Wednesday, 17 May 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


      written by miemie👄
                  5⃣8⃣



            Suit nasa ta cire masa tare da loosening tie na wuyar shirt nasan suka nufa kan dining table ta zaunar dashi tayi serving nasu abincin. Spoon d'aya Fudail yakai baki yace, "humm yummy! Sweery you're really a great cook you know." Saaly dake blushing tace, "kaii hun! Just eat your food." Besake fad'in komi ba yacigaba da cin abincinsa a yayinda itakuma sam takasa cin nata ta tsaya kallon Fudail ba tareda ko kefta ido ba kalamun Ikleema na "wallahi! Wallahi! Sena rabaki da Fudail kinji na rantse" suka fara zuwa kanta kamin ta hankara setaji idanta yacike da hawaye hannu tasa ta goge dawuri. Daidai lokacin Fudail ya gama cin abincinsa ya d'ago kai suka had'a ido hud'u da ita.

         "Sweery whats wrong? Bade kuka kke ba?" yana mganan yana nufowa gabanta, itama tsaye tayi suna fuskantan juna ta k'irk'iro murmushin dole "am not crying kawai..." Katseta yayi "you're not crying? Kin tuna promise namu? No lying to each other koh?" Kai ta giad'a masa setaji zuciyarta nasake karyewa dan irin k'aryan datama Fudail, k'aryan da she's sure duk randa gaskia ya bayyano zata rasa Fudail nata sbd Fudail made it clear bayasan amasa k'arya, be iya reacting akan k'arya ba. "Fudail dan Allah kayi hakuri, am so sorry I can't just tell you. Fudail I'm..I'm..." sekuma tafashe dawani irin masifaffen kuka cubbing nata yayi acikin jikinsa yana shafa bayanta ahnkl yana bata hkuri sede kansa ya d'aure ya rasa meke sata kuka haka, parlour ya k'arasa da ita ya zaunar da ita kan kujera shima ya zauna sannan ya rik'o hannunta.

         "Is okay ko sweetheart kukan ya isa" yasa d'ayan hannunsa ya goge mata hawayen sannan yace, "tell me, what is it that you can't tell me?" Jajayen idanunta ta d'ago tana kallonsa sede sam bakinta yakasa motsi ita tsoronta kar bayan ta gaya masa yace ze rabu da ita. Something she can't stand it knan a ranta tace, "I can't afford to lose you Fudail, you're already a part of me."

        Hannunta daya d'an matsa ne yadawo da ita daga duniyar data wula. A firgice tace, "Fudail kasan ina sanka ko?" Kai ya giada mata "and I love you too." Ta cigaba, "Fudail I cant afford to lose you wallhi ina sanka fiye da yadda kake tsammani If I were to be given a second life I'll still choose you as my husband. I love you beyond ur imagination and expectations. Dan Allah komin ya abin yazo ya kasance daga baya pls don't send me out of your life...don't ever leave me"

           Shide Fudail be gano inda ta dosa ba ganin wani k'wallan nasan zubo mata yasa yayi sauri ya hau kissing nata this is the only way his sure ze iya calming nata, sun jima suna abu d'aya sanda ya tabbata she's calmed sannan a hnkl ya raba bakinsa da nata, lamo ta kwanta a jikinsa tana mai da numfashi. Bayanta ya hau shafawa a hnkl "ban san meyake saki acting strange ba sweetheart but ki sani I'll never let you go, I cherish you, so stop worrying yourself okay? And about me kkeson fad'a min shknan banason ji tunda anytime kke san fad'a min sekinyi kuka" Kanta ta d'ago "Fudail but..." Hannu yasa ya rufa mata baki "no any *but* okay? Tashi muje muyi wanka" ya ce.

          "Wanka kuma hun? Saidai kai nikam ai nayi wanka just now" Mik'ewa yayi ya soma janta suna hawa kan stairs tana "nifa baran sake yin wanka ba bakaga kwalyan danayi maka bane?" Yace "nagani ai lipstick naki ya goge sabo nakeso" daidai nan suka isa d'akinsu ya d'au towel nata ya wurga mata sannan yafara cire kayansa. Tace, "toh ai kai ka goge min dakayi..." Sekuma tayi shiru. Ido d'aya ya kashe mata (wink) take jikinta ya mutu ba yadda ta iya da Fudail nata haka sukayi wankan*** bayan sunfito suka zab'a ma junansu kaya suka sa, Saaly ta sake cancare masa wata sabuwar kwalya yana zaune kan gado yana aiki a laptop ta k'araso kusa dashi kallo ya k'are mata sannan yace "woww!! Kinfi kyau ynxu sweery"

          Saaly ta turo pouted lips nata sannan ta kwanta a jikinsa tace, "ba wani kaide kawai ka fad'a ne if not na daxu yafi kyau." Matsota yasakeyi a jikinsa k'amshin turarensa na dukan hancinta yace, "duka sunyi kyau." Murmushi ta masa sannan ta dawo da kallonta kan laptop nasan "me kakeyi haka honey? Nifa na d'au inka dawo daga office bawani aiki kuma a gda ni gaskia ban yarda ba. I want to be with you more"

            "Awwn! sweery yanzu zan gama kinji? Don't worry. Ehemm daddy yace in sake tambayan ki you really don't want to go back to sch?"  "Eh ni banaso I'll miss you alot, sch zena shiga tsakani na dakai so banaso." Begama abinda yake yi a laptop d'inba ya kashe dan yadda yaji dad'in mgn da Saaly tayi nan suka hau wasanni da juna a yayinda na bugo legediz benz d'ina na bar musu d'akin.


 
beeenovels.mywapblog.com

No comments: