?" Yana kuka yace, "Daddy Saalihah ce, na kasheta daddy." "Me kake fad'a son kuna ina ynzu?" "Muna reemee." Nan da nan daddy ya kira abba yasanar dasu suma suka shirya sede koda ya gwada layin Ikleema bai shiga besan kuma mesa ba.
Duk a tare suka isa asibitin umma kam se kuka take tun kamin taga 'yarta, baaba kuwa duk ta rud'e. Fudail suka samu zaune a k'asa se kuka yake sha. Duk sukayi kansa suna tambaynsa meya faru. Kukan yake har ynxu yace, "daddy, abba, umma dan Allah kuyi hkr na kashe Saalihah nasan mutuwa zatayi dan Allah ku yafemin." Daddy ne ya matso kusa dashi "stop talking like that son, baka kasheta ba in shaa Allah zata samu lfya." Umma kam se kuka takeyi baaba da abba suna lalashinta. Haka Sa'ad shima se kuka yake sha...
An hour later...
Dr Hassana dawani dr suka fito daga d'akin da Saalihah ke ciki nan duk suka nufa kanta kowa da erin tambayan dayake mata. Ajiyar zuciya ta saki sannan ta watsa ma Fudail kallo ba tare da tace komi ba idanta cike da hawaye tafara mgnan.
"How could you Fudail? Taya zaka ma matarka haka? Kasheta kakeso kayi? Welldone then that was a nice try. Ai gashi sekaje ka ga critical condition da take ciki yanzu..." Kan kowa a gun ya d'aure ba wanda yagane abinda take nufi se Fudail dake kuka ba full stop. "No no no!" Abinda yake ta nanatawa knan "plz do something to save her, she can't die I have to ask her for forgiveness."
Umma se kuka takeyi "Dr dan Allah ina 'yata kibarni in ganta, wayyo Allah Saalihah" Da rud'anin yama daddy yawa ya daka masu tsawa dukansu dukda cewar a asibiti suke. "Can someone tell me whats going on in here?" Dr Hassana ce tace, "muje daddy is about time kasan abinda matarka Ikleema ta rigayi da kuma d'anka da ya biye ma foolishness nata" nan suka nemi waje suka zauna illa umma da zama ya gagareta se kuka take tana tmbayar 'yarta.
beeenovels.mywapblog.com
No comments:
Post a Comment