(Like Mother Like Daughter)
⚜⚜⚜♠♠⚜⚜⚜🌟
written by miemie👄
6⃣9⃣
"Honey??? Kud'in me wannan?" Ta tambaya duk hnklainta baiya jikinta "Just to show you how happy I am now that you're pregnant and to thank you" tace, "I feel like crying hun har 1 mil, bansan ta ina zan fara maka gdy ba." Tasowa yayi ya mik'ar da ita tare da hugging nata "no need to thank me sweery, ni ya kamata in miki gdy for bringing this twins to our lives. I love you so much Saalihah. I can't afford to lose you. I pray ba abinda ze shiga tsakani na dake"
★★★★★
1 MONTH 2 DAYS LATER...
Cikin Saaly nada 2 months 1 week, sosai take samun kulawa daga wajen Fudail nata. Duk kayan kwad'ayin daya gani kan hanya seya siya mata, kuma baya barin ta yin aikin komi gudun kar wani abu yasamu lfyr twins nasu, aiki ma yanzu tun 1 yake closing. Ikleema ko ta kawo ma Saaly turmin zanin super har biyu wai na tayata murnan k'aruwan da suka samu. Su Bint da Phaary ma sun mugun taya Saaly murnan wannan k'aruwa data samu. Komai tafya mata yake yadda takeso. Ikleema kuwa tana kan bakarta na raba Saaly da Fudail time kawai take jira.
Yau ranar ta kasance tuesday tun 8 fudail ya tafi office. Saaly tayi wanka tayi breakfast tana zaune a parlour tana kallo wuraren 10:10PM na rana wayarta dake kan centre table a parlour ta soma ringing tana kai dubanta taga new number sanda ya kusan tsinkewa ta d'aga nan ma batace komi ba. Bak'on murya me nuni cike da tashin hnkl taji ance "matar Fudail ce dan Allah?" A gigice tace, "eh eh itace." Mutumin ya cigaba "kiyi sauri ki k'araso wajen federal lowcost lungun Al-iman, mijinki ya samu accident yanzu haka ana shirin kaisa asibiti ne amman ana jiranki, yasamu kariya biyu a k'afa d'aya a hannu, gakuma kansa daya fashe..."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" take ta nanatawa ji tayi tama kasa numfashi, shiru kukeji... "Hello?" Mutumin ya fad'a "hjy kiyi hkr ki k'araso." Tuni idanunta suka cike da hawaye "ga..gani nan zuwa." Maganar ma dak'yar take. Wayar tayi wulli dashi kan kujera tajawo key'n motarta da mayafi ta fice da gudu. Allah yasota daman last 2 weeks ta amso motarta daga gda. Kuma koda tafita bata sanarda me gadi ko Habeeba inda zata ba. Wani erin mahaukacin tuk'i take Allah de kare kawai. Tana ficewa daga gdan sega Ikleema lab'e cikin keke napep ta toshe da dark glasses nan ta ciro wayarta ta kira T boi "hello Tasleem make sure you play your part well kaji ai? Gashi yanzun tabar gda." Nan ta katse wayar ta sallami me napep sannan ta shige gdan. Karo taci da Habeeba a parlour, bayan Habeeba tamata sannu da zuwa tace "yi sauri 'yar albarka ki dafo min indomie yunwa nakeji, ina Saalihah?" "Toh hjy, wlh nima bansan ina taje ba, tade fita da hanzari yanzun nan."
Ikeema tace, "toh Allah de sa lfya, yi sauri ki dafo min yunwa nikeji" Habeeba na shigewa kitchen Ikleema na d'ago wayar Saalihah dake kan kujera. Sede kash! Wayar da password. Sunan Saalihah tasa yak'i bud'uwa tasa na umma shima yak'i tana sa na Fudail ya bud'u wani hamdala tayi sakar. Nan tashiga mssgs ta ga alert na 1mil da Fudail yamata sendn one month ago. Baki wangalau ta bud'e "lalle ma wlh yarinyan na asirce min d'a tayi, wato har miliyan d'aya yake mata sendn? Karki damu daga yau dad'inki ya k'are a nan gdan, shgya kawai." Nan ta ciro wata k'aramar waya daga jakarta tayi typing mssg ta tura ta numban Saalihah. A wayr Saalihah kuma tayi replying haka ta rigayi kusan conversations guda 10 tayi biyar daga na Saaly biyar kuma daga d'ayan layin datayi saving as "my heartbeat" a wayar Saaly. Tana gamawa ta je call logs ta goge last call da Saaly tayi making (numban daya kira Saaly kan Fudail yayi hatsari, alhalin ba hatsarin da Fudail yayi, duk part of her plan ne) dariyar mugunta ta saki sannan ta ajiye wayar kamar yadda tasamu. Ta koma gefe ta xauna.
Isar Saaly federal lowcost keda wuya. Saidai sam bataga alaman anyi hatsari a wajen ba wayarta ta gwada lalima dan kirar numban d'azun. Sede ta manta bata fito dashy ba sterring motar ta daka "shit! Yanzu taya zan san layin da Fudail d'ina yake. Wayyo Fudail pls don't die and leave me, dan Allah be stong for your children" hawaye se shar shar suke a fuskarta. Wata bak'ar mota taga tasha gabanta wanda tana kyautata zaton motar T boi ne. Hankalinta in yayi dubu be tashi ba. Tirk'ashi yau akeyinta me T boy yake san mata. Reverse ta gwada yi only to see wata mota tayi blocking nata daga baya, gashi ba wayarta bale ta kira Fudail nata. A hnkl T boi ya bud'o motarsa.
Taku one by one yayi har ya iso wajen motarta kafin tayi locking motar jar ya riga ya bud'e tare da finciko ta waje. Abun haushin kuwa koda tayi ihu bame jinta sbd layin shiru yake yau ba mutane. Duk tsoro ya cike ta, se b'ari take. "Tasleem dan Allah kayi hkr karka min haka, kasake min hannu kaga inada miji be kamata ka kama min hannu ba, let me go. Dan Allah karkayi kidnapping d'in ka tausaya wa abinda ke ciki na." Murmushi ya saki ta gefe "gafara can wani aure? Ai ki sa a ranki yau auren ki ze mutu." Hannun nata ya sake fincika da k'arfi tare da matso da ita kusa dashi suna feeling air dasuke breathing.
Can daga gefe kuwa wani munafiki ne zaune cikin mota yana d'aukansu hoto a camera.
"Tasleem ka sakemin hannu dan Allah, matar aure ce ni" se k'ok'arin kwantan kanta take tana had'a sa da Allah tana kuka amman sam takasa dan yadda ya matse ta jikinsa. D'ayan hannunsa ya aza kan fuskrta yana shafawa a hnkl. Ba abinda Saaly keyi se kuka ba sauti. Tayi fad'an har tagaji daga k'arshe ta soma basa hkr "Tasleem dan Allah kayi hkr , ka yafemin na tuba dan Allah. Inada aure, be kamata ba ka rik'eni haka, dan Allah kayi hkr..." Haka tata had'a sa da Allah amman sam ko a kwalar rigarsa shafa jikinta ya rigayi, munafikin motan kuwa se hoto yake d'aukansu.
Se can ya saketa. "Saaly kisani sanki dana keyi ne yajawo haka. Zaki iya tafiya yanzu and bawani hatsarin da mijinki yayi, this is part of my plan." Yana kaiwa nan ya ja motarsa ya fice. A hnkl ta koma cikin motarta kuka takeyi kamar ba gobe, kuka me ban tausayi da kuma tsuma zuciya game sauraro. Tace da kanta "Fudail plz forgive me, bansan ya zanyi facing naka ba, banda k'aryan dana maka a baya gashi yanzu wani na miji wanda ba muharrami na ba yashafani naci amanarka Fudail dan Allah kayi hkr..." Haka tata kuka tana sumbatu. Idanun nan tuni suka kumbura sukayi jaa.
Motar ta kunna ta soma driving tana kuka har Allah ya kaita gda. Tana isa me gadi ya bud'e mata gate tashiga tayi parking sannan ta fito takama hanyan cikin gda. Tana bud'e k'ofar ta ga Ikleema zaune kan dining space tana wasa da fork a hannunta...
No comments:
Post a Comment