Monday, 29 January 2018

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
(Like Mother Like Daughter)
⚜⚜⚜♠♠⚜⚜⚜🌟
      written by miemie👄
                  6⃣3⃣



          Ikleema tayi gyaran murya sannan tace, "son akoi wata maganar da nikeson maka ne dama." Fudail yace, "sure? Ina jinki toh." Shiru tayi na d'an lokaci sannan tace, "nafison ace mu biyu ne kawai, don't feel offended pls Saalihah maganan private ne." Sam Saaly bataji dad'i ba amman yata iya? Tace, "ba komai mummy" tadawo da kallonta kan Fudail "barin haura sama okay?" Hannunta ya jawo "NO! Bazaki ko ina ba, ban tunanin akoi maganar da za'a min a fad'in duniyan nan wanda mata ta bara taji ba. So mummy, in har zakimin mgn in private Saalihah has to be there because she's my wife inhar kuma baraki iya fad'a min a gabanta ba shknan na yafe bansan ji." Yayi concluding yana rik'e da hannun Saaly gamgam.

       Cike da mamaki Ikleema tace a ranta "lallai Fudail, yarinyan nan bade asirce ka tayi ba. Me haka? Toh wlh ba asiri ba Allah sa bokan gabad'ai ta sauk'e maka agidannan wlh sena rabaku." Murmushin k'arya ta k'irk'iro "toh shknan tunda haka kace son, kuma kayi gaskia, matar mutum sirrinsa." Ta numfasa sannan ta cigaba; "dama kafin nazo nan daga asibiti nake ina 'yar k'awata da aka muku aure taren nan? Hamdiya?" Fudail yace, "ohh eh nagane ta, lfy daiko?" Ikleema ta murmusa tana kallon Saaly "eh lafya wlh shigan ciki ne da ita na wata biyu ma kuwa...

         ...Bakaga yadda mijinta yaji dad'i ba." Take jikin Saalihah yayi sanyi rananda take gudun zuwansa yazo. Rananda Ikleema zata zo mata mgn ciki. Batasan sanda hawaye ya ciko mata a ido ba. To Ikleema's suprise se Fudail yace, "ayya to yayi kyau, Allah raba lfy."  "Whatt!!??" Ikleema tace a ranta "taya Fudail ze nuna beko damu da rashin haihuwar wannan pand'ararriyar matar tasa ba, kode tana da ciki ne? Kai da kyar wannan hegiyar batai kalan me ciki ba. Toh mesa ze nuna bai damu ba? Aiko ba abin mamaki bane wannan yarinya asirce sa tayi, shknan ta asirce min d'a."

       Nan ta bar mgnan zucin tace, "ameen" da idanta kan Saaly. Ganin idan Saaly cike da hawaye yasa ta gano batada ciki and daga gani akoi wata matsala. Dariyan mugunta tayi a ranta sannan tace "toh son dama nima zancen daya kawoni knan, kasan na k'osa inga jininka. Inasan inga jika na nima." Fudail ya murmusa sannan yace, "karki damu mom, when the right time comes, muyi hkr mujira muma." Nan ne Ikleema tayi confirming Saaly batada ciki. Seta wayince "ban gane ba son, kasan ko kunkusan wata biyar da aure? Karka gaya min Saalihah batta da ciki har ynxu dan Allah!" Fudail yace, "abin mamaki ne?" Nanne ya dawo da kallonsa kan Saaly yaga fuskarta duk ya jik'e da hawaye. "Sweery kukan me kika kuma fisabilillahi?" Hannu tasa ta goge hawayerta batare da tace komi ba ta ruga a guje izuwa d'akinta ta bararraje kan gado tana kuka me tsuma zuciya, sekace zata cire ranta. Mik'ewa Fudail yayi zebi bayanta Ikleema ta kira sunansa da k'afi "FUDAIL!" Cak ya tsaya ta taso tasha gabansa.

       "Meke damunka Fudail? Me Saalihah ta maka? Kwata kwata ka soya halayenka, ace wata biyar da aurenku amman matarka batada ciki kuma baka damu ba? Yanzun da ana biki bayan wata d'ai kaji mata tasamu ciki amman kace kai baka damu ba...?

   ...Toh wlh in kai baka damu ba ni na damu, kuma dole muje asibiti ayi gwaji wayasan ko JUYA ka auro baka sani ba." Tsawa ya daka mata cike da b'acin rai "ENOUGH IKLEEMA!" Sanda takusan cin tuntub'e dan yadda tsawan ya tsora tata. "Not a word. Me naki aciki koda juya ce Saaly? And ba'a d'aukan shekara da shekaru ne sannan a haihu? Ni nasan matata ba juya bace haihuwa zata haihu sede ba ynxu ba and koda bata haihu bama ni baran damu ba. Ai dama kafin na aurota ba contract mukayi signing kan dole seta haihu ba. Haihuwa na Allah ne zancen zuwa asibiti kuwa be tashi ba. Ke da haka daddy ya miki zakiji dad'i ne? Ai gara Saaly ma akanki tunda ita its just 5months kekuma fa?  Bara ma ki iya irga shekaru ishirin danawa kkayi a gdan daddy baki haihu ba. Daidai da rana d'aya ya tab'a tilasta miki se kinje asibiti ne? Be fair once in your life Ikleema. Kinsan ko kin d'au alhakin Saaly yanzu? In kinsan nan gaba in kkayi stepping foot naki a gdan nan mganan da zakimin kenan plzz karki sake tako k'afafunki gda na. Leave, now!"

        K'in motsawa tayi. Maganan da Fudail ya gaya mata ba k'aramin k'ona mata zuciya yayi ba wato indirectly ya kirata da JUYA akan wannan shegiyar dayake kira da matarsa? Danne zuciyarta tayi tace, "son, wlh ga dukkan alamu asirce ka Saalihah tayi, she's the ine controlling all your actions, its obvious. Na yarda ni JUYA ce amman bekamata ni juya d'ana ya auro min JUYA ba. Haihuwa dole Saalihah setayi, kuma wlh gayawa daddy zanyi akan meh? Tun zuwanta gdan ne sede taci tayi kashi bata tunanin ajiye mana abu, toh ni hkr na ya k'are."

     Wawan kallo Fudail ya watsa mata da kanta tabar parlour'n a 360 dan tasan in ransa ya b'aci ko marinta ze iya kuma ba yadda ta iya ba abinda ta isa tayi. Tana ficewa, ya haura d'akinsu da gudu ya wangale k'ofar yaga Saaly kwance kan gado se kuka takeyi. Gabanta ya nufo da wuri yama rasa me zece mata baya ta juya masa ta cigaba da zabga kukanta me tsuma zuciya. Kneeling yayi awajen yama kasa koda tab'a ta, kukanta ba k'aramin tada masa hnkl yake ba, a hnkl yace "its all my fault sweery dan Allah kiyi hkr, I should have warned her never to step a foot in my house, plz forgive me sweery, stop crying dan Allah..."

No comments: