Tuesday, 30 January 2018

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
(Like Mother Like Daughter)
⚜⚜⚜♠♠⚜⚜⚜🌟
      written by miemie👄
                  8⃣2⃣



       Tunda ya zauna yake tunanin Saalihah just as yadda ya saba kullum har Habeeba tagama indomie'n ta kawo masa da ruwa da juice ta zuba masa a cup ta ajiye kan cntre table. Godiya ya mata sannan takama hanyan zuwa d'akinta. Sunanta ya kira take ta amsa yace, "zo in tambayeki." Nan ta dawo ta zauna a k'asa "gani uncle." Shiru yayi sannan yace, "aunt naki batada lfy ne?"  shirun  tad'anyi sannan tace "eh" a takaice. Yasake tambayarta "takira dr kokuma haka ta ta zama da rashin lfyar?"  "Bata kira ba uncle, sanda ummanta tazo yau ne ta kira dr Hassana ta duba ta. Kuma naji kamar tace wai BP'n anty ya hau kuma wai takamu da ulcer sbda ta kwana biyu bata cin abinci." Daman yana kishingid'e kan kujera ya mik'e ya zauna. "BP'nta ya hau kuma takamu da ulcer?"  "Eh uncle" ta sake jaddada masa. Salati kawai yakeyi duk seyaji he can't forgive himself.
   
        A ransa yace, "am so sorry Saalihah plz forgive me, ke kka jawo duk wannan abubuwa and thats why you're sufferering." A fili yace, "tunda na tafi fa, ta fita?"  "A'a bata fita ba uncle kullum tana d'aki dan rashin lfyrtan yazo yayi worse sosai ko nace muje asibiti setace bata tambayi izini daga wajen ka ba, barata ba." Ji yayi duniyarsa yana crashing. Mesa Saalihah take behaving kamar wacce batayi komi ba da abaya? Da in zata fita ganin Tasleem ta tab'a tambayan izini na ne? Wani zuciyan yace masa she's just trying to get your sympathy saisa don't be so easily fooled. "Shknan zaki iya tafiya ngd." Har ta tashi seya sake kiranta "and koda wasa karki gya mata munyi wannan mgn dake, understood?"  "Eh uncle" sannan ta fice. A hnkl yasamu ya cinye abincinsa se tunanin abinda Habeeba ta gaya masa yake. Guest room daya sauk'a yakoma ya rage kayan jikinsa sannan ya kwanta ya d'au wayarsa yana viewing pictures na Saalihah ahaka har bacci yayi awon gaba dashi.

     Washegary!
     Bayan ya dawo daga masallaci yabiya ta d'akin Habeeba yayi knocking. Tace, "ina zuwa."  "A'a basekin bud'e ba zan koma bacci in 6 yayi kizo kimin knocking a bak'in k'ofa zanje office, kinji?"  "Eh naji uncle, in shaa Allah zan buga maka." Nan ya fice zuwa guest room. Saaly dake lab'e a jikin staircase tajiyosa  sannan ta koma d'akinta. Six nayi ta sauk'o k'asa daidai nan Habeeba ma ta fito daga d'akinta. Bayan ta gaisheta Saaly tace, "bari zan tadashi."  "Toh anty ngd" ta koma d'akinta a yayinda Saaly kuma taje ta tsaya dab da k'ofar d'akin Fudail seta d'aga hannu zata mai knocking seta kasa da k'yar tayi knocking sau biyu taji shiru. Ta k'ara wasu biyun nanne taji yace "thank you." Can yace;

      "Habeeba wait kimin frying chips da egg knji?" "Uhummm" Saaly tace dan kar yagane muryarta. Nan ta fice kitchen dukda ba dad'i takeji ba taje ta had'o masa breakfast nan da nan tagama komi kafin yafito everthng is in place ta koma sama ta lab'e ta staircase tana jiran fitowarsa. Can tagansa yafito da wani jean sweaty trouser da black T shirt ya d'aura wata blazer me guntun hannu akai ya bala'in kyau sam shirin beyi kalan na zuwa office ba. Har tafara tunanin ko ina zasa setaga jakar laptop nasa a gefe, yasake tabbatar mata office zasa.

         Ta tambayi kanta "why is he not wearing his suit?" Se can ta tuna ashe duk suits nasa suna cikin d'akinsu. Zama yayi kan dining ya had'a tea yafara cin abincinsa hnklnsa kwance har yagama bata bar wajen ba sanda ya fita tukuna. Ta sauk'o ta karya da ragowar breakfast d'in sannan ta tattara wajen ta haura sama ta sauk'o masa da duka kayakinsa takai ta shirya masa cikin wardrobe na d'akin daya koma. Ta gyara kan gadon sannan tasa Habeeba ta share d'akin tare da wanke toilet d'in masa.

        Kafin ya dawo daga office kuwa Saalihah da Habeeba sun had'a masa lunch duk yadda Habeeba tayi da Saalihah tabari zatayi ita kad'ai tak'i. Had'a dining d'inne kawai tabar Habeeba tayi takuma ja  mata kunne kan koda Fudail ya tambayeta waya girka abincin tace ita da kanta tayi karta nuna ma Fudail tare sukayi. Habeeba ta amsa da "toh." Kasancewar Fudail ya kusa dawowa gda ta haura sama zuwa d'akinta. Tana jin k'arar honk ta lek'a window taga motar Fudail. Bayan yayi parking yafito kawai seta tuna da dane da ta sauk'a ta masa sannu da zuwa yamata kiss tareda tand'e mata jan bakin bakinta. Murmushi take alokaci d'aya kuma tana hawaye haka ta bisa da kallo har sanda ya shigo ciki taji Habeeba na masa sannu dazuwa.

      Zama yayi bayan Habeeba tayi serving nasa yana kai spoon d'aya ya tsaya ya kalli Habeeba yace, "who cooked this?" Tace "wani abune uncle?"  "Wayayi cooking wannan nace?" Jiki na k'yarma tace "ni..nice uncle."  "Qarya kke Habeeba bake kka girka ba." "Uncle dgsk ni na girka." Mik'ewa yayi "na k'oshi baranci ba." Sbd he's sure Saalihah ce ta girka haka girkinta yake exactly.  Yana shiga d'akinsan yaga komai tsaf! Be kawo wani tunani aransaba ace warsa Habeeba ce ta kimtsa masa. Bayan ya rage kayan jikinsa ne ya tuna kayan dayake da niyar sawa yana d'akin su can a sama gashi baisan shiga d'akin daga k'arshe Habeeba ya kira kan taje ta kwaso masa kayakinsa sama. Koda tashiga d'akin Saaly bata ce mata komi ba tana ganin Habeeba ta bud'e wardrobe na Fudail bata ga komi ciki ba, dan haka tace, "anty ina kayan uncle? Yace in kaimasa." Saaly tace "kice masa yana cikin wardrobe na d'akinsan"

           "Toh" ta amsa sannan tafice taje ta gaya masa. Cike da mamaki yace, "kinko gane abinda nake nufi? Kayakina fa nacikin wardrobe." Tace. "eh uncle anty ce tace yana cikin wardobe anan" nan ya shigo ciki ya bud'e wardrobe d'in segashi duk kayakinsa an kimtsa masa a ciki gefen jampa daban, suits daban sannan k'ananun kaya da jallabiya ma daban. Habeeba ya kita tashigo d'akin sannan ya tambayeta "ke kka shirya kayakin nan?" Kai ta kad'a masa da nufin a'a yace, "bansan k'arya fa"  "wlh uncle bani bane."  "To jeki shiknan." T shirt dayake da niyan sawan ya ciro ya sa tare da haurawa kan gado ya kwanta ya zura ma ceiling ido. Ya tambayi kansa "Saaly why are you doing all this? Kefa kkace bakiya sona den why are u acting like you care about me?" Sam yakasa amsa wad'annan tambayoyi. Ahaka har bacci yay awon gaba dashi.

         Haka fa abu kamar wasa Fudail yafita daga harkan Saaly kwata kwata. Inhar yaji motsinta a parlour to bai fitowa bale ma su had'u ta masa mgn dukda kuwa deep inside he's being hurt sosai. Koda ta masa mgn kuwa gasa mata mgn yakeyi iya san ransa tata kuka shima in yadawo d'aki yayi kukan. Yau k'imanin sati knan suna abu d'aya baya cin girkinta, baya mata mgn baya mata komi is like she's dead to him duk sanda ya tuna abubuwan data masa kuwa seyaji ya k'ara tsananta.

       Gashi ynxu ko abinci yabar ci sbd yasan Saalihah ke girkawa dan haka kawai ta hak'ura tabar Habeeba tafarayi dan batasan Fudail nata yayi starving.  Tun fitan Fudail office yau Juma'ah Saaly taje ta tattaro laundry'nsa sbd jiya taji yana fad'in ze kai wanki. Kap ta wanke masa kayakin cikin washing machine suka fita k'al sannan tayi draining  ta nannad'e ta mayar masa cikin wardrobe inya so seya kai guga. Yana dawowa daga office yaci abinci sannan ya shiga d'aki dan d'au kayan wankinsan sede begani ba a inda ya ajiye dan haka ya kira Habeeba.

         "Ya ina kka kaimin kayan wankina dana ajiye kan laundry basket dincan?"  "Gaskia bangani ba uncle koda na share d'akin banga kayan wanki aciki ba." Ransa yasoma b'aci cuz yasan shi ya ajiye kayan da hanunsa akai "taya zakice baki gani ba? Bayan ni na ajiue da hannuna."  "Uncle wlh bangani ba sede in tayaka dubawa" tsuka yaja ya nufa wardrobe nasa yana bud'ewa yaga kayakin aninke da alama har an wankesu. Cike da mamaki yace, "toh ke Habeeba bayan kin wanke min kayan ne kuma kkace baki gansu ba? Ba gsu nan ana ba."

       Ita de Habeeba tasan batai wanki ba yau, "wanki kuma uncle?" ta tambayesa "nifa banyi wanki ba yau." "Towa ya wanke" ya tambayeta a takaice "wlh nima bansani ba." Can yace a ransa "Saalihah knan, Saalihah must be the one responsible." Paper ya d'auko ya rubuta wani note ya mik'a ma Habeeba kan takai ma Saalilah. Nan ta amsa tare da haurawa sama tayi sallama bisa d'akin, Saaly tace ta shigo, "anty gashi uncle ne yace in kawo miki." Hannunta na b'ari ta amsa "toh ngd." Nan ta bud'e ta karanta kamar haka...

No comments: