KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
(Like Mother Like Daughter)
⚜⚜⚜♠♠⚜⚜⚜🌟
written by miemie👄
7⃣9⃣
"Tunanin Fudail kke koh? Kiyi a hnkl Saalihah, kinga baida kyau ma condition da kke ciki, kiyi hkr ki rage tunaninsa nasan ba abu me sauk'i bane amman yazama dole in bahaka ba zaki illatar da lfyar abinda ke cikin ki." Kai Saaly ta giad'a mata "nagode umma." "Yawwa 'yar albarka barin had'a miki ruwan wankan ko?" Nan ma kai ta kuma giad'a mata sannan Umma ta tashi taje bayi ta had'o mata ruwan ta mik'o mata towel tare da assisting nata zuwa toilet d'in.
★★★★
"Fudail dan Allah meh haka so kake ka kashe kanka ne?" Ikleema ta tambayi Fudail dake kwance kan gadonsa yayi ruf da ciki se kuka yakeyi. "This has to stop, haba son dan Allah kukan ya isa." Bece mata komi ba se kukansa da yake tayi. Wayarsa dake gefen sa ta mik'a hannu ta d'aga hoton Saaly kawai taga akan screen d'in, gaba da baya tayi taga duk pictures na Saaly neh a folder'n. A ranta tace, "se yanzu nagano dalilin wannan kuka, sbd pictures na shegiyan nan da ka kalla." Tsuka taja a fili sannan ta yi marking pictures d'in tas har zata danna delete se Fudail ya fisge wayar.
Da jajayen idanunsa yace, "me kkeson min a waya mummy?" B'ari tafara "inn..inaa... inasan namaka moving pictures d'inne sbd naga kamar duk sanda ka gansu se kayi kuka nikuma banaso." "Shknan karki damu, zaki iya fita zan kwanta" yace tare da juya mata baya. Hamdala tayi Fudail beyi suspecting nata ba. Jawo masa k'ofar tayi tayi tafiyarta.
Bayan maghrib din ranan da misalin k'arfe 8:30PM a gdansu Saaly suna zaune da umma a parlour. Sally ta duba agogo tace, "Umma anya baraki tafi ba? Kar abba da Sa'ad su shiga damuwa fa, karki damu about me, I'll take care of myself naji dadin jikina sosai d'an zuwan nan da kkayi." Umma ta numfasa sannan tace, "a'a Saalihah, baaba zata iya kula dasu ni ke nafi damuwa da, bakida lfya..." Katseta Saaly tayi "not at all Umma, wlh I can manage dan Allah karkisa in tauye ma Abba dasu Sa'ad hakk'in kasancewa dake."
"Ki tafi please. In shaa Allah if I need anything zan kiraki, nagode sosai umma Allah biyaki da gdan aljannah." Tasowa umma tayi ta zauna kusa da Saaly tareda rik'o fuskarta "kin tabbata 'yata? Karki damu dasu Abba, nasan ze gane mesa ban koma gda ba kuma aikinga zamu kirasa mu sanar dashi abinda ke faruwa..." "A'a umma dan Allah karki gaya masa banasan hnkalinsa ya tashi kinga kema banso gaya miki ba. Ki bari kawai tunda de yanzu nasamu sauk'i i'll be able to take care of myself Umma." "Toh shknan Saalihah tunda haka kkace, karkiyi wasa da maganinki kinji? Ki kuma dage da cin abinci ki rage tunanin Fudail na miki alk'awarin saki cikin addu'a." Saaly dake murmushi tace, "nagode umma na, ki gaida gda. Bari in raka ki." Umma tace, "a'a barshi kawai ai bakida lfya sannu ko semunyi yawa." Tana kaiwa nan ta fice. Ajiyar zuciya Saaly ta sauk'e ba tunanin wanda ya fad'o mata a rai se Fudail nata. Warhaka yawancin kullum suna zaune a d'aki suna hira. Hawaye kawai taji, da sauri tasa hannu ta share.
★★★★
Daidai 9:30PM a gidansu Fudail. Ikleema na zaune akan dining tanacin dinner kamar daga sama kawai tajiyo muryan daddy. A firgice ta mik'e. Kafin tayi wani k'wakk'waran motsi kawai tagansa a parlour'n. Yau akeyinta inhar daddy yaga Fudail a gda tana da tabbacin cewa da ita da Fudail gabad'aya zasu shiga trouble. Murmushin dole Ikleema ta k'irk'iro tare da masa sannu dazuwa ta k'ariso dashi kan dining. "Yaushe a gari alhj? Ba se upper week zaka dawo ba?" Ruwan Faro ya kurb'e tas sannan yace, "wlh, anyi cutting off meeting dinne saisa kawai nace zan dawo. Serve me, yunwa nakeji." Nan Ikleema ta zuba masa abinci se b'ari take. Allah Allah take ta zuba masa taje d'aki ta d'au wayarta dan texting Fudail kan kar ya baro site nasa daddy ya dawo. "Ina zuwa alhj" ta fada tare da mik'ewa.
Daddy dake tacin abincinsa yace, "haba Ikleema sekace bakiji dad'in gani na ba, kuma naga kmar hankalinki ba a kwance ba, wani abu ne?" Murmushi ta k'irk'iro "kai alhj na, kamar ya banyi murnan ganinka ba?" "Toh inhar kinyi murnan gani na kizauna sena gama cin abincin mua je d'akin tare." Ba yadda ta iya haka ta zauna hnklinta na kan Fudail. Hira daddy ke mata tana biye masa kad'an kad'an. K'ofar parlour'n suka ji an murd'a. A firgice Ikleema takai dubanta kan k'ofar tana addu'a Allah sa ba Fudail bane, Allah sa masu musu aiki ne.
Kasancewar duk masu shigowa parlour'n daddy basu bud'e k'ofar sesun yi sallama kuma an amsa yasa daddy yagano d'an gda ne dan haka yace, "Ikleema munada bak'i ne?" B'ari bakinta yake "ehm..ehm..." Bata karisa maganan ba Fudail yasa kai a parlourn. Ba k'aramin razana yayi ba ganin daddy, har da ze koma sekawai ya fasa. Bayan ya k'araso parlour'n ya zauna ya gaishe da daddy da kansa a k'asa, daddy ya amsa sannan yace, "son yaushe kashigo? Ina Saalihah?"
Bakin Fudail kasa furta ina Saaly take yayi. Ganin bece komi ba yasa Ikleema amsa tambayar daddy. "Ehmm Saalihah na gda kasan batada lfya, laulayi yasata gaba." Daddy yace, "ayya haka ne? Ka gaisheta da jiki toh." Yana maganan ne yana kallon Fudail. Sarai yasan halin d'ansa duk sanda Fudail ke k'arya mammatsa babban yatsansan hannun damansa yake tun yana yaro duk da cewan be cika k'arya ba se in abin ya gagara.
"FUDAIL!" daddy ya kira sunansa a fusace. A hnkl ya d'ago kansa "na'am daddy." Cikin muryarsa dake rawa "Ina Saalihah nace?" Daddy ya tambayesa. Shiru Fudail yayi bece komi ba. Ikleema tace, "alhj Saalihah na..." Bata k'are maganar ba daddy yace, "not a word Ikleema." Kup taja bakinta tayi shiru ganin yadda daddy is serious. Kallonsa yadawo dashi agareta yace, "Yanzu ni zaki kalli cikin idona kimin k'arya, iye Ikleema? Wlh ba haka nasanki ba. Ba haka kke ba Ikleema, ina Ikleeman danasani, me hnkl, mesan mutane, me tausayi dakuma fad'in gaskia a koda yaushe, ina take? Kin sauya halayen ki kap Ikleema tun kwanaki na lura da hakan kawai na miki shiru ne ina jiran ko zaki sauya da kanki amman kin kasa abin naki se worst yakeyi. Yanzu har Fudail kka sa akan hanya shima, d'a na da becika min k'arya ba se in takama."
Hawayen da Fudail yayi k'ok'arin rik'ewa ne suka fara zubowa cikin muryarsa dake rawa yace, "daddy dan Allah kayi hkr banso maka k'arya ba, karkayi fushi dani kayi hkr daddy." "Naji haushi Fudail, ka b'ata min rai. Abu d'aya zaka yi ka faranta min, ina Saalihah? Wani abu ne yashiga tsakaninku? Ko fad'a kukayi ka koreta gda kaikuma ka dawo nan sbd am very sure kayakinka ma anan suke dan tunda kayi aure baka tab'a visting gdan nan da dare haka ba. Gayamin meya faru. Ina jinka..."
No comments:
Post a Comment