(Like Mother Like Daughter)
⚜⚜⚜♠♠⚜⚜⚜🌟
written by miemie👄
8⃣5⃣
Hannu tasa ta share hawayerta sannan ta fara bawa dr Hassana labarin komai tun time da suka fara soyayya da daddy'n Fudail har suka samun misundersranding da Ikleema tun tana 'yar budurwa. Bata b'oye mata komi ba tas tabata lbrn komi... "Kinji abinda yafaru kenan dr" tayi concluding.
Dr Hassana tace, "gaskia dake da 'yarki kunsha gwagwarmaya a rayuwa and ba komai bane yajawo ma Saalihah wannan whalan da takesha se halinki umma, nasan ba uwar dazata so tasa 'yarta cikin wahala amman in akayi la'akari da wannan yanayi naku za'a iya cewa kece silan wahalar 'yarki. Halinki ta d'auka umma, KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA kuke, yakamata ke da kkayi nadama kka shiryu be kamata kibar Saalihah tayi duk erin abubuwan datayi da abaya ba, kamata yayi ki tsawatar mata amman kka barta tarigayi abubuwanda ba dede ba. Saisa akace in zakayi abu kana la'akari da consequences d'in am sorry to say this but kinga ke kinyi worse akan abubuwanda Saaly tayi amman tsakanin ki da ita fa, wayafi shan wahala a rayuwa? Itace. Wani sa'in laifin da muka aikata akan yaranmu Allah ke hukunta mu. Saisa akoda yaushe mutum ya kasance meyin abu tsakani da Allah, in ka aikata sharri either you or your daughter zakuyi reaping haka zalika in ka aikata abin alkheri."
Cikin kuka umma tace, "nasani dr, saisa ayanxu haka bakisan yadda zuciyata ke min k'ona ba nasan duk nice silan abubuwan dake faruwa da Saalihah, saisa nake san na gyara komi yanzu barata sake komawa gdan Fudail ba, be damu da ita ba yanzu." "Karkice haka umma Fudail ya damu da Saalihah fiye da yadda kke tsamanni ko yanzu shiya min waya kan nazo na kaita asibiti. Yazama dole yayi acting kamar yadda yake yanzu ne sbd in kkayi la'akari da erin hujjojin da Ikleema tayi gathering masa baida wani option than to agree with it musamman ma yadda yake sonta, he can't believe it har ynxu saisa yake duk iya abinda ze iya yaga shima ya k'untata mata. Thats it amman Fudail kam nason Saalihah karki yi forcing nata tabar gdansa kibarsu a hnkl zasui sorting out problem nasu kuma nima zan sa musu hannu aciki. Inhar abinda kkacemin gaskia ne kan cikin Fudail ne da Saalihah bana Tasleem ba and duk sauran hujjojin da Ikleema ta nuna masa weren't real kinga ko yazama dole muyi bincike dan gano gaskia, justice must be served."
"Likita bansan ta ina zan fara miki gdy ba, dukda cewar wannan abu be shafeki ba amman still kinasan ki taimaka mana. Mungode matuk'a Allah saka da alheri." "Ba komai umma nima abu d'aya zuwa biyu nesuke son sani gudanar da wannan investigation. Na farko yadda Fudail da Saalihah suke san juna, soyayyar dasuke ma juna is far beyond our immagination, suna san juna sosai tun lkcn dana tab'a zuwa gdansu na fahimci hakan saisa yazama dole in dawo dasu back together as how dey were before."
"Nagode sosai likita Allah biyaki da gdan aljanna yabaki mijin da ze soki kema haka." "Ameen" ta amsa da, "shknan kibar kuka in shaa Allah zamu b'ullo ma wannan al'amari. Barinje inkira Fudail muyi mgn dashy, excuse me." Tana fita umma tad'au hannun Saaly tana shafawa a hnkl, tana zubda hawaye a hnkl Saaly ta soma bud'e idanta har ta bud'esu. Fuskar umman ta tafara gani tana kuka itama kukan tafara take.
Umma tace, "shhh karkiyi kuka 'yata in shaa Allah wahalarki tazo k'arshe, bar kuka kinji?" Ta bata peck a goshi tana mata sannu. a hnkl Saaly tace umma Fudail ze sakeyin aure, ina Asma'u dana gaya miki 'yar uwar Ikleema? Shi takeson aura masa umma..." Kukanta ya tsananta. "Aure?" Umma ta dafe k'irji. "Bare miki kishiya ba in shaa Allah, Saalihah walakancin ya isa haka dan Allah daga nan karki sake komawa gdan Fudail kibarsa kifita daga harkansa baya sanki ynzu Saalihah. Taya zece ze miki kishiya? Gaskia baraki koma gdan sa ba." "Umma dole in koma tunda be sawwak'emin ba kinga ko yazama dole in zauna a k'ark'ashinsa and ba inda akace a al Qur'ani kan in mijinka ze sake aure kayi yaji kabar masa gdan. Ba daidai bane. In Allah ya k'addara matarsa ce Asma'u so be it ni zanyi welcoming nata in rungumi k'addara kawai kitayani da addu'a Allah sa me kirki ce ita umma."
Ba abinda umma keyi se kuka, Saalihah tausayi take bata, ga ciki me uban bata wahala, ga rashin lfyr dake damunta, ga hawan jinin k'aro auren da mijinta ze mata. Kuma duk wannan abu suna faruwa ne sbd gadon halinta da 'yarta tayi.
★★★★★
"Hello engr?" Dr hassana ta ceda Fudail a waya.
"Dr, ya jikin nata?"
K'arya ta masa tace "Jikin nata fa ba sauk'i Fudail BP'nta yasake shooting sosai, yanzu haka an sa mata drip ko zata d'an samu k'arfin jiki, yaran ma dey are not in good position."
Take yaji idanunsa sun cike da hawaye "dr plz do all that u can to save her, plz. Inma yaran dake cikin tan ne suke k'ara worsening situation d'in ni I don't care a ciresu inhar she's going to recover plz. I can't forgive myself inhar wani abu ya samu Saaly..." Yayi concluding.
"You cant forgive yourself inhar wani abu ya sameta while actually kaine kake worsening situation natan."
"Kamar ya dr?"
"Kamar yadda yake. Mesa kake abu kamar wanda beje boko ba Fudail? Da iliminka da komai zaka bar mummy tayi poisoning mind naka, how? Taya zaka bari Ikleema ta shiga tsakaninka da matarka? Gaskia am very disappointed in you."
"Hassana what are you talking about? Nifa bansan me kke cewa ba. Am hanging ni kawai make sure Saalihah stays fine"
"Don't hang up Fudail. Kafini sanin me nake nufi. Taya zaka yarda cewa cikin dake jikin Saalihah ba naka bane, taya zaka yarda cewa tana having affair da wani Tasleem a waje, how? How can u be so easily fooled? Can't you get it mummy so take ta rabaka da Saalihah dan ta aura maka 'yar uwarta..."
Kasa fad'in komi Fudail yayi, maganan dr Hassana ba k'aramin birkita masa brain yayi ba, hanging kawai yayi se faman hello takeyi amman shiru koda tasake gwada dialing kuwa ya kashe wayar. Brain nasa juyi yake masa. Yakasa gane what he is thinking of. Mesa maganan Hassana yake sounding kamar akoi gaskia aciki? Tun ba yau ba mummy keso na auri Asma'u is it true duk pictures da mssgs din weren't real? Was mummy just setting a trap for Saalihah dan mu rabu in auri Asma'u? No amman ai pictures d'in seems real and what about phone call da Tasleem yamata in my presence? Shima it was real ai, Ohh god, meyake damuna? Why cant I reason??"
★★★★
"Hello Tasleem kashirya fa ka kusan zama ango."
"Kai mama? Kice an samu progress a plan namu knan"
"Progress babba ma kuwa jiya dawowa na daga gdan Fudail na masa maganan k'arin aure kuma to my suprise ya amice min yace in 4days time ze bani feedback kaga d moment Saalihah taji ze k'ara aure nasan zata tada bori tayi yaji kaga daga nan seka yi making move naka ko ba haka ba?"
"Sosai mama, gaskia kinada ilimi sosai, wannan plan is the best lets just hope things will work out the way we want dem to."
"Ameen Tasleem se anjima..."
No comments:
Post a Comment