Monday, 29 January 2018

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA

๐ŸŒŸ⚜⚜⚜♠♠⚜⚜⚜
KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
(Like Mother Like Daughter)
⚜⚜⚜♠♠⚜⚜⚜๐ŸŒŸ
      written by miemie๐Ÿ‘„
                  6⃣1⃣



         'Yar murmushi ta saki sannan tace, "ko k'adan Tasleem, muje muyi mgn." Bayanta yabi daidai kan wata kujera suka zauna mganan yadda zasu bi su tozarta Saaly suka soma, sun kusan awa suna mgn can naji Ikleema tace, "daidai ne Tasleem, wannan shawarar taka tayi kaga in muka bi hakan, tabbas nasan dole se Fudail ya saketa, yana sakinta kaikuma se ka aureta nikuwa in aura masa cousin nasa, kokuwa?" T boi yace, "right mama! So ynxu ya zakiyi getting mana phone number'nta wanda take amfani dashi?" Shiru tayi na 'yan mintuna sannan tace, "oh yes I know how, yanzu de bani number'n ka" nan ya zuba mata a wayarta take tayi flashing nasa duk sukayi number'n juna. Ta mik'e "toh duk abinda akoi i'll let you know kabar tada hankalinka kaji? Saalihah will soon be urs." Se murmusawa yake "I hope so." Nan suka rabu***

          Yau ya kasance saturday ba aiki. Se bacci Fudail da Saaly suke sha se can around 10:30AM Saaly ta tashi dan ciwon da k'asar mararta ke mata. Wata ya zagayo knan. A hankl ta zame jikinta daga rik'on da Fudail ya mata ta fad'a toilet tayi wanka ta shirya kanta sannan ta fito tayi d'an light makeup taje wajen wardrobe sa kaya kawai ta zube a k'asa dan juyin da cikin ke mata "wayyo Allah!" ta saki k'ara da k'arfi. Take Fudail ya tashi a firgice "sweery!" ya nufo kanta "whats wrong?" Ya d'agota ya kwantar da ita kan gadon. Kuka shark'af shark'af Saaly ta soma tana rik'e kasar mararta. Duk tasa Fudail ya kid'ime yama rasa abinyi. Se sorry yake mata.

       K'asa ya sauka da sauri yaje ya b'allo mata mgn da ruwa sannan ya dawo har ynxu bata bar kukan ba. D'agota yayi ya kwantar da ita a  jikinsa, "sorry ko? Ungo sha." Ya mik'a mata mgani, amsa tayi ta sha yasake kwantar da ita a jikinsa yana shafa bayanta a hnkl har tasamu ta koma bacci. Nan yafad'a toilet yayi wanka sannan ya sauk'a kitchen shida Habeeba suka had'a breakfast.

      Komowa d'akin yayi ya zauna a gefenta tare da k'ura mata ido can ya d'aga hannunta ya had'a da nasa yana shafawa a hnkl. A hnkl ta soma bud'e idanta har ta bud'e duka. Murmushi ya saki mata, "sweetheart ya jikin?" Murmushin ta maida masa da sauk'i tana k'ok'arin zama. "Zaki iya sauk'a k'asa muyi breakfast ko in kawo miki nan?" Ya tambaya. "Awwn! You're so caring hun, karka damu jikin da sauk'i I can manage." Riga yaje ya zab'o mata wata simple ya tayata sawa sannan suka sauk'o k'asa, abincin ma shiya bata bayan sun k'are ci ne ya kalli fuskar Saalinsa seyaga kamar something is bothering her, hannunta ya rik'o cikin nasa.

       "Sweery wani abu ne? U seem bothered." Murmushin dole ta k'irk'iro "ba komai hun." Yace, "no we promised remember? No lying to each other, so tell me" kallon cikin ido ta masa sannan tace "Fudail don't you think is about time ace am pregnant?

       Yaufa 3months 2 weeks da bikinmu but har ynxu ba sign, yawancin wanda aka mana aure tare dasu duk sunada ciki. Is like bana haihuwa ne hun, abun yafara damu..." Katse ta yayi "shhh don't talk like that, its just 3 months? Ana kai shekara sometimes shekaru ma before asamu ciki so stop bothering yourself okay? When the right time comes zaki samu" ya k'are maganan yana mata murmushi. "Fudail promise me koda bana haihuwa barakamin kishiya ba please"

         Sema yaji ransa ya b'aci. "Taya zan miki kishiya sweery? Ure the only one, nifa ba haihuwar ki nakeso ba, ke nakeso sure in Allah ya bamu baran k'i ba but rashin samun cikinki be dameni ba ko k'adan and zancen bakiya haihuwa ma be tashi ba its just 3 months right? Mu tsaya mana mugani banasan in sake jin wannan mgn clear?" Kai ta giad'a batare da tace komi ba ganin yadda ransa ya b'aci. "Am sorry" tace kamar wacce zatayi kuka. "Nak'i" ya fad'a "sekinyi murmushi" murmushin ta masa a hnkl yace, "thats my lady, I love you"

            Can around 1:10PM. Ikleema na kwance bisa gadon d'akinta ta mik'e ta zauna sannan ta d'au wayarta ta kira kira Fudail alokacin kuwa Saaly na k'asa suna had'a lunch da Habeeba. Bugu d'aya biyu ya d'aga "hello mum?" On the other side tace, "son ya kake? Lfya qlou, you?" Ya amsa. Tace, "lfy daddy na gaisgeka ma."  "Ohh ina amsawa." Tace, "ya Saalihah kuma?"

       Yace, "lfyrta k'alau."  "Toh masha Allah ni banida ma number'n 'yar tawa gashi ko inasan mu gaisa."  "Ohh haba!" Yace "barin kai mata gu gaisa mana toh tana kitchen ai." Ikleema tace a ranta "shit! Ni lambarta nakeso ba gaisuwarta ba." Tace a fili, "aii barta mana kawai tunda tana aiki turomin number'n de zuwa anjima se in kirata mu gaisa ko yaya?" Fudaiol yace, "okay toh barin miki sendn." "Yawwa son ngd ina jira, se anjima" tayi hanging. Wani hamdala ta saki.

       Just a minute later Fudail yamata sendn number'n Saaly. Wani murmushin mugunta ta saki "Allah sarki Saalihah start couting your days a gdan Fudail sbd kin kusan barin gdansa, am very sure da wannan plan da mukayi coming up da Tasleem we'll be able to kick you out of his house. Nasan sarai Fudail ya washi a masa k'arya, da amasa k'arya gara anyi disgracing nasa a gaban mutane am very sure the moment gaskiar al'amarin nan ya iske sa hehe Saalihah sekin yi regreting sanin shi karan kansa Fudail din bale ni babarsa."

                 Number'n T boi ta lalimo ta kirasa bayan sun gaisa tace, "albiahirin ka?" Ya amsa da "goro" tace, "to ka kwantar da hankalinka number'n Saalihah na nan a wajena, yanzu Fudail yamin sendn" T boi ya daka tsalle sekace yana gabanta "haba! Min sendn dan Allah inji muryarta" Ikleema tace, "kaifa baho ne, taya zaka kirata? Ko ka manta plan namun ne? Ai har ka kirata yanzu toh ka b'ata mana plan din kenan. Kaide ka dad'a hkr nan da 'yan lokaci Saalihah will be all yours." T boi yace, "kinyi gaskia mama. Toh yanzu se yaushe xamui making move namu?" Tace, "nan koda da sati buyu haka sbd kar Fudail yayi suspecting wani abu."

     Toh masu karatu meh plan d'in wad'annan biyu?? Muje zuwa...

   

No comments: