written by miemiebee👄
3⃣1⃣
Bayan Saaly ta idda la'asar tafita amso result d'in can ita da Fudail suka had'u se addu'a take Allah sa yayi turning out yadda takeso harda alkwarin yin azumin bakance guda biyu. Cikin ikon Allah kuwa kamar yadda umma tace 'yar abbanta ce ita haka result dinma ya nuna bloodtype nasu d'aya da abba wani hamdala tayi tare da hugging Fudail duk sunji dad'i saidai tafisa ma jin dad'in nan sukayi photocopying kan shima yakai wa daddy d'aya, ahaka suka rabu. Sanda ta siyo musu kayan motsa baki sannan takoma gda ciki harda champagne wai na small party tunda ynxu zata iya auran Fudail nata, ba karamin dad'i abba yaji ba dan in akwai wanda yakeso a duniya befi Saalihah ba simply cuz tana da sunan marigayiya mahaifiyarsa, haka sukaci suka sha!
Baaba ma taji dad'i kam kodan ynxu za'a na d'an d'aga mata k'afa tunda ita baabar tace d'an breakfast na take away d'innan itama ana siya da ita!
Kusan to 6:00PM Saalihah na kwance bisa kan tapkareren gadon d'akinta da wayarta maqale a kunnenta tana hira da saurayinta baaba tashigo ta tsaya a bakin kofar tana sallama, Saaly naji ta mata banza sanda tayi kusan sau 4 sannan tayi holding call d'in "meh? Meh? Meh xan miki? Inba wai na manta ba ban hana ki shigo min site ba? Karkiga dan kin dawo baaba ta ki d'au d way I look at you will change, No no no bakida mutunci a idona tunda ranan agabanki wannan pand'ararriyar uwar Fudail tazo tana zagin min umma kika zauna kamar buhun dankali kina kallon yadda ake ci mata mutunci". Ita baaba akoi kwad'ayi da san kud'i akan abubuwa guda biyun nan xata iya yin komi. "Haba! Saalihah uwata dan Allah kiyi hkr ynxu fa abubuwa zasu canza a gdan nan dama can baya abinda yasa bana sanki sbd na d'au kedin ba jini na bane amman ynxu da aka gano bakin zaren ai se mu aje fad'a a gefe mu soma shiri ko mamana?" "Hmmmm lol lalle kam nasan meya kawoki", tasowa tayi daga kan gadon ta nufa inda take hanging bags nata ta ciro wata purse ta irga dubu biyu "ungo..." Har baaba ta kusa taka rug (carpet) dake d'akin Saaly tace "wait! Wait! Dakata zan kawo miki karki b'ata min wannan rug almost 200k na siyesa", baaba harda "yi hkr mamana" hannu na kyarma ta amsa "nagode mamana dama yunusa ne yace in miki saalama kasancewar na dawo daga mak'ota na gansa a waje".
Tuni Saalihah ta fusata "yunusa? Me wancen me zuciyan karen yazo yi anan? Ko be san ni ba class dinsa bace taya ina hawa mota yana fama da 2nd hand rakwababbiyar bajad nasa ze na zuwa wajena, ke mesa baki gaya masa inada tsayayye ba ynxu? Bani kud'i ne". Baaba tace "haba Saalihah fa na gayamasa amman yak'i ji". Tsuka taja sannan ta d'au wata brazillian hair nata wanda inbawai an fad'i bane za'a zata gashinta ne sbd 350k ta sayesa. Ko gyale bata yafa ba tafito da manya manyan wayoyinta a hannu ta samesa jin gine a jikin bajad nasa yana ganinta ya nufo bakin kofar se washe baki yake sekace an mai albishir da gdan aljanna. Kallo me rai da lafia ta watsa masa tuni ya had'iye gaisuwar sa yace "Saalihah yau ko mayafi baki rufe kanki dashy ba kinsan ko ba kyau mace tana barin kanta a bud'e kuma...." Katse sa tayi tare da d'aga mai hannu "hold it malam! In wa'azi kazoyi I keep on telling ga masallacin malam liman can sekaje ga d'au mic katayi yadda duk 'yan zango zasu jika amman ni banida time d'in sauraran so called wa'azinka da uban waye yace ma kazo in baraka iya juran gani na ba dankwali aka ba? Jimin mutum fa... Yunusa kake ko me? Mesa bakada zuciya ne? Shin kare ya tab'a lashe zuciyarka ne? tana nuni da motarta tace "kalli can! Mota tace kaikuma fa?" Ta dawo da kallonta kan rakwababbiyar bajad na yunusa harda kyal kyalewa da dariya "kalli fa? For goodness sake yunusa stay the hell out of my life, u may be goodlooking amman saurayina yafika kyau still, kyan ka bareyi amfani a nan ba kacire kwadayi ka nemi daidanka"
Yunusa dayayi mutuwan tsaye dakyar ya iya fad'in "haba Saalihah mesa kke ma wanda yakesonki walakanci ne? Tun kafin ki waye kifara hawa mota nake sonki shiko wannan saurayin naki sanda kka waye yace yana sonki..." "Toh ai it still doesnt matter to me kalli motar nan da kyau xaka iya sayamin erinsa? No! Kalli wayoyin nan, zaka iya siya min irinsu? The answer is no then mesa zan soka? Kasani money can buy everythng, u might be hansome amman kyan ka bare yi amfani a nan ba nida masu naira nake harka sbda haka ka buga bajad naka ka barmin kofan gda kafin in maka abinda baka tsammani".
Idansa dam yacike da kolla a hnkl yake mgr "haka kkace Saalihah? Amman kisani not everythng can be bought by money shi arziki nufin Allah ne a dare d'aya yakan azirta bawansa haka zalika ya talautar dashi. Nide na soki Saalihah kuma zan cigaba da sonki".
Tsuka taja "kai kaji wajen dama ku maza haka kuke so heartless, koda mutuwa zakayi I'll never nide na gaya maka kar ka sake tako gajiyayyun kafafunka dasunan kazo zance waje na, banza talaka da kai bana sonka bana son talaka! Tana kaiwa nan ta fice.
beeenovels.mywapblog.com
No comments:
Post a Comment