KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
(Like Mother Like Daughter)
⚜⚜⚜♠♠⚜⚜⚜🌟
written by miemie👄
7⃣1⃣
...tasowa tayi ta tattara pictures d'in Saaly da Tasleem da Fudail yayi watsi dasu a k'asa, ta matso hawaye kamar dgsk sannan ta matso inda yake "son nima bansan me zanyi ba, Saalihah tacuce mu, taci amamar mu for all this while she've been cheating on you despite tasan yadda kake sonta. Kalli pictures dinnan" ta soma nuna masa one by one. Daga wanda T boi ya rik'o hannayen Saaly bibbiyu da duka hannayensa, se wanda yake shafa fuskarta, se wanda ya rike kwankwasonta, se wanda fuskarsu kusa kusa da juna suna breathing air d'in juna. Abinde ba kyan gani.
Allah sarki! Fudail, he's world is crashing ji yake kamar ya kashe kansa right now that is the only thing he is feeling. Kuka yakeyi sosai, tun Ikleema bata gama nuna masa pictures d'in ba yasa hannu ya wabce yayi wurgi dashi. "Mummy wannan ba Saaly bace, tell me plz, ki gayamun me kama da mata tace, I know Saaly she'll never cheat on me. Saaly na sona kamar yadda nakesonta, this is just a trick. Mummy ki gayamun had'in computer ne, plz don't tell me Saalihah ta ce." Rungumosa tayi tana shafa bayansa a hnkl tana basa hkr wane d'an yaro making him feel home.
"Kayi hkr son, I know this is hard to believe koni ban yarda ba at firsrt danaga hotunan nan. Amman you're a well educated person Fudail kasan real images, da wanda computer ya had'a. Ka kalla dakyau wannan pictures ba had'in computer bane ita reality. Saaly is cheating on you. Ba kai takeso ba kud'inka takeso zuciyarta tana wajen wannan tsinannen dake shafata haka." Kansa kawai yake kad'awa har yanzu ya kasa yarda ga abude zahiri yanagani a gabansa amman brain nasa yakasa believing at all. Se kuka yakeyi me tsuma zuciya. "Kayi hkr son" Ikleema ta fad'a tare da sakosa tasa hannu ta share mai hawayen. Wayarta ta d'auko ta kunna masa recording da sukayi editting suka caccanza abubuwa da dama a ciki. Daga daidai wajen da Saalihah tace;
"Se meh? Fudail will never believe a word from you, he's blinded by my love. Na yarda talauci ne ya haifeni yakuna rene ni, ko bakisan nasan time da kka tab'a kai Fudail gdanmu bane? Sarai na ganki and nasan da zuwanki saisa ma tun kafin ki kawosa na nema mana gda muka bar wancen gdan. You shud give up Ikleema der is no amount of word a duniyan nan dazaki gayawa Fudail ya yarda cewa ni 'yar talaka ce..."
Sega muryan Ikleema wanda ina kyautata zaton a studio dinne tayi maganar bama a gdan Saaly ba tana fad'in
"Innalillahi wa inna ilaihi raj'un, Allah ya isa tsakani na dake Saalihah, yanzu fisabilillahi kin kyauta ma d'a na kenan? Duk san dayake miki ace kin masa wannan k'arya? Kika b'oye mana true identity naki, kkayi living as a shadow sabda ya aureki kinsan sarai inda ke talaka ce daddy'nsa bare bari ya aureki ba. Duk mun d'au 'yar babban gda ce ke ashe kud'in samari da sata kawai kkayi amfani da kk mayar da kanki me kud'i 'yar babban gda koh? Toh wlh sena gayawa Fudail and kinsan sarai Fudail hates being lied to. Just tell me how will he feel in yagano gaskia Saalihah..."
Muryan Saaly
"Se meh? Fudail will nva bliv a word frm you sbd he's blinded by my love. Jahilar jahiliya kawai...."
Hannu Fudail yasa ya k'wace wayar tare da yin wurgi dashi sanda wayan yayi breaking into pieces. Zuciyarsa tafasa yake, ko zaki ya gansa seya basa gu. Nishi yake kamar zakin dayaga naman daji, idanunsa sun kad'a sunyi jazir. Ji yake kamar kawai inyaga Saaly ya bugata da bango ya matse mata mak'ok'aranta seta bar numfashi. Har ya mik'e da nufin fita se kawai ya sake fad'i k'asa sbd yadda zuciyarsa ta karye, bayida k'arfi anymore, he has never felt so heartbroken like this. Duk yadda yayi k'ok'arin had'iye kukan yakasa jikin Ikleema ya fad'a yana kuka yana sumbatu.
"Mummy what wrong have I ever done to Saaly to deserve this? Mena mata plz, I've never once mistreated her, I loved her, she's my everythng, ina santa fiye da yadda nakeson kaina. Mesa zata k'arya min zuciya haka? Mesa zata ci amana na? Or maybe love dana bata was not enough, I should have tried harder. This is all my fault mummy..." Ya sake fashewa cikin wata erin matsanancin kuka.... "Its not your fault son, kadena blaming kanka sbd Saalihah ita ta zab'i bin mazan waje ba kaika sata ba. Ko a fairy tales bara a aibanta soyayyan dakake ma Saalihah ba. Kaso Saalihah son, Saalihah ta k'ika ta watsa ma soyayyan dakake mata k'asa, for all this while zuciyarta ba agunka take ba, ta aureka ne kawai dan taci kud'inka ba kai takeso ba... Saisa tun farko ni ban goye ma auren ku baya ba. Abinda babba ya hango yaro koda ya hau kan tudu bare gano ba. Akoi mumunan abinda na hango maka cikin auren wannan yarinya sesa nace banaso kar ka aureta amman sam ka nuna kai inba ita ba baraka aure wata yarinya ba. Sbd yadda nakesonka Fudail yasa na amince maka. Aiga irinta yanzu, kaga matsalar rashin jin maganar uwa knan."
Kukan nasa ne ya tsananta, ga wani zogin da kansa ke masa. Tabbas ba k'arya ko kad'an cikin abinda Ikleema tafad'a yanzu da yajita can a baya da Saalihah bata karya masa zuciya haka ba, daya ji Ikleema ya auri Asma'u da zuciyarsa bata karye ba yanzu da... "Am so sorry mother, am gravely sorry for not listening to your words, dan Allah kiyi hkr, nayi nadaman rashin jin mganar mother na. Danaji maganar ki da duk haka be faru ba..."
"Shhhh kukan ya isa son, ba laifinka bane, Saalihah ce take controlling maka hankali daba dan yadda natashi maka da addu'a ba wlh data gama asirce min kai gabad'aya. Stop crying yanzu se mu godewa Allah daya bayyana mana gaskiar al'amarin."
"FUDAIL!" Ta kira sunansa a hnkl ya taso daga jikinta wane d'an yaro yana kallonta da idanunsa da sukayi jazir cike kuma da hawaye, "na'am mummy" ya amsa. "KA SAKI SAALIHAH RIGHT NOW! KA D'AU TAKARDA KA SAKETA NACE. KASAKI SAALIHAH FUDAIL!" Ciwon kansa yaji ya k'aru fiye da na da. Ji yake k'wak'walwarsa yana tarwatse wa, he can't accomodate abinda kunnesnsa suke jiyo masa na kalman SAKI. Ji yake kamar ze haukace, how he wish duk wannan mafarki ne.
"Mummy I can't take this anymore, plz do something nabar tunanin wannan abubuwa in mafarki nake plz wake me up. Am tired I don't know what to think anymore, mesa Saalihah zata min haka? Mesa mummy? Taya zan saketa mummy? Through out my life ban tab'a kawo saki acikin plans na rayuwa na ba. Saalihah is carrying my baby, bansan mesa zata na ganin wani a waje ba bayan she's pregnant with my kids. Da tun farko tagayamin bata sona da..." Kasa k'arisa maganan yayi dan kukan dayafi k'arfinsa.
Komin rashin imanin mutum inya kalli Fudail se zuciyarsa ta karye ya tausaya masa dan yadda yake kuka. Ita kanta Ikleema sanda ya bata tausayi. Allah sarki! Fudail...
No comments:
Post a Comment