Saturday, 8 April 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


      written by miemiebee
                  0⃣8⃣


         Ko cikakken 3mins da zuwan Saalihah dakin ba'ayi ba wasu 'yan mata guda biyu 'yan farare farare dasu haka kyawawa, wanda barasu gaza 19 years ba, kallo daya za'a musu asan 'yan duniya ne dan ko daga shirin dake jikinsu, matsatssen fitted gown ne a jikinsu ko gyale basu yafa ba daga daurin dake kansu seshi, wacce tafi kyau din tana tauna chewing gum irin yadda 'yan bariki keyi dinnan  tace "phaary ashede dakin mu daya?" Phaary ta ciro dark sunglasses dake fuskarta tace "eh fa bint" gado kusa da juna suka kama suka ajiye jakukkunansu, Saalihah na kallonsu dan ba karya sun burgeta ita erin rayuwar da takeso knan! Daga bisani bint tace "emmata kema a nan dakin kke?" Saalihah tace "dani kke?" Bint tace of course, da mu nawa ne a dakin?" Saalihah tace "eh a nan dakin nake, any problem?" phaary tace "wow erinsu nikeson kawance da wollah frm all seeing yarinyan nan bata taking shit," bint tace "nima de abinda nagani knan nan" phaary ta kariso kan gadon Saalihah tace "am farida abdullahi AKA phaary, dis is my frnd" tana nuni da bint, "sunanta binta el mu'azu AKA bint." Saalihah tace nice names, bint tace "thanks kefa wats ur name?" Saalihah tace "Saalihah Ibrahim aka saaly baby" (ni miemie nace shgya Saalihah wato kema saaly baby.) Atare bint da phaary suka ce "wow nice nickname," bint dake tauna chewing gum tana qaqas! Dashy  tace "can we be frnds?" Kafin Saalihah tayi mgn taji hannun phaary a kafadarta "say yes pls" Saalihah tace "yes" tana me musu murmushi. Bint tace "ynxu de mu shirya kayakinmu tukuna ko?" Phaary tace "yes dear" wayar bint ce ta soma qara nan ta ciro ta daga cikin side bag datake rataye dashy wata samsung galaxy S7 edge ce tasha porche dankaren nan sekace ba waya ba, azuci Saalihah tace "ai ynxu makarantar nan ta soma dadi kalli waya!"  "Hellur baby" tafadi "eh ynxu isan mu sch, wallahi wata frnd itace ta haihu wanda nagayamaka an mata aure since muna ss2 dinnan? To ita ta haihu fa," on the other side baby (lol) yace "ohh ayya nawa kkeso knan, kiyi mata siyayyan kayan baby"... Bint ta daga hannu suka tafa da phaary, sannan tace "50k ma will be enough," baby yace "haba meh 50k, ai ynxu 50k yazamo kamar 5k cikin minti daya zaki kashe balle ma haihuwa fa kkace? Zan turo miki 100k," bint ta kuma kashe murya "kai thats why I love you baby, Allah bar min kai" sannan ta katse wayar. Wata tafin suka kuma yi phaary tace "shegge babeh aikinki na kyau, nima daxu sugar alhj na yace ze turo min 100k wai nayi siyayyar makaranta dashy." Saalihah ji take kamar mafarki take "100k? Cab! Lallai wannan kawaye su ake kira da long awaited frnds" bint ce ta katse mata tunani "Saaly naga kallon da kke mana yayi yawa kar wannan sexy eyes nakin su fadi a kasa fa," Saalihah ta kuma zaro idanunta waje, phaary tace "ya haka? Ai na dau 'yar gari ce ke ya daga jin ance sexy eyes kin wani zaro ido sekace iskanci tace kuyi tare." Saalihah tace azuci "yau naga wanda suka kureni a iskanci, kai amman fa yakamata in daina behaving kamar wata 'yar qauye in bahaka ba zasu raina ni dan wannan phaary da bint din 'yan rainin sense ne." Nan tabar mgn zuci tace "'yar gari? Zancen kkeso," nan ta basu lbrn irin danyen aikin datayi ma wancan alhj'n dakuma Ibraheem dan gdan chariman. Phaary tace "shgya Saaly kina wuta muna binki da petrol, ashede kedin 'yar babbar gari ce," suka tafa da bint "ai haka akeso, kema ynxu ya kamata mu hadaki da alhazan mu kema kisamu na kanki black beauty dake kuwa ba karamin kasuwa zakiyi ba, ban mu kashe," Saalihah ta dago hannu sukayi high 5 da ita.
          Suna cikin shirya kayakinsu Saalihah de nata ido ne dan wasu laces masu tsadan da take gani suna cirewa daga akwatunansu haka atamfofi ma ciki harda sengalis hadaddu na 'yan gayu ga shoes nd bag kusan dozen kowani colour akoi...wata budurwa ce tashigo dakin tare dayin sallama da kyar suka amsa mata tace "sannunku dan Allah nanne room 15" Saalihah ta amsa da "eh nanne" su bint kam sun kasa mgn dan har ynxu mamaki wannan budurwa ta basu ga doguwar hijabi har kasa ga nikaf ga gloves da socks acikin wannan zafi? Lalls kam dagaske take. Empty bed dake kusa dana Saalihah ta ajiye wasu trolley's nata guda biyu sannan ta yaye niqaf natan dukansu sanda suka razana dan erin kyawun halittan wannan budurwa komi a fuakarta kamar ita ta zana aka sa mata gata nan fara a hankali ta cire socks da gloves din saidai har ynxu bata cire hijabin ba. Cikin wata murya me dadin gaske tace dasu "suna na khadeeja Muhammad I hope zamuyi zaman lfya  mukuma karu da juna, Allah bamu iko," Saalihah ta amsa da "ameen Khadeeja, ni suna na Saalihah wannan binta dayan kuma farida," khadeeja tace "toh masha Allah" phaary tace "malama khadeeja zanfiso in da zaki na kirana da phaary, wannan 'yar uwar tawa kuma bint wancan kuma Saaly, koya kkace?" Khadeeja tayi murmushi "ai ba malama bace ni, ina kan neman ilimi nima duda nayi sauqa sau 3 da fassara da tafsir, na kuma sauqe hadisai da sauran littatafai da dama amman ai neman ilimi bai qarewa, sbd haka ba sekince min malama ba." Bint dake dariya tace "aww banda Qur'ani dama ana sauke hadisai ma nawaoo sannu da kokari sister, a dadinmu mun samu malama a daki ko ba haka b a qawas?" Kai phaary ta gyada mata "sosai ma kuwa"

No comments: