Page 29 is missing sorry!
written by miemiebee👄
3⃣0⃣
Tace da kanta "ikon Allah! Ynzu dama haka umma take da? No wonder ko time da na gaya mata abinda nayi nasamu kud'in da muka min shopping zuwa makaranta dashy bata damu tamin masifa ba. Ashe halinta na d'auko, mune like mother like daughter d'in, har gomma nima ban tab'a zina ba kuma baran tab'a yi ba in shaa Allahu. Shine wannan malama khadeejan tabi ta dameni da inbar abinda nakeyi, lalle kuwa ai yau ma nafara sabon sana'a tunda ga umma da har zina ta tab'a yi kuma Allah ya shiryar da ita bale ni ai kawai cin kud'in 'yan banza nake nima nasan at last in na auri Fudail zanbar yin abinda nikeyi in shiryu", ahaka tayi bacci.
Washegary! Kiran Fudail ne ya tada ta daga bacci kan "daddy ya yarda shima kan ayi DNA test d'in amman da kyar nasamu yayi convincing nasa cux shi kwata kwata so yake a rufe chapter na dake" Saalihah tace "ai ure not going to allow him ko? Fudail kasan wlh ina sonka, I can do evrythng to have you", yace "karki damu", a damop laboratory duk suka amince kan zasu had'u breakfast Saalihah taje ta siyo musu tinda tayi motar kanta yanzu tabawa kowa illa baaba haka suka gama ci ta d'au abba suka fice already su daddy da Fudail suna jiransu. Gaishe da daddy tayi cikin ladabi da biyayya shima fara'ar dole ya mata nan abba, daddy da Saalihah suka finciko gashin kansu aka fara yin processes na test d'in, zuwa anjima results will be ready. Bayan da suka fito Saalihah da Fudail sukayi gaba abba ya dawo da kallonsa kan alhj Ahmad yace "amman inhar Saalihah ba 'yata bace baran tab'a yafe maka ba alhj, haba! Da girmanka da k'imanka seka aikata zina?" Alhj Ahmad yace "haba abban Saalihah ya kake mgn kamar bakasan halin matarka wlh tlh kaji rantsuwa ba kaffara ni ban san time da abu yashiga tsakani na da Hajara ba..." nan ya kwashe labarin komi yabawa abba, sanda ya zubar da hawaye dan koda wasa be tab'a kawo wa a mind nasa Hajara zata iya aikata abu haka ba.
Suna isa gda abba yasa Saalihah ta kira masa umma, har k'asa ta durk'ushe tun kafin yasoma mata mgn take kuka gyaran murya yayi yace "ni ba kuka na kiraki kimun ba, kisani Hajara kin cuceni kin ci amanata a rayuwa, ace yadda nasoki tsakani da Allah da mind d'aya amman seki sak'a min da haka? Na farko kka min k'arya kan ke marainiyace na biyu kka shigo min da cikin wani gda..." Katsesa tayi "wlh malam Saalihah 'yarka ce ban shigo gdan nan da cikin alhj Ahmad ba, dan Allah kayi hkr nasan a da ban kasance mutumiyar arziki ba duk abinda kake zargi na dashy a ynxu kokuma abinda baaba ta gaya maka ba k'arya aciki wlh naso gaya maka asalin labarina amman gudun karka rabu dani ne yasa na fasa na maka k'arya kawai dan ina sonka kuma bana k'aunar rabuwa ta dakai, wlh na shiryu ynzu nayi tuba tsaftacacciya, pls kayi hkr mijina ka yafemin karka sauwak'emin pls..." ta k'are mgn cikin wata matsanancin kuka. Abba dashy ma keji kamar yayi kuka yace "naji Hajara a da nayi niyan sauwak'e miki ki tattara kayakin ki tas kibar min gda duk da yadda nakesonki naji baran iya yafemiki ba amman sbd bansan ina zakije ba in kka bar nan karki koma rayuwarki ta da, dakuma albarkacin Saalihah da Sa'ad kad'ai zan bari ki cigaba da zama a gdan nan amman kisani daga yau baramu sake had'a kwanciya dake ba kayakin ki nikeson ki tattara ki kai d'akin baaba ko Sa'ad kuna kwana tare kokuma site na Saalihah".
Kuka sosai umma keyi tana had'a abba da Allah amman ina ya riga yayi making up mind nasa, duk yadda take ta rok'arsa besa yayi changing mind nasa ba, gdan ma gabadai yafita ya bar mata haka tana kuka ta na tattara kayakinta taje tasamu auta amalala. Baaba kuwa se habaici takeyi tana zaginta duk sanda taga Saalihah setayi shiru sbd tasan ba k'aramin aikin Saalihah bane ynxu ta tsigaleta tamata tatas!
beeenovels.mywapblog.com
3 comments:
Godia muke sis, Allah ya kara basira.
Sis pls few of us will luv to b in ur grp pls if iys nt fully occupied pls send a grp invite link enx so dayawa.
pls miemie we are waiting d silent is too much
Post a Comment