(Like Mother Like Daughter)
⚜⚜⚜♠♠⚜⚜⚜🌟
written by miemie👄
7⃣2⃣
"Son, wai kukan nan be isa bane? Bafa kai yakamata kana kuka ba Saalihah ce yakamta tayi kika, you might be the victim in here but she's the one to pay, and the only way is in ka saketa. Ka buga mata saki, wlh zata shiga taitayinta kuma kana wani zancen tana d'auke da cikinka baraka iya sakin taba how sure are you cikinka ne bayan kasan tanada wadda takeso..." "No mummy, am sure cikina Saaly take d'auke dashi, mummy baran iya sakin Saalihah ba, for all my future plans, nayi involving nata aciki I just can't understand mesa zata min k'arya haka..." Ikleema tace, "sbd batta sanka kud'inka takeso, tashi muje gdan naku na nuna maka wani abin al'ajabi"
Hanky yaciro daga pocket nasa yayi wiping tears nasa sannan yace, "ni baran je ba mummy, banasan sake xuwa gdan can." "Wace erin banzar magana ce?" Ikleema ta tambaya "Ya kake mgn kamar na mace? Kana nufin ka bar mata wancen mansion d'in kenan?" "That is how much I love her mummy, ina san Saalihah fiye da yadda kke tsammani, she's carrying my babies I..." Katsesa tayi "Wai sau nawa zan gaya maka ba 'ya'yenka bane? Taso muje in gaskata maka" pictures d'in ta tattaro tare da jan hannunsa suka shiga motarsa tayi driving nasu har gdan Saaly. Bayan sun isa har tayi parking ta bud'o k'ofa Fudail ya kama hannunta "no mummy, stay here I'll talk to her myself plz, karki shiga..." "But son..." "Pls nace." Badan tanaso ba tace, "toh shknan ga pictures d'in." Amsa yayi tare da mata godiya ya bud'e mirror ya goge idanunsa saidai har ynxu kansa na masa ciwo. A ransa yace, "am willing to forgive all you've done to me Saaly inhar zaki iya gayamun gaskian komi da kanki, plz don't lie to me now." Nan yafita tun be k'arisa ba Saaly ta bud'o k'ofar parlourn murmushin data saba masa tayi "welcome back hun ina jakanka?" Fudail ji yake kamar ya had'a ta da bango, ji yake kamar ya shaqure ta ya kasheta shiya huta itama ta huta. Upon abinda tayi shine zatazo tana ce masa honey? She's too much.
Da k'yar ya iya sakin gajeren murmushi "yana office." Yace ba tareda ya kalli fuskarta ba. Ganin baida niyan kisssing nata yau yasa ta gwada yunk'urin masa seta ga yayi dodging kiss d'in abinda be tab'a yi ba kafin tayi mgn yaja hannunta suka shiga ciki ya zaunar da ita kan kujera shikuma yayi kneeling agabanta tun a nan zuciyar Saaly ya hau bugu 100 kan 100. "Allah sa Ikleema bata gaya maka komi ba Fudail, Allah sa ba saki na zakayi ba. Omg!" A ranta tace. Shiya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta fad'a daya kira sunanta complete abinda be cika yi ba. "Saalihah!" A razane ta amsa "na'am" cikin wani mirya me b'ari, da idanunta suna kallon k'asa. Hannu ya mik'a ya d'ago fuskartan suna kallon cikin idon juna tuni taji hawaye sun ciko mata a ido.
"Yau dana fita office kin fita?" Ya tambayeta a nitse.
Innalilliahi wa inna ilaihi raji'un abinda take ta nanatawa knan a zuci ko k'adan takasa amsa tambayarsan, gudun kar tace yes yace ina? Setace meh? Taje wani wai shi Tasleem ya shafa mata jiki? Tabbas tasan tashin hnkl babba ze biyo baya.
"Saalihah just answer me kinfita yau bayan dana fita office? And ina kkaje?" Fudail ya sake jefa mata tambaya
Yanzu kam hawaye ne suke tsiyaya daga idanunta bakinta se b'ari yake sam takasa amsa sa.
"Just answer me Saalihah!" Ya fad'a cikin wani erin tsattsawan murya a fusace. B'ari take sosai tana girgiza masa kai bata tab'a ganin Fudail a erin wannan yanayi na yau ba. Gani take kamar ba charming Fudail nata data sani bane. Da k'yar bakinta ya iya furta "NOO!. NO... fudail dan Allah kayi hakuri let me explain everything..." Ta fashe cikin wani erin matsanancin kuka.
Shima kukan ne yafi k'arfinsa. Cikin wani erin murya cike da tausayi yace, "again kin sake mun k'arya Saalihah, you've lied to me for the very last time, nabaki one last chance and kin sake watsi dashi. You've rubbed it to my face bakia sona Saaly." Enevelope d'in ya mik'a mata "explain this." Hannu na b'ari ta amsa ta bud'e ganin pictures d'in yasa tasake fashewa dawata erin kuka me tsuma zuciya bata gama gani ba ta ajiye kan kujera tasa hannu ta share hawayen da suke zuba har ynzu, hannunsa ta gwada rik'ewa yaja. "Fudail dan Allah give me a chance to explain, its really not what you're thinking wallahi I've never once cheated on you, am not having an affair. Wannan pictures... Wannan pictures..." Ta kasa k'arisa maganan se kukan dayafi k'arfinta
"Wannan pictures had'in computer kkeson kice?" Fudail ya tambayeta, zuciyarsa se k'ona take masa. "Answer me! Had'in computer ne?" Cafko ta yayi "answer me! Saalihah" A razane tace "NO ba had'in computer bane, ba had'in computer bane Fudail but..." Hannu ya d'aga mata "enough Saalihah. I've heard enough of your lies. Through out our marital life, ban tab'a harming naki ko mistreating naki ba, abinda kkeso shi nake miki, ban tab'a cheating akanki ba, ban tab'a miki k'arya ba I just cant understand mesa ke kka min duka wad'annan abubuwa. Why? Why Saalihah? Is it true bakia sona? Kinada wanda kkeso, and shine na kan picture'n nan and dama you are not who you told me you are? Mesa zakimin k'aryan who you really are. Saalihah ko a talakan ki kika zomin i'll love you and will marry you, you don't have to pretend to be rich. I just can't get it. Ina kka samu kudi har kka kama muku mansion dincan? And your car too? Saurayin kine duk ya baki?"
Kai kawai take kad'a masa how she wish zata iya amsa masa wad'annan tambayoyi. Hawaye se ambaliya suke a fuskarta "noo Fudail dan Allah kabary, stop it plz, none of these were true Fudail, I've loved you and I will always. Wallahi i've been wanting to tell you everything I just can't bring myself to tell you dan Allah kayi hkr. Wlh wannan ba saurayi na bane, kai nakeso ba shiba Fudail, I..I..."
"You what Saalihah?" Ya daka mata tsawa "Explain it then me kkeyi a jikinsa haka?"
"Fudail believe me this once, wallahi Tasleem ba saurayi na bane, am not having an affair with him" (se yanzu Fudail ya gane waye acikin hoton. Tasleem ex na Saalihah)
"Taya? Taya kkeso nayi believing naki Saalihah bayan you've never been honest with me, never once. Kinsani Saalihah I love you, I love you so much. Duk da erin k'arerayin da kkamin a baya I've decided to forgive you inhar zaki gayamun gaskian da bakinki but I just asked you a simple question yau kinfita dana tafi office? Kkace min NO while actually answer'n yes ne. Ni yanzu just tell this, shi kad'ai nakeson sani. Cikin dake jikinki is it mine or na Tasleem??? Plz Saalihah dan Allah karki min k'arya for once ki gayamun gaskia. Tell me, cikin waye ne?" Hannu yasa ya share hawayensa.
Sam ta kasa dena kuka, a ranta tace tayaya Fudail ze tambayeni wannan question bayan yasan shine d'a namiji daya fara kusanta ta, shi ya raba ni da MARTABA TA (littafin swt ummi aisha). Cikin kuka tace, "Fudail we both know cikin danake d'auke dashi naka ne, cikinka ne, ban tab'a kusantar wani d'a na miji apart from you ba, kai ka rabani da MARTABA TA Fudail kai..." Bata k'arisa maganar ba sukaji anyi banging k'ofar suna kai dubansu sega Ikleema wanda ga dukkan alamu tun d'azu take lab'e tana jinsu....
No comments:
Post a Comment