Wednesday, 17 May 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


      written by miemiebee👄
                  5⃣9⃣



        Se can na dawo naga Saaly kwance jikin Fudail nata tana aikinta na kullum, shafa kan packs nasa shikuma yana shafa bayanta a hnkl ta turo pouted lips nata sannan tace, "hun gaskia ni baran yarda ba kullum nasa lipstick (jan baki) bayayin good 1 hour seka tand'e." Murmushi yayi yaje ze sake kissing nata hannu tasa da sauri ta capke bakin nasa "am serious fa, zaka fara biya na kud'in lipstick anytime you kiss me." Yace, "deal, nawa ne guda d'aya?" Tace, "ai ni elizabeth arden nake using, jan baki d'aya is worth 17K" Fudail yace, "fine, seki fara keeping record how many times nayi kissing naki a month ending each and every month nikuma zan biya. Every kiss is worth 17k agreed? But fa in har ke kka fara grabbing lips d'ina baran biya ba."

       Dariya sosai yasata "kai honey you're too much nifa wasa nake maka, taya xaka na bani 17k after every kiss am all your remember?" Peck ya bata a goshi "yes but still ni zanna baki inhar bara kina counting ba kuma ni zan..." K'aran knocking ne ya katse sa frm saying "zanna yi" "waye ne?" Ya tambaya. "Habeeba ce uncle, hjy ce tazo." Saaly tace, "mummy kuma? She just left some hours ago." Fudail yace, "meta dawo yi kuma? Is like tana visiting nan sosai ko? I don't want abinda ya faru tsakanin daddy da real mother na ya faru da ke Saaly I can't afford to lose you, tell me is she making you uncomfortable?"

         Saaly tayi shiru kamar me nazarin abu shirunta yasa Fudail ya gano answer'n "yes" ne. Yace, "fine i'll talk to her ta rage zuwa nan banasan ta tak'ura miki." Saaly tace, "honey is that necessary? Kabarta kawai is her right to come over here duk sanda takeso ai. Je ka sameta kar ta fusata." Fuskar Saaly ya d'ago da hannunsa "NO zan mata mgn okay, karki damu" yabata light kiss a baki sannan ya tashi ya zura jallabiya ya fice Saaly ta bisa da kallo. A ranta tace, "bansan how life will be without you ba Fudail, kora min hegiyar nan, daman banda gulma ba abinda ke kawota gdan nan." Hannu ta mik'a ta ciro wayrta daga side bed drawer wanda tun dawowarsu daga NY bata kunna ba.

       Nan ta kunna bint ta fara kira sekuwa suna tare da Phaary kuma maganarta ma suke kan kwana biyu sunjita shiru. Ringing d'aya biyu bint ta d'aga "Saalin Fudail knan kinyi aure kin manta damu." Saaly ta kyalkyale da dariya "amman fa sunan yamin dad'i Saalin Fudail." Bint tace, "naga da Nigerian line naki kka kirani karde har kun dawo?" Saaly tace, "tsohon zance ni nama mance inada waya am always busy with my husband yanzunma yafita ne nace baran kira inji ya kuke" bint ta wangale baki "Allaaaahh? Sekace a kanki a ka soma aure toh mukan muna lfya ya angonmun? Shima tunda kukayi aure ko d'an ace mana hi baiyi." Saaly tace, "lol mezeyi daku toh? Ina Phaary?" Bint tace, "yanzun nan tafita" Saaly tace, "ayya tadawo ki gaisheta am hanging up." Nan ta katse ta ajiye wayar.

        Toilet ta nufa tayi wanka tafito ta yi light makeup tasa wata guntun gown iya cinyarta na shan iska sannan ta zira hijabi akai ta sauk'o k'asa tasamesu suna zaune akan seperate kujera wajen Fudail nata taje ta zauna tace, "ina wuni mummy?" Ikleema ta murmusa sannan tace, "lafya 'yata da hijabi a wannan zafin?" Murmushi kawai Saaly tai batace komi ba. Hannunta Fudail ya rik'o yasoma wasa dasu, Ikleema na hararan hannun kamar zata cire idanunta. Can k'asan zuciyoyinsu kuwa inbanda d'ura wa juna ashar ba abinda sukeyi. Some minutes later Ikleema tace zata tafi Saaly ta d'au mata flask da basket nata suka mata rakiya bayan ta shige mota ne tace;

         "Ai 'yata barakina gani na kwana biyu ba zan d'anyi tafiya." Jaka ita a tunaninta Fudail be gayawa Saaly akan ze mata mgn ta d'an rage zuwa kwana biyu ba.   Saaly da dariya ya k'eto mata tayi k'ok'arin had'iyewa "ayya mummy ba komai Allah dawo dake lfya."  "Ameen" ta amsa "toh se anjima" ta kunna motarta ta fice.

        Fudail kuwa yaji dad'in amsar da Saaly tabawa Ikleema dukda tasan k'arya take. "Oya honey muje kayi wanka ko?" Saaly tace.  Yace "yes, sure kefa barakiyi bane?" Tace, "nikam ai nayi fitanka" Hannunta yajawo suka soma tafiya yace, "nifa na gaya miki kima dena yin wanka alone in ina gda dan definately semun sakeyi tare." Baki ta turo " hun (short form na honey) ni wlh mura ze kamani yau bansan so nawa nayi wanka ba agdan nan." Siririn hancinta yaja "in ya kamaki ai akoi magani and am sure ma bare kamaki ba."

        Suna shiga ciki suka haura d'akin su suka sake wankan*** Yau k'imanin one month knan rabuwan Ikleema da gdan d'anta. Ba k'aramin damunta abin yake ba ita so take ta sa musu ido tana watching Saaly closely sosai.  Saaly kuwa ba k'aramin jin dad'in rashin zuwan Ikleema gdanta taji ba. Batada wani worries ynxu kula da mijin ta take sosai ba ruwansu da fad'a. Gda kuwa taje musu sau biyu suma sun sake zuwa mata sau d'aya amman banda abba.

        Kasancewar yau friday tun 12 noon Fudail ke dawowa daga office. Bayan ta shiryasa office da safe ko bacci bata koma ba suka fara aikin fried rice da shredded beaf se pass 11 suka gama ta fad'a toilet tayi wanka ta cancare kwalya. Some minutes after 12 Fudail ya dawo as usual har wajen parking lot take zuwa ta taresa yauma kamar kullum tun awajen ya tand'e mata jan bakinta. Bayan sun shigo tayi serving nasa abinci sanda  yagama ci sannan suka koma d'akinsu ya rage kayan jikinsa ya rage daga singlet se boxer yace, "sweery ina recording list naki? Yau deal namu yacika one month lets balance your money." Kan Saaly ya mugun d'aure dan ita tama manta sunyi maganar cuz dawasa ta d'au maganar segashi Fudail be manta ba.

         Daman tana manne a jikinsa ta taso ta zaro idanunta sannan tace, "hun! Seriously baka manta da maganan ranan ba? Nifa da wasa na maka taya zaka biyani kud'i dan kayi kissing d'ina am your wife not your prostitute (karuwa)..."  katseta yayi "shhh I don't mean it in a bad way. So ina list nakin?" Tace, "babu" a takaice. Mik'ewa yayi yaje wajen wardrobe nasa tare da ciro wata paper sannan ya dawo ya zauna yasake kwantar da ita a jikinsa tare da bud'e paper'n ya mik'a wa Saaly karantawa tafarayi.

       Date; 03/03/2016 time; 7:56AM venue; parking lot (before leaving for work)

  Date; 03/03/2016 time; 4:25PM venue; parking lot (after returning from work)


Date; 03/03/2016 time; 9:25PM venue; bedroom (about sleeping)


 Haka yata rubuta kowani kiss da sukayi a watan daya gudana ko d'aya be bari ba. Ba k'aramin mamaki yabawa Saaly ba. "How? Yaushe duk ya ringa rubutun nan ni bansani ba?" Daga k'ark'ashin paper'n ta ga sum total N1,020,000 (miliyan d'aya da naira dubu ishirin) baki ta bud'e wangalau tare da zaro lumshashshun idanunta. "Whaaatttt!!???"



beeenovels.mywapblog.com

<script type="text/javascript" src="//ylx-1.com/bnr.php?section=General&pub=943192&format=300x250&ga=g"></script>
<noscript><a href="https://yllix.com/publishers/943192" target="_blank"><img src="//ylx-aff.advertica-cdn.com/pub/300x250.png" border="0" /></a></noscript>

No comments: