KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
(Like Mother Like Daughter)
⚜⚜⚜♠♠⚜⚜⚜๐
written by miemie๐
8⃣3⃣
You've been waking me up several times and making me breakfast, arranging my room and my closet and now kinmin wanki. Thanks but dont ever do it again kinfini sanin condition da kke ciki. High BP, ulcer gakuma ciki. So for ur own health dana yaranki stop it banaso. Banasan abinda ze na had'ani dake why trying to impress wanda kkace bakiya so? Just stop it... Murmushi take da hawaye duk a lokaci d'aya. She's happy sbd Fudail really cares about her tunda har yace tabar yin aiki sbd condition nata, na biyu kuwa yayi appreciating abubuwan data masa tunda har ya mata gdy. On the otherside kuwa she's sad sbd yace bayasan abinda ze sake had'asu su biyu, kuma har yanzu gani yake kamar bata sansa T boi takeso. Paper'n ta eungume tana hawaye ganin haka Habeeba ta bata waje.
Gugan kayan nasa yakai a hanyar dawowa ya had'u da Ikleema data ma daddy k'arya kan zatazo duban Saaly da Fudail ta sake musu sulhu takuma musu nasiha. A tare suka shigo kowa yayi parking motarsa sannan suka shiga ya mata sannu dazuwa Habeeba tayi serving nata drinks. Ikleema tayi gyaran murya sannan tace, "son kayi bak'i fa gaskia, I can see u are suffering alot. Ya kake da Saalihah? Kun shirya?" Kallonta yayi na d'an lokaci sannan yace, "nup lets not talk about her" ba tare da ya nuna damuwa ba dukda kuwa deep inside so yake su shirya.
Ya cigaba da yin abinda yakeyi a ipad nasa. Can yace, "ni tunda nazo gdan nan ma ko word be had'ani da ita ba." "Kayi daidai son, haka yakamata kana yi dama." Yace, "taya zan bata hkr mummy, she's the one at fault I shouldn't be the one apologising." Nanma tace, "You're absolutely right son" saidai kanta ya juye mata dan da daddy ya kira Saaly cemasa tayi Fudail yabata hkr shikuma Fudail yace ko word be had'asu da Saaly ba, kasa hkr tayi sanda ta tambayesa. Yace, "ni ban bata hkr ba, nakega ra'ayin dayace taso Tasleem akaina shiya sa tace wa daddy nabata hkr amman dekam ni ban bata ba. Duk kayakina ma na tattara daga d'akinta na sauk'o guest room can nake kwana." Ikleema murna knan? Ji take kamar takunna rangem tayi rawa ai ko a babu Fudail yabar ma Saaly mgn kuma yabar had'a kwanciya da ita and she must be suffering alot. "Son abinda kayi daidai ne ka mun burgeni kuma haka daman na miji me zuciya yakamata yayi ba duka ba zagi."
"But mummy is like Saalihah is willing to change, kwana biyun nan aiki take min dukda tasan batada lfya har wanki tamin yau. Is kike am loving and hating her duk a lokaci d'aya" Ikleema tace a ranta "karka damu d'an love da kake matan ma ze koma hatred very soon." Sannan a fili tace, "uhn uhn son karka bari tausayinta ya kama ka she made is crystal clear to you kan bata sanka Tasleem takeso kai kud'inka kawai takeso am very sure wannan ma wani trap take setting maka so dnt let her sympathy get to you. Kuma kace tun dawowarka a guest room kake kwana?" Kai ya giad'a mata tace;
"Allah sarki son wlh you must be suffering alot, Allah ya isa tsakaninmu da Saalihah abinda ta maka is unforgivable. Amman sanin kanka ne baraka iya cigaba da zama ba mace ba Fudail dole musan nayi is either kayi hkr kawai ka yafe ma Saalihah..." Katse ta yayi "in yafe mata mummy? Are u kidding me? Ko kin manta abubuwan data min ne, cikin dake jikinta ma is not mine how can I forgive her..." Ganin har ya fusata tace, "gaskia ne, bekamata a yafe mata ba." Can cikin zuciyarta kuwa daman da biyu ta gwada tambayarsa dan jin bakinsa.
"Toh amman son baraka iya k'arisa rayuwarka haka ba, inhar bara ka iya yafewa Saalihah ba den seka..." Sekuma tayi shiru yace, "ya kikayi shiru mummy? Ina jinki." Tace, "a'a kbr kawai da k'yar kaso idea d'inma but kasani I only want the best for you koh?"
"I know mummy sesa nakeson jin wannan shawarakin. Ai shawaran uwa bai tab'a zama me negative impact kan d'anta so tell me. Ni yanzu mummy banda kamar ki, for not listening to ur words before naga illarsa. I've learnt a valuable lesson in life mummy from Saalihah. Tun farko da kkace karna aureta da ban aureta ba and she wouldn't have broke my heart like this"
"You're right son, ni duk abinda zan gaya maka to in shaa Allah abinda ze amfane ka ne." Ikleema can't keep calm yau Fudail na kwatanta ta da uwa. Dama its part of her plan Fudail yayi earning trust nata, kuma gashi tayi succeeding yanzu jin maganarta yake. Na biyu kuwa yanzu so take ta aura masa Asma'u na uku kuwa ta kori Saaly daga gdan sbd tana kyautata zaton cewa Saaly najin za'a mata kishiya koba takardan saki zata bar gdan setaje can su k'are da Tasleem, 'yar uwarta Asma'u kuwa ta more Fudail.
"Dama wannan shawara ba komai bane illa in zaka yarda ka k'ara aure son. Yakamata ka k'ara aure. Saalihah nasan kasheka ne, nikuma baran iya juran ganin mutuwarka ba yakamata ka auro wacce zata soka for who u really are badan kudinka ba, wacce zata kula dakai barakuma ta maka k'arya ba, wacce zata warkar ma da ciwon da Saaly ta jima a zucia and ba kowa bane illa cousin naka Asma'u yarinyan nan tana sanka Fudail, gata well educated har masters tanada, am very sure zata kula dakai sosai. If not wlh Saalihah zata kasheka takuma kwashi gado dga nan taje tasamu Tasleem masoyinta, jibi yadda ka rame fa har haskenka ma ya ragu wlh, zuciya na namin rad'ad'i anytime naga only son d'ina haka."
Shiru yayi yana nazarin abinda Ikleema tace, agaskia shi auren morethan one wife baya cikin tsarin rayuwarsa but sbd abinda Saaly ta masa neman aikata abinda zeyi ya k'untata mata yake kamar yadda ta k'untata masa shima. Neman abinda zeyi yayi getting on her nerves yake dukda kuwa can k'asan zuciyarsa yana san Saalihah sosai but he can't foegive her. Koda yayi niyan yafe mata duk sanda ya tuna da pictures nata da T boi seyaji ya k'ara tsananta nd he cant forgive her. Ba wanda ze ga pictures d'in yak'i yarda kan ba budurwa da saurayi bane su, as in hoton ko k'adan be nuna Saalihah ma rok'an T boi take ya saketa ba instead seya nun kamar kallon soyayya ma suke ma juna musamman yanda T boi yawani zagayeta da hannunsa ta kwankwason ta. Shi kansa yasani yana san Saaly aman so yake yana nuna mata baya santa sbd itama tasha wahala kmar yadda tabasa wahala.
Ikleema ce tadawo dashi daga tunanin dayake "son kayi shiru? Inhar shawaran be kama ba fa shknan am not forcing, I only want the best for you." Murmushi yamata "nasani mummy. And shawararki tayi sosai, but I need some time to think maybe koda nan da d'an 4 days haka." "Ure right yakamata kasamu time kayi tunani, ina nan ina jira daga gareka son. Allah zab'a mana mafi alheri." "Ameen" yace sannan taja jakarta ta mik'e "to na gaisheka son zan tafi." Rakiya yamata har wajen motarta tabasa hug yamata gdy sannan ta fice yadawo ciki.
Habeeba dake aiki a kitchen kap taji abinda suke da shirin yi. Ita ta rasa me anty tama hjy da hjy ta tsaneta haka. Ita setaji tama tsani maman uncle natan nan, muguwa ce kuma munafuka ita daya kamata tamusu sulhu amman kuma setana k'ara ma yanayin nasu matsala? Ita tarasa me anty tama hjy ta tsaneta haka, a iya zamanta da Saalihah, Saalihah bata tab'a mata ba daidai be Gaskia ya kamata anty tasani.
Nan ta ajiye tsumman dake hannunta ta haura zuwa d'akin anty tayi knocking taji shiru dan haka kawai ta shiga. Taga Saaly ta na bacci a gefenta a k'asa ta zauna tafara tashenta a hnkl "anty anty kiyi hkr ki tashi." Cikin gigin bacci Saaly tace, "wani abu ne Habeeba?"
"Eh anty akan uncle ne." Firgit ta mik'e ta zauna tare goga idanta dan wassakar da baccin dake ciki jin ankira sunan uncle. "What about him? Wani abu ya samesa ne?" Ta tambaya a kid'ime. "A'a anty saidai yanzu hjy tazo kuma ta tafi." Saaly ta zaro idanunta "hjy? Mummy fa knan, me tazo yi?" Habeeba tace, "Wlh anty da kunne na na jiyo tana cema uncle yak'ara aure wai zata aura masa wata 'yar uwarsa sunanta Asma'u" bata k'are maganan ba taga already antyn nata na kuka setaji dama bata gaya mata ba. "Anty dan Allah kibar kuka ni wlh danasan ze saki kuka dama tun farko ban gaya miki ba."
No comments:
Post a Comment