(Like Mother Like Daughter)
⚜⚜⚜♠♠⚜⚜⚜🌟
written by miemie👄
6⃣8⃣
"Wallahi Tasleem nima tambayar dana kasa amsawa kaina knan, yarinyan nan bansan ko mutum ko aljan bace, wai cikin ma har na 'yan biyu bama d'an d'aya ba mstww."
"Toh yanxu me kke da shirin yi??"
"Hummm I have to do some deep thinking first, sbd nasan koda mun gudanar da plan namun nan it'll be hard for Fudail to divorce her sbd darajan cikin da take dashy..."
A fusace Tasleem yace, "then do something mama, kema kinsan ina san Saalihah, inasan ta dawo gareni."
“Jimin d'a ai baka kaini san raba Saalihah da Fudail ba. Kuma har ynxu ina kan bakata na senaga k'arshen Saalihah” ta kwashe dawani shu'umin dariya daga bisani tace, "ohh yes I think nasama mana better plan Tasleem, cikin da Saalihah tasamu will be of great contribution to our plan, believe me Fudail dole se ya kori Saalihah, Allah sarki Saalihah sekinyi nadaman samun cikin nan da kkayi wlh.”
★★★★★
Shigowar Fudail d'akin da cup a hannunsa yayi daidai da ajiye wayar Saalihah akan side drawer. Har gabanta ya nufo "gashi sweery, sannu ko?" "Thanks hun" ta amsa tare da zama "yanzu na gayawa umma am pregnant with twins, bakaji ihun data rigayi cikin wayar ba wai gbe zata zo ma." Bayan ya zauna kusa da ita yace, "mesa baratayi ba? This is such a great news ai sweery." Oya try kisha tea'n kinga you are carrying two babies yakamata kinacin abinci sosai kobahaka ba?" "Right baby" ta fad'a masa. Suna hira tana kurb'ean tean ta da kaurin sa yayi kamar kunu har tasamu ta shanye.
Bayi suka fad'a sukayi wankan bacci sannan yajasu sallah suka kwanta. Da hannunsa kan cikinta har bacci b'arawo ya sacesu*** Washegary! Fudail da kansa ya tashi, a hnkl ya raba jikinsa daga na Saaly sannan ya shirya office ba tare da ya tada taba, har ya tafi bata sani ba se bacci takeyi, da alama cikin magunanta akoi na bacci aciki. Se kusan 9:50AM ta tashy taga Fudail bai kan gadon, tana kai dubanta kan agogo taga goma saura. "What!?" Tayi exclaiming. "Oh no! Fudail will be late for work today.” A hnkl ta mik'e kan gadon tayi knocking bisa k'ofar toilet d'in a zatonta ko yana ciki jin shiru ba'a amsa ba yasa ta fad'a taga wayam ba kowa k'asa ta sauk'a taci karo da Habeeba tana shara. Bayan ta gaisheta Saaly ta tambayeta "ina Fudail" ta ce "ya tafi office tun d'axu." Zaro idanunta tayi "waya shirya sa ya masa breakfast?"
Bata tsaya jin abinda Habeeba zata ce ba ta haura sama ta kirasa a waya. Ringing d'aya biyu ya d'aga "morning sweery, har kin tashi?" "Honey seka tafi office kuma baka ta dani na shirya kaba? Am sorry I overslept nakega akoi sleeping pills cikin maganin da dr'n can ta bani, am so sorry."
"Ai seki b'ata min mood sweery, bakida lfy thats why ban tayarda ke ba, ai ni ynxu na sauk'e miki obligation na kula dani, just take care of yourself and our little ones." Murmushin jin dad'i take sosai wane Fudail na gabanta kan gado ta fad'a ta aza hannunta kan cikinta, "your babies are saying hi, sukace I should extend their greetings to their awesome dad, wai they are missing you already yau kar ka kai 4 a office, they didn't get to say goodbye to you before leaving" "tell them am missing them too, and yau 1:00PM zan dawo."
Tsalle ta daka "dgsk honey?" Yace, "Ohhh se ynzu na gane, so actually mom nasu ne take missing d'ina basu ba." Had'e gira tayi tare da zumburo baki "toh haramun ne? Am damn missing you, kadawo by one d'in kaji hun?" Murmushi yayi "no worries takw care of yourself for me I love you." "I love you too" tace "blow me a kiss" "*muahh*" ya mata sannan yayi hanging. Bayi ta fad'a tayi wanka tafito tasa wata pink atamfa da torches na red sannan ta sauk'a kasa taci abinci tasha maganinta. Door bell aka danna nan da nan Habeeba ta bud'e ganin ummanta yasa ta ruga a guje tayi hugging nata. Umma tace, "ah ah Saalihah ta kiyi a hnkl kamin in rasa jikokin nawa." Fuskarta ta rufe da hannu "kaii umma! Ina su baaba da Sa'ad? "
"Suna can makarantansu Sa'ad wai yau open day, ita taje masa." "Ohh ayya Habeeba had'o ma umma breakfast" ta dawo da kallonta kan umma "a soya miki k'wai umma?" Umma tace, "eh to daman ban wani karya ba nafito duk na k'osa in ganki." Nan Habeeba ta fice zuwa kitchen. "Toh ya kke Saalihah? Ya k'arfin jiki?" "Alhamdulillah umma, kufa ya kuke acan dasu abba?" "Kowa qlou, abba ma na gaisheki kuma yana taya ki murna haka baaba ma."
"Awwwn! Ina amsawa umma." "Toh ya kke da Ikleema, kuna shiri kuwa?" Umma ta jefa ma Saaly tambaya. Shiru Saaly tayi bata ce komi ba dan haka umma tasan akoi matsala. Baro kujerar datake zaune akai tayi ta matso kusa da 'yarta "gaya min Saalihah, tana tak'ura miki?" "Eh a da kamin nasamu ciki ba, amman tunda taji inada ciki yanzu nakega tayi hnkl." Umma tace, "karki gayamun ta gwada miki gorin haihuwa?" Murmushi Saaly ta mata "mance kawai umma ai ya wuce yanzu." Umma tace, "duk laifi na ne, Saalihah daba dan abubuwan dana ma Ikleema da ba da baratana treating naki haka ba. Ikleema mace ce me hnkl da hak'uri ba ruwanta, batada problem kuma, tana miki duk abubuwan data miki a baya ne a matsayin ramako. Ramawa take akanki Saalihah kiyi hkr dan Allah kiyafe wa ummanki. Kisan ummanki bataso haka ba itama. Wlh nasan daba dan abubuwan da suka tab'a shiga tsakani na da Ikleema ba da se ince kinfi kowa sa'ar surika. Kiga yadda takesom Fudail mana, dukda baya mutunta ta amman daidai da rana d'aya bata tab'a giving up ba. Kiyi hakuri kinji 'yata in shaa Allahu zata gano gaskia wataran ku fara zaman lfya."
"Haba umma! Ya kke mgn haka? Sekace ke kke forcing nata take abubuwan da take, ni ko kad'an basu damen ba tunda Fudail na sona itakuma tana jin maganarsa kinga banida wata matsala. Dan Allah kibar wannan mgnar ni ba abinda kka min, kinji umma na?" "Toh shknan tunda haka kkace ummah" nan da nan Habeeba ta had'o ma umma breakfaat d'in bata jima sosai ba ta tafi bayan kyautan kud'in da Saaly ta mata.
Tana dawowa ciki suka soma had'a girkin rana se toshe toshen hanci take ahaka har suka samu suka gama. Ta haura sama ta canza kaya ta cancare masa kwalya yaukam dake tad'an ji dad'in maganin. 1:26PM Fudail ya dawo gda. Yaukam tun a parking lot ta taresa, yau ma kamar kullum bebar jan bakin bakin nata ba, hannunsa ta rik'o suka shigo ciki ta rage masa kayan jikinsa sannan tayi serving nasu abinci bayan da suka gama ci ne yace, "sweery ina wayarki?" "Uhmm yana kan cntre table I guess" nan ta mik'e ta d'auko "wani abu ne?" Yace, "check out your messeges." Nan tashiga ta duba. Ido ta zaro sanadiyar alert na 1mil dataga Fudail yamata sendn a acct nata.
No comments:
Post a Comment