Thursday, 13 April 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


      written by miemie👄
                  2⃣8⃣



           Lafiyayyar mari abban Hajara ya wanke ta da "nace waya miki ciki?" Cikin kuka tace "wlh abba ahmad ne yamin, gashi nan ku tambayesa", nan fa kakanka ya dawo da kalonsa kaina yana jiran amsata shirun danayi yasa ya tambayeni, "wai haka ahmad? Kaikama Hajara ciki?" Tuni na rasa amsar da zan basa courage nayi gathering sannan nace "Abba dan Allah kayi hkr, tabbas cikin dake jikin Hajara nawa ne amman wlh tlh bada san rai na na mata cikin ba hasali banma san yaushe abin yafaru ba". Tsawa ya daka min "what are u saying?" Nan nashiga b'ari nace "abba dan Allah ka yafemun wlh nima kaina bansan ya hakan ta faru ba, believe me wlh..." Ban kare maganar ba kakanka ya wanke ni da zafaffun mari lafiyayyu guda biyu "tarbiyyan dana baka knan ahmad? Amman wlh kabani kunya! Ciki! Ciki! Kama 'yar mutane a dalilin meh? Kaida nakusa maka aure sekaje kama wata ciki?" Masifa sosai kakanka ya soma min ana cikin haka wata baaba ta ta iso gun danko tun ina k'arami take yaba wa hankl na tana jin abinda ake zargi nada ta qaryata dan tasan de da hnkl na baran aikata abinda ake zargina dashy ba nan fa tata had'a abba da Allah daya bani cahnce nayi explaining kaina da kyar sannan ya yarda aka bani chance kan nayi explaining abinda yafaru a ranan.
           Kasancewar kullum ina yawo da wasikar da Hajara tabar min nan na ciro na miqa musu kowa ya karanta ciki harda abban Hajara tun ban fara basu labarin ba duk suka yarda dani suka kuma bani gaskia, haka na labarta musu komi tatas! tsinannen duka abban Hajara ya mata har se sanda baaba da kakanka suka shiga suka karb'eta agaban mu ya tsine mata albarka yakuma ce duk sanda ta dawo masa gda seya kasheta haka abin tausayi ta fice ba tare da munsan ina ta dosa ba. Dukda k'azafi da abinda Hajara tamin still naji ina sonta.
          Tun daga ranan bamu sake jin news kan Hajara ba, ba wanda yasan ina tashiga. Iklima kuwa koda dataji abinda na aikata bata nuna damuwa ba sbd tasan ba a hnkl na nayi ba tadage still tana son ta aureni haka aka mana aure amman abba yace baramu iya zama a yola ba sbd kusan 'yan gari kap sunsan abinda na aikata mu canza gari kawai badan inaso ba na yanke hukunci kan mu dawi Bauchi mu fara new life inda bawanda yasanmu a can. Haka mukayi parking  muka dawo Iklima na kula da both of us sosai matsalar d'aya ne sam kak'i ka yarda da ita as ur mother, kak'i bata chance tayi proving kanta as ur mother kai kullum cikin tambayar Hajara kake. A hnkl na fara mancewa da Hajara".
         Daddy na kaiwa nan ya numfasa sosai sannan ya ce "kaji abinda yafaru knan son kasani daddy'nka ba mutumin banza bane Hajara ce silar komi!" Fudail da hawaye ke ambaliya a fuskarsa yaji ya tsani Saalihah atake badan komi ba kuma dan abinda ummanta tama daddy'nsa duda yasan Saalihah has nothing to do with what happened years back. Jin Fudail be furta komi ba yasa daddy riko hannunsa tare da fad'in "baka ce komi ba son". Murmushin dole Fudail ya kirkiro "I should have known father tun randa na fara sa Saalihah a ido na tamin kama da wanda nasani nd naji kamar na jima da saninta ashe father d'aya muke sharing. Forgive me father for being rude to you..." Rungumosa daddy yayi yana fad'in "u dont have to be sorry son, I should be ni ne silar rabuwanka da macen da kakeson aura da ban shigo da Hajara cikin rayuwata ba da duk haka be faru ba, kuma da na san bayan da abbanta ya korota daga Yola nan Bauchi ta taho wlh da ban zo nan ba nima kaga da baku had'u da Saalihah ba. Thank you for understnding ur fahther. Na maka alk'awarin nida kaina zan nemo maka matar da zaka aura son"****
           Umma kuwa ba yadda batayi da abba ba sam yak'i mata mgn balle tamasa explaining abubuwa, d'akin ya bar mata ma kwata kwata yaje yasamu baaba ya kwanta a kasa dan kwata kwata besan me zema Hajara ba. Kwana zaune umma tayi ranan tana kuka itama Saalihah haka ne takasa bacci a daren ranan. Washegary around k'arfe 11:30AM bayan abba ya fita kasuwa umma na zaune a tsakar gda ta wula duniyar tunani, baaba kuwa se habaici take tayi, koya akayi Iklima ta san gdansu Saalihah oho se Allah sega tanan kamar aljana cikin gdan. Umma na ganinta ta zabura, baki na rawa tace "ik...iklima? Iklima kece?" Kai mummy ta giada mata tare da karisowa gabanta mari me rai da lfya ta tsinke umma dashy rik'e gun tayi kawai hawaye na bin kuncinta dan takasa rama marin.
       Iklima tace "karuwar banza karuwar wofi ashe baki mutu ba kina raye, bayan duk irin sharrin da kka ma alhj be isheki ba kka turo shegyar 'yarki data zo ta yi ruining life na Fudail ko? To wlh kisani Allah ya fiki dake da 'yarki haka zaku k'are, abin maza zaku k'are..." haka tata cin mutuncin umma a gdanta inbanda kuka ba abinda takeyi baaba kuwa kujera ta jawo ta zauna tana kallon show. Can Saalihah ta faso da motarta tun daga bakin kofa takejin hayaniya da sauri ta shigo taga wata mata nata cin mutuncin ummanta a fusace ta nufo gabar matar "ke jakar ina ce? Kin tab'a ganin inda akazo har cikin gdan mutum ana cin mutucinsa? Kekuma baaba Allah wadar din ki, kin zauna kina kallon yadda wannan jakar take zagin umma baraki shiga mata ba?" Nan ne iklima tace "well well well ko ba a gayamun ba nasan kece shgyar Saalihah ko? Nd wace jaka anan?" Saalihah tace "eh nice Saalihah 'yar wanda kke cima mutunci, sorry nace miki jaka sbd shi kad'ai yazo min baki amman kisani kinfi jaka jakanci ko dabba seya baki gu..!


      beeenovels.mywapblog.com

No comments: