Monday, 29 January 2018

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
(Like Mother Like Daughter)
⚜⚜⚜♠♠⚜⚜⚜🌟
      written by miemie👄
                  6⃣6⃣



           ★★★

     Isar Ikleema gda keda wuya,  ta jefa jakanta kan gado se nishi take wane zaki. "Wlh baki isa ba Saalihah, I have a better plan in store for you, mstwww"****

        ★★ 3 WEEKS LATER.

     Saaly da Fudail nata kuwa ba abinda ya k'ara had'asu. Ciki de har yanzu ba labarinsa. As for Ikleema kuwa tana kiran Saaly yawancin bayan 3-4 days suna gaisawa. Ameenatu ma ta kawo mata visit haka su Bint da Phaary ma. T boi kuwa har ya gaji da jiran rananda Ikleema zata gudanar masu da plan nasu, kullum yamata mgn se tace da sauran time.

        Yau ranar ta kama monday tun daren jiya Saaly kejin wani iri-iri kaman zazzab'i saidai be kwantar da ita ba, ga wani k'yank'yamin datake ji dashi. Ko kitchen tashiga seta toshe hanci. Yau monday ma da kyar ta tashi ta had'a ma Fudail ruwan wankan duk kasala takeji.

(ni miemie nace bade ciki ne dake ba Saaly, aikuwa da munyi rangem nida fans)

         Haka sime-sime ta shirya Fudail office. Bayan tafiyarsa ta samu ta kwanta tasha bacci sosai. Se can after 12 ta tashy tayi wanka ta d'anyi light makeup sede yau ko kamshin turare battaso. Haka akayi wanka ba a shafa turare ba. Sauk'a k'asa tayi ta kira Habeeba suka fara had'a lunch by mistake hannun Habeeba ya buge k'wai ya fad'i ya fashe a k'asa take k'arnin k'wan ya tashi ya fitini Saalihah. Amai kawai ta fara kwararowa cikin sink d'in kamar zata harar da hanjinta. Se sannu Habeeba ke mata. Rakota tayi ta zaunar da ita a parlour, "in kawo miki ruwa ne anty?" Kai kawai ta kad'a mata da nufin a'a "barshi jeki aza macaroni, minced meat za'a sa ciki kinji kiyi sauri kar uncle ya dawo ba abinci." "Toh anty sannu" tace sannan ta shige kitchen d'in.

        A hnkl bacci me nauyi ya isketa Saaly akan kujerar. Se kusan to 4:00PM ta tashi ta haura sama da k'yar ta sake wanka tayi alwala tayi sallah. Powder kawai ta shafa ta sa wata red doguwar riga voyle me torches black, ta d'aura kanta sannan ta d'au wayarta ta d'an kikkira gida dasu Phaary. Can taji k'arar shigowar motan Fudail. Badan tanaso ba ta sauk'a ta taresa daga parlour sede kallo d'aya ya mata ya gano batada lfy sosai. Dan yau ko kwalyan da aka saba masa ma ba ba'a masa ba yau.

          Hugging nasa tajeyi se k'amshin turarensa ya hanata da sauri ta koma baya tareda toshe hancinta. Har tasa Fudail tsarguwa ya d'au ko wari yake yau. "Sweeey lfy?" Kafin tayi mgn aman yafi k'arfinta guest toilet dake parlour'n tafad'a da gudu, Fudail yabi bayanta da wuri, amai ta ringa kwararo no full stop. Sanda tayi me yawa sannan yataya ta wanko bakinta suka fito tare kan kujera ya zaunar da ita. Wani jiri jiri take ji. "Sweery whats wrong? Kinci wani abu ne ko bakida lfy ne?" A hnkl tace, "wlh nima bansani ba hun, but don't worry I'll be fine kamshin turaren naka ne banso, kwata kwata banasan kamshin turare again." Fudail yace, "tohhh ba lafy ba, dole muje asibiti a dubaki."  "Honey no need, nakega zazzab'i ne kawai hurry kaci abinci kar yayi sanyi, ina Habeeba je kiyi serving uncle."

       Fudail dake kallonta tausayinta na kamasa yace, "sweery muje asibitin kafin nan, bakida lfya gashi har idanunki sun fad'a, Habeeba d'auko mata mayafinta a d'aki." Har Habeeba takama hanyar d'akinsu Saaly ta dakatar da ita. Haka tasa Fudail cin abincin dole. Hankalinsa duk na kan ta, yau ko abincin ma bata iya taci ba. Indomie zalla batare da an masa had'i ba Habeeba ta dafa mata shine ma tasamu ta d'an ci.

          Haka ranan ta wuni tanayin abu langwai-langwai ga ko kad'an battasan k'amshin turare. Da daddare kam da zatayi wanka ma tak'iyi da sabulu wai shima wari yake mata. Washegary kuwa Fudail da kansa ya shirya zuwa office dan kwata kwata Saaly batada k'arfi sede alhmdllh ba zazzab'i, kawai kasala ne. Yau ma indomie farinsa Habeeba ta dafa mata da d'an kaza akai.

          D'an b'antaran kazan tayi taga jini da gudu ta fad'a toilet ta rigayin amai sannan tafito. "Habeeba! Habeeba zo nan" nan da nan ta iso d'akin "na'am anty"  "kalli kazan can" tana nuni da plate d'in abincin data tura gefe dan batta ma k'aunar sa kwanon a idanta again. "Haka ne kin wanke kazan? Ga har jini aciki. D'auke min plate d'in daga gani ki had'o min black tea kawai."  "Toh anty, kiyi hkr" bayan 2mins ta dawo da black tea ta mik'a mata.

        Yauma haka tayi wanka ba sabulu koda tafito kuma bata fesa turare ba kayan kawai tasa tashafa powder ta kwanta, Habeeba ce ta girka lunch, tun daga sama k'amshin girkin ke tayar mata da hnkl haka ta ringayin amai kafin Fudail ya dawo Saaly tayi amai a k'alla sau 3. Tazo ko k'arfin tashi ma batada. Haka ta zube kan gado kawai har zuwan Fudail tana jin k'arar motarsa amman bata iya tashi ba. Shima de yau kamar jiya Saaly bata masa sannu dzuwa daga wajen parking ba anyways daman baya expecting yau sbd yanayin daya barta da safe.

         Yana shigowa ciki yaga Habeeba na had'a kan dining sannu da zuwa ta masa sannan ya haura sama. Yana shiga Saaly na ajiye wayarta "sannu da zuwa honey, wlh kwata kwata banda k'arfin sauk'a k'asa yima sannu da zuwa am sorry"  jakarsa ya ajiye kan wata couch sannan ya k'ariso gabanta "mummy ce ta kirani yanzu wai tana gaisheka." Be amsata ba yace;

         "Sweery bakida lfya, whats wrong?" hannu tasa ta toshe hancinta, "honey turaren nan wari yakemin" take ya cire kayan jikinsan ya rage da shorts kawai sannan ya matso kusa da ita ya tab'a jikinta yaji de ba zafi sosai. Nan ma se toshe hancinta take dan k'amshin ya riga ya kama jikinsa. "Sweery, kinga period naki this month?" Ya tambayeta, shiru tayi na d'an lokaci sannan tace "no, yakamata tun shekaran jiya yazo but naji shiru."  "Then you must be pregnant!" Ya fad'a yana murmushi.

          Batasan sanda ta zauna ba "am what? I can't be, I can't be pregnant Fudail karma mu sa kwadayin mu ciki." Murmushi ya mata sannan ya d'au wayarsa yakira wata family doctor'nsu. Ko k'adan Saaly batasan Fudail ya matso kusa da ita dan batta son k'amshin jikinsa. Daga can gefen gadon ya zauna yana mata sannu. Can Habeeba tayi knocking bisa k'ofar "uncle ga likitan tazo"   "toh kushigo" nan ta bud'e kofar tashigo da dr'n ciki itakuma ta koma k'asa.

         Bayan sun gaisa da Fudail ta gaishe da Saaly da jiki sede kallo d'aya tama Saaly ta gano shigan ciki ne da ita. Murmushi ta saki sannan tace, "ahh congratulations ango, your wife is PREGNANT!" cike da rashin fahimta Saaly tace, "am what?" Fudail kam sujjada yayi tuni a wajen. Dr'n ta murmusa sannan tace. "you are pregnant dear." Saaly kam takasa believing abinda takeji "kide gwadani dr d'an zazzab'i nefa kawai." Pregnancy test strip kawai ta mik'a ma Saaly kan tashiga ta gwada da kanta ma. Hannunta na k'yarma ta amsa ta shiga bayi Fudail yabi bayanta.

        Ta gwada, bayan 'yan lokaci yayi reading positive haba!! zo kuga murna gun Fudail da Saaly. Besan sanda ya d'agata cak a bayin ba itama dan murna bata san sanda tayi kissing nasa ba.

      Ni mimie nace ashede Saaly'nmu ba juya bace, lokacin ne kawai beyi ba. Nide na kunna rangem!!!

No comments: