Monday, 29 January 2018

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
(Like Mother Like Daughter)
⚜⚜⚜♠♠⚜⚜⚜🌟
      written by miemie👄
                  7⃣0⃣



        Ikleema ta numfasa sannan tace, “Wannan wace erin yarinya ce? Daga fitan mijinki seki tafi yawon banza kema? Wato k'afansa k'afanki, Allah de sa ba yawon gantali kke zuwa ba karki kwaso mana k'anjamau nida d'a na sbd ina kyautata zaton wannan ciki ma bana Fudail bane na d'aya daga cikin samarukan da kke alak'a dasu ne." Daga yadda Ikleema ke mgn yasa Saaly ta gano dole she has somethng to do with what happened just now. Hannu tasa tashare hawayerta, taku d'ai d'ai tayi har ta k'araso inda Ikleema ke xaune, ganin haka itama ta mik'e suna fuskartan juna. "Ko baki fad'an ba nasan keda Tasleem bakin ku a had'e yake sbd tunba yauba kkeson rabani da Fudail sede Allah yafi k'arfinki Ikleema. Inba jahilci da k'arancin ilimin addini ba taya zakisa k'aton banza kamar Tasleem yashafa miki matar d'a? Ai inba jahilar jahiliya ba, bameyin wannan jahilcin." Dariya sosai Ikleema ta saki, "kirani da duk wani sunan zagin da kkeso a fad'in duniyan nan Saalihah baran damu ba sbd kin kusan barin gdan nan, nan bada jimawa sbd haka tun wuri kije ki soma tattara kayakin ki, zan maidake hell where u came from. Talaucin daya haifeki, ya reneki shi xaki koma garesa, ko bakisan nasan asalin ki bane? Talaka cefa ke, kika b'oye ma Fudail asalin identity naki kka riga sata da cin kud'in samari and made Fudail believed ke 'yar babbar gda ce. How do you think he'll react in yayi finding out gaskian al'amarin kan matar sa dayakeso sosai ta masa k'arya.”

         Take taji zuciyarta ya karye, tabbas ba k'arya cikin  abinda Ikleema tace and her biggest fear is ranada Fudail ze gano gaskiar al'amarin. If only zata iya saminsa ta gaya masa gaskian da tayi amman barata iya ba. Batasan ya rabu da ita a sanadiyar haka. Cikin b'acin rai Saaly tace, “se meh? Ai ina sane sarai kinsan kowace ni sede da saninki da rashin saninki duk d'aya ne sbd it will not change a fact btw us. Sbd Fudail will nva believe a word from you, he's blinded by my love. Na yarda talauci ne ya haifeni yakuma rene ni, ko bakisan nasan time da kka tab'a kai Fudail gdanmu bane? Sarai na ganki nd nasan da zuwanki sesa tun kafin ki kawosa na nema mana gda muka bar wancen gdan. You should give up by now Ikleema, there's no amount of word a duniyan nan dazaki gayawa Fudail ya yarda cewa ni 'yar talaka ce.

       Ikleema tace, “humm humm humm yarinya nagode sosai da wannan information, it will be of great help to me” tana kaiwa nan ta fice. Tabar Saaly cike da mamakin abinda ta fad'a. "Kamar ya tagode da wannan information?" Ta tambayi kanta. "Innalillahi! Ya Allah kasa ba recording abinda nafad'a anan tayi ba. Wayyo Allah, ka d'auki raina kawai in mutu in huta..." Sauk'a tayi a k'asan gun tata shark'an kukanta without a full stop. Ikleema kuwa tana ficewa ta zarce inda sukayi zasu had'u da T boi. Already har an wanke pictures da wancan munafikin ya d'add'aukesa shida Saaly. Amsa tayi ta kalla one by one sannan tace, “nice job Tasleem. Aiko just as we expected abinda nike da niyyan banzan tafad'a shi ta fad'a  barin maka playing kaji.” Nan ta ciro wayar ta kunna masa karara kukejin muryan Saaly daidai wajen tayi trimming recording d'in sannan suka shiga cikin studio'n akayi editting audio d'in. Duban agogo tayi taga 11:00AM on the dot, nan sukayi sallama ta koma gda. Jira kawai take k'arfe 1 ya buga ta kira Fudail.

         Saaly kuwa da k'yar ta tattara kanta ta haura sama dan kukan datayi ko k'arfin tafiya batada, Habeeba ce kad'ai ta girka lunch. 30 mins to 1 ta fad'a toilet tayi wanka sede duk yadda tayi k'ok'arin b'oye mood nata ta kasa musamman ta tuna erin rik'o da shafa tan da T boi ya rigayi, wani sabon kukan taji nason k'eto mata. 'Yar powder kawai ta shafa tasa wata simple abaya me kwalyan purple stones. Ta sauk'o k'asa ta zauna parlour tana jiran zuwan Fudail nata.

        Daidai 1:00PM Fudail ya baro office se Allah Allah yake yadawo gda yaga sweetheart nasa, a hanya ya tsaya ya riga saya mata kayan k'walama just as yadda ya saba. Yakusan shiga unguwansu wayarsa tayi k'ara yana dubawa yaga Ikleema, d'agawa yayi tare da fad'in

"hello mom?" Shiru tayi bata ce komai ba dan haka ya kuma fad'in “hello...?” Se k'aran kukanta ya jiyo

       Cikin kuka take maganar “son, ina kake?”

“Mummy, lfya kke kuka? What si going on plz, wani abu ne? Ina kke?”

 “Ina gda son, kayi sauri kazo you won't believe abinda zan gaya maka...” Taja hanci sannan tace, “ina jiranka.” Nan tayi hanging ba tare da jin abinda ze fad'i ba. Wata murmushi ta saki sannan ta tanadar masa da komi kan centre table dake parlourn gashi da ma daddy bai nan yana Abuja. Ko cikakken 20mins da gama wayar sun beyi ba sega Fudail yashigo gdan. A rikice ya fad'a parlourn yaganta zaune kan kujera tayi tagumi kamar wacce aka ma rasuwa. Nufowa yayi gabanta duk jikinsa ya mutu dan gani yake kamar wani abu ne yasami daddy'nsa. A gabanta ya tsuguna “mummy meya faru?” Shiru tayi sannan ta d'ago jajayen idanunta data shafa masu robe ta mik'a hannu kan cente table d'in ta d'au wata envelope ta mik'a masa.

         Amsa yayi a takaice, “me wannan? Me aciki? Mummy talk mana in wani abu ne yasamu daddy plz let me know am not a child.” A hnkl cikin murya nitsattse tace, “kaide ka bud'e son baran iya gaya maka ba innalillahi! Wannan yarinya taci amanata, taci amanarmu Fudail” ta sake fashewa da kuka... Hannunsa b'ari yake sam ya kasa bud'e envelope d'in dukda ya k'osa yaga me aciki and wata yarinya Ikleema ke referring to? Wace yarinya cetaci amarmu? Ko k'adan be kawo a hnklinsa Saalinsa bane.

        Daga k'arshe yasamu ya bud'e envelope d'in tare da zaro pictures aciki wanda aka kafe bayansu. Zuciyarsa na bugun d'ari kan d'ari ya juya abinda ya gani ne ya mugun razana sa tare da basa mamaki. Kai kawai yasoma kad'awa kamar k'adangare take idanunsa suka cike da hawaye bakinsa na b'ari haka duk wani sashen jikinsa ma. Take farin fatarsa na fuska ya koma pink. Kallonsa Ikleema take kamar TV, ganin yadda hawaye ke d'iga daga idanunsa ya k'ara bata mamaki, abinda ta jima bata tab'a gani ba,  barata iya tuna when last Fudail yayi kuka ba, for sure shima Fudail bare iya tuna when last yayi kuka ba.

        Hoton Saalinsa ne, matarsa wanda yafi santa fiye da kowa, fiye da ransa ma da wani k'ato wanda sam ya kasa gane ina yasan fuskarsan amman de yasan for sure he's familiar with the face. Mutumin rik'e da matarsa, da d'ayan hannunsa kan kunkuminta  d'ayan kuma yana shafa fuskarta ga yadda yawani matsota kusa da jikinsa suna kallon juna. Wurgar da pictires d'in yayi a k'asa ba tare da yaga sauran ba. Ihu ya saki “NOOOOO!!! this can't be true. Wannan ba Saaly na bane, me kama da ita ne, ba ita bace Ikleema. Plz tell me ba Saaly bace” Yana kuka kamar d'an yaro ji yake kamar duniyarsa na juya masa tuni wani erin ciwon kai me k'arfin gaske ya rik'esa se nanata “this is not my Saaly”  yake a zuciyarsa. “This is not my Saaly, wannan ba Saaly na bane, she'll never cheat on me like that. I know her, ba ita bace...” haka yata sunbatu wasu erin zafaffun hawaye suna zubowa daga idanunsa, abinda ban tab'a gabi ba. Ban tab'a ganin Fudail a erin yanayi haka ba. Ji yake kamar zuciyarsa zatayi exploading ta fashe...

No comments: