Wednesday, 17 May 2017
KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
written by miemiebee
5⃣5⃣
Already daddy ya turo musu driver nan ya d'aukesu tare da sa musu kayakinsu a bayan mota. Saaly na kishingid'e a jikin Fudail nata. Ahaka har suka iso gda, bayan driver ya cicciro musu kayakinsu ya mik'a musu basket na abincin da Ikleema ta tanadar musu. Watsa ruwa sukayi a tare sannan suka sa kayan bacci suka biya sallolin da ake binsu sannan suka ci abinci suka kwanta***
Washegary around k'arfe 10:30AM suka tashi daga bacci sukayi wanka a tare abinsu, suna cikin shiri aka danna door bell Fudail ya sauk'a yaje ya bud'e yaga Ikleema ce da kanta da basket a hannunta. Hugging nasa tayi "welcome back son. Wow gaskia New York ya karb'e ka son kalli yadda skin naka ke glowing." Murmushi ya mata tare da karb'an basket d'in "kai mom banda zolaya mana, bismillah kishigo" nan tashigo ta zauna a parlour a yayinda ya ajiye abincin kan dining. "Son ina amaryar tamu ne? Kode bata tashi ba?" Ta tambaya tana mai masa murmushi. "Nop ta tashi tana sa kaya" ne ya amsa ta. Tace, "aww toh."
TV ya kunna mata "ina zuwa" tare da haurawa sama. Binsa tayi da kallo. Yana shiga d'akinsu Saaly har tagama shiri cikin wata jar atamfa super exclusive wacce tasha d'inki me kyan gaske dagani cikin kayan hana gorinta ne. "Honey wayazo?" ta tambayesa ganin tun shigowarsa beyi mgn ba banda kallonta dayake. Gabansa ta k'ariso tare da shafo sajensa "honey kallon beyi yawa ba?" Nanne yadawo hankalinsa yace, "kinyiiii kyau!" Light kiss tabasa a baki "thank you hun! So wayazo?" Hannunta ya lalimo ya rik'e "mom ce tazo takawo mana breakfast."
Zuciyarta kawai taji ya buga. "Ita da kanta?" Ta tambaya. "Eh" ya amsata "muje mu karya ko?" Kai ta giad'a masa hannunta rike cikin nasa suka sauk'o k'asa. Tundaga kan stairs Ikleema ke hararan hannunsu, a zuciyarta tana fad'in "shgya shafa min d'a ki moresa kamin na tona miki asiri." Murmushin dole ta k'irk'iro lokacin da su Saaly suka sauk'o daga kan stairs d'in suka zauna kan 2 seater kusa kusa da juna da hannunta cikin nasa yana murzawa softly. "Ina kwana mummy" ta fad'a cikin siririyar murya Ikleema dake kallon kayan jikin Saaly tasan super ce kuma exclusive saidai bata sa mata wannan zani cikin kayan laife ba, she's sure, kode kayan hana gori d'iyar nan ta had'o?"
Murmushin take ta amsa da "lafya Saalihah, kema naga kin k'ara fresh gaskia wannan New York ya karb'e ku." Murmushi duka Saaly da Fudail sukeyi sannan yace, "muje mu karya ko mummy?" Tace, "a'a ainikam na riga na karya kude kuje" ba gardama suka tashi suka nufa dining area ikleema de se k'are ma zanin jikin Saalihah kallo take ganin sun had'a ido kusan sau 2 da Fudail yasa ta dawo da kallonta kan TV'n badan ta so ba. Suna k'are cin abincin Saaly ta tattara plates d'in takai kitchen da niyan wankewa se in Ikleema tazo tafiya ta tafi da abinta. Har tafara wankewa Fudail ya shigo kitchen d'in "sweery me kkeyi?" Tace, "washing dishes hun, se mummy ta tafi da abinta kar mu rik'e mata kwanuka" "Ohh haba stop it, banasan kinayin wani aiki bar wanke wanken."
Saaly ta bud'e baki zatayi mgn knan Fudail ya aza yatsansa kan lips nata "not a word" nan ya wanke mata hannu suka fito suka samu Ikleema zaune kan kujera tana kallo suma sukayi joining nata. Fudail yace, "mom ai you're not in need of flasks nakin ko?" Ikleema tace, "lfya? Ka tambaya" Yace, "na hana Saaly wankewa ne sbd bana san ganinta tana aiki in aka samu me aiki seta wanke akai miki." Ikleema tace a ranta "lallai Fudail kana sakalta wannan pand'ararriyar matar taka dan iskanci wai ko wanke wanke baratayi ba? Ko
dashike banga laifinka ba kallon 'yar masu naira kake mata not knowing 'yar talaka ce wanda tayi girman wahala. Enjoy yourself while it last Saalihah!"
Fudail ne yadawo da ita daga tunanin data tsinci kanta ciki yace, "kinyi shru mom" murmushin dole ta k'irk'iro "ahhh ai kayi gaskia bekamata mubar amaryarmu da wanke wanke ba, zan nema muku me aiki ta area'n mu bara a rasa ba." Fudail yace. "yawwa plz do." Hira sukeyi jifa jifa banda Saalihah data k'unsa baki tana wasa da hanun Fudail nata. Can Ikleema tace zata tafi suka mata rakiya.
beeenovels.mywapblog.com
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment